Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 52

Sponsored Links

*PAGE* 5⃣2⃣

Koda suka fito daga toilet d’in da mamaki yarima yaga zarah bata d’akin ammah ko’ina angyarsa fes room d’in sai k’amshi yake, murmushi yayi dan ya san ko ba’a fad’aba toh aikin zarah ne.

Ita kanta sumayya saida tayi mamaki dan bata ta6a tunanin haka daga zarah ba.
Ta6e baki tayi cikin ranta tace gulmammiyar kawai duk dai abinda zakiyi bazanta6a fasa k’udirinaba akanki, muryar yarima taji ya ce muje kizauna.

Haka yarik’ota sukaje bakin gado yazaunar da ita, marairaicewa tayi tace please kashiryani.

Wani irin kallo yayi mata yace shiryawarma bazakiyi da kankiba?

K’wallah ce tacika mata ido tace kaga fa banda lafiya, Banza yarima yaimata nan yamik’e yaje yabud’e wardrobe d’inta yad’auko mata kaya, saida yashafa mata lotion sannan yataimaka mata tasaka kayan.

Komawa tayi takwanta yarima kallonta yayi yace bari intafi hospital

Sumayya cikin muryar tausayi tace yau bazaka hak’uraba?, kaga fa banda lafiya.

Wani irin kallo yarima yaimata sannan yace zan turo miki kuyanginki in akwai abinda kikeso sai sutaimaka miki,, yana fad’in haka yajuya yafita yabar d’akin.

Sumayya ba haka tasoba cikin ranta tace ammah da wacchan gajarce ai da ka zauna,,nan tak’ara jin wata irin tsanar zarah, knocking d’in k’ofa da akayine yasa tabada izinin ashigo.

Kuyanginta ne suka shigo nan suka zube suna kwasan gaisuwa wajen shugabartasu tare da yi mata ya jiki.

Sumayya fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa musu sannan tace sufita subata waje tana son hutawa, cikin sauri har suna rige-rige suka fita sukabar d’akin.

Nan Sumayya tagyara kwanciyarta dan Wani irin bacci takeji, ahaka bacci yai awon gaba da ita.

 

 

Bayan sallar la’asar zarah fitowa tayi tanufi part d’in Sumayya dan tadubata da jiki.

Lokacin Sumayya tana Kwance suna waya da zinat dan tunda tafarka baccin taji zazza6in ya safka dan har wanka tasamu tayi taci abinci sannan tasha drugs d’in da yarima ya aje mata.

knocking zarah tayi ahankali, Sumayya jin ana knocking yasa tabada izinin shigowa dan tayi tunanin ko kuyangintane.

Ahankali zarah taturo k’ofar tashigo tare da yin sallama,,, ganinta yasa fara’ar da take fuskar Sumayya tagushe ahankali tace baby ina zuwa bata jira jin abinda zinat zataceba takashe wayan tana kallon zarah a wulak’ance, cikin d’aga murya tace me yakawoki part d’ina?.

Zarah murmushi tayi tace Aunty Sumayya ya jikin naki?

Harara tawurga mata tace wannan ba damuwarki bane kar kik’ara shiga sabgata ke ni ko ganinki banason yi saboda bana sonki na tsaneki,

Zarah da mamaki take kallonta ahankali tace Sumayya har ga Allah ni da zuciya d’aya nake zaune da ke kuma inaso kisani ni ban iya irin wannan zamanba dan ita rayuwa duka nawa take.

Tsawa Sumayya tayi mata tace ke kifita idona duk wani dad’in bakinki bazaiyi tasiriba akaina kuma wannan cikin da kike tak’ama da shi ke kina jin dad’i zaki haifarma yarima magaji toh indai ina numfashi bazaki ta6a haihuwarsaba.

zarah bataji haushin kalaman da Sumayya tafad’aba dan idan da sabo toh tasaba jin irinsu, Ta6e baki tayi tace Sumayya kenan ciki Allah ne yabani kuma shikad’ai zai iya ikonsa akan abunsa ni na yarda da k’addara duk abinda yasameni nasan *DAGA ALLAH NE* bazan ta6a jayayya da ikon Allah ba dan shi musulmi anaso yadinga yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau, dan haka *K’ADDARA CE* kawai zatasa cikin nan yabar jikina.

Sumayya har ta bud’e baki zatayi magana sai ga yarima ya bud’e k’ofa, cikin sauri tafashe da kukan k’arya tace yanzu saboda Allah zarah ni zakiyi ma gorin haihuwa?

Zarah mamakine yacikata cikin sauri takalli yarima da yake gefe wata irin harara yawurga mata.

Sumayya dasauri tataso tazo tafad’a jikinsa tana kuka, cikin sheshek’ar kuka tace yarima kana jinta tana min gorin ciki ni dan Allah bai baniba.

Yarima tausayinta yaji nan yarungumeta jikinsa,, zarah mutuwar tsaye tayi dan bata ta6a tunanin makircin Sumayya ya kai hakaba,,, k’wallah ce tacika mata ido muryarta tana rawa tace please yarima kafahimceni wlh ba haka bane.

Wani kallo da yarima yaimata zarah saida takusan sakin futsari cikin 6acin rai yace kin kyauta gorin ciki kikayi mata, shin ke wayonki ko dubararki suka baki?,

Zarah matsowa tayi tace yarima kar kayarda da maganarta wlh duk abinda tafad’a ba haka bane.

Hanya yarima yanuna mata yace kifita tun kan ranki ya6aci.

Zarah kallon Sumayya tayi da take manne a k’irjin yarima tana mata gwalo, juyawa tayi tafita tabar d’akin cikin 6acin rai tare da nadamar zuwanta.

Sumayya tana ganin zarah ta fita nan tasake fashewa da wani sabon kukan, cikin kuka tace yarima kana jin abinda tacemin ko, daman mutum yana ba kansa haihuwa?

‘Dagota yayi daga jikinsa cike da tausayinta yace Sumayya kidaina cewa haka kiyi hak’uri ita haihuwa ubangiji shi yake bayar da ita ga wanda yaso sannan kuma shi yake hana wanda yaso, a tsawon dad’ewarmu kin ta6a gani na nuna damuwata dan baki haihuba?

Girgiza kai Sumayya tayi,
yace gud, dan haka kar kik’ara damuwa kema Allah bai mance da keba in da rabo zaki haihu.

Sumayya rungumesa tayi cikin jin dad’in maganarsa tace na gode sosai ranka yadad’e….A chan k’asan zuciyanta kuma cewa tayi koma me zakace bazan ta6a amincewa waccan jakkar tarigani haihuba dole ind’au mataki akan cikinnan nata.

Yarima janyeta yayi daga jikinsa tare da tallabo fuskarta suka k’ura ma juna ido, murmushi sumayya tasakar mai.

Yarima har ya bud’e baki zaiyi magana nan wayansa tafara ruri, ganin daddynsane yasa yasaki sumayya tare da d’an matsawa kad’an sannan yayi picking d’in wayan tare da yin sallama.

Daga chan 6angaren sultan Ahmad amsa masa yayi.

Yarima cikin girmamawa yagaishe da mahaifin nasa, nan sultan Ahmad ya amsa masa sannan yace yarima kana ina yanzu?
Ina gida daddy,,,cewar yarima.
Kazo yanzu kasameni.
Toh daddy.
Juyowa yayi yakalli sumayya da tatsaresa da ido yace ni na wuce.

Sumayya cikin rashin jin dad’i tace Toh.
Nan yarima yafita yabarta.

Sumayya tana ganin fitarsa nan tabushe da dariya cikin jin dad’i tace lallai yarima da ni kakeja ai wlh ba abinda zai hanani d’aukar k’wak’waran mataki akan wannan bagidajiyar matar taka, yanzu ko tana ina? Nasan dai ana chan ana ta kuka,,,nan ma Sumayya tayi dariyar jin dad’i sannan tawuce taje tabud’e bedside d’inta tad’auko wani pills tasha sannan tahau saman gadonta tajanyo wayarta takira zinat nan sukacigaba da wayansu.

 

Zarah bayan ta bar part d’in gimbiya Sumayya nata takoma tana shiga bedroom d’inta tamaida tarufe, saman gadonta taje tazauna tadafe kanta mamakin makircin da Sumayya tayi matane yadameta, maganganun da yarima yafad’a matane suka cigaba da yawo cikin kunnuwanta.

Ita ba komai tafi ji ba sai yadda yarima yayarda da maganar da yaji Sumayya ta fad’a , ba abinda yafi 6ata mata rai irin taga yarima yana fushi da ita.

Duk yadda taso tadanne kukan da yake cinta kasawa tayi nan tarushe da kuka,,,,haka tasha kukanta tak’oshi sannan tamik’e taje tawanke fuskarta tare da d’auro alwallah nan tazo tashimfid’a darduma tad’auko alk’ur’aninta tacigaba da karantawa dan samun sauk’in k’uncin da takeji a zuciyanta.

Tana nan zaune har aka kira sallar magrib tayi sallah.

 

 

Bayan sallar isha’i wanka taje tayi tai shirin baccinta tahaye saman gadonta takwanta.

 

Yarima kasancewar fita sukayi da su daddy basu dawo gida ba sai around 9pm, koda suka dawo part d’in sumayya yawuce dan yadubata, lokacin da yashiga kwance yatarar da ita tana waya, ganinsa yasa tayi saurin janye wayar a kunnenta tare da sakar mai murmushin rashin gaskiya.

Kallonta Yarima yayi yace dawa kike waya?
Gabantane yafad’i chan dabara tafad’o mata tace am daman ummah ce muke waya da ita ta kirani ne tayi min ya jiki.

Ta6e baki yarima yayi sannan yace ohk, ya jikin naki ina fatan dai yanzu yai sauk’i dan naga tun d’azun zazza6in yasafka?

Sumayya langwa6e kai tayi Sannan tace dasauk’i.

Yarima duba agogon da take manne a hannunsa yayi sannan yace ohk, Allah yak’ara sauk’i, kikwanta kiyi bacci.

Murmushi sumayya tasakar mashi sannan tace toh dear Allah yakaimu.

Ciki-ciki yarima yace Ameen sannan yafita yabar d’akin.

Sumayya na ganin ya fita tajanyo wayarta takanga a kunne tare da cewa baby kina jinmu da mutumin?

Zinat da ta saurari duk hirarsu dariya tayi tace ina jinki baby da wannan munafukin mijin naki ai bari inzo garin wannan cikin da yake tak’ama za’a haifa mai sai munga bayansa.

Dariya sumayya tayi tace baby ina fa jin haushi idan kina ce ma mijina munafuki.

Daga chan 6angaren ta6e baki Zinat tayi tace yoh wanene inba munafukinba ai tunda har ya amince yayi miki kishi toh na gama ganinsa da mutunci.

Murmushi sumayya tayi tace kina sa ina jin haushi in kina tunomin da waccan bagidajiyar.

Dariya zinat tayi tace ai wlh bari inshigo garin zata gane kurenta, dear yanzu dai kikwanta kiyi bacci dare keyi.

Sumayya kallon agogon da take manne a bangon d’akin tayi tace nasan dai yanzu akwai abinda zakiyi saisa kike korata.

Dariya zinat tayi tace yoh mefa zanyi.

Hmm kedai kika sani wlh nasan bakida gaskiya, yanzu dai kije kar intsaidake….sumayya na fad’in haka tayi switching off d’in wayanta tana dariya ta aje saman bedside sannan tagyara kwanciyarta tare da kashe gloves.

A 6angaren yarima koda yakoma part d’insa bayan ya yi shirin bacci kwanciyarsa yayi, zarah ce tafad’o masa a rai, wani irin haushi yaji lokacin da yatuna gorin haihuwan da tayi ma sumayya, tsaki yaja sannan yajuya yayi kwanciyarsa.

 

Tun daga ranar zarah take 6oye kanta a room d’inta dan bata yadda kwatakwata suhad’u da yarima koda abun yana damunta kawai dai daurewa take.

 

yarima ma shi kansa daurewa kawai yakeyi duk yadda zaiji yanason ganinta danne zuciyansa kawai yake koda daman shi a tunaninsa ba ita yakeson ganiba saboda babynsa da yake manne a cikintane kawai yasa yake jin kewarta.

 

Sumayya ko gaba takaita dan tunda tafahimci yarima da zarah basu jituwa nan wani irin farin ciki yadabaibayeta dan hakane ma tatsiri k’ara shige ma yarima dan ma baya bata had’in kai sosai.

 

*BAYAN SATI ‘DAYA*

Yarima ne zaune d’akinsa yana cike wasu files, wayansa yad’auko yakira abban sumayya bayan sun gaisa yake tambayarsa sauran files d’in, daga chan 6angaren abbah cewa yayi ai d’azun da sumayya tashigo nabata tabaka halan bata bakaga?

Murmushi yarima yayi cikin girmamawa yace abbah ina tunanin mantawa tayi bari inmata magana.

Sultan Abbas yace toh lafiya lau kome kenan sai kakirani.

Yarima yace toh abbah nagode sosai.

Bayan sun gama wayan yarima lalubo number d’in sumayya yayi yakirata ammah har tak’arashi ringing batayi picking ba, tsaki yayi yace ko ina taje ta aje wayar….mik’ewa yayi yafito yanufi part d’in sumayya a parlournta kuyanginta ne kawai cikin girmamawa suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baibi ta gaisuwar da sukeyi masaba yace sumayya fa?

‘Daya daga cikinsu ce tace ranka yadad’e tana cikin d’akinta, wucewa yarima yayi yashiga bedroom d’inta da mamakinsa yaga babu kowa motsin ruwan da yaji a toilet ne yasa yagane wanka take, waje yasamu a gefen gadonta yazauna, abinda yahangone saman bedside d’inta yasa yamik’e yanufi wajen da mamakinsa, tsaye yayi kamar wanda ruwa yaci sai chan yakai hannu yad’auko saida yarazana da yaga drugs jibgi guda, d’aya bayan d’aya yad’auka yana dubawa inda zuciyansa tashiga bugawa da k’arfi, daidai lokacin sumayya tafito daga wanka dan saurin da take kenan tazo takwashe gudun kar yarima yashigo yagani, tsaye tayi kamar wadda ruwa yaci tsoro da fargaba duk suka cikata.

Yarima juyowa yayi yalalleta da idanuwansa da suka rine suka koma launin ja saboda 6acin rai..

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

Back to top button