Ni da Patient Dina Book 2 Page 57
kerma kawai jikin areef yakeyi ganin dan uwanshi mansoor zahiri agabanshi hakan ya matukar girgizashi dakuma daga mishi hankali dan kowa yasan de mansoor ya mutu.
Magana mansoor yafara mishi da murya me matukar sanyi ya ce ” ya areef ni ne fa! kanin ka mansoor, nayi kewarku sosai , kunsan waye sanadiyar mutuwa ta kuwa ?” har wannan lokacin jikin areef be bar kerma ba bin Mansoor da kallo kawai yakeyi dan bawani gane abinda yake fada yakeyi ba kawai ganin bakinshi yayi yana motsawa amma tsaban a rude yake bayajinshi . Mansoor yasake cewa ” mommy ce fah tayi sanadiyar mutuwa ta ita ce musabbabin komai wallahi itadin muguwa ce ku kare kanku daga sharrinta” duk wannan bayanin da fatalwar Mansoor keyiwa areef baya jinshi dan hankalinshi baya jikinshi yana razane. areef ji yayi an fincikoshi qara yayi yana” Mansoor ne wallahi Mansoor ne na ganshi da ido na” girgiza shi da karfi fawwaz yayi ganin yafita a hankalinshi yana wasu sambatu dago kai areef yayi yaga fawwaz ne ya ce ” fawwaz wallahi naga Mansoor yanzun nan yana nan wajan har yanamin magana ” yana magana yana fisge jikinshi daga rikon da fawwaz ya mishi, sosai fawwaz yasake rikeshi yana tunanin kode kwakwalwarwashi ne yafara samun matsala saboda shigowarshi garden din ne ya ganshi yana tsaye shikadai yakafe waje daya da ido ga jikinshi da ya ke rawa kamar wanda aka jonawa shocking shisa yazo ya rikeshi.
dakyar ya iya jan areef har cikin falo ya zaunar dashi , duk ya rude dakyar fawwaz yashawo kanshi ya nutsu sannan ya tambayeshi ” meyafaru?” bayani yafara mishi dalla_dalla akan ganin Mansoor da yayi cikin sigan kwantar da hankali fawwaz ya ce ” areef ka kwantar da hankalinka kawai is just imagination amma katabajin wanda ya mutu yadawo ne , Mansoor is gone kadinga mishi adduah”. ” hmmmm ” kawai areef ya ce dan shi kadai yasan me yagani tabbas ganin Mansoor da yayi bawai mafarki bane kokuma gizo dagaske ya ganshi amma hankalinshi yakwanta jin kalaman fawwaz, haka fawwaz yadinga kwantar mishi da hankali har time din sallah yayi suka tafi masallaci gabatar da sallah mangrib.
Hairah tagama shigo da food flask din abincin dare da zaaci tazauna agefen auta dake faman yiwa Mama surutu wai ita ahakan labari take bayarwa tun mama na amsa mata harta fara bata amsa da “uhmmm, eh, hmmm” hairah se dariyansu takeyi ganin mama de adole take amsawa auta , dan auta in tana bawa mutum labari yayi shuru ya shareta seta fashe da kuka shisa inde tana bada labarai gudun rigimarta suke amsawa dukda wani lokacin bagane abinda take fada sukeyi ba .
Baba da ya usman ne suka dawo daga masallaci sunyi sallah isha suka zauna a falon dan cin abincin dare , gaishe da baba hairah tayi ya amsa fuskanshi asake , satan kallon ya usman tayi dake zaune yana danna waya ta ce ” ya usman barka da dawuwa?” batare da ya kalli inda take ba ya ce ” yawwa hairah barka de ” fuskanshi ba yabo ba fallasa sabanin da inde ze amsa gaisuwanta fuskanshi dauke da murmushi kuma se ya kalleta kafin ya amsa gaisuwan amma tunda wannan abin yafaru daga ranar da ya furta mata kalmar ” I won’t force you again” ya canza mata sosai he totally changed hakan baya mata dadi,
se lokacin da tace zataje bashi hakuri sekuma ta fasa . Sawa kowa abinci mama tayi tuwon cus_cus ne da miyar stew dayaji namomi aciki, suna cikin ci sukaji muryan hafiz . cire hannunta tayi acikin abincin dasukeci ita da auta ta mike da gudu taje ta rungume yayanta sannan ya tsuguna ya gaishe da kowa suka amsa da fara’a akan fuskokinsu zama yayi hairah ta gaisheshi, kallon auta yayi ya ce ” abokiyar yau ba magana ne ” cike da iyayi ta ce ” ni ai babu ruwana dakai ya hafiz dakai da ya areef no me no you” dariya duka sukayi dan sunsan abinda yasa ta fadi hakan , saboda ranar da areef da hafiz sukazo gidan ta na ce seta bisu wajan anty fanan dinta sukuma ba gida zasuyi ba , ta tayar musu da rigima aikuwa sukayi wayo suka gudu shine yau da hafiz yazo taki kulashi, kama kunne hafiz yayi ya ce ” sorry yar autanmu ” batako kalleshi ba ita adole tana fushi ta ce ” ina wuni ” kunshe dariya hafiz yayi ya ce ” lafiya lau yar auta” cikin zolaya ya usman ya ce ” hafiz kayiwa Allah karka daga mana rigimarta da wannan daren” nanma dariyar sukayi baba yamusu alama dasuyi shuru dan kuwa auta ta cika tayi bam kamar zata fashe kafin su gama dariyar tasu ta bare baki ta fashe da kuka kamar wacce akawa wani abun.
Lallashinta sukeyi amma takiyin shuru mama ce tadauki wayan wuta ta ce ” kifa kiyayeni yarinyar nan ko in miki dan banzan duka tam” mit auta tayi kamar bata falon, dama kukan ba hawaye tayi shuru taci gaba da cin abinta tana turo baki , karawa su ya usman abinci tayi dan su biyu ne shida hafiz . sun gama cin abinci hairah da auta sunkai komai kitchen suna zaune suna hira baba mikewa yayi ya ce ” tom nide na shige seda safen ku” suka mishi seda safe yashige bedroom dinshi haka ma mama ita da auta suka tafi yarage daga hairah,hafiz se ya usman.
Hafiz ganin dare yayi ne har karfe 9 yasa yamike ya ce ” ya usman bari inwuce dare nayi ! hairah seda safe ” rakashi har bakin gate sukayi inda driver ke jiranshi ya tafi , wuceta yayi zeshiga falo yasa hairah tayi saurin riko hannunshi, dakatawa yayi yajuya ya ce ” lafiya? ” narai_narai tayi da fuska tasake rike hannun gam ta ce ” ya usman dan Allah kayi hakuri natuba kayafemin ” raba hannunshi da nata yayi zesake wuceta tasha gabanshi ta tare mishi hanya , ba’ta fuska ya usman yayi ya ce ” malama kiban hanya in wuce bacci nakeji ” cika idonta yayi tab da kwalla suna kokarin zubowa ta ce ” ya usman wallahi bazan iya jure wannan baqar horon da kakemin ba ! Kasan yanda nakeji kuwa ? kasan yanda raina yake kuna kuwa ji nakeyi kamar in mutu bazan iya jurewa ba zuciyata nada rauni sosai kayi hakuri” ta karishe maganar tana sheshekar kuka hade da sunkuyawa kasa tana kuka , shikanshi dama kawai jurewa kawai yakeyi amma rashin kulata da bayayi yafi kowa shiga damuwa amma yau dole ya hakura dan baze iya jure wahalar da zuciyoyinsu ba , sa hannu yayi ya riko kafadunta yadago ta tsaye ya kalli cikin idonta cikin tsokana ya ce ” to dear yakikeso in miki ? nabarki ne kawai kisamu irin freedom din da kikeso, za ki iya auren wanda kikeso ” sake fashewa tayi da wani kukan tana ” banaso ! banaso ! banaso kadena fadamin haka ko in hadaka da mama ” dariya yayi ya ce” to shikenan kinyarda muyi aure wata daya me zuwa ?” dasauri ta gyada mishi kai alamar amincewa , murmushi yayi ya ce ” to shikenan gobe zanwa baba magana anema min aurenki ” murmushi ne ya subuce mata tafara blushing murmushi shidinma yayi ya ce” ki shirya go be zankaiku yawo keda auta ” nanma gyada mishi kai tayi kafin ya mata seda safe suka shiga ciki ko wanne ya shiga bedroom dinshi hankalinsu kwance zuciyarsu fes dauke da farin ciki.
Khairatyyy dake gefensu tana kallonsu tayi murmushi ta ce” alhamdulillah Allah nagode maka daka bani iKon sasanta wannan lamarin cikin sanyi ” tafada tana murmushi sannan tafara tunanin ayanda tahada su.
Wata rana tanata shawaginta aduniyar bil adama tazo dede anguwar pantami kawai Allah ya nuna mata hairah da ta fito a firgice ko takalmi babu a kafanta tana rike da wata tsohuwar naira ashirin (20 naira) ta tsaya abakin kofar wani karamin chemist ta ce abata paracetamol mugun kaman da sukeyi ne yaba khairaty mamaki dayasa seda tasa hannunta ta shafa nata fuskan , karban maganin hairah tayi tashiga yar karamar gidansu da ginin yafara daddarewa , bakin randar kasa taje tadibi ruwa a kofi tashige daki bin bayanta khairaty tayi domin ganin ina zataje , acikin dakin kuwa tasamu hairah zaune da wani kyakyawan yayanta da suke matsanancin kama . barewa hafiz maganin tayi tabashi hade da ruwa ya karba yasha yakwanta ta lulubeshi da tsohuwar bargo da taji jiki, wani tunani ne yafado ran khairaty yasa taje tadaura hannunta akan goshin hafiz nan take jikinshi yayi zafi yafara rawan sanyi tsorata hairah tayi nan take tafashe da kuka tafita a gidan da gudu inda tasan zata samu me gidan hafiz da yake hayan bairon dayakeyin dako tayi , aikuwa tayi saa ta sameshi a bakin kasuwar waya ta badaru , suna zaune acikin majalisa tazo tana kuka take fadamishi yayanta ba lafiya yataimaka ya kaishi asibiti, me gidan hafiz kuwa ganin idon mutane akanshi ne kowa najiran yaji mezece yasa badan, yayi niya ba yace muje gidan naku , ya tari napep suka shiga gidan aka dauki hafiz zuwa asibitin medical center zuwansu yayi dede da kawo ya usman da akayi yana aman jini , gado akabawa hafiz aka rubuta musu magani na kusan dubu bakwai me gidan yatafi da sunan siyan maganin daga nan ya gudu, har gari ya waye babu wani likitan dayazo kan hafiz da sunan dubashi hakan yasa hairah fitowa tana kuka ga tashin hankali ga yunwa , office din likita take nema , shafe duk wasu kofofi khairaty tayi yarage hairah kofa daya kawai tagani inda ya usman yake kwance kenan , tashiga dakin domin yin magana da likita anan ne ya usman yaganta dakowa dake wajan . Hakan yasanya khairaty farin ciki sosai saboda bataso ace saboda ita wani ya cutu nan take ta bace. Wannan kenan.
9:40pm hafiz suka dawo gida bayan driver yayi packing yafita yana kokarin shiga part dinsu kawai ya hango matashin saurayi sanye da fararen kaya har daukan ido sukeyi yana tsaye daga dan nesa yana kallonshi , mamakine yakama hafiz yafara tunanin dama bayansu ya fawwaz da ya areef akwai wani na miji agidan ne betaba ganinshi ba kuwa , ko ajikinshi yakarasa inda fatalwar Mansoor yake tsaye yana kallonshi, mika mishi hannu yayi dan suyi musabaha, girgiza kai fatalwar Mansoor yayi ya ce ” ni bakamar kowa bane hafiz ! nasan bakasanni ba sunana Mansoor yaron mommy kuma nima ada ni kanin su ya azaad ne ” wasu maganganu dayakeyi ne ya daurewa hafiz kai dan maganar abaibai yayisu yakasa fahimta ya ce ” ban gane me kake nufi da kai kanin su ya azaad bane ada ? to ayanzu kenan kai ba kanin su bane ? amma meyasa to? sannan ya akayi kasan sunana dan ni nasan bamu taba haduwa ba ? ” ya jero mishi tambayoyi atare , girgiza kai kawai fatalwar yayi ya ce” bazaka gane ba hafiz se anjuma kacewa kowa ina gaishesu inka shiga ciki ” yagama magana yajuya yafara tafiya , hafiz afili ya ce ” to ai hikenan” yashiga falo duk suna zaune abinsu harta ummi da Mr azaad fanan ce kawai bata falon taje dakin ummi neman dabino, zama shima yayi kusa da areef ya gaishesu ummi ta ce ” hafiz harka dawo kenan ni na daukama ai tare kuka tafi da areef ashe yana nan shi ” ya ce ” eh ummi nadawo ! nace mai ai yazo mutafi yacemin shi tsoron rigimar auta yakeyi yasa ya ki bina dan yasan haduwarsu ” dariya ummi da zeenat da fawwaz sukayi zeenat ta ce ” lallai ya areef wato kai karasa ma wacce zaka tsokano se auta rigima ” nanma dariya sukayi , hafiz ya ce ” ummi dazan shigo na hadu da wani wai yacemin sunanshi Mansoor sannan Kuma yacemin in gaisheku sosai , ashe shima kanin su ya fawwaz ne ” duk dagowa sukayi har suna rige_rige wajan kallon hafiz dake magana yasa lamarin basu mamaki da daure musu kai dan kuwa sunsan de tabbas hafiz be san Mansoor ba balle yayi irin wannan maganar, jikin areef ne yadauki rawa ya mike yana kallon fawwaz ya ce ” fawwaz bana fada maka ba wallahi Mansoor na gani dazun amma kacemin sam bashi bane to gashi hafiz ma yaganshi ” riko areef Mr azaad yayi ya ce ” calm down areef ” zama sukayi amma har lokacin jikin areef be bar kerma dayakeyi ba. shiko hafiz mamaki ne yakamashi ganin yanda firgici da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu lokaci daya dan kawai ya fada musu yanda sukayi shida Mansoor din . Mr azaad ne yakalli hafiz ya ce ” hafiz aina ka kalli shi Mansoor din ?” fada mishi hafiz yayi sannan Mr azaad yasake maida kallonshi kan areef ya ce ” ka kwantar da hankalinka kafadamin aina kaga Mansoor din ?” duk abinda yafaru a garden din areef ya fada mishi sannan yakara da ” yayi tamin magana wanda nakasa gane me yake nufi amma naji yafadi wata kalma ‘ku kare kanku daga sharrinta ‘ wannan kalmar ce kawai zan iyacewa naji ”
zeenat kam uwar tsoro tunda taji aka ambaci sunan mansoor ta kankame fawwaz kam ta ki sakinshi. girgiza kai ummi tayi ta ce ” karku daga hankulanku akan wannan mansoor yariga da ya mutu kawai sharrin shedanu ne da jinnu amma kun tabajin wanda ya mutu ya dawo ne ” zaro ido hafiz yayi shima lokaci daya jikinshi yafara rawa jin wai Mansoor din da ya hadu dashi har sukayi magana wai matacce ne ya rigada ya mutu babban tashin hankalinshi shine inya tuna yar maganar da sukayi na wasu yan mintuna , da mugun karfi zuciyarshi yake bugawa sakamakon jin maganar yayi kamar saukar aradu hakan yasa yadafe kirjinshi da karfi sauka yayi akan kujera yaduqa kasa yana rike da setin zuciyarshi dagashi Mr azaad yayi yadan rungumeshi dan dama yasan hakan seya faru muddin hafiz yaji dan bakowane yake da wannan karfin guiwan tunkarar magana makamancin wannan ba ace kayi magana da wanda yarigada ya mutu baka sani ba daga baya inkaji hakan dole hankalinka yatashi , kokarin zaunar da hafiz Mr azaad yakeyi yaji yakara nauyi nan yagane suma yayi yasa ya kwantar dashi akan kujeran dauko ruwa fawwaz yayi yamikawa Mr azaad ya yayyafawa hafiz shuru be farfado ba , zama ummi tayi kusa dasu ta daura kan hafiz akan cinyar ta tarike hannunshi tana murzawa da dan karfi ko hakan ze temaka duk suna tsaye akanshi , saukowa fanan tayi tana murna tasamo dabinon dataje nema, ta samesu duk sunyi cirko_cirko sannan ga hafiz dake kwance dasauri takaraso falon , tambayar fawwaz tayi meyasa meshi karya yamata yafada mata kancewa sunga yarike kirjinshi ne daga bisani kuma yasuma zama tayi agefen kujeran ta rike hannunshi dede wajan pause dinshi taji yana harbawa da wuri tasake sa hannunta akan kirjinshi nan taji wani irin lugude da zuciyarsa yakeyi hakan ne ya tabbatar mata da tabbas wani abune yagani ya razanashi ko kuma wani abun yaji daya firgitashi kallon ummi tayi ta ce ” yadan shigo yar doguwar suma amma zuwa nan da 4hours ze iya farfadowa amma kuma in muka bari ya farfado ahaka tabbas akwai matsala , ze iya samun matsalar brain kokuma yashiga firgici har nan da sati daya ” tagama musu bayani tana karasawa kan center table tadauki pen and paper data gani ta rubuta allurai da magunguna ta mikawa fawwaz karba yayi yafice dasauri dukda darene zeyi wuya susamu pharmacy abude sede yadangana asibiti, duk suna zaune fanan ta kalli Mr azaad ta ce ” Mr azaad meyasa meshi ” bayason yafada mata yasa kawai ya ce mata ” baby we don’t know kawai ganinshi mukayi ahaka yarike kirjinshi” ta ce ” Allah sarki inna mishi alluran nan in sha Allah zeji dama dama dan zesamu baccin 12 to 14 hours kuma baze tashi da wannan firgicin ba ” jinjina kai yayi ummi ta ce “zeenat tashi kije ki kwanta dare yayi ko ” make kafada tayi alamar ah ah dan duk atsorace take bazata iya kwana ita kadai ba , taso basu dariya areef kuwa shuru yayi yana binsu da ido , haka fawwaz ya dawo da allurai da magunguna , allurai fanan tayi mishi sannan Mr azaad yadaukeshi cak kamar wani yaro karami yayi part din su fawwaz dashi yakaishi dakinshi yakwantar dashi hade da rufeshi da blanket sukafito . Ummi tabasu umarni da kowa yaje ya kwanta haka suka shige part dinsu , Mr azaad maganar mansoor ya tsaya mishi arai amma zesan yanda ze bullowa lamarin .
Duk wannan wainar da ake toyawa mommy bata da masaniya akai tana nan tana neman hanyar da zata kashe kaf yan gidan hatta yayanta suma seta kashesu bazata bar kowa ba dan dukkansu ta tsanesu mansoor ne kadai takeso shikuma yarigada ya mutu, tamafi tsanan anty shayida shisa aduk sanda anty shayida tasamu karamin ciki , tunkafin sunsan da cikin mommy take cinye dan tun a mahaifa, kusan sau takwas anty shayida nasamun ciki mommy tana cinyewa tunkafin yazama hallita take cinyewa. Haka tasoyiwa anty zainab amma dake mijinta atsaye yake gashi babban dan siyasa kuma malami.
Bauchi state
Fitowa suhaima tayi daga bedroom dinta tana rike da waya tana video call da fawwaz har karfe 11:30 nadare ta farajin yunwa tafito tashiga kitchen din ta ajiye wayar yanda yana kallonta ta daura indomie akan wuta yadafu taje falo tazauna tanaci fawwaz ya ce ” ba bismillah kenan? ” Yar dariya suhaima tayi ta ce ” hubby tom ai kona maka bismillah bazeyu kaci ba sede inci mana ka ji ” tafada tana ci gaba da cin indomie fawwaz ya ce ” to babynah kici mana din ” haka suka dinga hira kafin ya kashe kiran dan dare yayi suka sauka a online din .
fanan ta dade dayin bacci while Mr azaad idonshi biyu beyi bacci ba dan so yakeyi adaren nan yayi clearing issues din dasuke faruwa acikin gidan sulalewa yayi yafice adakin yasauko ya bude kofar part din gaba daya yaje garden din shikadai kamar wani maye ko ina yayi tsit se kananun maganganun dayakeji kasa_kasa which is yasan nasu wayene haka yazauna yana girgiza kafa.
Mommy na kwance akan makeken gadonta fatalwar mansoor yabayyana atsaye agefen gadonta, murya da dan karfi yafara kiran ” mommy! mommy! mommy! Ki tashi kina bacci wato kin barni inata garari Koh?” adan firgice mommy ta tashi daga bacci tana mustsuka idonta rass ta waresu akan Mansoor dake tsaye yana sanye da fararen kaya tashi tayi tazauna dakyau tana kiran ” Mansoor dina kaine? dana nayi kewarka” daka mata tsawa yayi ya ce ” karki sake kirana da danki muguwa azzaluma, ke ba uwa ta gari bace annamimiya kawai . hankalinki yakwanta dakikayi sanadiyar barina duniya?” ya daka mata wani gigitacciyar tsawa ” nace hankalinki yakwanta yanzu? bazan taba samun salama ba harse asirinki ya tono senayi hanyar dazan fadawa kowa ke matsafiyace yar kungiyar BAPHOMET masu shan jini da shirka , yanzu wato babban burinki shine ki kashesu ko ?” hawayene yake zuba akan kumatun mommy taduqa akasa ta ce ” my son kayafemin yanda nakesonka bazan taba barin komai yasameka ba bare har inyi sanadiyar rayuwarka sannan magana akan daukan fansana dole sena kashesu kaf dinsu Koda shugaba tanzarzar be amince min ba sena aiwatar da hakan , daga zaran munyi nasarar gamawa da shafin sarauniyar nasminaya sesune target dina ” girgiza kai kawai fatalwar mansoor kafin lokaci daya yabace bat .
Inbanda tsuma da jijjiga babu abinda jikin Mr azaad yakeyi tsabar bacin rai da bakin ciki idon nan yajuya yazama mugun jajir da karfi yake cizan libs dinshi na kasa da har gurin yayi ja sosai yafara tsastsafo da jini . yau bayajin ze iya barin mommy ta kwana daranta seya kasheta dan daga inda yake zaune a garden yana yana jiyo duk wani maganar dasukayi da ita da fatalwar mansoor tabbas mommy ta cucesu ta ha’incesu yanzu dama all this while suna tare da munafuka matsafiya agida daya basu saniba tom tabbas shi zedau mumunar mataki akanta tunkafin abba yadawo daga marley sede yadawo yaji labarin kawai ya kasheta. yana cikin wannan mugun bacin ran fatalwar mansoor yabayyana agabanshi fuskanshi dauke da murmushi ya ce ” yayana yanzu nayi farin ciki dakasan gaskiya akan mommy zansamu salama yanzu bazaku kara ganina ba se adarul salam nabarka lafiya ” yafada yana me bacewa yanawa Mr azaad bye-bye shima bye-bye din ya mishi duk da yana cikin matsanancin bacin rai, hakan be hanashi maida mishi da martanin murmushin daya mishi ba, domin yafayyace musu komai dangane da mommy.
Tofa ana wata ga wata yaude alhamdulillah asirin mommy yatonu shikenan.
Ina jiran ruwan comments dinku duk wanda yasan ina binshi bashin comment yafito yamin abuna tam.
Se munhadu ranar laraba jibi kenan inme duka yakaimu da Rai da lfy .
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
⚕️⚕️ NIDA PATIENT DINA
⚕️⚕️ NIDA PATIENT DINA
Story & written by ✍️
MRS ISHAM
JARUMAI WRITERS ASSOCIATION
Gargadi
ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba takowani siga ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin.