Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 53

Sponsored Links

{53}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Wannan karon gida na wuce kuma acan na sauka, kowa yayi murnar ganina domin nayi kyau na canja nayi ƙiba, wuni muke muna waya da shi dama kuma can haka ya sabar min dashi, kwana biyu da zuwana na fita na yiyyi ziyara har gidan uncle dinsa naje wato gidan anty Amina, duka yaran nata suna nan iya munira ce kadai ban gani ba akace tana school, washe gari gidan yaya Abdurahman naje daga nan na wuce gidan ƙawalli, nasha mamaki sosai ganin Irfan yana takawa sai dai ba sosai ba dan tafiyar bata gama nuna ba,

“yanmatan Abuja me samz din naki yake baki ne kiketa habaka haka?”

“ƙawalli wai har yanzu sunan nan bazai fita daga bakin ki ba? Idan ba zaki kirashi da Muhammad ba ki hakura”

Dariya ƙawalli tayi tare da ajiye min uban tiren da ta jibgo min kayan dadi akai danginsu kwalam da makulashe,

“Allah ya baki hakuri na daina, a gafurceni…”

“to dai ya fi miki” na fada ina ajiye Irfan kusa dani,sai da muka sha hira muka koshi na gama cika cikina sannan na fara sanar da ita damuwata,

“ƙawalli nifa rashin samun cikin nan nawa yafara damuna, tun abun baya daga min hankali yanzu yafara daga min, abun yayi min jinkiri….”

“kar ki fadi haka ƙawalli, ki daina irin wannan maganar domin Allah yana sane da komai sannan kuma shine zai magance ma kowa damuwarsa, ki daina daga hankalinki akan batun ciki Insha Allah ubangiji Allah zai baki masu albarka nan bada jimawa ba, komai fa lokaci gareshi…. ”

” haka shima yake cewa amma ni damuwata kinga mahaifiyarsa da ƴan uwansa ba kaunata suke yiba to rashin haihuwata da wuri zai sake kawo wata damuwar tsakaninmu…. ”

” hakane amma kuma ai komai daga Allah yake sannan shine mai badawa kuma naga haihuwar nan kin taba samun ciki bawai baki taba samu bane bare ace bakya haihuwa, wallahi karma ki daga hankalinki ”

” ƙawalli ba zaki fahimceni ba kamar yadda shima nasan ba zai taba fahimtata ba, ni kadai na san damuwata da irin yadda nake ji, ni yanzu ma kafin na koma zanje asibitin Dr Aziza in ganta ko da akwai shawarwarin da zata bani bayan ta dubani saboda shi naga kamar abin bai dameshi ba duk lokacin da nayi masa maganar muje asibiti a duba mu ko da matsala sai yaki yace babu wani matsala ”

” to ai da gaskiyarsa ni banga laifin sa ba akan me zaki dage sai kunje anyiwa Allah shishhigi? ”

” ƙawalli zuwanmu asibiti yana da nasa advantage dinfa, kinga idan akwai wani abu zasu fada mana idan ma lafiyarmu ƙalau sai in samu peace of mind in kwantar da hankalina…”

“hakane ƙawalli kuma na fahimceki tabbas kin zo da magana, to ki samu kije kiga Dr din before ki tafi”

“Insha Allah zanje, ke ai naga kamar harma kin kusa juye na biyu”

Dariya tayi ta kai min duka na goce, kamar koda yaushe wuni nayi ciss gidan ƙawalli sai bayan da nayi sallar magriba sannan suka mayar dani gida, dama tun a hanya yake kirana bana dauka saboda yaya Abdul Hakeem yana wurin shiyasa ina zuwa gida na wuce dakina na bararraje sannan na kirashi,shagwaba naji yafara yimin kamar yadda ya saba,

“baby what have i done to deserve this punishment??”

“am very sorry sweet, you did nothing, yanzu gashi na dawo bazan sake tafiya ba har sai lokacin da ka sallameni…”

“thank you baby….” mun raba dare muna yin waya dashi kafin bacci ya daukeni ban ma san lokacin da na ajiye wayar ba,

Da yake anty salaha tana dab da haihuwa ana igobe zan koma Abuja ta haihu wannan dalilinne yasa ban koma ba na kirashi ina fada masa haihuwar da akayi kuma gara in zauna ayi suna agama akan ace sai na koma sannan in kara dawowa, ba dan ya so ba ya kyaleni ya hakura akan hakan.

***

Tun bayan tafiyata shalele ta cigaba da uzzura masa tare da matsa masa duk da shi bai santa ba kai baima taɓa ganinta ba, ranar da na cika 1 week da tafiya sai gata ita da Malika a gidanmu da yamma da yake shi baya fita ko ina kwata kwata bai iya yawo ba daga gida sai office sai ko yan bukatun da ba arasa ba, ranar a gida ya wuni yana bacci wurin 3 ya tashi ya kirani vedio call wai yunwa yake ji so yake yayi girki in koya masa,

Murmushi nayi ina kallonsa dan a bisa dukkan alamu ya sha bacci babu laifi,

“to yanzu me zaka dafa?”

“jallop rice baby….”

“Ok tom shiga kitchen”

Tashi yayi ya shiga, inata faɗa masa yadda zai yi ina nunnuna masa da haka har yayi jallop din wadda ya wadata ta da kayan lambu dan tasha carrot da cabbage babu laifi, zubawa yayi a flate ya koma falo yana tsokanata wai banji yadda jallop dinshi tayi dadi ba, shagwabe masa fuska nayi kamar zanyi kuka ina cewa,

“nima ta ban sha’awa ina so sweet”

“don’t worry baby idan kika dawo zan dafa miki wanda tafi wannan dadi….”

“awwwwn that’s my favorite person…”

Sai da aka fara kiran sallar la’asar sannan muka yi sallama. Wanka ya shiga yayi ya fito ya feshe jikinsa da turare sannan ya saka kananan kaya yayi salla, tun yana yin sallar yaji ana buga door bell, yana sallama ya tashi ya nufi kofa dan ganin waye zuciyarsa fal tunani iri iri dan yasan babu mai zuwa mana a daidai wannan lokaci, yana budewa idonsa suka yi tozali da yanmata guda biyu, duk a tunaninsa wurina suka zo shiyasa ya dan saki fuska kadan ya amsa gaisuwarsu,

“am bata nan fa…. Ta dan yi tafiya”

“ayya Allah ya dawo da ita lafiya, sai dai amma dama ba wurin ta muka zo ba kai muka zo nema” Malika tayi magana cikin karfin hali,

“ok but ban ganeku ba”

“dama ai baka sanmu ba”

“meya faru?”

“wannan itace suhaila wadda ta jima tana tura maka da text massage kana ignoring…”

“to me kuma ya kawoku gidana?”

“gani muka yi idan hagu ta ƙi zai a koma dama….”

“I don’t understand this….. But inada mata, am married soo pls stay away from me”

Sosai maganarsa ta yiwa Malika ciwo kuma ta kona mata rai, in banda sharrin so da kaddarar so ya za ayi har su zo wurin namiji ya nemi raina musu hankali, Shiru tayi saboda ta gama kuluwa da kalamansa, ita kuwa suhaila da yake ance abinda zuciya ke so ai sam hakan bai bata mata rai ba sai ma sake burgeta da yayi, ji tayi kamar ta durkusa kasa ta soma rokon soyayyarsa amma sai ta dan fuske, yana kokarin maida kofa ya rufe samha na fitowa daga gidanta nan ta tsaya tana kallonsu har Malika wacce ke kule tace “baiwar Allah da magana ne?”

“to ai na ganku kuna fitowa daga cikin gidan nan ne kuma ni a iya sanina matar gidan tayi tafiya tun last week…”

“to ai dama ba wurin ta muka zo ba wurin mai gidan muka zo” daga haka suka wuce ta suka kama gabansu,

Wannan lamari ya daurewa samha kai kuma ya bata mamaki, kwafa tayi ta sheke da dariya kafin tace “wayyoni Allah dama ai dadina da gobe saurin zuwa, wanda bai ji bari ba zai ji hoho, maganin ki widat ba kince namiji dan goyo bane, ai wallahi sai na fesa miki wannan labarin kin ji shi, gashi nan ke da kike tattalin mijin hakan bai sa yaji tausayinki yaki bibiyar matan banza ba, mu da kike yiwa kallon bamu iya ba sai gashi namu mazajen basa bin yanmata bare har su kawo su har cikin gida… ”

Ban san me yake faruwa ba ina can gidanmu hankalina kwance inata sabgogina har akayi sunan anty salaha inda jaririya taci sunan mama amma zamu rinka kiranta da Ammah, ana gama suna na fara tarkata nawa i nawa dan komawa Abuja duk da acikin Satin za a kawo kudin auren Bishra daga Bauchi amma Abba yace tafiya zanyi wai ai na jima kuma ba tarone na mata ba mazane zasu kawo gara in koma gidana wurin mijina, lokacin da nake bawa samz labari dariya ya rinka yimin yana cewa Abba yafi sonsa akaina nikuma harda su kukan shagwaba kamar gaske, cikin kwanakin na kammala na koma. Ni na kawo kaina gida ban jira yaje ya taho dani ba kawai dai ya san cewa yau zan dawo but bai san time dinba ni kuwa tunda safe na shirya na biyo jirgin rana saboda nima nayi missing mijina kamar yadda shima yayi,

A bakin kofa na tsaya na danna door bell ina shirin sake dannawa sai gashi yazo ya bude banyi wata wata ba nayi hugging dinsa shima rungume ni yayi yana yimin sannu da zuwa,

“welcome back my baby love….”

Traveling bag ɗina ya dauka muka shiga ciki har lokacin muna manne kamar wani mayen ƙarfe da ya hadu da dan uwansa, daga shi sai t shirt da short nicker da yake weekend ɗin, a falo muka yada zango ya dorani bisa cinyarsa yana rike da hannuwana wadanda suka sha lalle,

“baby kika tafi kika barni ni kaɗai…..” ya fada cikin shagwaba yana sinsina kirjina,

“am sorry boo, bazan sake ba, Kaci abinci?”

“nayi mana girki ina jiranki ki dawo muci….”

“awwwwn….. Me ka dafa?”

“let’s go and see…” yace dani yana daukata har zuwa kan dining din, jallop din shinkafa irin wadda yayi rannan sai chicken pepe, murmushi nayi ina yaba yadda naga girkin yayi kyau a ido domin komai shar shar,

Da kansa yayi saving dina kafin muka fara ciyar da junanmu kamar yadda muka saba, ai fa tunda na dawo shikenan fita ko zuwa kofa sai ta gagareshi dama kuma weekend ne nanfa muka yi kamar zamu cinye juna tsabar soyayya kuma bashi ya fita ba sai ranar Monday da ya fita office, baccina na shaka kamar yadda na saba bayan azahar na tashi nayi wanka nayi salla na shiga kitchen kenan babu jimawa naji an danna door bell nan na fita na bude, Samha ce shiyasa sai da nayi tsaki cikin raina haka ta biyoni muka shigo tare tana zuba kamar kanyar da bata da zaƙi, zama tayi muka gaisa tayi min sannu da zuwa sannan ta kada baki ta fara fadar abinda ya kawota.

“Widat ban san yanda zaki dauki maganata ba sannan ban san wacce irin fahimta zaki yi mata ba amma koma dai yayane ya zama dole in sanar dake abubuwan da baki sani ba kodan ki san ta yadda zaki kare kanki……”

“ban fahimceki ba Samha, kawai ki tafi straight forward ki fada min abinda kike son fada kibar wani kwana kwana…. Me ya faru?”

“dama na sha fada miki maza ba abin yarda bane kuma duk macen da tace namiji ubane to wallahi sai ta mutu marainiya, namiji rigar ƙaya ne kuma tabarmar ƙashi, namiji ƙanin ajali ne sannan duk abinda zakayi dan ka tarairayeshi ka burgeshi hakan bazai hanashi ya watsa maka ƙasa a cikin idanuwanka ba, mijinki duk yadda kike kyautata masa da wahalta masa da bakya nan wallahi tallahi mata yake kawowa cikin gidan nan…. ”

Ras Ras naji gabana ya fadi a karon farko amma sai na daure kuma na danni zuciyata,

” wannan shine abinda kika zo ki fada min? Indai shine bana bukata dan fada min din baida amfani ”

” dama na san ranki zai baci amma ni a matsayina na makociyarki wacce tafi kusa dake dole in sauke wannan hakkin makotakar, sannan yanzu cututtuka sunyi yawa na zamani kar kije kina zaune akwaso miki cutar da zata illata ki ”

” duk na fahimceki amma sai nake ganin dani dake duk muji da matsalar da ta damemu ya fiye mana akan mu sakawa mazajen wasu ido muna gano laifunsu dan muma namu mazajen baza arasa irin nasu laifin ba wanda suke boye mana suna aikatawa a bayan idon mu…”

“ohh widat abinda zaki fada min kenan akan na kawo miki laifin mijinki? Wannan bakaken maganganun zaki jefeni dasu?”

“ba bakar magana na fada miki ba abinda ke raina na fada miki kuma mijina mutum ne kamar kowa ba ma’asumi bane bare ace dole bazai aikata laifi ba, dukkanmu masu laifi ne musamman mazajenmu to amma ni kazantar da ban gani ba na dauketa a tsafta, tunda yana respecting dina yana tattalina wannan labarin da kika zo min dashi bazai sa in juyawa mijina baya ba mutukar ba wai canja min yayi ba… ”

” to shikenan Allah ya gani na sauke duk wani hakki na zaman tare da ya rataya kuma ya wajaba a kaina… ”

” idan kin gama zaki iya tafiya saboda aiki nake yi ” nace da ita cikin jin haushi dan ita da ta kawo min labarin tafi bani haushi fiye da shi samz din da ya aikata laifin……

*_Ummi Shatu_*

Back to top button