Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 5

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na biyar_

 

https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc

___________

*UMMUL~ADNAN DATA SERVICE*
We offer you the most affordable and cheapest data
*MTN*
500mb ➖ 170
1gb➖340
2gb➖640
3gb➖940
4gb➖1250
5gb➖1550
10gb➖4000
Check balance=*131*4# or *460*260#
*GLO* *CORPORATE GIFTING*
500mb➖150
1gb➖270
2gb➖540
3gb➖790
5gb➖1300
Check balance=*127*0#
*AIRTEL*
500mb➖150
1gb➖270
2gb➖530
3gb➖800
5gb➖1270
10gb➖2510
Check balance=*140#

*9MOBILE*
☑️500mb➖140
☑️1gb➖240
☑️2gb➖480
☑️3gb➖660
Check balance = *228#

All network valid for 30days

*PAYMENT*
Through this acct
7032785536 ZAINAB SARKI AHMED
OPAY
CABLE SUBSCRIPTION ARE ALSO AVAILABLE
Phone no 07032785536

________

…….A sanadin wannan abu daya faru mahaifin Khadijah yazo har makarantar tasu, yanda yayma malaman tas akan abinda ya faru na rashin ɗa’a da akaima yarinyarsa amma basu ɗauki mataki ba yasa aka hukunta Dafeeq. Dan shima har sai da mahaifinsa yazo makarantar. Abinda ya bama kowa mamaki shine kai tsaye ya amsa laifinsa, ya kuma bama Khadijah haƙuri. Abune da bai taɓa faruwa ba, dan ko mi zai aikata duk irin hukuncin da za’ayi masa bai taɓa bama koda malamai haƙuri ba saboda shegen girman kansa da rashin ji. An sallamesu komai ya wuce. Tun daga ranar kuma idan suka haɗu sai ta hararesa ta murguɗa masa baki. Shiko baucewa da ita komai sai dai ya ɗauke kansa ko yay dariya kawai. Sabon salon nasa na bama abokansa mamaki, dan akwai randa akai taren masu latti ƙiri-ƙiri ya hana a daki Khadijah. Abun nasu kamar wasa a wani hutu sai ga Dafeeq a gidansu. Da farko nunawa yay baba yazo gaidawa, a dawowa ta biyu kuma ya ƙulle da ƙaninta. Tun yana zuwa ya tsaya iya ƙofar gida har takai baba ya bashi damar dinga shiga cikin gidan ya gaida Umma. Ko kallonsa Khadijah batayi da farko, amma kafin hutun nan ya ƙare sai gashi ta fara sassautawa har tana gaishesa. Sannu a hankali al’amarin nasu ya fara sauyawa har yana koya mata karatu ita da sauran ƙannenta, da farko iyayen Khadijah basu ɗauki al’amarin komai ba, dan daga Dafeeq har Khadijah yarane. Kasancewar Dafeeq ya ɗan samu matsala a harkar karatunsa a baya ya bama Khadijah kusan shekara huɗu, dan ita bazata wuce 16years ba, shiko zai iya kaiwa 20 gashi kuma da tsayi. A haka Dafeeq ya kammala makaranta su Khadijah suka shiga ss3 suma. Yawan zuwan Dafeeq da yanayin da suke kasancewa da Khadijah yasa Umma ta fara fahimtar akwai magana a kansu, dan haka ta faɗama Baba. Yayi matuƙar mamaki da jin batun dan yasan dai su ɗin yarane, dan haka ya zaunar da Khadijah ya mata nasiha da sake tabbatar mata da burinsa akan tayi karatu mai zurfi kuma yasan itama shine babban burinta. Shima Dafeeq ɗin baba ya sameshi da nasiha akan ya dage ya cigaba da karatunsa su ajiye maganar wata soyayya gefe idan ma yana son Khadijah ne ya bari sai nan gaba yanzu su yara ne, amma idan sun kai girma yayi alƙawarin zai aura masa ita. Kamar Dafeeq da Khadijah sunji wannan nasiha fa, sai kuma gashi bayan watanni kamar biyu aka kawoma Baba shaguɓen yafa saka ido akan Khadijah kada yaron nan dake zuwa gidansa ya lalata masu ita. Hankalin Baba ya tashi, sai dai baima Khadijah magana ba ya fara bibiyar al’amarinta batare data sani ba. Ilai kuwa sai ga Baba ya gano inda Khadijah da Dafeeq ke ɓuya yin hira wai. Ranar ya zaneta duka irin wanda bai taɓa kwatanta mata ba, ya kuma takama Dafeeq burki da zuwa gidansa gaba ɗaya.
Al’amari kamar ya lafa sai kuma wasa da karatun Khadijah ya ɓullo, dan takai sam bata maida hankali har suna shirin fara jarabawar ssce. Tun Umma na lallashinta da mata nasiha a ɗaki su kaɗai har tadai faɗama Baba. Shi rasama abin faɗa yayi a wannan gaɓar, dan haka ya kira Khadijah ya tambayeta mi take buƙatane? Babu kunya babu tsoro kamar ba Khadijahrsa ba tace ita aure take so. Kuma Dafeeq take so. Kallonta kawai baba ya tsaya yi, sai da yaja wasu mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya da fuskantarta. Cikin lallashi da nuna kulawa yace to yaji zai mata auren, amma ta maida hankali akan jarabawarta da suke shirin farawa. Bayan ta kammala secondary ya mata alƙawarin tana fara jami’a koda wata biyu ne zai mata auren. Amma fa ta sani bada Dafeeq ba. Dan Dafeeq dai a yanzu haka yaƙi karatu, baya kuma sana’ar komai sai yawo da abokai, sannan iyayensa sunce ba aure zasuyi masa ba yanzu. Kuka ta fashe masa dashi tare da rantsewar itafa shi ɗin take so. Kuma idan ba’a aura mata shi ba zata bishi su gudu kamar yanda ya buƙata suyi aurensu acan wani waje. Cike da takaici da gatse Baba yace ga hanya nan ta tafi to. Daga haka ya buga babbar rigarsa ya fice a gidan ransa a ɓace.

Maganar Khadijah tamkar a wasa ko ƙuruciya bayan kamar wata biyu aka nemeta aka rasa ita da Dafeeq. Hankalin kowa ya tashi, tako ina aka shiga nemansu amma babu labarinsu. Da ga ƙarshe aka samu saƙon wasiƙa daga garesu suna bama iyayensu haƙuri akan sunje suyi aure, amma in sha ALLAHU watarana zasu dawo garesu.. A take Baba ya yanke jiki ya faɗi, ranar sai a asibiti ya kwana. Yayinda iyayen Dafeeq keta tujara wai Khadijah ta janye musu hankalin yaro da asiri, ya daina jin maganar kowa sai tata da tasu Baba. Maganganu marasa daɗi dan har gida sukazo suka cima Umma mutunci da Baba dake kwance yana fama da kansa…
Duk da wannan labari duk ya shiga kunnen Dafeeq da Khadijah basu koma gida ba, sai ma tattarawa sukai suka ƙara gaba. Sunyi aure kamar yanda suka shiryama kansu da taimakon hakimin yankin da sukaje. Dan sun haɗa masa ƙarya da gaskiya ne shi kuma ya amince. Sai dai bayan auren nasu ya basu shawarar komawa gida. Sun yarda da hakan, amma sun nema alfarmar a ɗaga musu ƙafa sai bayan lafawar abubuwa sosai. Wannan dalilin ne yasa ya barsu, tare da basu gida matsakaici, ya kuma zuba musu kaya a ciki masu ƙyau tare da nemawa Dafeeq aikinyi a wani Company. Aikin ba wani aiki bane babba can, dan na sharane acewarsa ya fara kafin a samu mafita, yadai samu abinda zai riƙe matarsa.
Ansha amarci na nunama tsara tsakanin Khadijah da Dafeeq. Dan Son juna suke tamkar zasu cinye kansu. Kowa ƙoƙarin ƙyautatama ɗan uwansa yake. Sun manta da gida da iyayyensu gaba ɗaya. Sam Khadijah bata tuna jarabawarta da ta baro a lokacin da ake gab da farawa duk da tsananin son da takema karatu a baya. Idonta ya rufe gaba ɗaya babu wanda take tunawa da gani sai Dafeeq. A haka sukaci watanni huɗu, sai ga ciki. Sosai Dafeeq ya nuna farin cikinsa da samuwar wannan ciki, ya shiga tattalinta kamar ƙwai, sai dai bayan kamar sati biyar sai kuma tayi ɓari. Tasha kuka sosai dan ta mugun ƙwallafa rai a cikin nan, haka shima Dafeeq ya shiga damuwa, daga baya dai suka lallashi kansu suka cigaba da rayuwarsu ta faranta ran juna. Ba’a ƙulla wata biyu ba sai ga wani cikin dai, nan ma sunta murna, sai dai shima bai kai labari ba ya zube. Nan ma kuka suka dingayi rurus har sai da matar hakimi ta dinga musu nasiha sannan suka haƙura. Bayan shi Khadijah ta sake samun ciki sau biyu yana zubewa, zuwa lokacin kuma sun ƙulla shekara kusan biyu da barin gida. Tun daga ciki na huɗu daya ɓare bata sake samun ciki ba, tun suna damuwa har suka dangana, a yanzu haka kuma shekara ta uku suke. Khadijah nada shekara goma sha tara, Dafeeq nada Ashirin da uku cikin da huɗu. Basu da wata matsala sai ɗan faɗan masoya irin na yau da gobe, basa jimawa kuma suke shiryawa saboda ita Khadijah nada sauƙin kai, koda Dafeeq ya ɗauki zafi da ita takan nuna masa itace a ƙasansa ta bashi haƙuri tana kuka da roƙonsa da magiya. Har yanzu Dafeeq na aiki a companyn nan, da ga shi har ita basa zancen komawarsu makaranta, shiko bayan shara a kamfani baya sana’ar komai, dubu sha takwas ɗin da ake biyansa duk wata acewarsa ai ya ishesu rayuwa. Khadijah bata taɓa damuwa da haka ba, dan tana son mijinta, shi kaɗai ta sani a sabon garinsu, sai gidan baba hakimi da takan ɗan je lokaci-lokaci ta gaishesu. Shima kuma bayan ita da gidan baba hakimin babu wanda tasan ya sani sai abokan aikinsa na Company, amma abin mamaki yau sai gashi da key na gida da mota yana faman farin ciki da iƙirarin wai nashi ne. A ina ya samu? Waye ya bashi? A dalilin mi aka bashi?. Waɗan nan tambayoyin take zumuɗi da burin yazo ya amsa mata ko zata samu nutsuwa a zuciyarta itakam….

(To Khadijah muma dai zamu so san jin ina Dafeeq ya samo key na gida da mota haka. Amma bari mu leƙo JJ na amarya Alimah mu dawo dai).

★★★…..

Cikin ƙarfin hali JJ yay wanka ya shirya a ƙananun kaya marasa nauyi. Duk tunaninsa su Baba na falo ne basu wuce ba, dan haka ya fito cike da ƙwarin gwiwa. Amma sai ya samu falon wayam. Zuru yay yana kallon kujerun, sai kuma ya shiga laluben aljihunsa cikin tsumar jiki alamar neman waya. Babu komai, da alama ya barsu a ɗaki ne ko. Ya ayyana a zuciyarsa yana komawa da baya zuwa ɗakin. Babu wayoyin nasa duka biyu anan ma, dan haka abin ya bashi mamaki kuma. Fitowa yay da ɗan hanzari, sai hakan yay dai-dai da fitowar Alimah da ga nata bedroom ɗin. Suna haɗa ido tai azamar rissinar da kanta cikin jin kunya, sai kuma ta fara magana ƙasa-ƙasa da badan yana kusa da ita ba ba lallai yaji ba ma.
“Ai ban san ka fito ba. Ga abinci to dan ka samu kasha magani kamar yanda Yaya ya faɗa”.
“Sun tafi ne?”.
Ya faɗa kamar cikin rawar murya. Kanta ta jinjina masa batare data ɗago ba ta ce, “Eh, ai kana shiga ciki suka wuce su kuma. Shine ma Yaya Mujee yace daka fito kaci abinci kasha maganinka”.
Cikin kullewar kai da rashin makamar riƙewa ya jinjina mata kai kawai. Ga wani irin matsanancin tsoro na ratsa masa zuciya. Amma dai ya dake a zahiri dan yana son tabbatar da abinda ya faru a daren jiya. Murya a sanyaye ya ce, “To muje ki bani”.
Babu musu tai gaba ya biyota a baya har zuwa tsakkiyar falon. A ƙasan carpet ya zauna kamar yanda yaga tayi itama a gaban kwanikan abincin. Ya zuba mata idanu yana kallon yanda take zuba abinci, sai ƙafafunta da yake kallo suma lokaci-lokaci. Zuwa can kamar wanda aka zaburar ya ce, “Alimah na tambayeki dan ALLAH?”.
Duk da tayi mamakin jin ya kira sunanta kai tsaye sai ta jinjina masa kanta batare data bar abinda take ba ko ta ɗago. Shima bai damu da rashin ɗagowar tata ba ya cigaba da faɗin, “Daga bayan dawowata raka abokaina jiya zuwa sanda kika kira aka kaini asibiti miya faru?”.
Cikin ɗan jin kamar mamakinsa ta ɗago ta kallesa. Sai kuma ta sake maida kanta da sauri ƙasa. Kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa a hankali. “Bayan ka dawo ka sake samuna a falo, shine kace muje ciki muyi salla, ka ajiyeni saman gado kace na jiraka anan kayi alwala, shine ka shiga bayi ni kuma barci ya ɗaukeni. Da’alama dai banyi nisa ba na farka a dalilin jin ihu da nayi, na tashi a firgice sai naji motsinka a bayi, baifi mintina biyu ba tsakani ka fito, shine kace na koma falo na jiraka kana zuwa. Ban jima a falon ba ka fito ka sake samuna, shine ka sake cewa na tashi muje sallar. Kaine ka kaini har ƙofar bayi dan nayi alwala, bayan na kammala na fito na sameka a ƙasa ka faɗi, na nufeka ina ƙwalama kira ka tashi ka maran, sai kuma ka sake sumewa, ni kuma kawai na fara haɓo. Nata kuka ina zuba maka ruwa baka farka ba shine nai kiran Rabi’ah lokacin kusan ƙarfe huɗu na dare, shine sai ita kuma ta gayama Yaya Mujee yazo muka tafi asibiti da asuba.”
Tunda ta fara maganar jikin JJ ke rawa. Dan gaba ɗaya muryarta ta koma ta wadda bazai taɓa mantawa ba a rayuwarsa. Duk da kuwa bai kamata ace itace kaɗai zata zauna masa a zuciya fiye da sauran na baya kafin ita ɗin da bayanta ba. Jin shiru yasa Alimah ɗagowa a hankali. “Yayana wlhy ni fa duk a tsorace nake”.
Wani irin yankawa ƙirjinsa yay na tsantsar firgita. Tuni ya zabura yay tsalle gefe cikin kaɗuwa. “Anoosh!” ya faɗa cikin rawar baki jikinsa na ƙara ɗaukar rawa..
“Anoosh kuma?”.
Cewar Alimah tana masa kallon tsoro. Zaraf ya miƙe har yana taka plate data zuba masa abinci. Baibi takansa ba ya kwasa da gudu zuwa ƙofa, sai dai yana isa ruff ta rufe kanta da kanta. Baya yaja da wani irin rawar jiki yana zaro idanunsa gaba ɗaya waje. Sai kuma ya waiga bayansa da sauri. Alimah na tsaye tana kallonsa, da sauri ya juyo gabansa, nan kuma Anoosh tsaye jikin ƙofa itama tana kallonsa. Rigifff ya zube ƙasa kamar wani tsohon amalen raƙumi daya gama morar duniya……✍️

( Uncle JJ namu).

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button