Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 19

Sponsored Links

*PAGE* 1⃣9⃣

ummi kiran mama tayi a waya lokacin mama tana zaune tsakar gida ita da abbah suna cin abinci, mama jin wayarta tana ringing yasa tad’auko ganin sunan sultana bilkisu da yabayya yasa tazaro ido tare da cewa malam sultana ce take kirana.

Abbah yace toh toh d’aga muji abinda zatace, mama saida ta saita nutsuwarta sannan tayi picking d’in call d’in tare da yin sallama.

daga chan 6angaren sultana bilkisu ta amsa mata cike da fara’a, nan suka gaisa cike da girmama juna, ummi tace ya su zarah dafatan duk suna lafiya?
mama tace lafiya lou, nan ummi take shaida mata akan maganar neman auren zarah da za’a zo gobe.

mama kallon abbah tayi da yake sauraren firar tasu, alama yayi mata da tace toh.
mama tace toh ranki yadad’e Allah yakaimu.
cike da jin dad’i ummi tace Ameen mungode sosai, ammah idan mahaifinsu yana kusa kiban shi inaso muyi magana inkuma baya kusa idan yadawo zan kira,

mama tace ranki yadad’e yana ma kusa gashi, nan tamik’a ma abbah waya.

Abbah kar6a yayi tare da yin sallama nan suka gaisa cikin mutunta juna, sultana bilkisu tace yauwa daman akan tsaida rana ne agaskiya mu a Royal family d’inmu ba’a yin baiko ad’auki lokaci shine nakeson in rok’eka alfarma dan Allah kar asa lokaci dayawa,

Abbah Jim yayi yakasa cewa komai.
sultana bilkisu tace kayi mamakin jin haka ko? kuyi hak’uri wlh tsarin masarautarmu ne haka.
Abbah cike da damuwa yace ranki yadad’e gaskiya hakan bazai yuwuba domin mu ba halinmu d’ayaba idan mukace ayi bikkin cikin gaugawa toh gaskiya zamu cutu tunda bamu fara tara komaiba da dai ataimaka asa ranar da d’an nisa domin musamu muyi mata abinda Allah yahore mana.

daga chan 6angaren ummi murmushi tayi tace kar kadamu ni zan d’aukema zarah duk wani abu da iyaye yakamata suyi ma ‘ya’yansu wlh ko da ba d’ana zata auraba zan iya yi mata haka.

Abbah yace a’a ranki yadad’e kar hidimar tayi yawa kibari dai zamuyi.

ummi tace kar kadamu tunda nace zanyi kubarsa kawai wannan yazama sirri tsakanina da ku domin bana fatan wani yasan da hakan saboda gori da wulak’anci

maganarta tayi ma abbah dad’i sosai ganin yadda take Royal Family ammah bata d’auki kanta komai ba tasan abinda yadace da wanda bai daceba, muryar sultana bilkisu yaji tana cewa bawai ina nufin naraina k’arfinkuba wlh ko d’aya ko da ace ba zarah bace zan iya yi ma wata barema zarah da zata auri jinina dan Allah ka amince ma buk’atata a karo na biyu, malam yace toh ranki yadad’e mungode sosai Allah yabiyaki da gidan Aljannah,
ummi tace Ameen nice da godia da kuka amince min sai kunjimu, agaishe da su zarah.
malam yace haba bakomai ranki yadad’e, su zarah zasuji.

bayan sun gama wayar Mams kallon Abbah tayi tace malam toh yanzu ya za’ayi? wannan neman aure ba ko shiri.

Abbah yayi murmushi yace gaskiya mutanen nan suna da kirki sosai bamuda abinda zamu biyasu da shi saidai muyi musu addu”a.

mama tace hakane da ace haka masu kud’i suke da ansamu sauk’in wani abun ammah yanzu sai kaga maikud’i sai d’iyan masu kud’i, Hajiya da Alhaji, d’an malam Audi me goro sai ‘yar Malam idi mai icce, bakowane iyaye suke amincewa ‘ya’yansu su auri ‘ya’yan talakawa ba,
Abbah yace hakane abun ne yanzu sai addu’a domin masu son talakawa suna ra6arsu basuda yawa wani lokacin ni abun har mamaki yake bani ince toh wai su mancewa suke da Allahn da yabasu zai iya amshewa a duk lokacin da yaso? ko suna mancewa Allahn da ya azurtasu shine yayi talakka kuma ba dan baya son saba, ko suna mance fad’arsace cewa shi yake azurta wanda yaso yakuma hana wanda yaso, Allah dai yasa mudace.

mama tace Ameen y rabb.
Abbah yace toh yanzu sai kurubuta duk abinda kuke buk’ata na tarar bak’in sai insiyo muku, ko kuma kuta6a kud’in nan kud’ibi yadda zasu isa kuje kasuwa yanzu kusiyo abinda kuke ganin ya dace dan ni yanzu fita nakeson yi zan ma biya gidan yaya manu inshaida masa dan yasan da zuwansu gobe yashigo da wuri,

mama tace toh malam Allah dai yashige mana gaba, bari inje insanar da yaran chan.

Bayan Abbah ya fita mama tashi tayi tanufi d’akinsu zarah lokacin zarah tana kwance saman katifarsu gefenta Rauda da Aysha ne zaune suna hira itadai bata sanya musu baki ammah tana saurarensu.

shigowar mama ne yasa suka tsagaita daga hirar da sukeyi mama kallonsu tayi tana murmushi tace ‘yan albarka kuna nan kuna hira?

murmushi Aysha da Rauda sukayi sannan Rauda tace eh mama akwai abinda kike buk’ata da za’ayi ne?

mama tace a”a bakomai sannan tamaida kallonta ga zarah da take kwance tace gobe in Allah yakaimu za’a zo neman auren zarah, wani irin fad’uwan gaba yaziyarci zarah ahankali tamaida idanuwanta talumshe tana jin wani iri a ranta.

Rauda da Aysha murna suka shiga yi suna kai wlh munji dad’i mama ashe zamusha bikki, bikkinma na princess zarah inji Aysha tare da kallon zarah taga idanuwanta a lumshe suke.

mama tace toh yanzu dai Aysha kitashi kishirya zamuje kasuwa musiyo abinda yadace dan haka Rauda ke zaki rubuta abinda kike ganin yadace asiyo.

Rauda tace toh mama nan tamik’e tad’auko paper da biro tashiga rubutawa.

 

Bayan su mama sun tafi Rauda kallon zarah tayi tace sister nasan abinda kikeji game da auren nan musamman ma da yakasance ba wanda kikeso bane zaki aura, kiyi hak’uri kikar6i k’addararki insha Allahu zakici ribar hak’urin da kikayi. zarah bud’e idanuwanta tayi da suka cika da k’wallah ahankali tabud’e baki tace yaya Rauda bawai nak’i ta taku bane wlh na amince saidai ina tsoron abinda zaije yadawo domin bana tunanin shima yana sona nasan dai had’in iyayensane inma bahakaba tun daga yanayinsa kinsan yafi k’arfin kasancewa mijin zarah, zarah duk yadda taso ta6oye kukanta kasawa tayi fashewa tayi da kuka tare da kallon Rauda da tazuba mata ido tace Yaya Rauda kiduba kiga ko da sau d’aya baizo da sunan mugaisaba kingako wannan aure namu kawai za’ayisane ammah yarima suhail ya wuce ajin zarah duk kyawawan ‘yan matan da suke garin nan arasa wadda za’a basa sai zarah?

yaya Rauda cike da tausayin k’anwartata tarik’o hannun zarah tace inji wa yace zarah ba maikyau bace? kema kinsan kanki kuma natabbata shima zaya soki domin kina da halayyar da yadace kowane namiji yaso mace saboda su, wlh zarah kin cancanci asoki, murmushi Rauda tayi tace nayarda da k’anwata zata iya sace zuciyar kowane namiji.

Zarah jikin Rauda tafad’a tare da k’ara sautin kukanta tace a’a yaya rauda kar kice haka wlh wannan yana da jin kai tun daga ma yanayinsa da nagani a wajen saukarmu kuma kema nasan kinga haka saidai idan zaki 6oye gaskiyane kuma fa su Abbah sunce mana yana da mata.

Murmushi yaya rauda tayi tare da shafa kan k’anwartata tace zarah nayarda dake nasan zaki iya k’watar ma kanki ‘yanci.

zarah mik’ewa tayi tashige toilet tamaida tarufe tacigaba da kukanta kamar wadda aka aikoma da sak’on mutuwa saida tayi me isarta sannan tawanke fuskarta tafito bata damu da kallon da rauda takeyi mataba tayi kwanciyarta tare da maida idanuwanta tarufe ganin haka yasa rauda takyaleta.

 

 

Tun da asuba da sukayi sallah shirye-shirye suke natarar bak’i inda aka rabama kowa aikin da zaiyi, girki sukayi masu rai da lafiya kala biyu, aka soya kaji kafin kace mi gida ya gaure da k’amshi sannan suka had’a drinks iri-iri .

 

wajen k’arfe sha d’aya suka gama komai kowa yaje yashirya ammah banda uwar gayya saida yaya rauda tace zata je ta sanar da su mama sannan tatashi taje tayi wanka suka d’auko mata atamfarta cikin kayan da ta d’inka da kud’in da tasamu na walimar safkarsu tasaka.

 

wajen k’arfe 12 lokacin su Abbah da d’an uwansa malam manu suna zaune waje suna jiran isowar bak’i, motocine guda ukku suka tafo a jere a k’ofar gidansa sukayi parking dogarawane suke fitowa daga ciki dasauri duk suka nufi wajen motar tsakiyar suka kare tare da baza manyar rigunansu suka bud’e wa su sultan Abbas(Abban sumayya) da waziri suka fito nan dogarawa suka take masu baya suna ranku yadad’e takawarku lafiya.

ganinsu yasa su Abbah suka mik”e suka nufi wajensu domin sun gane waziri, ganin sun nufosu yasa d’aya daga cikin dogarawan yace ranku yadad’e ga maigidan nan, suna isowa waziri da sultan Ahmad suka mik’a musu hannu cikin sakin fuska suka gaggaisa, Abbah yace bismillah kushigo daga ciki.

basuyi musuba sukabi bayansu a zaure suka zauna saman k’atuwar tabarmar da aka shimfid’a dogarawa a k’ofar gidan suka tsaya.

Nan suka k’ara gaisawa sannan su Abbah suka shiga gida suka kwaso kulolin abincin da aka shirya.

 

A gabansu su sultan Abbas suka jerasu, sultan Abbas yagabatar da kansu a matsayinsa na k’anen mahaifin yarima sultan sannan yagabatar da wazirin sarki,

nan shima malam muda yagabatar da kansa a matsayin yayan mahaifin zarah sannan yagabatar da malam musa a matsayin mahaifin zarah,

 

Nan suka shiga tattaunawa akan maganar neman auren dakyar suka samu abbah ya amince akan ayi bikkin nan da sati shidda masu zuwa dan shi cewa yayi sai nan da wata ukku,

dubu d’ari ukku sultan Abbas yabada yace kud’in nagani inaso da na neman aure,

abbah yaso arage kud’in saboda shi aganinsa sunyi yawa ammah sukak’i,
dubu d’ari suka bayar sukace ga kuma sadakin zarah, nan waziri yaba dogarawa izini da su kwaso kayan da suke cikin boot d’in mota,

nan aka fara shigowa da kwalayen biscuits, chewing gum sai sweets, sai alkyabba kala ukku da atamfa biyar akace na amarya ne, sai shadda yadi goma-goma kala ukku akace na uban amarya ne, sannan sai atamfofi kala biyar su kuma na uwar amarya.

Abbah rasa bakin godia yayi nan sukayi ta jero musu addu’o’i, dakyar suka samu su sultan abbas suka amince suka d’an ci abincin sauran akaba dogarawa suma sukaci,

bayan sun gama Abbah shiga yayi gida yace su zarah suje sugaisa, gaba d’ayansu suka fito zarah rufe fuskarta tayi da gyale saikace sabuwar amarya, nesa dasu kad’an suka tsaya suka tsugunnah cike da girmamawa suka gaishesu, cikin sakin fuska suka amsa musu tare da tambayarsu ya gida? sukace lafiya lou.

Waziri ne yace ina amaryar tamu cikinku? Aysha ce tayi saurin nuna zarah da take k’ara sunkuyar da kai tace gatanan.

Sultan Abbas da Waziri sukace masha Allah amaryartamu dai ta cika kunya dayawa toh Allah yasa alkhairi Allah yakaimu lokacin saidai kinyi hak’uri domin kinsan cikin danginsa zaki zauna kinsan dai yanayin gidan namu na sarauta.

Abbah yace haba bakomai ai shi aure babu inda baya kai mutum duk inda mace tatsinci kanta hak’uri zatayi tazauna.

gaba d’ayansu sukace hakane Allah yasa alkhairi.

su zarah tashi sukayi suka koma cikin gida, inda su Abbah sukayi musu rakiya har wajen motarsu gaba d’ayansu godia sukeyi ma juna irin karamcin da suka nuna ma juna, saida su Abbah sukaga tafiyarsu sannan suka dawo gida.

shigowa sukayi da kayan nan sukaita gani suna mamakin ganin neman aure kawai aka kashema wannan mak’udan kud’in, nan abbah yake fad’a musu yadda suka tsaida shawara lokacin da za’ayi auren, itadai uwar gayya tana d’aki ta k’umshe kanta harda kukanta.

Abbah shadda kala d’aya da dubu ishirin yaware yaba yayannasa, sannan ya d’ibar masa kayan sa ranar bikkin dayawa, malam muda godia yayi cike da jin dad’in kyautan da k’anen nasa yayi masa.

 

 

A chan 6angarensu Sultan abbas da Waziri a cikin mota sukaita labarin kirkin iyayen zarah,

ko da suka isa a fada suka safka lokacin memartaba da suhail sai mahaifin suhail ne zaune a fadar suna lissafin wasu kud’i.

nan sultan Abbas da Waziri suka labarta musu irin kirki da karamcin da suka samu daga wajen iyayen zarah.

Yarima suhail yana saurarensu shidai baice komaiba.

memartaba murmushi yayi tare da kallon yarima suhail yajinjina kai yace natayaka murna za6enka yayi kyau sosai, tun daga nan nasan d’iyar mutuncice zaka aura, ko da mahaifinka daman yafad’amin ba d’iyar masu kud’i bace wlh naji dad’i sosai domin suma talakkawa suna da ‘yancin shiga gidan sarauta kuma ta haka mutane zasu k’ara tabbatarwa bamu banbanta kowa dukansu namune.

yarima suhail murmushi kawai yayi,

nan su sultan Abbas suka d’auka Allah yaja da ran sarki me adalci

 

Sultan abbas ko da yafito daga fada turakarsu dada yaje yagaishe da mahaifiyartasa lokacin sultana bilkisu da sultana sadiya sunje gaisheta,

nan sultana bilkisu tagaishesa suka gaisa cike da mutunta juna, inda sultana sadiya taketa had’e fuska ita ala adole fushi take domin tun kafin yatafi saida sukayi ‘yar rigima akan zuwan da zaiyi neman ma Yarima suhail aure cike da 6acin rai suka rabu.

Dada tace har kun dawo kenan?
Sultan Abbas murmushi yayi yace eh ranki yadad’e gaskiya mutanen suna da mutunci sosai dan sun karramamu yadda yakamata, nan yake basu labarin irin tarbar da akayi musu yace ko da iyayenta masu k’aramin k’arfine ammah sunyi k’ok’ari sosai wajen ganin sun tarbemu a mutunce.

Sultana Sadiya ce tayi karaf tace au wai duk jin kan na yarima ammah akan d’iyar talakkawa yak’are?

Sultan Abbas murmushi yayi yace inbanda abinki sadiya ai talakka da me kud’i duk d’ayane.

Dada tace ina akwai banbanci domin bakowane talakka ake amince mawaba, ga yaron nan kaifi d’ayane ba a isa abashi shawara yad’auka ba.

ita dai sultana bilkisu tana saurarensu batace komai ba.

Sultana Sadiya tace ma dada Ranki yadad’e ai harda laifin mahaifiyarsa da ace tana yi masa magana ai da gyara.

Dada tace a’a kar kice haka rabani da suhail ni nasan halinsa natabbata ko itama bai zama dole yaji kowace maganartaba ni nasan halinsa.

Sultana Bilkisu murmushi kawai tayi, Sultan abbas yace ranki yadad’e aikin gama ai yariga da yagama addu’an zaman lafiya kawai za’ayi musu.

Dada tace hakane duk wad’annan surutan basuyi fatanmu dai kamar yadda kace sun karramaku toh muga karamcin da mutuncin atare da ita.

sultan abbas yace hakane ranki yadad’e, Sultana sadiya bahaka tasoba taso ace dada tahau tazauna tace ba zata amince ayi aurenba.

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_Yau page d’in mallakinkune ku kad’ai *Umm Abideen nd Queen Meenali* hak’ik’a ina muku so na hak’ik’a, chancantar kuce taja da haka_

Back to top button