Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 21

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*GARIN DAƊI……!*

 

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

*Wattpad:ummishatu*

21

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Sake buɗe idanuwa nayi da kyau ina kallonsa dan gaskata shi ɗin ne ko kuma wani ne me kama da shi tabbas Yaya Faisal ne, ko kaɗan ban nuna cewa na ganshi ba sai shine yake ta waiwayenmu bayan ya wuce mu, zuwa can ya sake dawowa, wannan karon bai wuce ba yayi mana sallama, ni kaɗai ce na amsa banda samz wanda ke riƙe da hannu na har lokacin,

“Kamar Widat ko?”

“Ehh nice” na bashi amsa kaina tsaye,

“Ashe haka kuka yi da madam ɗina…. Wallahi ban san ta turo miki wannan massage ɗinba tayi blocking ɗin ki sai jiya take faɗa min no wonder naga 2 days bana ganin ki online bana ganin status ɗin ki ashe blocking ɗin ki tayi bayan ta goge contact ɗin ki…. ”

” Ayya babu komai ai nayi tunanin ma ko kaine ”

” Haba haba wallahi bani bane, kuma da farko itace fa ta nuna min tana son in haɗa ku kuyi zumunci may be taje wasu sun zugota ne, dan Allah kiyi hakuri ”

” karka damu ya wuce, nima Allah ya bani nawa rabon gashi… ” na nuna samz da ɗayan hannuna wanda bai riƙe ba, kuma da biyu nayi dan Samz yafi yaya Faisal komai da ake buƙata wurin namiji, cikakken namiji ne har over matsalar shi ɗaya shi Christian ne,

“Masha Allah, Allah ya tabbatar da alkhairi” ya faɗa yana barin wurin, sai bayan da ya tafi sannan samz ya matsa hannuna yana tambaya ta,

“baby wannan waye?”

“Family friends muke dasu, a gidanmu ya zauna yayi karatu, da ya soni amma yanzu yayi aure shine matarshi take kishi dani”

“Kin fi matarshi kyau shiyasa take kishi dake….. I love you baby”

Lumshe idanuwa na nayi kafin na bashi amsa da,

“I love you too”

“Ki bani labarin ki pls…..”

“Labarina kamar yaya?” na buƙata ina kallon kyakkyawar fuskar shi, i mean komai da ya shafeki, abubuwan da kike so da wanda bakya so…. ”

Ɗan maƙale kafaɗa nayi kaɗan na turo baki tare da faɗin” uhmm… Kai ka fara ” murmushi kawai naga yayi dama nidai ban taɓa ganin fushinsa ba ko me nayi masa ko nace masa sai dai inga yayi dariya ko murmushi,

” Ai ni kin sanni sannan kin ɗan san abubuwa a kaina, abin da ya rage wanda baki sani ba babu yawa sosai….”

“To ka faɗa min wanda ban sani ba….” zuba min ido yayi kafin yace “Baby kece last born a gidanku?”

“no am second to the last, me ka gani and why did you ask?”

“kina da shagwaɓa, shagwaɓarki tayi yawa….I thought ko kece last born, shagwaɓarki na burgeni kuma tana yi miki kyau and tana ɗaya daga cikin abubuwan da nake so atare dake….. Soo keep it up”

Hararar wasa nayi masa sannan cikin turo baki nace “ni ai fushi nake yi dakai…. Kayi min laifi idan baka sani ba”

“Really? Haba baby”

“Ehh mana”

“ok am so sorry, laifin me nayi?”

“kuɗin da ka turo min na menene? Gaskiya nidai bana so ka daina idan har ba so kake yi in daina kula ka ba, dan idan ka cigaba da yimin kyauta irin haka zan fara tunanin ko da wata manufa kake sona….”

“no,no baby, kar kiyi min mummunar fahimta dan Allah, ina son ki da gaske ba da wani abun ba, ki fahimceni dan Allah”

“shikenan amma dai ka rage, kyautar tayi yawa”

Mun jima a wannan wurin muna hira saida muka ci muka sha sannan muka tafi tare har unguwar su Anty ya rakani daga nan muka yi sallama ya juya, daren ranar raba dare muka yi muna hira dan har 3 muka kai saboda shi wai baya baccin dare shiyasa na taya shi hira ranar duk da yana ta kora ta wai ya sallameni in kwanta in yi bacci amma naƙi tun yana ƙi har ya dawo ya haƙura hira ta fara daɗi yana ta bani labarin lokacin da yana school da irin ƙin jin da yayi lokacin, washe gari ai wuni nayi ina bacci, tun daga lokacin nima na koyi ƙin baccin dare dan hirarmu mai daɗi bata tashi sai dare yayi, cikin kwanakin da nayi a Abuja kafin na koma Kano munyi mutuƙar shaƙuwa dashi, satina ɗaya na koma gida, a ranar da na dira ƙawalli na zuwa na fara bata labarin samz da labarin irin son da muke yi wa juna,

“Lallai widat matsalar ki bata ƙarewa… Yanzu kuma ki rasa wanda zaki jajiɓo sai kafiri? Widat Christian fa, duk mazan duniyar nan hausa Fulani ki kasa samun wanda yayi miki har sai kin ɗauko Christian? To wallahi bari in faɗa miki gaskiya wannan guy ɗin ba don Allah yake sonki ba…. Akwai abin da yake so atare dake wanda da zarar ya samu keda shi za ku yi hannun riga…. Ke koda bayan kunyi aure ma wallahi ba abun yarda bane shi dan tsaf zai yi ƙoƙarin rinjayarki dan haka ki rufawa kanki asiri ki rabu dashi tun wuri tun kafin duniya ta sani ta fara zagin ki tana yi miki tofin Allah tsine….. ”

” Haba ƙawalli maimakon ki bani ƙwarin gwiwar yin soyayya dashi amma kece zaki yi discouraging ɗina? Ƴanmata nawa ya tsallake yazo gare ni? Sannan shi bada wata manufa yake so na ba da aure muke son junanmu ”

” Hmm ke yanzu ko ance ki auri wannan sai ki aure shi? Ƙazami manemin mata mashayin giya…. Uwa uba yaranki, suma zasu zama confuse saboda fsmilyn baban su kafirai ne na uwa kuma musulmi irin wannan ne ba fata ake yi ba zaki ga yara sun zama mix kuma ko bayan ya musulunta to ki sani wata rana zai iya komawa ruwa ”

” Samz baya bin mata kuma baya shan giya ”

” ta ya akayi kika sani? ”

“munyi maganar dashi kuma shida bakin sa ya faɗa min”

“hmmmmm kin taɓa ganin wanda ya faɗi laifinsa da bakin sa musamman a wurin da yake ganin zai iya rasa damarsa? Wannan samz ɗin ba mijin aure bane tun wuri ma ki sani, dan haka kiyi tunani” daga haka ta tattara tsarabarta da na kawo mata ta fita ta barni zaune tsumu tsumu kamar kazar da taji gishiri, gaba ɗaya ji nayi duniyar tayi min ƙunci komai ya tsaya min kuma bana jin dadinsa sannan sam bana cikin yanayi na farin ciki wannan dalilin ne ma yasa na kashe wayata nayi zaune cikin bedroom ɗina ina nazari tare da tunanin mafita……..

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

_*Ummi Shatu*_

Back to top button