Banana Island Hausa NovelHausa Novels

Banana Island 27

Sponsored Links

___________
Tunda suka isa gida barci kawai takeyi mai ƙunshe da damuwa ta rasa gane kan mijinta ,koda yaushe Sex ? Wani mutum ne wannan?

Sai wajen 2pm ya shigo ɗakin ganin still tana barci . Yasa ya sama gefen gadon ya zauna ya juya mata baya . Sarai taji shigowarsa Amma taƙi magana ,kuma bata motsa ba bare ta buɗe ido . Shima a ɓangarensa yasan tana jinsa don haka ya soma magana ƙasa²

“Iftihal na damu da damuwarki ,banajin dadin yanda nike takura maki Saidai halittana ne se*x halittana ne in fucking mace badly ,nasan I’m too selfish Amma wata kila Genesis ne wannan. I mean blood line dinmu haka Babana yake amma girma yasa ya sauya ƙila nima zan sauya….kiyi hakuri nasan bana maki adalci ,bayan kinyi barci momy ta kirani kuma tayi mun fada sosai akanki nasan ta fahimci abinda naso inyine a gaban surukanta maza da kannnena da iyayena ….Mrs mie bansan ne yasa ba nikan zama blind idan inason in fucking mace.” tsit tayi duk jawabinsa baisa tayi magana ba

“Yanzu ,do you like to go?”

Idonta a ƙulle tace “Ina ?”

“Gidanku mana”
Buɗe ido tayi gaba-daya sannan tace “Yes i do”

“Ki shirya in kaiki”
“Na rokeka ka Barni in bi commercial ,wallahi banajin dadin ko’ina ina yawo a jirgi nidai nafison mota ,banaso inje ma iyayena a matsayin superior”
***
4pm
Yasa aka kaita filin jirgin ,daga ita sai school bag da tarkacen kayanta da zata bukata a can
Mutane sunkai 20 wa’inda suka shiga jirgin,kowa kafin ya shiga zai nuna ticket ɗin sa a nuna masa inda zai shiga, kafin aka zo kanta,itama ta nuna nata tikitin maaikaciyar na ganin itace jiki na rawa tace tazo a kaita Vip .

Zumɓura baki tayi a ranta tace Adnan Yayi mun fuck up ,a jirgin ma sai ya nuna ma mutane Ni watace.

Kunna wayarta tayi ta tura masa “Gamu zamu tashi ,Nagode da abinda kayi mun amma zan zauna inda gama garin mutane suke ”

Minti biyu ya turo mata da amsa
“Me yasa kika kashe wayarki? Ki bat wayarki a kunne ,sannan kibi umurnin da na bada….safe journey”

***
Suna isa ta hadu da drivern mamanta ,yazo ɗaukanta mamaki abun ya bata don ita bata sanshi ba ,don haka tace bazata bishi ba ,saida ya kira wayar maman taji muryarta sannan ta biyoshi …..aikuwa tasha kukan murna don batasan Adnan ya sauya masu rayuwa ba har haka ,wai mamanta ne takeda driver? Ga mai mata gyaran gida da girki ,ga abinci a store available ,ga lafiya ya samu …..A sarari take jero ma Adnan Addu’a tana hawaye mamanta na amsa mata da amiin

Lafiyayyen tuwon semo aka kawo mata dukda ba’a san da zuwan taba ,miyan yaji nama da busashen kifi ,da kunun ayanta mai sanyi

Tunda aka shimfida mata ledan cin abincin ta zauna ta tasa abincikan a gaba ta kasa loma uku ,kawai tunanin rayuwarsu na baya suke ,a ranta tace ko Adnan baici darajan in masa biyayya saboda aurensa ba ,zan masa biyayya saboda mahaifiyata da ya sauya ma rayuwa .

Ƙarshenta dai barin abincin tayi ta wuce daki tayi wanka da sallah ta sauya kayan barci ta haye gado . Ta kashe lamp.

Ummanta data leka gidan harɗo duba jikin matarsa ta barta tana cin abinci ganin ta dawo Bataci wani abincin kirki ba yasa ta bita daki don taji dalili ,da sababinta ta shiga

“Ku ƴan boko bakucin tuwo sai rayis ko?” shiru tayi ganin dakin an kashe fitila ,tasan ta kwaso gajiyar hanya tabbas tan bukatar hutu. Saɗaɗawa tayi taje ta tofe mata jiki da addu’a ta ja mata bargo ta fita.

Itama tana fita Ifty ta buɗe ido ta tashi zaune tana cigaba da tunanika kala kala

A sanyaye ta lalubi wayarta ta tura ma Adnan sako
“Nayi missing ɗinka sosai ….kana kusa kuwa?”

Message ɗin ya shigo wayar Adnn ne daidai ya fita da abokinsa Faisal (Yaron shugaban kasan Canada…yazo Nigeria ne a matsayin yayi ma iyayensa yaji sun matsa masa ya fidda mata shi kuma yace baida ita su samo masa gashi duk wanda aka samo sai yace batayi ba ,sanadiyyar hakan ya gudo wajen abokinsa Adnan don ya samu rlf zuwa su huce don iyayen sunce Yina zubar masu da mutunci a wajen iyayen yaran da suke nemo masa )

“Gani na fito dinner da abokina”

Tana kwance ne tayi maza ta mike zaune ,in da bata daukan motsinsa a komai ynz tanaji saboda tasan Yina tsananin buƙatar mace kar rashinta ya sashi afkawa zunubi .

Da sauri ta tura msa da sakon “Wani abokin? ”

A daƙale ya tura mata “Dont worry about that”

Shiru tayi ta rasa wani amsa zata bashi don haka ta maida wayar ta ajiye .

Jin shiru shiru bata sake magana ba yasa ya nemo numberta ya soma kiranta ,Ifty tana kwance ta maƙalƙale kanta a pillow tana kuka sai ga wayarsa ya shigo wayarta

Kallon wayar tayi ta sharesa

Haka ya cigaba da kiranta ƙarshe ma ta sashi a Flight .
***
Next day

Wajen 11 ta shirya masu outing ita da mamanta ,wajen shan ice cream ta fara kaisu a motar da Adnan ya Bata ,coz tana zuwa ta ganshi pake an turo mata daga Lagos ɗin tun kafin ta iso ,ashe ita bata sani ba .

Zama sukayi a conducive waje suna jiran a kawo masu abinda suka hada ordern

Tana kallon maman tana bata labarin makaranta da rayuwar Lagos gabaɗaya.
Wayarta ne ya soma ɓurari .

Kallon wayar tayi ta sharesa
Umman a hankali tace “Dauki wayar mana” ta masa magana. Da fulatanci.

“Umma…” kafin tasan maganar da zata ce mata ta ganshi a gabansu,da drivern mama a gefenshi kenan shi ya kawo shi .

Masu wajen suna ganinsa sunga kudi gashi jar fata suka fara rawar jikin tambayarsa mai za’a kawo ,waigawa yayi ya kallesu ya fara hora ma’aikatan wajen da haɗaɗɗen turancinsa da suke tsintar kalmomin ciki da ƙyar,haka ya lissafo masu abinda yikeso wanda a ciki babu ɗaya da suke dashi sai ruwan Eva.

Don haka suka bashi hakuri suka wuce.

Umman Ifty haɗa ido da ƴarta tayi ta murmusa itakuwa iftyn ta daure fuska
“me kike ma murmushi” ta tambayeta da yarensu

“Kawai yayi mun ne ,surukina haɗaɗɗene” caɓe baki tayi saboda juyowar sa yayi kansu ,a mutunce ya gaishe da umman kafin Ifty tayi zaraf tace “Me ya kawo ka?” da turanci

A sanyaye yace “I come to see you”
(Nazo in ganki ne)

Umma cak ta mike tabi driver ɗin ta ya maida ita gida ,Yina ganin hakan ya murmusa yayi maza ya samu kusa da ita ya zauna ya daura hannunsa akan kujeran da ta jingina bayanta ya haɗe fuskarsu kusa da kusa ,shonewa tayi tai maza ta dauki abun ice cream din takai kusa da fuskarta zata sha ,hannu yasa ya amsa ya ajiye a gefen table ɗin da suke

“Ina bukatar natsuwarki” a tausashe tace “Yaya dinner dinku kaida friend dinkan?” dafe kai yayi

“Ayyah ,ya salam! Shiyasa kikaki daukar wayata ? I seemed so. Oya now , Namiji ne fa ,sunanshi Faisal Yaron président of canada…yazo wajena yesterdays late evening shikann”

Ajiyar zuciya tayi “Uhm na ɗauka macece” sa hannu yayi yaja tsinin hancinta

“To kinji ba hakan bane ba…tashi muje yau ranar farko kin sani na karya dokan zuciyata na hau mota ,saboda In ganki ,duk kin ruda Ni ,tnk god motar gidansu matata na hau nasan I’ll be safe” zaro ido tayi

“Really da mota kazo nan?” jinjina mata kai yayi ,jirgina na wajen gidanku zo muje ”

Kallonsa tayi “Bari insha ice cream ɗina mana”

“Ba dadi muje In din kikeso zan kaiki America kisha OG 1 ba wannan ba”
Batada zaɓi sai na ta bisa subar wajen

Suna fita car lot ya Mika mata hannu “Ban car key ɗin let me drive u”

“Taf ka manta yanda ake tuƙa mota wlh karka watsar damu a lalataccen titinmu na Gombe”

“ki bani ko In maki cakulkuli” da sauri ta miƙa masa tana murmushi ,tasan zaya iya

Driving yakeyi a kasaitance kamar ya samu titin gidansu ,ganin ya dauke titin fita wajen gari yasa ta tambayesa

“Ina zaka kaini?”
“Wait abit surprising ɗinki zanyi”
Lumshe Ido tayi “Kullum dama na saba amsar cluster of suprises”

Waigawa yayi ya kafeta da ido ,da sauri tayi masa pointing hanya

“Man ka kalli hanya kar ka watsar damu a kwalta ,nan ba titin jirgi bane da babu cunkoso”

“Kince na saba baki tarin mamaki ….any?”

“Yanzu haka ma a cikin mamakin nake kawai sai gaka dirif a Gombe babu notice!”

 

Oum Aphnan
09065990265️ _*BANANA ISLAND*_
_(Billionaire’s paradise)_

Book 3
Page *W*

Na…
Oum Aphnan ✍

Back to top button