Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 29

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_

 

*GARIN DAƊI…..!*

 

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

PAID BOOK #500

*Wattpad:ummishatu*

29

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Cikin farin ciki da ɗoki nake shaƙar iskar garina kuma tushena wato Kanon dabo tarin Allah, sai murna nake yi wadda ban san ko ta mecece ba amma ni dai na san ba murnar aure bace,

Lokacin da naje gida tun daga ƙofar gida na san anyi gyara na musamman a gidan domin gashi nan ya sha sabon fenti ko ina an gyareshi tsaf, ƙawalli tana gidan dan haka rungume juna muka yi muna tsalle yaya Abdul Hakim da fitowarsa kenan daga sashen Annie ya bimu da harara wadda ba mu san ma yana yi ba, sakina tayi tana ƙare min kallo sakamakon canjawar da nayi nai ƙiba da haske saboda supplements din da Anty ke bani na gyaran jiki da sauran abubuwa ita kanta bata san yawan kuɗin da ta kashe ba wurin gyara ni tun daga kan su dilke, magungunan infection, na gyara fata da dai sauran su,

“Tabdijam…… Samz zai kwashi lagwada….” ta faɗa a hankali ta yadda wani ba zai jiyo ta ba, harararta nayi nace “ya ranki”

“Wataƙila daren ranar da aka kaiki ki samu ciki ƙawalli…..”

“Ta Allah ba taki ba ƙawalli……insha Allah sai bayan shekara biyu zan haihu”

“a wannan samz ɗin naki zaki kai shekara biyu baki haihu ba?”

Kallon yanda ta riƙe haɓa kamar wata tsohuwa nayi dariya nayi nai gaba abina ta biyo baya na, gani nayi gaba ɗaya ƴan gidanmu sun zama busy dan ban samu mama agida ba wai sun fita kasuwa ita da Anty Salaha sai iya Annie kaɗai da sauran abokan arziƙi wadanda suka zo ganin kaya dan har yau ba agama zuwa kallo ba, ni dai ko ta kan kayan ban bi ba sai wadanda aka dinko min su na dudduba ciki harda wanda zanyi fitar biki dasu na kamu da dinner, ƙawalli ke tsara yanda shigar tawa zata kasance, ni dai duk jikina yayi la’asar da ganin dagaske gidan zan bari in tafi gidan samz ada babu abin da nake so irin maganar aure na dashi amma ahalin yanzu idan ƙawalli tayi min faɗa ma muke yi ita kuma tunda ta gane shikenan bata da aiki sai tsokana ta, gaba ɗaya ji nake auren ya fice min arai kamar a sake ƙara watanni amma na san hakan ba zata taɓa faruwa ba, ƙawalli na kalla dake ta haɗa min kaya na wuri ɗaya ina daure da towel da hijabi a jikina fitowata kenan daga wanka,

“yaushe angon zai shigo ne?”

“oho masa ni na sani ne” na bata amsa ina ƙokarin zama gefen gado, dariya naji ta fashe da ita,

“ohh Allah me iko wai ashe dama zanga widat haka? Ashe wannan ranar zata zo da zata rinƙa jin tsoron Samz”

“Wallahi ji nake inama a ɗaga…..” na faɗa ƙwalla na taruwa acikin idanuwa na dan duk da ina sonsa yanzu ji nake bana son haɗuwarmu kwana kusa balle har mu zauna inuwa ɗaya,

“ai idan aka ɗaga ina jin sai an baki gado a asibiti…. Mutumin da kike ta jinya a kansa yanzu kuma kice wai so kike a ɗaga….”

Ban sake tanka mata ba kawai na fara kuka, lallashi na ta fara tana cemin to kuma menene abin kuka har itama ta fara a haka anty ta shigo ta same mu,

” kin jimin yara da shashanci kunzo kun zauna kun ƙule a ɗaki kuna kuka kamar waɗanda aka yiwa mutuwa…. Dan Allah ni karku ɓata min lokaci ungo ku zaɓa…..”

Wayarta ta miƙo mana, decorations ne kala kala take son mu zaɓi kalar wanda za ayi, ƙawalli ce ta zaɓi wani kamar na gargajiya gargajiya amma yayi bala’in kyau, karɓa anty tayi tana cewa,

” Ranar kamun wanne kaya ma zata saka? Ungo ku zaɓi na dinner ”

“Golden ne Anty” ƙawalli ta bata amsa, sake zaɓar na dinner ɗin tayi ta miƙa mata wayarta ta fice ta barmu kamar yadda tazo ta same mu, kafin kace mi har magriba tayi wanda hakan ke sake tada min da hankali,

Bayan tafiyar ƙawalli ɗakin mama naje muka zauna tana ta haɗa kan kayan da ta siyo na amfanin kitchen wanda za a tafi dasu jere gobe laraba ranar Alhamis za ayi kamu juma’a dinner asabar kuma za a ɗaura aure ayi yini akai amarya ɗakinta, duk ji nake kamar inyita kuka har sai an fasa bikin nan yanzu Ala basshi nan gaba sai ayi, shi kansa samz ɗin yanzu bana doguwar hira dashi dan gaba ɗaya haushinsa nake ji daga ya kirani zan tambayi menene sannan ina gama bashi amsa zan kashe wayata, ba wai laifi yayi min ko daina sonshi nayi ba a’a haka kawai nake jin bana son kusancinmu dashi, duk da hakan da nake yi masa shi baya zuciya ya kan kirani kamar yadda ya saba, dan ko yanzu da na zo kwanciya saida ya kirani amma nace bacci nake ji, cewa yayi to shikenan in kwanta in yi, kashe wayar nayi gaba ɗaya ina ta juye juye nama kasa baccin gaba ɗaya, daga ƙarshe hijabi na nasa na fita, sashen Annie na shiga na buɗe ɗakin bishra wacce ke kwance tana bacci sakamakon zirga zirgar da itama tasha yau, kusa da ita naje na kwanta naja bargo na lulluɓa sai hawaye, na jima ina zubar da hawaye kafin bacci ya ɗauke ni wanda bani na tashi ba sai bayan asuba irin ƙarfe 6 ɗin nan wannan ɗinma anty ce ta shigo da ban san ranar tashin mu ba daga ni har Bishran, ɗakina na koma nayi wanka a gurguje bayan nayi salla, sama sama nayi breakfast sannan na tafi gidan ƙunshi nida Anty wadda tayi dropping ɗina sannan ta wuce kasuwa ta can kuma zata wuce gidana, sai bayan da aka gama min ƙunshin sannan ƙawalli ta sameni a gidan,

“Rangaɗi…. Amarya komai naki na dabanne… Gidanki mai kyau wallahi….”

Shiru nayi mata dan bana son jin zancen gidan nan hankalina tashi yake idan naji an ambaceshi, ƙunshin aka yi mata itama amma iya baƙi saɓanin nawa da aka haɗa harda ja na seletif, bayan azahar muka bar gidan ƙunshin muka koma gida yau dai nafi ganin gudun yinin fiye da na kowacce rana dan kafin ƙiftawa da bismillah har magriba sunyi kuma sai lokacin ƴan jere suka dawo kowa yana santin gidana, daren ranar kasa bacci nayi dan haka na tashi na koma cikin su Anty waɗanda ke falon mama suna aiki, kan dugowar kujera na kwanta anan nai bacci dandanan kuma naji gari ya waye kuma a ranar aka fara gudanar da biki, shi dai ango bai zo ba yace sai ranar Juma’a zai dira wanda ni hakan ma yafi min.

Tunda garin Allah ya waye bayan na dawo daga gyaran gashi ake kwaskware ni ana sake kwatalle ni dan wata me gyaran jiki ta musamman Anty ta kirawo wacce tazo ta sake gyara min fatata gyaran da yafi na baya sannan ta turare min jikina da wani turare wanda ya sha haɗi na musamman nan take fatata ta kama ƙamshin gam ta riƙe sai zuwa yamma na samu kaina hannun matar nan bayan ta sakani nayi wanka da wani ruwan turare, me kwalliya ce ta zo itama ta fara nata aikin babu jimawa kamanni na suka canja na tashi daga widat ɗin da aka sani na koma kamar wata balarabiya ko ƴar India, kayana milk colour ne amma an sirka da golden haka takalmi da yar jakar da na riƙe da gwaggoro na duk golden, sai bayan da aka gama ɗaukata hotuna sannan aka sakani a mota muka nufi wurin kamu dan Anty sai waya take iyowa wai mutane suna jirana, faɗin irin kyawun da nayi da irin kuɗin da aka kashe ɓata bakine da ɓata lokaci, anci an sha haka kuma an sha hotuna, dangin ango suma sun zo matar uncle ɗinshi Anty Amina da wasu mata su biyar sai bayan da aka gama kamu sannan suka tafi, duk na gama gajiya da zaman nan da tashi, bamu muka bar hall ɗinnan ba sai 8 saura shiyasa a mutuƙar gajiye na koma gida, ranar kam da wuri nayi bacci. Washe gari ango ya baƙunci Kano dan tun 1 ya kirani yake sanar dani ya sauka shida abokinsa Ahmad dan anan ma suka yi sallar juma’a, kamar jiya yauma wuni aka yi ana hidimtawa fatata har tsawon wani lokaci ga uban ƙamshi da ake manna mata babu ƙaƙƙautawa, tun kafin magriba na isa gidan kwalliya nida ƙawalli amma can ta tafi ta barni, har bayan ishah aka kai ana yimin kwalliya salla ce kaɗai ke tadani, kwalliyar yau ai har tafi ta jiya kyau da matsayi domin yau ne na fito a asalin bride, ƙamshi kuwa ai ba a ma magana dan ta ko ina tashi yake, misalin ƙarfe 8 daidai suka zo ɗaukata, babu kowa atare dasu daga shi sai abokinsa, komai nawa blue sai ɗan ratsin silver kaɗan saboda takalmi na da pose ɗina duk silver colour ne da sarka da earrings harda zobuna da agogo duk silver, a hankali nake tafiya saboda tsinin takalmin ƙafata gashi rigar ta baya tana jan ƙasa, ganin ina ƙoƙarin fitowa ya buɗe motar ya fito sai lokacin na ganshi bayan tsawon kwanaki rabona da shi, shima blue ɗin shadda ya saka mai kyau da tsada harda hula itama blue dama ba ƙaramin kyau manyan kayan ke yi masa ba to kyawun yau har yafi na kullum,

“Baby….” yace dani bayan ya ƙaraso kusa dani,

“zo ka riƙe min rigata ta baya dan Allah”

Matsowa yayi dab dani nan muka shaƙi ƙamshin juna,

“why not in ɗauke ki maimakon riƙe miki riga ai kamar zai fi ko….”

Tun kafin in bashi amsa naji ya tarairaye ni ya ɗaukenin zuwa inda motar su take, bani da zaɓi illa in lafe cikin jikinsa,

“Ya biki? Kin gaji ko?”

Kai na ɗaga masa cikin shagwaɓa ina ɓata fuska kamar zanyi kuka,

“Ayya… Am soo sorry baby”

“Ahmad buɗe mana ƙofar nan pls”

Sai lokacin naji kunya ta kama ni da naga abokin shi ya fito ya buɗe mana ƙofar baya, ji nayi kamar inye me dan kunya, sakani yayi ya rufe ƙofar sannan ya zagayo ta ɗaya ɓarin shima ya shigo, hannuwana ya kamo cikin nasa masu mutuƙar ɗumi da laushi wannan dalilinne yasa sau tari idan ya riƙe hannuna bana iya ƙwacewa hannunshi is very soft and warm, jana jikinshi yayi yana raɗa min,

“matso muyi sirri kar Ahmad yaji mu…”

Banyi magana ba illa kallon fuskar shi da nayi wadda tasha gyara tun daga sajenshi zuwa gemunsa, rungume ni yayi sosai a jikinsa yana yimin raɗa,

“kinyi kyau baby…. You look… Just amazing….. Let me snap u” ya faɗa yana ciro iPhone ɗinshi daga aljihu ya ɗaukeni sannan yayi mana nida shi,

“kaima kayi kyau” na faɗa murya ta na rawa, hannunnshi ɗaya na riƙe da nawa ɗayan kuma na gadon bayana yana wasa da zip ɗin rigata cikin wayo da dabara yake sauke zip ɗin bai san duk ina ankare dashi ba, wuya na zai yiwa kiss na yi saurin toshe bakin sa da hannu na, da ido yake tambaya ta wai why? Raɗa masa nayi,

“Zaka karya alƙawarinmu…. We promised ourselves sai bayan munyi aure”

Kanshi ya ɗaga sama sannan ya ƙwace bakin sa daga tsohewar da hannu na yayi masa,

“amma ai ba zaki hanani wannan ba….” ya faɗa yana sauke zip ɗin rigata a hankali ta yadda Ahmad ba zai ji mu ba,

“ni dai a’a wallahi… Is part of our promised” na faɗa ina riƙe hannunsa,

“Oh my God…” ya faɗa yana kallo na da shanyanyun idanuwansa wanda yau suka fi kullum shanyewa, saukar da nawa nayi ƙasa daga cikin nasa, gadon baya na yake shafawa yana faɗin,

“please baby…..”

“Naƙi wayon” na faɗa cikin raina ina maƙale masa kafaɗa, duk yadda yaso ya min wayo ƙin yarda nayi sai wani marairaicewa yake yi yana lumshe min ido amma naƙi furr tunda har yanzu ba a ɗaura mana aure ba sai zuwa gobe, ƙyaleni yayi kuma yayi shiru ya daina roƙo na may be fushi yayi wanda sam hakan bai ɗaɗani da ƙasa ba, kuma duk da ya daina kulani hakan bai sa na bar jikinsa ba dan kamar mage haka nake idan na samu jikinsa, kaina kan kafaɗarsa na zagayeshi da hannuwana duka biyu na maƙale, bai ƙara kulani ba sai hirarsu da suke yi shida abokinsa da kuma waya da yake amsawa jifa jifa a haka har muka ƙarasa event center ɗin da dandazon ƴan uwa da abokan arziƙi keta dakon zuwan mu……….✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_

Back to top button