Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 14

Sponsored Links

page 1⃣4⃣

Zarah ko da tashiga gida d’akin mama tashiga ta tarar da mama tana linkin kaya ganin zarah yasa tasakarmata murmushi tare da cewa ‘yan makaranta andawo?

zarah ma murmushi tayi tace eh mama dafatan mun sameki lafiya?

mama tace lafiya lau, nan zarah takama mata suka cigaba da linke kayan, cike da nutsuwa zarah tad’auko kud’in tamik’a ma mama tace mama ga kud’in da kuka bani.

mama da mamaki take kallonta tace zarah ya haka? ya naga kin maido kud’in?

murmushi zarah tayi tace mama daman da naje inbiya shine akace malam bello ya biyamin kuma na kai masa kud’in yace bazai kar6aba shi dan Allah yayi min nayi-nayi yakar6a ammah ya k’i.

mama tace Allah sarki gaskiya yana d’awainiya dayawa mungode sosai Allah dai yabiyasa, yanzu kud’in ki aje wajenki kinga sai kiyi anko d’in da su,

zarah tace toh mama nagode sosai Allah yak’ara girma da rufin asiri.

mama cike da jin dad’i tace Ameen ‘yar albarka nidai fatana a kullum Allah yakawo muku mazaje nagari kuyi aure.

zarah dagudu taficce tabar d’akin cike da jin kunya, mama dariya tayi sannan tacigaba da linkin da takeyi.

 

tun ana saura kwana hud’u ayi walimar aka bugo Invitation card aka gayyaci mutane da dama daga cikin wanda aka kaima katin gayyata har da maimartaba.

 

A gidansu zarah suma shirye-shirye suke daidai k’arfinsu, Abbah bakin gwalgwado yasiyo mata abinda zata raba ma abokanta da ‘yan uwa.

 

malam Bello ma ba’a barsa a bayaba domin carton din lemu yasiyamata yakai mata dakyar yasamu zarah takar6a.

 

ana gobe za’ayi walimar gidansu zarah tun dare aka fara shirye-shiryen abinda za’a raba ma mutanen da suka gayyata kasancewar da k’arfe goma za’ayi walimar.
_______________

yarima tun daga lokacin yafita harkar sumayya ganin tana neman rainasa akan hak’insa yasa yajefar da ita gefe yacigaba da hidimarsa, sumayya tun tana daurewa itama taji bata iya daurewa.

yau ma kwance take tana ta juyi saman makeken gadonta tsaki kawai takeja tana neman mafita, chan tayi nisa tace daman ace zinat zatazo da nad’an samu sauk’in abinda nakeji, ammah bari inkirata ko ta flight ce tabiyo tazo yau, wayarta tajawo takira zinat ammah kashe wayartake,

tsaki sumayya taja tare da wullar da wayar tace matsalata da ita kenan ayita nemanta ba’a samu.

 

Sultana Bilkisu ce zaune a turakarta tana kallon wata drama a faskekiyar TV d’in da take manne a bangon d’akin, gefenta kuyangine zaune k’asa suna jiran jin umurni daga wajen mai d’akintasu.

Sultan Ahmad ne yashigo da sallamarsa dasauri duk suka zube suna kwasar gaisuwa, cike da fara’a ya amsa musu, nan suka tashi suka ficce daga d’akin ahankali yataka yaje inda matarsa take zaune tazuba masa ido fuskarta d’auke da murmushi,

shima murmushin yayi tare da zama kusa da ita, rik’o hannunsa sultana bilkisu tayi cike da kulawa tace daddynsu suhail barka da dawowa muje daga ciki.

sultan Ahmad tallabo fuskarta yayi yace sultana ai banje ko’inaba yau ina fada daga chan naje wajen dada munata shan hira.

Sultana Bilkisu tace Allah sarki, ya wajen memartaba duk kwanan nan bamu gaisa da shiba duk lokacin da zanje gaishesa toh yana chan fada.

sultan Ahmad yace lafiya lou, daman nima sawa yayi aka kirani yayi min magana akan wata walima da aka gayyacesa shine yace ni inwakilcesa inje tunda gobene zaya fita, kuma babu dad’i ace babu Wanda yaje daga wajensa.

Sultana Bilkisu tace tabbas hakane k’ara ko kaine kaje, murmushi sultan yayi yace ai tare da ke zamuje goben, yarima ma zan kirasa domin yashirya muje tare.

Sultana Bilkisu cike da farin ciki tace Allah yakaimu da rai da lafiya.

Sultan Ahmad yace Ameen, taso mushiga daga ciki akwai maganar da nakeson muyi,

dariya Sultana Bilkisu tayi tace kai Abban suhail kawai dai kace mushiga ciki ammah nasan babu wata magana da zamuyi.

 

 

wanshekare chan makarantarsu zarah cike take mak’il da mutane, daga wajen islamiyyar aka kafa rumfuna inda daga tsakiya aka tanadi wajen da za’a gudanar da walimar.

Rumfa d’aya aka fitarma da Yarima Suhail, Sultan Ahmed da Sultana bilkisu dukkansu sanye cikin kayan alfarma sai dogarawansu da kuyangi da suka zagayesu, nan aka cika musu gabansu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,

shi dai yarima suhail tun da yazauna dannar wayarsa kawai yake ko da sau d’aya bai d’ago kai ba, domin tun da yazo yaga anzuba masa ido mata da maza suna kallonsa saisa yajawo wayarsa yashiga dannawa.

 

inda daga bisani mai gabatar da shiri yafita yafara bayan ankira shugaban makaranta ya bud’e taron da addu’a nan aka fara gabatar da kowa, bayan angama aka fara kiran d’aliban da zasuyi walimar da d’ai-d’ayansu suna fitowa sugabatar da karatu.

Daga chan gefe nahango zarah da k’awarta khairy zaune cikin anko d’insu sunsha dogayen hijab d’insu.

zarah kallon khairy tayi da take ta kalle-kalle tazungurota tace ke wai mekike kallo tun d’azun kin zuba ma waje guda ido?

Murmushi khairy tayi tace wlh wancan yarima din nake kallo ya burgeni sosai kiduba kiga yadda ya hakimce, harararta zarah tayi tace kekuma rashin aikinyi miye abun kallo, ke nifa tunani nake anya zan iya fita inyi karatun nan? wlh jikina yayi sanyi sosai kuma nasan ganin mutanen da nayine.

Dariya khairy tayi tace nifa tsiyata da ke tsoron mutane gareki, kidaure kisa ma ranki babu kowa wajen insha Allahu zakiyi karatunki batare da fargaban komai ba.

zarah murmushi tayi tace nagode sosai khairy Allah dai yasa zan iya.

khairy tace Ameen.
kiran khairy da akayine yasa tamik’e tanufi filin tazauna bisa kujerar da aka tanadar masu nan aka mik’a mata lasifika tafara karatu.

tunda aka kira khairy zarah hankalinta ya tashi sosai nan gabanta yashiga fad’uwa, addu’a tashiga yi cikin zuciyanta ahankali taji nutsuwa tazo mata.

bayan khairy ta gama kiran sunan zarah aka yi, k’in tashi zarah tayi saida aka maimata kiranta sannan tamik’e ahankali tana tafiyarta a nutse, duk wanda yake wajen kallonta yakeyi yanayin yadda take takunta a nutse ta sadda kanta a k’asa ahaka ta isa filin taron tazauna, nan aka mik’o mata lasifika.

amsa tayi nan tad’anyi shuru na d’an minti biyu saida tasaita nutsuwarta sannan tafara karatun cikin muryarta mai dad’in saurare inda take karanta suratul bak’ara daga izif na ukku _Sayak’ulus-sufaha’u minan-nasi ma wallahum ank’iblata humullazi kanu alaiha_…… cike da nutsuwa take karatun, wajen yad’auki tsit kowa saurarenta yakeyi, yarima suhail tunda aka fara bai d’ago yakalli kowaba ammah lokacin da zarah tafara ji yayi yanason ganin wadda ta mallaki muryar, ahankali yad’ago kansa yasafke idonsa akan zarah da take karatu a nitse, kallo d’aya yayi mata yajanye kansa bai k’ara kallontaba har tagama sannan tamik’a lasifikar tare da mik’ewa tabar wajen.

gaba d’aya aka d’auki kabbara daga nan aka cigaba da kiran saura suna fitowa sunayi har aka gama.

bayan angama aka kira wasu daga cikin d’alibai sukayi drama ta larabci, da suka gama aka kira zarah tayi tafsirul alk’ur’ani kowa na wajen ya jinjina mata, da tagama nan aka d’auki kabbara, yarima suhail magana yayi ma iyayensa sannan yasa aka kira masa shugaban makarantar yadamk’a masa kud’i daganan yawuce yashiga motarsa yabar wajen.

daga bisani aka fara raba kyautukan da aka tanadar ma wad’anda sukayi walimar.

ko da akazo kan zarah, Sultana Bilkisu ce akakira tazo tabata itama ta azamata kyauta ta musamman sannan akayi musu pic’s.

zarah har da k’wallarta ganin kyautukan da tasamu dan ko na makaranta kusan guda ukku tasamu sannan wanda mutane sukayi mata.

 

bayan angama raba kyautuka nan akayi d’an bayani sannan aka rufe taro da addu’a aka fara watsewa,

sultana bilkisu kallon d’aya daga cikin kuyanginta tayi tace taje tatafo mata da zarah,

ko da taje tafad’ama zarah zarah bata musaba tabiyota.

tun da suka tafo sultana bilkisu tazuba mata ido ganin yadda take tafiya a nutse har suka iso nan zarah taduk’a ta gaishesu, cike da fara’a Sultan Ahmad da Sultana Bilkisu suka amsa mata, sultana tace ‘yanmata ya sunanki?
ahankali tace zarah,
sultana tace nice name, nan sultan Ahmad yad’auko 50k yabata.

cike da ladabi zarah ta amsa tare da yi masu godia sannan tawuce tabar wajen itadai Sultana Bilkisu binta kawai take daga kallo daga bisani suka tashi suka koma gida.

 

Zarah tattara mutanenta tayi tatafi dasu gisansu tabasu abinci na musamman sannan taraba musu kayan da tatanada, ita kanta ta jinjina ma ‘yan gidansu ganin namijin k’ok’arin da sukayi dan sufitar da ita kunya, bayan anci ansha nan aka watse kowa yana murna.

nan zarah tad’auko kyautukan da tasamu taba iyayenta nan aka bud’e ana gani ana murna, kud’in da tasamu tadamk’a ma iyayenta rabi, sauran taraba taba ‘yan uwanta rabi tad’auki sauran rabin, nan sukayi ta mata godia,

 

___________

Sultana Bilkisu ce zaune gefen Sultan Ahmad suna hira chan ta nisa tace Daddyn suhail wlh walimar da mukaje ta burgeni da alama makarantar akwai karatu sosai.

murmushi sultan Ahmad yayi yace nima ta burgeni sosai

sultana bilkisu tace ka san wani abu wlh yarinyarnan ta yi min sosai,

sultan murmushi yayi yace ai naga alama saisa kika aika aka kiramiki ita,

sultana bilkisu d’an guntun murmushi tayi tace inama yarima ya amince ya aureta, wlh da naji dad’i domin daga ganinta kasan ta fito daga gidan mutunci wlh inason yarinyar takasance surukata, kallon sultan Ahmad tayi taga yana ta dannar remote yana canza channel, hannu takai taruk’o remote d’in nan yajuyo yakalleta kwallah duk ta cika mata ido.

sultana bilkisu murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace daddyn suhail nasan sumayya d’iyar d’an uwankace ammah kataimaka ka amince da yarima ya auri zarah domin inaji ita alkhairi ce, ina ji ajikina aurenta zaisa yarima yasamu nutsuwa da kwanciyar hankali.

sultan Ahmad rik’e hannun sultana yayi yace Bilkisu ba wai na k’i bin maganarkibane kawai dai ina tsoron abinda zaije yadawo, kina tunanin suhail zai amince yasota? kina tunanin su memartaba zasu aminta da hakan?

murmushi sultana bilkisu tayi tace insha Allahu zasu amince yarima bamuda matsala da shi domin mu muka haifesa, indai su memartaba sun amince toh komai ya yi daidai, kabani izini inje gidansu yarinyar mugana da iyayenta inyaso daga baya sai muyi tunanin yadda zamu 6ullo ma lamarin.

dogon numfashi sultan Ahmad yaja yace toh tayaya kike tunanin zasu amince batare da ansha wuyaba?

murmushi sultana tayi tace kafara bani izini inje gidansu yarinyar ingana da iyayenta, muji idan zasu amince mana subamu aurenta.

shima sultan murmushi yayi yace nabaki izini Allah dai yashige mana gaba.

cike da jin dad’i sultana tace Ameen.

 

_*BAYAN SATI ‘DAYA*_

Sultana Bilkisu ce naga tayi shiga ta alfarma ta yi kyau sosai bayanta kuyangi biyar ne suka take mata baya, wajen wata dank’areriyar mota daga cikin jerin motocin ukku da take tsakiya naga ta nufa tunkan ta isa aka bud’e mata baya, dan haka tana shiga aka maida aka rufe.

kuyanginta d’ayar motar suka shiga nan aka tada motar, dasauri maigadi yahangame musu k’aton gate d’in suka fita daga Amir palace.

bayan ‘yan mintina suka isa islamiyyarsu zarah,

a mota sultana bilkisu tazauna tatura dogari yaje yayi mata magana da shugaban makarantar.

bayan kamar minti ukku sai ga dogarin ya fito bayansa shugaban makarantane yana ta zuba sauri.

duk’awa yayi yana gaishe da sultana bilkisu cike da fara’a ta amsa, nan kuyangi da dogarawa suka d’auka sultana ta amsa gaisuwarka kaima angaisheka,
sannan sultana tace inason k’arin bayani akan d’alibarku mai suna zarah musa.

dasauri d’aya daga cikin dogarawan yace sultana tanason sanin wacece ita, ina ne gidansu.

shugaban makaranta washe baki yayi yace toh toh zarah musa ai gidansu yana chan gaba da nan kad’an.

sultana bilkisu signal tayi ma driver da ido.

driver yace yimin kwatancen gidan yadda zan gane, nan shugaba yayi masa kwatance saida yafahimta sannan yaduk’a yace angama ranki yadad’e

sultana bilkisu kallon kuyanga tayi tace tamik’o mata jakkarta, dasauri kuyanga tamik’o mata nan sultana tad’auko bandir d’in ‘yan 1k tamik’a masa tace ga wannan kun k’ara wajen hidima.

jikin shugaba yana kyarma ya amsa tare da duk’awa yana godia nan suma dogarawa suka hau yi ma sultana godia.

sultana izini tabada aka tayar da motar suka kama hanyar gidansu zarah.

ko da suka isa driver tsayawa yayi yatambayi wasu matasa da suke zaune a majalisa, basusha wahalar gane wadda yake nufiba kasancewar kusan kullum zarah ta gabansu take wucewa taje islamiyya kuma tadawo, sukace yak’ara gaba kad’an yashiga hannunsa na dama gida na ukku, nan yayi musu godia sannan sukacigaba da tafiya.

 

A k’ofar gidansu zarah yayi parking, daidai lokacin malam musa ya dawo gida, ganin dank’areriyar mota k’ofar gidansa yasa mamaki yacikasa dasauri ya ida isowa, daidai lokacin driver yafito daga motar, malam musa sallama yayi mashi yace wani gida kuke nemane?

driver yace eh gidan su wata zarah musa.

malam musa yace toh toh ai nan ne nine mahaifinta.

driver zuwa yayi daga bayan mota yayi knocking d’in glass d’in, jin knocking yasa sultana bilkisu tawane glass d’in.

driver duk’awa yayi yace ranki yadad’e nan ne ga ma mahaifinta nan.

sultana bilkisu kallon mahaifin zarah tayi dasauri shima yaduk’a yagaisheta domin yanayinta kawai da yagani da dogarawan da suke tare da ita yasa yagane daga babban gida take.

sultana bilkisu cike da fara’a ta amsa.

malam musa yace ranki yadad’e ko dai wata zarah d’in ce kuke nema?

murmushi sultana tayi tace zarah dai taka, munaso kayi mana izini mushiga ciki sai mutattauna abinda yake tafe da ni.

malam musa jikinsa yana 6ari yace bismillah kushigo,
dasauri dogarawa sukazo suka bud’e mata murfin motar tafito nan kuyangi suka take mata baya, akabar dogarawa tsaye wajen motocinsu,

malam musa yana gaba har cikin gida, suna shiga yafara k’walama mama kira yana zainabu! zainabu!!

dasauri mama tafito daga d’aki tana malam lafiya? ganinsa tare da wasu mata yasa tayi tsaye tana malam bak’i mukayi?

malam musa yace kinyi wani tsaye kiyi sauri kid’auko musu tabarma mana, ina yarannan suke? .

mama tace basunan sunje gidan kitso sannan takoma d’aki tad’auko sabuwar tabarma tazo ta shimfid’a tace bismillanku.

sultana zuwa tayi zata zauna dasauri kuyanginta suka k’ara kakkafe tabarmar suna cewa ranki yadad’e azauna lafiya sarauniya, bayan ta zauna nan kuyanginta sukayi tsaye gefenta.

ganin haka yasa su mama suka ida fahimtar koma daga ina wannan tafito toh motar wani babbace, Dan haka mama tazo taduk’a tagaisheta.

fuskar sultana d’auke da murmushi ta amsa, nan kuyangi suka d’auka ‘sultana ta amsa gaisuwarki kema angaisheki’

malam musa jikinsa yana 6ari yace bari inje insamo musu ruwa susha.

sultana murmushi tayi tace kabarsa nagode kazauna kawai muyi magana akan abinda yakawoni.

dasauri mama taje tad’auko wata tabarmar tashimfid’a ita da malam musa suka zauna.

sultana kallon kuyanginta tayi tace mero kubamu waje zamuyi magana.

dasauri duk suka zube sukace angaisheki sultana atashi lafiya sannan suka tashi suka bar wajen.

sultana kallonta tamaida ga su malam musa tace kune iyayen zarah ko?

malam musa da mama sukace eh ranki yadad’e .

sultana bilkisu tace toh Alhmdllh ni matace ga d’an sarkin garin nan, agaskiya ba zan 6oye mukuba tun lokacin da mukaga d’iyarku wajen walimarsu da sukayi a islamiyya nan muka ganta kuma mun yaba da halinta da tarbiyarta dan haka muke neman ma d’anmu *yarima suhail* aurenta.

ba mamaba hatta shi kansa malam musa ya firgita a tsorace suka d’ago kai suka kalli juna jin an anbaci yarima suhail Wanda suke jin sunansa a bakin mutane, dasauri suka maida kallonsu ga sultana bilkisu,
atare suka had’a baki sukace zarah ta auri yarima suhail?

sultana gyad’a kai tayi tace indai kun amince zaku bamu aurenta.

shuru sukayi na d’an lokaci sannan malam musa yace ranki yadad’e kiyi hak’uri gaskiya ba zamu iya amincema buk’atarkiba…….

 

_*Comments d’inku shine k’warin gwiwana Indai babu more comments toh hakan zai tabbatar min da baku tare da ni dan haka nima zan dakata da rubutawa daga wannan page d’in, dan haka muje zuwa*_

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_*Jinjina agareki My Dala inaso kisani akoda yaushe ina ji dake*_

 

_Sak’on gaisuwa agareka *Mu’az* a duk inda ka kasance wannan *page* d’in mallakinkane kayi yadda kakeso da shi nagode sosai da kulawa_

 

Back to top button