Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 54

Sponsored Links

Hajiyarsu amira ce zaune afalo tagama list din abubuwan da zata aiki amira kasuwa , fitowa amira tayi daga dakinta sanye da riga da wando ta daura after dress baki akai tayi rolling din gyale akanta tayi kyau sosai,se turo baki takeyi, kama baki hajiya tayi tana kallon amira dake turo baki gaba tace ” to ba baki za ki turo ba ! Ko wuya zaki turo sekinje kasuwar nan yauwa” kamar amira zatayi kuka tace ” hajiya yanzu da yamman nan zakice min inje kasuwa kibari gobe da safe” ” to ban bari ba ga kudin nan da list, in kin gadama kije ” cewar hajiya . Daukar kudin tayi tasaka ajaka da paper tafito , tana tsaye abakin titi tana jiran masu napep se ga motar ya al ameen ya tsaya agabanta yasauke glass , kallonta yayi yace” yar kanwa ina zuwa haka ?” turo baki tayi tace” hajiya ce ta aikeni kasuwa ” ganin yanda take ta babbata rai ne ya bashi dariya yace mata ” shigo muje ” bude murfin motar tayi ta shiga tace ” ya al ameen ina wuni ?” amsawa yayi da fara’a akan fuskarshi yace ” wata kasuwa kenan ?” ” Main market ” okay yabata amsa kafin yace” nikam yar kanwa yaushe ne zamusha bikinki ne ?” dariya tayi sosai dan tambayar yabata dariya tukun tace ” ya al ameen Allah kaban dariya ! Tom ba yanzu ba tukun dan yaron abokin daddy da muke soyayya dashi mun rabo dan bashida dabi’a me kyau , shisa ni yanzu bazan sake bawa ko wani na miji dama ba tukun gudun kar abatamin lokaci , se na gama karatu tukun ” jinjina kai kawai ya al ameen yakeyi dan ya gamsu da maganar ta yace ” tofa yar kanwa kina nufin bazaki bawa ko wani namiji dama ba kenan harda yayanki da ya dade da dakon sonki aranshi ? ” Kamar saukar aradu haka taji maganarshi cak taji ruwan jikinta ya shanye ta gagara ko da kwakkwaran motsi , tabbas ya shammaceta batayi tunanin haka ze fada mata ba kunya ne yarufeta, nunawa tayi kamar bata gane me yake nufi ba tace ” ya al ameen wani yayana din kenan?” Murmushi ya al ameen yayi yace ” yayanki da kuke tare acikin motar yanzu kuna tafiya zuwa kasuwa ” yabata amsa cike da barkwanci , sa gyale tayi ta rufe fuskanta takasa magana har suka isa main market yayi packing , Bude motar tayi tasa kafafunta waje sannan tace ” se anjuma ya al ameen nagode” ” noo my mirah baki ban amsa ba za ki tafi?” daburcewa tayi dan tarasa amsar da zata bashi yasa tace ” ayyah ya al ameen mu karisa magana a waya ” ta fada tana shagwaba fuska . gyada mata kai yayi tafice ko juyawa batayi ba taci gaba da tafiya amma tanaso tajuya ta sake kallonshi ko da sau daya ne, juyowa tayi suka hada ido yana tsaye ajikin motar yazuba mata manyan idonshi irin na fanan , seda taji meyasa tajuyo gudu_gudu , sauri_sauri takeyi saboda ta bacewa ganin shi seda ya tabbatar da tashiga kasuwar sannan yashiga motar , yana murmushin nasara dan yadade yanason amira kawai be taba fada mata bane .

Bayan sati biyu soyayya ya kankama sosai tsakanin ya al ameen da amira kuma har manya sunshiga ciki an yanke zaa hada rana daya dana fawwaz,ya al ameen sekuma na yaseer da zeenat dasuma yanzu suke shan soyayya ruwa_ruwa, ya usman kuwa yanzu ne suka fara shakuwa da hairah ahankali yake samata sonshi a zuciyarta duk da she’s just 16yrs , kuma an komar da ita school tana jss 1 haka hafiz ma an sashi a school yana ss 1 , suna samun gata sosai kamar yan gida sun saki jiki gashi alhamdulillah suna fahimta a makarantan dan brain dinsu naja.

Nusaiba anyi aurenta da yayanta lukman dukda madina takawo tashin hankali sosai amma hakan be hana auren ba saboda alh me ruwa ya sanar mata muddin ta hana auren a bakin aurenta shisa ta zubar da makaman yakinta bawai dan tanason auren ba.

Yau ne su suhaima da ya al ameen suka fara shiryawa domin komawa bauchi state gobe zasu wuce da sassafe zasu dau hanya shiryawa suhaima da auta sukayi ya al ameen ze kaisu gidansu Mr azaad suyiwa fanan sallama , sun fito har sun shiga motar amira tazo itama zata bisu komawa baya zeenat tayi tazauna tabata front site hakan kuwa yayiwa ya al ameen dadi, haka suke tafiya suna hira shida mirah shi .
bayan isarsu gidan duk afalo suka samesu suna zaune banda Mr azaad da fawwaz da suka fita office, anty amina tun sati daya da ya wuce takoma, fanan ta warke sumul tana tafiyanta dede kamar da, takara fresh da kyau sosai suna falo ita da ummi da zeenat,areef . shigowa falon sukayi suka zauna suna gaida ummi . Amsawa tayi fuskanta cike da farin cikin ganin su , auta kuwa rungume fanan tayi tana dariya tayi luf ajikinta , zeenat ce tace” ohhh su auta akwai son jiki kamar mage ” dago kai auta tayi tace” ummi ina wuni ? Anty zeenat Ina wuni? Anty fanan ina wuni” ya alif Ina wuni ?” Amsawa sukayi suna dariya jin bata iya kiran sunan areef ba sede tace alif, areef ne yace” baby auta dan Allah kibarni karki batamin suna ” dariya sukayi dan auta da areef insun hadu haka zasuta drama yana biye mata.
gaida ya al ameen zeenat da fanan, areef sukayi ya amsa yana tambayar areef ” Ina fawwaz?” ” Fawwaz ya fita office” cewar areef gyada kai ya al ameen yayi .
Shigowa abu me aiki tayi da su drinks da fruits hade da snacks ta ajiye musu.

Amira ce tace ” besty kinji suhaima ko? wai gobe zasu koma bauchi ” da sauri fanan ta kalli ya al ameen tace ” ya al ameen wai dagaske dama tafiyar taku gobe na nan ?” kafin ya al ameen yabude baki yayi magana suhaima ta rigashi da ” ahhh lallai matar nan da kin dauka wasa ne ko yanzu ma sallama mukazo miki ” har ran fanan taji ba dadi tafiyarsu da zasuyi dan tunda suke basu taba zuwa sun dade sosai ba irin wannan setaji dama kar su tafi dukda ma suhaima kam gombe zata dawo kuma a gidan amma taji ba dadi , kwabe fuska tayi tace” ayyah sweet sis karki tafi kinji ? , Ya al ameen ku kara wata 1 ” dariya taso bawa ummi ganin yanda lokaci daya walwalarta ya dauke yasa tace ” karki damu feena kafin lokacin bikin ai zakije in kun dawo daga dubai zaku tsaya acan kinji ?” ” tom ummina ” fanan tafada tana kwantar da kanta akan cinyar ummin . yanda ummi take da fanan kamar ita ta haifeta ,matar batada matsala ko kadan hakan ya faranta ran ya al ameen da suhaima hatta amira taji sun burgeta adduah takeyi Allah yasa itama nata surkan suzama haka dukda bata san cikekken halin umma rahina ba , dan duk zuwan da sukeyi gaisawa ne kamai yake hada su.

Haka suka ta hira har 4:30pm , tunda me gadi yabude musu gate yakejin maganganunsu da hiran da sukeyi duk a kunnenshi dukda nisan dake tsakanin packing lot da compound din gidan sannan a shiga part din ummi har izuwa main falo akwai tafiya me yar rata amma duk yanajin hiran , packing driver yayi security ya bude mishi murfin motar zuro hadaddiyar farar kafarshi guda daya yayi waje seda yakusan 5mint sannan yafito securities na biye dashi da system dinshi da wayarsa hade da jacket din suit dinshi, da kyakyawar fuskarta ya faracin karo tana kwance akan cinyar ummi se hira sukeyi da su suhaima da zeenat duk basu ga shirgowar shi ba , tsinkayar muryanshi me dadi sukayi yana ” barka da hutawa ummina ” duk maida kallonsu sukayi kanshi ” yauwa!son yau ka dawo da wuri kenan ?” ” Uhmmm” kawai yace dan yanda Abubuwa suke neman dagula mishi lissafi a yan kwanakin nan yasa bayason wani dogon magana, haurawa upstairs yayi yawuce part dinsu securities na binshi , kallon fuskan fanan tayi taga bata da ma niyar tashi tace ” feena tashi kije part dinku ” mikewa tayi batace komai ba tahaura , a falo ta sameshi yana zaune ko takalman kafafunshi be cire ba ya kwantar da kanshi ajikin kujeran ya rike kanshi da hannu daya duk wanda ya mishi kallo daya ze gane yana cikin matsanancin damuwa , ita kanta fanan taga sauyi daga wajan shi , ako da yaushe se taga kamar yana cikin damuwa amma yana iya kokarin shi wajan boyewa.
Zama tayi akan carpet ta daura kafarshi daya kan cinyoyinta ta cire mishi takalmi da safa haka dayar kafarma tayi sannan ta mike ta balla botil din rigarshi zuba mata ido yayi , ita dinma shi take kallo tace ” sannu da dawuwa habiby yau naga ka gaji sosai ” ” yeap” bude fridge tayi ta dauko ruwa me sanyi tasa mishi a glass cup tabashi karba yayi yasha ya ajiye cup din mika mata hannunshi yayi ta kama ya jawota jikinshi kwantar da kanta tayi akan faffadar kirjinshi ji tayi zuciyarshi na bugawa da sauri da sauri ” habiby meyasa kake boyemin abinda yake damunka ne , ni matarka ce bazanso inganka a cikin wani hali ba dan Allah kafadamin kaji ” kiss yamata a goshi yace ” baby karki damu is not necessary kawai de wasu irin abubuwa strange ne suka shigo rayuwata ” bude baki tayi zata sake magana ya girgiza mata kai hade da daura yatsanshi akan libs dinta ba yanda ta iya haka tayi shuru , can kuma yace ” gobe su al ameen zasu koma kenan ?” kallonshi tayi tace ” amma ya akayi kasani ko ya usman ne yafada maka?” Itama ta wurga mishi tambaya batare da ta bashi amsar tambayar da yamata ba ” no ba wanda yafadamin kune naji kuna hiran ai” tashi tayi daga jikinshi tazauna tana kallonshi sosai cikeda al ajabi dan itade tasan tunkafin ya yashigo falon suka dade da dena maganar amma taya akayi har yaji ganin kallon tuhumar da take mishi ne yasashi mikewa yayi bedroom dinshi dan yayi wanka , har yayi wanka yadawo falon anan ya sameta yanda yabarta tana nan tanata tunanin abinda Mr azaad yafada mata , kallonta yayi ta kasan ido yace ” wifey in kin gama tunanin I need food” tashi tayi tawuce dinning yana biye da ita abaya zama sukayi tayi serving dinshi tuwon semonvita da miyar egusi yau favorite food dinta ta dafa dukda batasan ko yanaci ko bayaci ba , yanacin abincin tana kallonshi tanaso taji mezece taga harya kusan gamawa bece komai ba yasa tadan bata rai tace ” habiby bakace yayi dadi ba ” murmushi yayi yace ” yayi dadi sosai wifey dadin abincin nema ya hanani magana ai” seyanzu taji hankalinta yakwanta .

Barinshi tayi a dinning din tashiga bedroom dinta ta bude babban make up kit dinta tadauki fashion bag tazubawa su suhaima da amira kayan make up dinta dasu perfume ta dau wata ledar ta zuba chocolate sosai aciki ta fito dasu falo samunshi tayi yana zaune ya gama cin abinci ” habiby bari inje downstairs inkaiwa su suhaima ” mikewa yayi ya karbi bag din hannun nata yace ” kawo in tayaki ” fitowa sukayi daga part dinsu suna kokarin fara taka staircase din yaji ummi na waya da abba ita datake can part dinta amma yana iya jiyota, haka suka gangaro duk maganar da akeyi afalon tun kafin su karaso duk yaji . ji yayi kamar ya koma inda yafito be sake girgiza da lamarin ba seda yaji muryan anty shayida da shigowarta gidan kenan taje part din mommy, tana gaishe da mommy , mommy tace mata ” ke uban me yakawoki gidan nan nace ina bukatarki ne ? To ki tattara kikoma part din uwarki aysha tunda kunfi fifitata akaina ” hakuri anty shayida tabata , dafa kanshi yayi dan baze iya daukan wannan sabon al amarin ba ji yakeyi kamar zeyi hauka karasowa falon sukayi suhaima suka gaida Mr azaad amsawa yayi yana zama akan kujeran da fanan take yace ” ashe gobe zaku koma ?” “Eh in sha Allah ” suhaima tabashi amsa auta dake buga game a wayar zeenat batasan da shigowarshi ba seda taji muryanshi tasowa tayi takoma kusa dashi ta zauna tace ” Yaya balarabe good afternoon ” dan jan kumatunta yayi yace” afternoon cutie kina lfy?” ” Lfy Lau yaya balarabe kalli game din dana keyi ” kallon wayar yayi yace ” good ashe kin iya” dariya auta tayi jin yace ta iya yasa ta gyara zama taci gaba dayi abinta , areef da ya al ameen kuwa sun fita suna garden .

Daff da mangriba suka musu sallama zasu tafi sosai ummi ta musu sha tara na arziki haka Mr azaad ma , basu kayan make up din fanan tayi tabawa auta chocolate dinta sannan suka rakasu har packing lot inda ya al ameen yayi packing sosai suka musu godiya sannan sukayi ban kwana hade da adduah Allah yatsare hanya suka tafi ,sukuma suka koma ciki suna shiga ciki kuwa anty shayida tazo suka tafi part din ummi ta zauna abinta acan tunda zuwa kusada nata mahaifiyar ya gagara .

Haka dare yayi Mr azaad yakasa bacci har fanan tayi bacci tabarshi , se ya rufe ido se yadingajin kana nan maganganu kasa_kasa na aljanun dasuke gidan shiya hanashi baccin yasa kawai yatashi yayi alwala yazo yafara nafilfilu har hudu na dare kafin yaji yafarajin bacci yakoma kan gadon yakwanta .

Washe gari

 

Gidan yayiwa su mama girma dan su ya al ameen da suhaima sun tafi sun dau hanya tun 7:00am suka tafi sosai sukayi kewarsu wannan karon sun jima musu dayasa suka zo tafiya sukaji kamar karsu tafi mama yanzu ne tasakejin kewa gashi ba fanan din ba suhaima daga ita se hairah da auta sukuma duk makaranta suke zuwa in suka tafi 7:30 se 5:00 suke dawuwa .

 

Karfe 10:00 dede suka shiga garin bauchi direct hanyar gidansu sukayi dake cikin gra horn ya al ameen yayi me gadi yabude musu washe baki buzu me gadi yayi da hausarshi dabe gama fita ba yana ” ah ! ah ! ah ! al ameenu kune yau agarin ah sannunku da hanya ” amsa mishi ya al meen yayi “yauwa baba sannu da aiki” haka yashigo yayi packing ganin motar uncle kabir ne ya tabbatar musu da yana gida yau be fita ba rike da trolley dinsu suka shiga falo aikuwa uncle kabir da umma rahina suna zaune afalo suna kallon labarai sukaji sallamar su dagudu suhaima tafada jikin umma rahina tana ” umma nayi missing dinki” dariya uncle kabir da umma sukayi lokaci daya tace ” sannunku da hanya amarya ” rufe fuska suhaima tayi tace ” umma banaso kibari ” ya al ameen ne yace ” Allah ko amaryar hubby ” uncle kabir yafara magana” ka ganka al ameen? zan saba maka akan amarya haba yarinya takusa aure amma kadameta zo nan autar daddy ” me umma da ya al ameen zasuyi in ba dariya ba, haka sukata nishadi su hudu ne abunsu a gidan se me aiki da me gadi , uncle kabir sosai suke kama da baba komai dinsu kusan iri daya harta muryansu iri dayane , umma rahina mace ce wacce tasan yakamata bata da matsala ko kadan halinsu daya da mama kamar ciki daya suka fito sede mama in aka kureta tanada dan zafi amma umma rahina kam batada son tashin hankali sannan dukansu yaran duk suna kama da iyayensu ne kasancewar su fulani sunada farar fata fanan ce kawai tafita daban ita chocolate color ce.

 

In Allah yaban iko da dama in sha Allah gobe ma zanyi posting Allah yakaimu darai da lfy .

 

 

Back to top button