Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 4

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*4* free page

Inna batayi baccin kirki ba a wannan daren tana tunanin wace sana’a zasu fara gashi kudin dake hannunta 20k ne idan ta bada kudin daki 5k ne zai rage, ko pure water zasu fara ne? gashi basu da sutura babu kayan amfani babu abinci da wannan tunanin tayi bacci washe gari Maman Nana bata fita kasuwa ba sai da suka tafi sabon gidan da zata Kama suka bada kudin dakin daga nan suka tattara suka tare sai da yamma tayi tuwo ta shirya fita Inna tace ” Mmn Nana dama shawara nake nema, don Allah wace sana’a zan fara kinsan zaman banzan bazai taimaka ba” ” hakane inna, toh me kike son ki fara siyarwa? ” ehh dama nace koda pure water ce sai na dan fara kafin nan ” ” Allah ya bamu saa kinga muzo kije ki siya a can gidan ruwan tafi arha ga sanyi, Leda 170 ne kuma kinsan yanxu 20 ake saidawa ” xuwa sukayi inna ta siyo Leda uku suka tafi. Cikin ikon Allah inna ta samu ruwan ya kare saboda duk Wanda ya siyo tuwo sai ya siyo ruwa a wajenta don suna xaune tare har bayan isha sannan suka koma gida cike da farin ciki, a takaice dai wasa wasa inna ta fara xuwa da kula na pure water da zobo ana siya baya ragewa cikin wata guda tayi nisa cikin harkar har mutane sun fara sanin hajjo,da yamma inna take xuwa hajjo kuma da safe sai gashi sun sami rufin asiri har kayan gwanjo suka siya da kayan abinci da dare tana koyawa hajjo karatun Allo da hadisai ganin haka Maman nana tace ” inna da dai kin bude islamiya kina dan samun hamsin dari na yara da manya naga kina da ilimin addini sosai” murmushi inna tayi tace ” hakane Mmn nana, shikenan zan gwada mu ga abinda Allah zaiyi ” cikin satin kuwa ta bude islamiya ta yara da yamma matan aure kuma da safe duk sati 100 ai kaman jira ake dalibai suka fara xuwa y’ay’an makota da na unguwa bayan sati biyu matan aure suka fara xuwa saboda ganin kwazon inna ta iya bada karatu sosai, hajjo taci gaba da xuwan talla da safe da yamma don inna ta koma aikin koyarwa tare take xuwa da nana da yAmma kuma da mamanta wannan kenan.

________________
Ayman na kwance bisa resting chair a study room din Aman yana karanta littafin Riyadhus saliheen a rayuwarsa yana son Islamic studies amma agida an hanashi karantawa gani sukeyi kamar asiri aka mishi shiyasa ya tsani boko basusan cewa yana son ya zama Islamic scholar bane, ya ajiye littafin ya tashi kenan yayi karo da mutum ” auch… ” Aman ne ya shigo dakin tsaki Ayman yayi yace ” baka iya sallama bane “” ban iya ba sai ka koyamin ” ” idan kana bukata sai a koya maka don naga kana bukatan ilimin addini ” kada kai yayi tare da kwafa ya wuce Ayman ya juya ya fice. da dare suna wajen cin abinci tare da Ammi babu mai kula wani tana kallonsu da take taken nasu ta ajiye spoon tace ” ku shirya an kammala muku registration gobe zaku fara xuwa school ” da sauri suka hada ido Aman yace ” Ammi are u serious? ” ” karya nake maka dan rainin wayo” sosa kai yayi yace ” am wane skul please? ” ” wane school kake tunani ” ” uhmm.. Baze , Nile, veritas, ko outside d country ” “nasarawa state university keffi ” wAat.. Ammi ba cikin FCT ba Nasarawa, shii.. Is not fair Ammi Haba ” murmushi tayi tace ” I told you dama zan koya muku hankali, wllhi duk ranar da kukayi skipping baku je ba ban yafe ba. ” ” Haba Ammi ” Ayman da sai yanxu yayi magana yana kallonta tace ” yes I min it ban yafe kuyi skipping ba sai da dalili ok ” sauke numfashi sukayi daga haka kowanne ya ajiye spoon suka tashi tabi bayansu da kallo tana murmushin samun nasara.
D next day motoci 5 aka shirya da bodyguards suna jiran fitowar yan gata kowanne yasha wanka yana jida kansa suka fito Ammi na murmushin jin dadi ta kallesu tace ” masha Allah my handsome boys, Allah bada saa sai a maida hankali ko ” Ammi sai mun dawo ” take care please Allah ya tsaremin ku ” ameen suka amsa, Aman na waka ” today is the day the first day of school so many new things to learn n do, I’m so exited n nervous too I feel good ” yana yi yana satar kallon Ayman yayi banza dashi, suna fita Ayman ya kalli motocin yace ” all these just xuwa school, no.. Gaskiya is too much mota daya ta isa ” Aman yace ” sai dai ka tafi kai daya don nidai dole a rakani I need some respect at the school ” ” sai dai mu raba hanya don gaskiya bazan iya tafiya da wannan Uban gayya ba ” fauzan na dariya kasa kasa Ayman yajuya suka hada ido dashi yana hararinsa Ammi da bataji tashin motocin ba ta fito ” lafiya har yanxu baku tafi ba? ” Ayman yace ” Ammi naga bodyguards din ne sunyi yawa mutane zasuyi noticing namu sosai n for security reason nace mota daya ta ishemu ” shiru tayi daga bisani tace ” hakane kuma ka bada shawara mai kyau, ku dauki mota dayan ku tafi ” godiya yayi ya shige mota Aman kuwa haushi kamar yayi me don bahaka yaso ba dama can Allah yayi shi mutum ne Maison nuna kai, Dole ya shiga motar da Ayman ke ciki suka Kama hanya. Babu Wanda ya sake magana har suka sauka ciki school din Aman Geography and Ethnography ya samu Ayman kuwa criminology and security study ya samu donhaka kowa ya nemi venue na lectures nasa ya tafi. Aman na tare da bodyguard d’aya Ayman kuma yana tare da fauzan basu sake haduwa ba sai bayan azhar a Gst kowdda yayi tamkar baisan dan uwansa ba, 5 na yamma suka tashi komawa suna tafiya
Kamar kurame suna xuwa under bridge Aman ya hango pear a gefen titin ana saidawa yace driver yayi parking, da kansa ya fito yana tafiya cikin kasaita har ya iso wajen mai fruits din ya gama siya ya bada kudi ya juya kenan yaji an buge hannunsa ledar ta goce kayan wasu sun zube a kasa, hajjo da ta gama rudewa ta sunkuya tana kwashe na kasan wani Uban tsaki yaja yace ” shit… Wat nonsense baki da idone u dirty pig ” tazo zata mika masa ya kwasheta da Mari ” how dare you zaki bani abunda ya zube ya zama dirty, so kike ki kasheni ne ” Allah ya isa mugu azzalimi kawai” Aman na kokarin Kara mata Ayman dake kallonsu ya fito da wuri ya rike Aman hajjo sai kuka take Aman na zage zage Ayman ya kalli hajjo yace ” sorry just Kiyi tafiyarki kawai, dauki ledan ki tafi dashi ” Aman yana ta surutu Ayman yace ” bansan baka da wayo ba sai yau, if not me abin Mari a nan is just a small mistake n it normally happens ” tsaki yaja suka koma mota driver yaja suka tafi. da dare Aman sai faman jan tsaki yake yana safa da marwa shi kadai Ayman ya kalleshi yayi murmushi ” dariyan me kake min bcos I was humiliated shine kake jin dadi right ” ” u r not serious ” ya hararesa ya tashi ya fice Aman ya buga kujera ” shit men.. I have to look for the girl dole sai ta bani hakuri if not Ayman zai rainani ya dauka bani da class ” da wannan shawara ya samu sauki a cikin zuciyarsa.

,, ______ __________________
Hajjo na hira da inna a waje tare da Mmn Nana suna shan iska a kofar gida saboda farfadan gidan nasu babu wadataccen fili kuma yau alhamis babu karatun dare don da dare hajjo ke karatunta, Mmn nana tace ” inna me zai hana ki sanya hajjo a makaranta gashi Allah ya kawo rufin asiri ana dan samu ” inna tace ” wllhi ni kaina Ina tunanin hakan don a can adamawa ta fara firamare amma yanxu kinsan kudin birni da na kauye ba daya bane ” ” ah ah inna ga nan Aso primary school ai ta gwamnati ce kudin da dan sauki ai gara ta cigaba da xuwa kinsan zamanin yanxu sai da ilimi musamman boko”” shikenan gobe sai muje ayi register, nagode Maman nana Allah ya bar zumunci ” sika cigaba da hira har dare ya farayi sosai kafin suka shiga ciki. Wshe gari Friday akayiwa hajjo registration 7k inna ta bada kudin daga nan suka tafi siyan yadin uniform primary 4 aka ajiyeta saboda iliminta duk da cewa a can kauye ba sosai ake koyar dasu ba amma cikin ikon Allah duk abunda aka tambayeta ta sani, hajjo na wajen talla da yamma kamar ance mata ta daga kai ta hango Aman na tsaye yana waige waige da alama neman wani yake nan gabanta ya fadi Allah yasa ba ita yake nema ba tana tsoron kada ya Kara marinta. Kara sunkuyar da kai tayi gabanta na faduwa hannun mutum taji a kafadarta da sauri ta tashi Nana ce tsaye tana dariya ” ke hajjo minana ya bakki tsoro haka” bata fuska tayi ” nana wllhi kin tsoratani ” juyowar da zatayi suka hada ido da Ayman yana jingine jikin mota da gilashi a idanunsa, da sauri ta sunkuyar da ka ta sake dagowa yana kallon direction nata murmushi yayi don dama jiran Aman suke da ya fito neman hajjo tun dazu hajjo tana kallonsa bini bini yana da matukar kyau gashi ba fari ba amma kyaunsa mai daukar hankali ne, Aman ya gama dube dubensa ya koma cikin mota yana faman jan tsaki haka suka koma gida batare da yaga hajjo ba. Ran Saturday da sassafe Ayman ya fito jogging da kananun kaya a jikinsa yana zagawa cikin estate din nasu a hanyarsa ta komawa ya nemi waje Ya zauna yana share zufa, ruwa aka miko masa ya daga kai Aman ya gani yana smiling ” weldone bro ” hararinsa yayi yace ” yaushe ka fara ” tsaki yaja yace ” siyata da kai kenan bakasan gwaninta ba” murmushi yayi ya tashi suna tafiya ” kasan jiya na hango yarinyar da kake nema? ” what? Shine don Wulakanci ka bari nasha wahala ” murmushi yayi horn suka jiyo daga bayansu babu Wanda ya juya, wata yarinya kyakkyawa daga gani bata wuce saanninsu ba tayi parking ta fito ” Hi guys ya kuke ” Aman mayen mata yace ” Hi gurl u look stunning ya kike ” Ayman ko kallon inda take baiyi ba suna tafiya tace ” if u don’t mind ko na dan rage muku hanya ” Ayman yasa hannu a aljihu ya cire yan dubu dubu ya cire ya watsar a gabanta yace ” in case idan baki da fuel u can use it, kinyi kadan da ragemin hanya ” fuu.. Yayi gaba ya wucesu Aman yana sosa kai ” am.. am sorry u know ki share kawai haka halinsa yake sai shegen girman kai cos he is a prince ” ” wow… I like this haka nakeson guy mai swaggs saboda haka… ta risina ta dauki dubu daya ta koma mota ta dauki pen ta rubuta numbarta ta mikawa Aman tace ” well.. Am Zee Armani, ga numbata kice prince ya kirani thank you bye ” ta juya ta tafi Aman ya sake baki har ta wucesa da motar yana tsaye yace ” wait.. Armani ba sunan vice president ba if am not mistaken, mahmud Armani kodai just family name ne? ” haka ya Kama hanyan gida, Ayman na cikin tafiya Zee ta leka ta window tace ” bye my prince ” tsaki yaja ya cigaba da tafiya yana girgiza kai meyasa mata basu da kai ne? daga ganinsu a titi kawai ta fara shige musu ” hmm zaki gaji don nasan duk nacinki baki kai sabreena ba ” murmushi yayi ya tuna da dramar sabreena a haka har yakai gida.

NASARAR rayuwata is not for free just pay 300 n read peacefully, tuntubi 07030077024 for payment details thank you.

Back to top button