Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 52

Sponsored Links

{52}

 

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Sake maimaita abinda na gani naketa faman yi acikin raina gashi abun ya tsaya min cikin rai kamar me shiyasa duk yadda naso in daure na kasa daurewa zuciyata banda tafarfasa babu abinda take yi jira kawai nake ya fito in amayar masa da ta cikina ko zanji saukin abinda yake ta sukar ƙahon zuciyata,

Bai jima ba sai gashi ya fito, “baby haɗa min tea, yau bana son cin abu mai nauyi….”

Shiru nayi masa kamar banji ba har sai da ya sake maimaitawa, faɗar irin kunar da zuciyata keyi bata lokaci ne shiyasa na miƙa masa wayar nace “Gashi nan budurwarka da ka turama kudi ta turo maka massage tana godiya….. Wallahi wannan rainin hankalin ya isa haka kuma na gaji dashi, kaima idan gajiya kayi kawai ka sallame ni in koma gidanmu, koda yaushe nuna min kake yi ni kadai kake so bayan alhali ba haka bane acikin zuciyarka….. ”

” Baby wai me ke faruwa?”

” gashi nan ka duba wayarka…. ” daga haka na juya na fita naje falo na zauna na hada kai da gwiwa ai sai kuka, ina jin motsin fitowa rasa amma ban ko dago kai na ba bare yasa ran zan saurare shi,

” baby…. Am very sorry…… Let me explain this to you clearly…. ”

” wallahi ni babu abinda zaka fada min saboda duk abinda zaka fada min karya ne, last time wata har aiko maka da gift tayi kace min baka Santa ba na yarda yanzu kuma again ka turawa wata kudi sannan yanzu kazo kana cemin zaka yimin explaining, i don’t want your explanation, i don’t want to hear it…. ”

” please baby, please….. ” ban barshi ya karasa ba na tada bori da rikici nan duk na burkice masa naƙi saurararsa kwata kwata, duk da yadda yaso yayi min bayani ban bashi dama ba sai ma baƙaken maganganu da nake ta fada masa kishi ya rufe min ido duk maganar da ta fito daga bakina kawai faɗa nake ai banma san lokacin da na kirashi da maci amana ba, kallona kawai ya tsaya yana yi bai ce min komai ba,

Koda nazo bacci banma je bedroom dinba kan doguwar kujera na kwanta, biyoni falcon yayi ganin ba zan kwana acikin dakin ba,

“baby Meyasa ba zaki kwanta acikin bedroom ba? Ki shiga ni sai in kwana anan tunda bakya son kwana tare dani…”

Ban kula shi ba haka ya gaji da tsayuwarshi ya koma ciki, da yake na saba da kwanciya a jikinshi yana yi yana yimin tausa yau duk sai na kasa baccin sai juyi amma taurin kai da zafin kishi sun ki barina inje gareshi ni kawai kiransa da darling da naga wata tayi shine ya tsaya min arai har nake tunanin akwai wata alaƙa a tsakani. Da ƙyar na iya bacci shima baccin babu wani dadi haka nayi shi, washe gari ma kin kula shi nayi gaba daya naki yi masa magana har ya gama shirinsa ya tafi wurin aiki, wanka nayi na shirya fuskata duk ta kumbura saboda kuka da rashin isasshen bacci, duk da ban kula shi ba acan wurin aikinma bai hakura ba sai kirana yake amma bana dauka, WhatsApp yaje ya turo min massage da yaga ina online,

“Am very sorry my sugar baby” budawa nayi nagani amma banyi reply ba, sake turo min yayi please say something my dear nan dinma ban tanka ba daga karshe sai na sauka, ina sauka ya turo min da text massage wanda ko bi ta kai banyi ba. Karfe 6 saura ya dawo ciki ciki na amsa masa ya shige ciki yayi wanka ya fito, zama yayi kusa dani yana kokarin zama nayi niyyar tashi ya rikoni ai sai na fashe masa da kuka, waya yafara kira ya saka a hands free nan naji muryar yaya Abdul hakeem,

“ke……. Widat kina jina?” ya fada cikin tsawa wadda ta sani tsorata dan da mugun bacin rai yayi maganar dama kuma shi babu wasa cikin tsarinsa shiyasa muka fi tsoronsa fiye da kowa cikin yayyenmu,

“ba magana nake yi miki ba?” ya sake fada cikin tsawa,

“Ah ah, Abdul hakeem….. You na calm down please, nifa ban kira ka akan ka ɓatawa matata rai ba, i just call you dan ka bata hakuri…..” samz ya fada yana jawoni jikinsa saboda na fara zubar da hawaye, wannan ai shine a dakeka a hanaka kuka,

“wanne irin a bata hakuri sai kace itace gaba da mutane, ka barni da ita inci ƙaniyarta tunda bata da mutunci, mijinki kike kin yima magana dan kawai yana sakar miki fuska? To wallahi ki bude kunnenki da kyau ki jini idan kika bari kika sake ya kara kawo min kararki sai naci mutuncinki marar kunya kawai….. ” ni dama a rayuwata na tsani faɗa bana son a sakani a gaba ana yimin fada ana daga min murya yanzun nan zai sakani kuka, wannan fadan na yaya Abdul hakeem ai kamar an yi min mugun duka haka naketa tsiyayar da hawaye,shima da yaji fadan na yaya Abdul hakeem yayi yawa kashe wayar yayi yaci gaba da rarrashi na kamar yadda ya saba dan shi baya yimin fada bare tsawa rarrashina yake da lallaba ni a koda yaushe,

“am very sorry baby, kiyi hakuri Kinji……”

“yanzu abinda kayi min kayi min adalci? Kaje kana mu’amala da wata awaje har kana tura mata kudi da idona naga text massage ta turo maka tana yi maka godiya kuma tana kiranka da darling, akan na nuna bacin raina shine zaka kira gidanmu ka fada musu a kirani ana yi min faɗa…….. ” na fada cikin kuka,

” kiyi hakuri ba zan sake ba…… Ki daina kuka please…. ”

” kana jin irin fadan da yaya yayi min…. ”

” ba zan sake ba kiyi hakuri my baby love ” ya faɗa yana sake hadani da jikinsa, kuka nake yi sosai mai dauke da dalilai biyu, na farko massage din da na gani na biyu kuma fadan da yaya Abdul hakeem yayi min,

” kiyi hakuri baby…. ” shine abinda yake ta cemin yana share min hawayen,

” baby munira fa na turawa 20k wai tana school but trust me wallahi ban tura mata da wata manufa ba and babu komai tsakaninmu sai zumunci, ta tambaye ni kudi kinga bai kamata in hanata ba tunda matsayin kanwa take gareni……” idanuwana jajur hawaye na bin kumatuna na kalleshi,

” babu komai tsakanin ku amma shine harda kiranka da darling?”

“kiyi hakuri zan fada mata kar ta sake tunda bakya so….. Ni ina ta so kiyi kiyi ki gama period in baki baby amma shine zaki rinka fushi dani?” jin abinda yace ya sani kallonsa yana share min hawayen nace,

“to ai ban gama ba kuma may be sai next tomorrow…..” murmushi yayi acikin ransa dama yasan tunda yayi maganar ciki to zai samo kaina da wuri dan ya fahimci yanzu shi kadai ne damuwata, matsalata kuma burina, bani da wani buri wanda ya wuce inga na samu ciki amma shiru kamar an shuka dusa,

” ai babu problem koma yaushe ne zan jiraki ki gama….”

“ni dai sweet ina tsoro…..”

“tsoron me kike yi baby?”

“Allah yasa mu samu cikin nan…. Bana son ka kara aure saboda bana haihuwa”

“baby wannan wanne irin magana ne kuma? Babu auren da zan kara kuma zaki haihu at the right time Insha Allah…..” ya fada yana kissing bakina,

Lafewa nayi cikin jikansa ina cewa “Allah yasa”

“amin but stop crying baby….”

“ba kaine ba…..” na fada cikin shagwaba ina turo baki,

“to ai na baki hakuri, baki huce ba?” kai na ɗaga masa,

“in riƙe cikina kenan bakya so?”

Harararsa nayi bayan na turo baki na shagwabe fuska,

“wannan kuma ai hakkina ne….”

Dariya yayi ya sumbaci lips ɗin nawa ya sake rungume ni yana shafa bayana,

“baby sarkin rigima, muje kici abinci….”

“ni bazan ci ba…”

“please my love…..”

Lallabani yayita yi har muka ci abincin muka gama sannan na ɗan warware, shi dai dukufa yayi yana aiki a system dinsa nikuma ina kallo har dare ya raba, jikinsa na matsa nayi pillow da cinyarsa anan bacci ya kwasheni. Wasa wasa kafin mu baro Lagos sai da na murmure jikina yayi lumi lumi subul subul sai uban sheki da ɗaukar ido nake shiyasa duk wanda yaga yanda nake glowing zai dauka ciki gareni amma ni da shi mun san ba cikin bane kawai weather din garin ne ta karbeni haka kuma samz ya kula dani sosai kamar yadda nima na kula dashi a takaice dai mun kula da junanmu yadda ya kamata mun zuba soyayya mun bawa junanmu farin ciki kamar babu gobe, koda suka gama aikinma bamu tafi ba yace sai mun ƙara 2 weeks ya ɗan huta sannan sai mu koma Abuja, ai kuwa na gayawa yan garinmu dan koda yaushe yana nanuke dani wuni zamuyi cikin daki daga bacci sai rigimarsa dan babu inda yake zuwa idan na shagwabe fuska zanyi complain sai yace wai to shikenan tunda bana son cikin kai gaskiya samz akwai wayo koda yake ai wanda ya fika ya fika shiyasa dole wayonsa yafi naka kuma idan idanuwanka suka rufe da son abu tofa babu wahala an ɗana maka tarko ka faɗa shiyasa yake yimin wayo shikuma yadda jikina yayi kyaune halittu na suka sake cika gaba da baya sune suke sake rudarshi baya iya hakuri dani wannan dalilin ne yasa yanzu na gane samun ciki kawai rabone daga Allah idan ya baka ya baka idan bai baka ba kuma sai dai haƙuri. Duk da bani da ciki amma hakan bai hanani lodar kayan baby ba lokacin da muka shiga kasuwa, kaya na siya sosai sannan na sissiyi ƙananan kaya dan na fuskanci yafi sonsu idan yana tare dani, shima na siya masa inner wears da kayan bacci amma bai sani ba har sai da muka koma gida da ina sake dudduba kayan anan ya gani, yau dai da wuri nayi bacci saboda gajiyar da na debo a kasuwa,

Munje duk inda ya dace muje dan bude ido da shakatawa sannan muka koma Abuja, makota na duk babu wadda ban yiwa tsaraba ba haka yan uwa da danginsa duk na sissiya musu duk da na san bafa lallai in burge ba ko inyi gwaninta dama dai kawai dan Allah nayi dan na san baza ataba yaba min ba.

Washe garin ranar da muka dawo abokinsa Ahmad ya kawo matarsa muka wuni tare da ita dan kusanma ita ta tayani yan gyare gyaren da na tashi dasu na gidana saboda ko ina yayi datti, mai nutsuwa da ita da kamun kai babu ballagazanci da shirme irin na wasu matan tabbas na yaba da kirkinta da nutsuwarta shiyasa nima na sake da ita, sai da suka dawo daga office muka ci abinci tare dasu sannan ya dauketa suka tafi, ai muna shigowa ciki da rakiyar su ya jani jikinsa yana shagwabewa “baby yau munyi fada da ke…..”

“tunda munyi fada to bari inje inyi kallona……”

Makale ni yayi yana hararata, “ina zaki je? Bayan yau wuni guda baki kulani ba…”

“oh my God, duk da nayi bakuwar so kake in sakata a gaba ina waya da kai saboda kawai ni nafi kowa miji a duniya….”

“yes nah….”

“am sorry boo….” na fada ina kissing lips dinsa,

“ni ban hakura ba…..” ya fada cikin shagwaba, nima shagwabar na fara yi masa har tsawon wani lokaci kafin ince masa,

“sweet ina son zanje Kano….”

Dakatawa yayi daga wasan da yake yi da kunnena guda daya,

“baby any problem?”

“babu komai boo kawai ina son inga gida ne….”

“ni kuma sai kibarni da wa?” murmushi nayi na rungume kansa a kirjina ina shafawa, “ai zan kasance da kai cikin kowanne lokaci sweet”

“zaki yimin wayo dai kawai” ya fada yana cigaba da wasa da kunnena kuma cikin shagwaba,

“no darling…..”

Da lallama da rarrashi da wayo dai na samu ya amince ya barni zanje amma wai 1 week kadai ya amince inyi, hakanma yayi tunda kawai ganin gidane sai tsarabarsu da zan kai musu ba suna ake yi ko biki ba bare ince yayi min kadan, babu wanda na fadawa zan zo bare a hanani zuwa duk da cewa rabona da gidan tun haihuwar ƙawalli gashi yanzu Irfan din tsaiwa yake yana neman fara tafiya sai ko lokacin da muka je bikin abokinsa wannan kuma bama na saka shi cikin lissafi dan babu inda naje, ranar Juma’a da safe ya rakani airport na tafi shikuma ya koma gida…..

_*Ummi Shatu*_

Back to top button