Hausa NovelsYar Aikin Karuwai Book 2 Hausa Novel

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 46-50

Sponsored Links

Meenal jin zagin kadai da Cele ta duro sai data tsorata,Cele mikewa tayi zaune tace ohoooo wato shi yasa naga kuna lashe lashen harshe kamar micizai yanzu na gane,ke Meenal kike ko wa Cele tana magana ta sake kunna light me hasken tace Meenal me kike tabawa? Meenal tace kawai dai kin birgeni ne mene a ciki sai kace na kashe Dan mutum ni har kin tsorata ni ma akan wannan mene a ciki,ki tsaya ki fahimta Dadi Zaki je abu a saukake ba sai kinbi maza ba,Cele tace yau naga mummunar ballagar tsohuwar balagaggiya ke a kusa da dakin Allah a nan abinda wasun ku ke yi kenan,zama ta gyara tace yau Zaki ci ubanki wallahi tunda kika taba min kirjina da abinda ke jikin kirjin Zaki gane kurenki wallahi yau sai kin tsotse ruwan nononki tas,Meenal ta zaci ma kawai zance ne sai da taji uban Mari a kumatunta Cele ta tuge mata dankwali ta jefar ta jawo gashinsa sosai ta sake kifa mata Mari tace wannan dukan na taba na bangaren Daya saura Daya,Meenal zafi ya hadata tace ai kin mareni dazu biyu kenan,Wancen ya zube dan banbanki fasika ta samu ta hambare Meenal,zuciyar Meenal ta hangulo tace Nima fa Ina da karfin Dan uwarki ta cakumi Cele,wohoho yau ashe za ayita Cele tayi wata dariyar takaici,tace bari in nuna Miki Dan uwarki cak ta dauki Meenal ta damfarata da kasa ta sa kafa ta take wuyanta tace ke din banza Namiji ma rago irin Ahsan Saluhu ubansa zanci bare ke,ta hau jibgar Meenal da kafa da hannu kamar Allah ya aikota,Meenal tana ihun Neman agaji,Sameera tace Subhannallahi kinga abinda na fada Miki ko kika jin magana wallahi Cele bata gajiya Sameera ta taho zata kwaci Meenal Cele ta jawo Sameera ta fara jibgarta dim dim tace Yan iska lalatattu dama abinda kuke kenan wallahi kinji kunya,Meenal tana hawayen Wahala Cele tace sai kin biyani nono na da kika shafa Ina bacci,Meenal ta fara rokonta tana magiya wallahi bazan sake ba,Cele tace Idan kina bani hakuri wani takaici kike Kara min kin san ni ba a bani hakuri wani Kara harzuka nake.

Kaya ta hau cirewa Meenal sai da ta mata sintir ta koma ta Watso Samira waje ta sawa kofar key sabo da matan gida sun fara fitowa zasu shugo ceto,Wayar wuta ta jawo ta fara laftar Meenal tana ihu,tace kinga abu gwanin sha’awa ko? Ke ko tausayina baki yi kina ganina na kukkumbura amma kizo nema na shegiya dangin shedan shegen Kai kamar na Dujal nono kamar gugan danko Dan ubanki sai kin fara Shan naki ta zabga mata bulala Meenal tana ihun Neman agaji,Yan gidan sai bugun kofa suke akan Cele ta Bude amma taki,dattijuwar da ta bawa Cele daki tace Zaki ci ubanki wallahi kisan Kai zakiyi zan sallameki daga gidan nan kaga yar iskar yarinya a haka kamar ta kirki,Cele tace kece yar Iska Kuma wallahi Idan na fito duk sai naci me muku wanka kuna Yara yau sai ta biyani nono na,matar tana daga waje tace akan nonon banza nonon wofi ko na saniya ya fishi daraja kamar wani Gold aka taba ubansa nonon ni kizo ga nawa kiyi ta tabawa,Cele tace naki ai ba fresh bane tuni ya gama mutuwa ni kuwa nawa sabo ne gal ta sake fisgo Meenal ta lankwaso kanta sosai tace sai kin shanye naki shegiya kalleki gaba daya suffar kabewa ce dake, wato Ina bacci kin lallabo har da tabawa yau sai kin kwana ba bacci daga gani sai ke,Cele tana jibgar Meenal tace me kama da cuta ai ke cuta ce shegiya me kama da kyasbi,makero,karzuwa kekam ai sai dai shekararren gyambo,Meenal tace ni dai kiyi hakuri bazan sake ba shike nan,bakin Cele ta bige da karfi na fada Miki ba a bani hakuri ni ta kama wuyan Meenal tare da Shaketa sosai tana kakari ga duka da kafa kamar zata kashe Meenal sai da taga tana numfashi da kyar sannan ta kyale ta tace wallahi duk ranar da kika sake taba min ko yatsa ko ma da wasa ne sai na kusa kasheki,kofa ta Bude ta tsaya a bakin kofa tana kutuntuma musu ashar tace Idan akwai me shigar mata tazo komai tsufan mace wallahi sai na kirbata a turmi,shi yasa kuke ta lashe lashen baki to Ina gidan nan zaku ga tsiya jin dadinku ya Kare,har da ku dattijan banza ku koma gida kuyi aure ku zauna cikin sutura Kun zabi zama a nan ana wulakantaku mutanen banza wallahi ku kiyayi Allah kuna mutuwa sai yankin Annabi Lut can za a kaiku banzaye Wanda akuya ma ta fiku hankali,Kun taba ganin Dabba ma ta nemi yar uwarta mace sai ku mutane komai kina da shi abu iri daya me mace zata baki tana da shi kina da shi ai kije Hajiya a baki babban itace,duk Kun samu harshenku ku Saka masa karfen banza ku ga Yan iska ana ganinku anga fasikai.

Wata Hajiya ce tace ke Dalla ki barmu muyi bacci ke Zaki mana wa’azi,Cele tace yau ba bacci a gidan nan duk Wanda ya Hana uwarsa bacci to Shima bazai runtsa ba,dakunansu suka koma suka rufe Samira ta koma daki ta kwanta tayi mukus,Meenal tana kwance a kasa taci duka jikinta yayi rudu rudu duk sahun bulalar Cele.
A haka Cele ta tsaya a tsakar gida da dare haka Daya bayan daya take bi tana bugar kofar mutane ba Wanda ya Isa yayi bacci a gidan a cewarta an hanata bacci to kuwa Babu me yi,sai bacci ya fara daukansu sai tabi kofa kofa tana bugu Kuma bana wasa ba kamar zata balla kofar haka take yi ranar haka suka kwana a gidan Babu Wanda yayi bacci.

Washe gari Ahsan bayan sun dauki wanka suka fita Neman Cele ba inda basu duba ba suna nema wajen takari to ba a Santa ba tunda bata Dade da zuwa Makkah ba,Ahsan wata ya samu bahaushiya yana jikin motarsu me tsada Husam yana cikin mota,Ahsan hannunsa rike da tab din Iphone yana dubawa ya Dan Kira matar,karasowa tayi yar hausar da ya iya wajen Cele yayi mata ya nuna mata pics din Cele sanda tana gidansa gata nan zaune a kasa lokacin tana da ciki ta Bude cikinta tana tabawa,yace wannan ka sani nashi? Matar tace a’a larabci ta masa tace ko a hanya bata taba ganin me kama da ita ba,godiya ya mata can sai ga Samira zata wuce sai kallon Ahsan take yi tana cewa ina ma wannan hadadden zai Soni ga kudi ai da na huta,tafiya ta canja ko zata birge shi,Ahsan bai San tana yi ba ma,ya kirata da larabci ya nunawa Samira hoton Cele ya tambaya ko kin Santa? ta gane tsab Cele ce amma bakin ciki kar ko son Cele yake yar uwarta bahaushiya sai tace bata Santa ba tayi tafiyarta
Yini su Ahsan suka yi suna bin layin da suka san Hausawa na zama driver yana Kai su ko Ina amma ba a dace ba,karshe ma a kofar gidan su Cele suka tsaya suna tambaya Babu wacce ta fito daga gidan sai Meenal to tana jin haushin dukan da Cele ta mata sai tace ai na Santa amma jiya jiya nan ta koma Madina,Nan take Ahsan ya juya da mota suka wuce Airport sai Madina a jirgi.

Meenal gida ta koma ta samu Cele tana guga tace yanzu wani balaraben Yazo nemanki wai daga Riyad suke wani kyakyawan gaske matashi wai sunansa Ahsan,Cele ta dago da sauri tace yana Ina? dariya Meenal tayi tace ai nace kin koma Madina jiya,wani bakin ciki ya kama Cele ta kama Meenal ta sake nada mata duka tace bari na karasa Miki dukan jiya Dan ubanki,Meenal tana ihu tace ai indai Ina raye baza kici gababa wlh Zaki gani,sai dai naga Alheri Dan ubanki Abbana ma ya ja Dani ya hakura Cele dashen Allah ce yar iska me Neman mata tun Ina karama ba a so na rayu ba Kuma gashi har na zama budurwa ma Kalli kirji a cike yafi karfinki wannan daga mijina sai Yayana,kwartuwa yanzu sabo da bakin hali Ahsan guda Yazo kika ce bana nan Allah ya tsine Miki inshallah sai an kamaki kin koma Nigeria,takaici ya sa Cele ta dinga fatan tsiya a gidan nan,wannan gidan da muke ciki Allah ka kawo gomnati tayi katafila da shi,Allah yasa unguwar nan gaba daya gomnati ta kwace ta rushe ko Ina ta bajeta Yan iska Yan hassada.
Hajiyan gidan ce ta fito itace me karbar kudin haya tace ke Cele bafa tsoronki muke ba tunda kika zo gidan nan kin Hana kowa zaman lafiya kullum bala’inki ake ji kashe yar mutane zakiyi ko kece kika haifeta? Cele tace bani na haifeta ba amma jiya ta sha nono na Ina bacci ai na shayar da ita Kuma ina mata baki sai ya bita,Meenal baza ki albarka na na daga Miki nono Allah wadaranki kije ga duniya nan ta isheki,na Miki baki ke Kam ke da Albarka shike nan a haka Zaki dai daice ki watse karshe ki mutu kici ubanki,Meenal tace ai ba uwata bace ke ai kin jawa kanki na shayar dake,wallahi Allah ban sha nononki ba ina tabawa ma kika Farka ki tambayi Samira,Cele tace ba ruwansa kin sha yawwa na shayar dake kawai.
Yan gidan suna jin bala’in Cele suma basu yi shuru ba itama bata kyalewa.

Cikin mutanen mu malamai ma Yan tsubbu suna tafiya saudiya takarci suna baje kolinsu na tsafe tsafe da kulunboto,suna samun mahaukatan kudi har larabawa matan aure ake kawo musu suna musu aiki suna biyansu kudi masu yawan gaske suje suna bata musu mutane takari suna koya musu yanda mace zata mallake mijinta ko tayiwa wani ko wata asiri,akwai malamai Yan tsubbu Wanda da dama an kamasu suna can suna prison wasu Kuma an kashe musu passport ba dama su koma kasarsu ko da wasa akwai Wanda Kuma ba a San da su ba suna nan sun cika gari suna tsafe tsafe a can,ko Meenal tana yiwa Larabawa mata hanyar malamai yan tsubbu ana bata kasonta tafi samun kudi ta nan ita,yau ma da wuri taje ta dauki wata balarabiya wai suna yawan fada da mijinta shine aka hadata da Meenal zata mata hanyar malamai,ai kuwa Meenal ta kaita har gaban wani marar tsoron Allah ya Dade a saudiyya yana bata musu Yan gari,suma cikinsu marasa tsoron Allah ke yarda,balarabiyar tayi godiya tace waccen aikin yayi sabo da yana bata kudi yanda ya kamata sai dai Kuma suna yawan fada haka yanzu,Malamin yace an gama yace za ayi yanka,za aje ayi wani aiki a ka’abah ya kissafa makudan kudade balarabiya ta biya harda Kari,bayan ta tafi Meenal ma Malamin ya bata kasonta sannan tace Malam Nima Ina da bukata akwai wata da na gani Ina sonta Ina so na biya butata amma Malam taurin kanta yayi ga karfi wlh ta min shegen duka naji jiki,ni kawai ta yarda Dani duk bukatata kawai ta yarda Dani,Malamin yayi dariya yace bani sunanta ita din banza,Meenal tace sunanta na gaskiya Rufaida,yace na karyar fa? Tace Cele yace tafi abinki zuwa kwana uku kawai ki fara tabata Zaki ga baza tace komai ba zata biye Miki kawai,Meenal taji Dadi ta tafi abinta.

Ahsan tunda yaje Madina a nan Kuma yana da abokai sune suka wuce masa gaba dake Madina ma ba a zama musu a state sai yan Makaranta ko wani aiki da shedu ba irin Makkah bace bakaken Basu da yawa Kuma yawancin na kirki ne ko Ina da suka je Babu ita,Abokin Ahsan ya koma Riyad shi sabo da aikinsa, shi kuwa Ahsan yafi yarda tana Makkah sai ya dawo Makkah ya kama hotel yayi zamansa kullum zai fito a mota da driver ya zaga duk inda bakake ke zama amma baiga Cele ba,hankalinsa a tashe yake kullum,yau kwana uku da dawowarsa Makkah da zama ya fito a mota shi da driver yana bayan mota ya harde yanda ya Saba zama Ya sa anyi parking a hanyar Harami yana can yana danna waya Cele ta wuce ta jikin motarsa ta dawo tare da Kaka ya Rakata ta sauke Umrah sabo da aikin hajji ya kusa,yinin ma Ahsan haka ya koma masauki ba tare da ya ga Cele ba.

Zuwa dare Kuma Meenal tasan kwana uku ta cika wacce malam yace ta taba Cele zata yarda da ita, Cele ta gaji da wuri ta kwanta cikin kayan baccinta blue masu kyau,Samira tana danna waya,Meenal ta tashi ta koma kusa da Cele ta haye saman gadon Cele ta kwanta a gefenta kamar wata mijinta,Samira wani kishin Meenal ya kamata bata so ta kula wata sai ita, sai kace Namiji zai mata kishiya kishin na hauka,tace kin san Allah Babu me cetonki yau tam shike nan gani mene amfanina sai kije inda ba a sonki Dan Allah Baby ki Daina min haka,I love you kin sani wannan cin fuska ne a gabana Zaki kula wata bayan kece kika sabar min,kika min kalamanki na yarda dake ashe abinda kike fada min karya ce,Meenal tace ina baki hakuri wannan dandane kawai zanyi zan dawo gareki ai magani sai da tsohuwar Zuma,Samira kamar zata yi kuka sabo da kishi,Meenal ta fara shafa Cele ta dage rigarta ta fito da Boobs dinta nufinta Cele tana farkawa kawai taci Karo da shi su fara lalata,Cele da wuri ta Farka ta bude idonta,tsoro ma dukiyar fulanin Meenal ya bata ta saki ihu tare da furta mene haka Turus a gabana tayi tsalle ta dire kasa ta kunna light me hasken ta ga Meenal ce tace wallahi yau sai na sumar dake sai kin bar gidan nan,ta cakumi Meenal ta kama Na shanunta ta jawo kamar ta dame danko zata harba, Meenal sai da ta sume Nan take sabo da wannan wajen ba a sa masa karfi Cele ta haye kanta ta dinga jibgarta tana sume, da kyar matan gidan suka hadu aka banbare Cele daga kan Meenal,ruwa aka dinga shafawa Meenal har ta samu ta farfado Cele tana ganin ta mike ta sake zubura aka riketa tace wallahi sai ta bar gidan nan ko na halakata ta fisge ta kwaso kayan Meenal ta dinga Watson su waje,Meenal taga masifa matar da tazo ta same su a gida itace wai take korarta kamar gidanta,da kyar aka samu daki a boye aka canjawa Meenal daki aka kawo Raliya dakin su Cele,Itama Raliya sai Cele take birgeta,Samira ma tashi tayi ta koma dakin da Meenal take aka canjo da Ameera yanzu Ameera,Raliya sai Cele su ma Yan masifa ne na gaske sannan Kuma sunfi Meenal ma maita Idan suka kwallafa rai suna son mace,matar me canja dakin tana sani ta kawowa Cele su Raliya haka suke wannan muguntar Idan kinki biye musu sai suyi ta canjo maki mata daban daban ko za a samu wata tayi nasara,Idan kinki Kuma ko ba Dan Allah ba sai su hade Kai sun jefa ka ciki ta karfi.

Bayan sati daya Cele dai bata ga su Raliya sun nemeta ba sai dai suyi ta lashe lashen harshe suna kallonta,Cele ta fara soya Awara tana kaiwa gidajen bakaken fata a bakin wani gida suke zama,tana uban ciniki Kuma har layi ake mata tun tanayi kadan har ta koma yi da yawa dake ana Kai waken suya suna samu a can,matasa har Wanda Suke haifaffun can bakake suna siya,Katsam Ahsan ya biyo ta wajen da mota yana baya ya kame,yaga an yanyame wata maza da mata tana ta zuba musu abu a Leda tana karbar kudi,hannunta yake iya gani sai yaga kamar Hannun Cele dinsa a wajen yasa aka yi parking,mutane suna yin sauki ya iya ganin Cele ce,shi kadai ya saki wata dariyar da bai shirya ba,farin ciki ya kama shi matuka wani nishadi ya kama shi,Driver yace kamar itace wannan Sir ya furta da larabci,Ahsan idonsa yana kan Cele ko kyaftawa baya yi ya bashi da amsa da ae itace Alhmdllh,yace to kaje wajenta,yace a’a ba yanzu ba so nake sai nayi winning zuciyarta kawai mu Jira ta tashi mu bita naga gidansu,yace to ba damuwa,Ahsan yana ta kallon Cele tana ta ciniki sai masifa take duk Wanda Yazo da rainin hankali sai taci ubansa tana ta musu ba’a yanda ta Saba,wani ne Yazo ta zuba masa ya karba sai ya bata kudin ba dai dai ba ta hau bala’i Kai nifa ba Hajiya Salamatu bace yawwa ba Sallamammiya bace ni ko na maka kama da Sa’ida sanyi kalau ko Saratu ce ni sarkin asara?,ka dawo hankalinka ni ba Sailuba bace wallahi ubanka zanci Karka ga wai ko an haifeka a nan kace zaka rainani naci uwarka da Mai da yaji wallahi kwadon uwarka zanyi na kwadata da Mai da yaji ko nayi kwadon daddawa da ita na ci Dalla matsa Kai gaba daya Kai aka kalla a ka samu sunan Takari Kai Dalla ware,Yaron ya tafi yana dariya irin zagin Cele shi bai taba jin zagi haka bama,Ahsan yana mota wacce ta sha tint fara Kal ya kwanta a kujera ya zubawa Cele Ido yana kallonta cike da
Shauki har saura kadan ta siyar sai ga Meenal tazo ta Miko kudi tace ni Kam na gama siyar da abincina gida zan tafi a bani Awara my love,I love you wallahi Ina sha’awarki, Cele kudin ta fasa karba ta mike taci kwalar Meenal ta wani mugun mata duka a baki Nan take bakinta ya fashe ta hankada ta fadi a gefen kwalta,botikin awarar ta dauka ta bugawa Meenal a kanta sai da ta farfasa daya botikin a kan Meenal,tace wallahi duk ranar da kika sake cewa kina so na sai naci ubanki shegiya mayya marar zuciya,ta dauki Daya botikinta karamin ta rike da kudinta ta zuba a lalitarta,Yan sanda ne suka taho yau ba ranar kame bace amma ganin su Cele suna musu fada a titi suka taho kama su ai Meenal ta Riga Cele ma takewa da uban gudu ita da take yashe a kasa,Ahsan yana mota yana murmushi duk da bai San me ya hada su ba yasan Cele ce da gaskiya bata fada haka kawai,ya furta itace me gaskiya da larabci,ji Ahsan da son Kai.

Driver yacewa ya kunna mota su bita a hankali ya San gudu zatayi sabo da masu kame sun zo,kafin ya rufe baki Cele ta rike bokitinta ta take a million suma Yan sanda suka bita tana gudu tana waigen baya tana Zagin Yan sandan, Ahsan suna binta a mota a hankali yana ta dariya har driver tana gudu amma masifa take tana cewa dama ai garinku bakwa son mutane ku da kuka Kori Annabi daga garinku sai hijira yayi ya koma Madina sabo da rashin ta Ido Annabi guda ma Kun Kore shi Ina ga mu,Tana hada larabcinta tana fada musu sun Kori Annabi ma da sahabbansa sai hijira sukayi zuwa Madina su waye da Yan Makkah zasu kyale su,da Hausa Kuma tace ai Kun shiga uku da gori kune kuke da abin kunya a duniya Dan uwanku Annabi guda Mafi daraja kuka kora,tana gudu tana waigen su suna binta kuwa wai ta musu sharri sun Kori Annabi ma,Ahsan yau yana mota dariya kamar me sai lungu lungu suke bin Cele tana gudu ko gajiya bata yi,tana zuwa saitin gidan Kaka ta hango kaka Abayarta ta rike da hannu mayafinta ya zame tana cewa Kaka shiga gida shegun Suna baya ku shige gida,Kafin su karaso duk wani baki dake wajen sun bace ba’a ganin kowa a waje,Kaka ya leko da Kansa yana cewa Shugo nan jikata Ina Cele ta wuce ma ko jinsa bata yi ba,Kaka ya leko da Kansa wani askari ya Mika hannu zai damko Kaka ai tuni kaka ya Kai Hawa na daya da gudu, yana cewa Kai tunda nazo garin nan nake motsa kuruciyata,kuruciyata sai dawowa take, Ahsan a mota suke ta bin Cele da askarawa Ahsan yana ta dariya domin botikin ma ta jefar da shi ta gyara mayafinta tana gudu har tazo kofar gidansu a nan taja birki tana uban haki ta shige daga Dan zauren ta leko da kanta ta zazzagi askarawan da larabci ta shige ciki abinta,suka ce ai sun gane gidan Jira suke gomnati ta basu damar kame gida gida,Ahsan kuwa ji yayi kamar kar ta tafi bai gaji da kallonta ba,a fili Kuma yace yanzu zai fara bibiyarta driver ya shirya.
Layin kasuwar takari yasa aka kaishi a mota yasa Driver ya fita ya siyowa Cele kalar botikin awarar ta gudu biyun da babba da karami,kawai ya samu wata takari ya bata Yan kudi yace ta shiga gidan tace a nuna mata Cele sai ta bata botikan,ta karba kuwa Ahsan shi yana mota hankali kwance ya ga Cele to,takari bakar fatar kawai ta gani suna bata sun ja mota suka bar wajen, ita Kuma takarin ta shiga gidan Neman wace Cele bata San ma balaraben ne yasa a kaiwa Cele ba sabo da yana bayan mota ga Motar da tint,driver ne ya ba.

Auta karatunsa ya kankama sosai ga bikin su Sultana yana gabatowa,Mami da Baffa suka kira shi ya zauna Baffa yace Autana naga Alama baza ka iya zabo matar nan ba mun Yanke hukuncin aura maka Omaira kanwar Rabia,Auta yace gaskiya Baffa a’a nasan Dan kyau tana da kyau ai ba kyau ne so ba,so ba a kyau yake ba kawai ni nasan ta cancanci a sota amma ta min karama,Mami Ido ta zaro tace Auta Omaira 19yrs ce tayi maka karama? Auta yace ae ni babba nake so a samo min kamar Wise matar Papa ko kamar Auntyn Nawwar matar Yaya yawwa irinsu nake so,why? Baffa ya tambaya,yace gaskiya Karka ku sa nayi rashin kunya amma kamar Omaira me zata bani, Baffa yace zaman kudu ya lalata min Yara da a Arewa ne yaushe Auta zai iya fadan haka Okay fine mu dai Omaira ce zabin mu,Auta ya mike yayi tafiyarsa, Mami tace Kar a takurawa Autana Honey a kyaleshi tukun ya samo,wannan yaron za a bari ai kuwa za a ga ba daidai ba tunda Allah ya hore ayi masa shine dai dai,Mami tashi tayi tace bari naje na lallashi Autana,ke kike shagwaba yaron nan wlh,Mami dai ta wuce bedroom din Auta.

Samun Auta tayi ya zauna yana kunci,tace Babyna,baki ya turo gaba tace ni na Daina kulaku tunda da abinda zaku Saka min kenan,Mami tace Auta abinda zan iya cewa mun baka sati daya ka kawo mace kana gani biki saura sati biyu kacal me kake Jira,Why are you so stubborn? Sai kace dole nace na fasa auren,wallahi baka Isa ba Auta aure zamu yi maka,Auta ya bude baki,wayarsa ce ta dauki Kara ya duba yaga Baso yace Mami zanyi waya,amma kafin nan ni a wanne gidan zan zauna? Mami tace gidan da ka zaba a Gina maka shi ake maka amma tunda dama yaro ne Kai ga part guda nan za a baku a gidan nan ku zauna da Amaryarka kafin muga kamun ludayin naka muga ya zaka rike yar mutane Idan munga normal sai a karasa gidan ku koma gashi yanzu Alhmdllh ranar da ba lecture kana zuwa Office har weekend Masha Allah saura matar muga yanda Auta zai riketa, dariya yayi ya furta 9 months dai dai ta haihu Mami Idan Ina sonta Idan kuwa bana sonta shekara Tara maybe Kya samu jikan Auta ya furta yana dariya,Mami dariya tayi tace Oh Auta ko kunya ai shike nan zamu gani ta mike ta fita,Baso ya Kira back yana dagawa ya jishi a cake ga Salma nan tana ta ihu a gefensa,yace kazo ka siyeta ko na aikata lahira ta isheni bana sonta tam,Auta yace Kai wanne hauka ne wannan muna da danganta ne da zaka dame ni ya ja tsaki ya kashe wayarsa.

Washe gari kuwa Salma ce ta durkusa a gaban Baso jiki na rawa yana zaune yana fushi ya harde hannaye a kirji,a Hankali tace kayi hakuri indai akan nace ka biya Sadakina ne kake wannan fishin kayi hakuri ga abincin Dan Allah Kaci,kayi hakuri na Daina cewa ka aureni Dan Allah Kaci abincin kaji,ya kalleta ransa a bace yace karki sake cewa kina so na Idan ba haka ba bazan sake cin abinci ki ba ko mutuwa zakiyi banza kidahuma ana soyayya dole ne? nace bana sonki ko dole ne mayya, Karar tsaiwar mota suka ji a kofar gidansu, Auta ne Yazo motar ma ta Abokin Nawwar ne ya karbo bayan ya sauka a jirgi,uban Swagga cikin kana nan kaya wando duk a farfashe pencil me shegen kyau da tsada arsh,sai Riga fara me dogon hannu ya dora top a Samanta marar hannu maroon and arsh,takalminsa Snickers me kyau arsh wandon nan harda sarka a gefe Daya gashi ya zazzago shi boxers dinsa a waje suma taci kudi sai sheki take an mata wani shegen gyara,yana kamshi ya fito da wayarsa a hannu ya mugun haduwa.

Tafiyar gayu yake yana taku dai dai ana wani bubbudawa irin na Samari masu tashe, sallama yayi ya shiga gidan Kai tsaye,Baso yana ganin Nawaf ya mike yace bros yana ihun murna yace Oga chansa chansa Chau Chau sa’ade ya wani yin ta Yan daba,Auta dariya yayi ya mikawa Baso hannu suka gaisa sannan Baso ya jawo masa benchi ya zauna ya masa tayin abincin yace ya koshi,Auta yace na shugo ne ya deal dinmu? Baso ya sheke da dariyar murna yace yana nan Idan ka shirya,ya kwalawa Salma Kira yace baki ga abokina ba ne? Salma tazo tana murguda baki ita Baso take so ala dole ta durkusa tace ina kwana? Auta ya kalleta a banzance yace I’m good ya shareta,Baso sabo da kar a ji sirrinsu ya ja Nawaf kofar gida yace nawa zaka siyeta? yace Million daya a Hakan ma kafin na roki Baffa ya bani sai na sha wahala kasan ni dan Makaranta ne sai yanda aka yi Dani,Baso yace Allah mutumina to ka gane Kace Baffa ya baka dubu dari uku,Yayanka dari uku Mama ma dari biyu a haka Zaka hada kudin a saukake,Nawaf yace kamar ka sani haka nayi a Hakan ma da kyar kowa cikinsu ya bani,yanzu ya za ayi nan da sati fa za a daura aure ka samu manya ka sanar musu,amma kana ganin zata yarda Salman? Baso yace ita din banza na karyata kuwa,ai ka kwantar da hankalinka yanda nace haka zata bi kawai ayi komai na biki sai ka bani kudina ranar Kuma a Kai maka amaryarka,Auta yace Iyayena ne fa zasu zo bincike karka yi shaye Shaye please kar a samu matsala Dan ni taimakonta zanyi kaima na taimaka maka kawai ba wai sonta nake ba, Auta har ga Allah taimakon Salma zaiyi ba wai ko yana jinta a ransa bane kawai dukan da ake mata gata marainiya gashi Baso baya kaunarta abin ya mata yawa shine dalilinsa na aurenta amma shi Kam ba abinda zaiyi da ita ya fiso ya samu su Mami su kyaleshi tunda Idan yayi auren hankalinsu zai kwanta shi Kuma a hankali sai ya samu zabinsa katuwa nunanniya ya auro abarsa ya sha soyayya,haka suka gama tsare tsarensu da Baso da zai tafi har dubu ashirin ya bawa Baso,yana komawa gida yace wa Mami ya samu mata,tace har kayi wata budurwar? Karya yayi yace ai sun Dade tare kawai yaga karama ce 19yrs tazararsu ba yawa amma ya duba yaga tana da hankali,ya Basu Address,Baso tsabar bukatar kudin da yake baiyi Shaye Shaye ba,ya samu Salma yace Salma aure fa zan Miki,da mamaki Salma ta kalle shi,ya bata rai yace kinga karki zubar min da damata kudi zan samu sai na samu babbar sana’a na Gina mana gida daga baya yace zai sakeki sai ki dawo muyi aurenmu Muji Dadi,Shima yaron iyayensa ne suka takura masa sai yayi aure shi Kuma baya so a masa auren dole sai nan gaba zai sakeki ya auri zabinsa kinga Nima sai na aureki lokacin nayi kudi abinmu ya kika ce?

Salma mamaki ya kamata da tsoro tace Idan kana so na Baso ta ya zaka bawa wani ni ya aura? Baso a ransa yace Dan baki sani bane siyar dake nayi,Gaskiya baka so na nidai bana son wannan yaron Kai nake so wallahi ta fashe da kuka,Baso ya hade rai yace wallahi zan karyaki ni na baki Umarni amma kice baza ki ba,nifa Zaki taimaka ashe karya kike bakya so na,Idan kina so na ai Zaki so farin cikina,kiyi acting kamar film karki sake ko ya aureki kice Zaki masa fitsara a hankali zai sakeki kawai ki bada hadin Kai kamar dama kina sonsa,Salma tana goge hawaye tana shesheka tace to zanyi sabo da Kai amma ka tabbatar zaka aureni nan gaba? Baso yace ya zama dole kawai kiyi abinda duk na tsara Miki,tana shesheka tace Allah bana son tafiya na barka,bana so nayi nesa da kai har kudu fa haba,Baso lallabata ya shiga yi abinda bai taba to ba yace kiyi hakuri zan dinga zuwa Ina ganinki kema Zaki dinga zuwa karki ji komai,haka ya dinga lallaba Salma da karya da gaskiya har dai ya samu ta amince zata Auri Auta amma Sabo da Baso Kuma da sharadin ana sakinta zata dawo ya aureta ba abinda Kuma Kuma zai shiga tsakaninta da Auta.

Mami,Baffa, Papa da Nawwar suka zo gidan su Baso sunga gidan sunga Salma Kuma sun basu tausayi matuka,Salma ce ta sauke su da girkinta da ruwa da lemo da Baso ya siyo,Baso harda basu kabarin tarihinsu amma sai yace muna zaman mu da Kanwata Ina ji da ita Ina matukar kaunarta Ina fata dama Allah ya bata Miji na gari Kuma Alhmdllh ta samu yaro yana sonta tana sonsa,Salma dai daki ta koma tana rusa uban kuka ganin da gaske fa auren zata yi,Baso da shi aka tafi cikin dangi can jigawa,bayan sun gama komai Baffa sai da ya sake bincike ya samu suna da asali me kyau Papa ne ya koma ya Kai kudin aure aka Yanke biki saura sati daya za a hada Dana su Sultana, abinka da talaka Wanda komai yi masa za ayi to fa sai yanda akayi da shi, lefe sai da aka kawo akwati goma cif kaya na kece raini komai me daraja aka yiwa Salma sabo da dama su Mami sun shirya dole da Auta za ayi auren shi yasa komai da shirinsa akayi,Auta sai gayya yake ba ruwansa da wani ba soyayya bai so a gane murna yake nunawa a fili yace ranar ma sai yayi rawa duk da Baffa ya Hana party yace suyi bikin da kidan a gida baya son taron nan.
Duk wani Shirin biki anyi shi Salma dangin uwa suna ta gyarata sosai ta Kara haske da kyau sai kamshi take,ana gobe biki aka mata lalle me kyau da gyaran gashi ita ba kawar data gayyata sai Hajara kawai,Hajara suna tare Amarya ta zuba tagumi Hajara tace wai mene ne haka ne ni wlh Banga abin so a wajen Baso ba da kika nace sai shi,mutumin da sai Shaye Shaye ya iya kullum ya Miki dukan tsiya ya zage ki tas zakunci iri iri mene abin so a Baso gashi kin samu yaro matashi kyakyawan gaske gasu masu kudi Kuma da Alama yana da hankali me kike nema.

Salma ta goge hawayenta tace aure kamar wasan Yara Hajara sabo da masu kudin su zasu yi mana komai ki duba yanda sati daya kacal aka sa bikina Kuma ni yanzu garin ya min nisa ya zanyi da Baso kullum Idan ban Ganshi ba bana jin Dadi,Hajara tace naga Alama baki San ciwon kanki ba Salma Allah ya Miki canji kina hauka,ni to yaro ne fa nawa yake,Hajara tace ke kika sani aure dai ba fashi gobe I yanzu kina gidan Mijinki,Salma tana ta kuka ita sai Baso Kuma baza ta cire shi a ranta ba,Ango kuwa ko a jikinsa mantawa ma yake da ita Idan ya aureta sai Idan yaga wata dai dai da shi irin kalar da yake so sai ya aura abinsa ya huta da su Mami,amma Idan suka bashi Omaira ta karfi zasu sa ya fara sonta ma yace baza a mallakeni ba ga yayarta nan ta mallake Nawwar daga taimako bada ni ba Autan Mami,yace su Aunty Rabi gadon soyayya suka yi sun iya love tunda ji yanda mamansu da Abbansu suka hadu sai soyayya, da sun aureka ka gama yawo soyayyar tsiya ce da su.

Bangaren gidan Baffa Yan uwa da abokan arziki sun zo,Aunty Rukayya da yaranta haka Binta ma da yaranta duk Yayan Iyamami ne basa zuwa sai da dalili sabo da Halin uwarsu Iyamami,Wise kuwa uwar Ango da ita Nawaf yake shawarar bikin,Umman Rabi,NazifaNazira sai Bilkisu sunzo bikin Hadi da ganin gidan auren yar uwar su daga baya Kuma su Omaira zasu zo hutu suma,Wise ma wasu sunzo bikin Auta a danginta,gida ya cika an gama Shiri Auta uban abokai kamar me ko Ina sune a gidan ana ta Dj Su Sultana Amare suma komai tsaf an shirya sun sha gyara,tun ana gobe suka Fara Dj a gidan.
Auta ne ya shugo Ina kallonsa a Palon Mami nayi dariya nace Angon gobe,Kallona yayi yace fadi ki Kara,su Bilkisu ma suna tsokanarsa,Duk inda Auta ya juya tsokanarsa akeyi,Nawwar ne ya shugo Shima Ido muka hada ya kashe min Ido daya Nima na kashe masa nawa,Auta yana kallo yace Allah ya kyauta,Autan Mami Ango Dan banza wallahi sai munga rukonka ya za a Kare cewar Star da shigowarta kenan,kowa yace Auta kaza kaza ana ta dariya,Kasa kasa yace da Wise Mama karama an goge min kayan angwancin nawa? Wise itama kasa kasa tace tun yaushe yace karku min dariya wlh kwaila ce matar itama,nayi gudun gara na afka zago,muka dinga dariya muka ce ai kowa zai gani da idonsa,Seraline ta furta ka shiga uku duk karyar Ina ta Kare gaskiya Auta ka fado,yace ya na iya da kaddara danya ce to ta dai fara alamun bura zata Dan fara nuna kadan,Auta yana ta bamu dariya har shewa muke,Wise tace na siya maka man power Auta,Auta da sauri yace Natural…. Natural… Mama karama ni Natural ne ba sauki,Muka dinga dariya, Nace Auta ya kaga shaddojin? Yace sunyi Aunty ai kin iya zabe akwati guda kika min fa na kayan angwanci nima kin hada min lefe tnx,nace Auta namu ai kadan ne ma,Wise kuwa takalma masu tsada ta siyawa Auta sun Kai set goma,ga su Star an siya masa agoguna da huluna na angwanci komai anyi,Part din Auta a cikin gidan aka canja masa komai da tsari 3 bedroom ne sama 2rooms kasa bedroom Daya,Palo kitchen komai an zuba an kashewa Auta kudi sosai,Mami tace guiding danta zata yi sai ta ga kalar zaman nasu, amma sai take ganin kamar Auta yana boye mata wani abu.

Washe gari daurin Aure Auta wanka yaci ubansa ranar Shaddarsa fara Kal komai fari tas har hular ya sheka kyau yana zuba kamshi,babbar rigar ma ta matasa Yan gayu cass da shi,wasu ma a can jigawa suka kwana wasu Kuma a jirgi suka tafi can Jigawa a gidan Iyaye na gado cikin dangin Salma a nan aka cika aka daura Auren Salma da Nawaf akan Sadaki dubu dari uku,ana daurawa Auta sai murna kamar yana son matar ma haka yake murna,
Baso Kuma ana daurawa yaja Nawaf gefe yace Alhmdllh saura kudina Nawaf ya masa transfer kudinsa Million Daya chas sai murna Baso yake.

A lokacin dangin Salma suka tattara kayanta da lefenta da abubuwan bukata aka hada Salma da mata uku wanda zasu rakata can kudu gidan mijinta,Salma kuka take kamar ranta zai fita ita duk abinda ya dameta Baso ne,zata Daina ganinsa,shi kuwa Baso kiransa akayi a matsayinsa na uban ya Wanda ke rike da Salma akace ya mata nasiha,ya Kalli Salma dake uban kuka cikin lafaya me kyau da tsada,tana kamshi tana kuka,Baso yace kiyi hakuri Dan kutmar….ya duro mata ashar su kadai ne a daki yace ki min shuru ko na farfasa Miki baki,Kuma na fada Miki wallahi kiyi abinda nace kiyi abinda ya dace Idan ba haka ba sai na kusa kashe ki,na rigada na aurar dake ki nutsu ba a wasa da aure karki masa ae yane ko baki gane bane,Nawaf abokina ne yanzu Ina sonsa wallahi karki sake naji an kawo min kararki sai na sassaba Miki kamanni,saura Yazo yace ki Dan buda masa kika ki yarda sai naci ubanki shegiya me suffar aljanu ki min shuru munafuka,Salma tana goge hawaye Umarnin Baso kamar Umarnin Allah haka take jin maganar Baso sabo da so,yace kar naji kar na gani fito na rakaki mota,Ango yana bayan mota a zaune suna jiran Amarya zasu wuce Airport
Kwayar Baso ce ta motsa yace da matan da zasu raka Amarya Dan uwar kowacce gyatuma ta koma gidan mijinta uban waye ya rike min ita Idan bani ba to baku da amfani sai ranar aure sanda muke wahala akwai Wanda ya taba zuwa gidanmu ya tambaya Yaya muke ci muna koshi wanne Hali muke ciki Babu,sabo da bani da kudi ko gidanmu bakwa zuwa ziyara sai Idan mu munga dama mu neme ku,yanzu na aurar da ita lafiya mun rabu lafiya Kun kwaso tsofaffin kafafunki zaku tafi kaita gidan Miji uban me kuka taba taimaka mana,to ba shegiyar da zata Kai min kanwa gidan Miji ni zan kai abata da kaina na damkata Amana,Anji jirgi an taho za aci baza naga shegiyar da na gani a jikin motar nan,ya juye ya Kalli Salma yace ke shiga muje,Salma ita murna take da farin ciki Baso zai kaita har can ko banza ta dinga kallonsa taji Dadi, daga Baso sai Amarya sai Ango da wasu tsirarin abokai tunda har Baffa duk an koma ana daura Auren Sultana da Nasira suma akan Sadaki dubu dari biyu biyu,ana ta shagali ana ci ana sha ga Selfie ana yi ga kida na tashi munyi rawa har mun gode Allah.

Baso da Salma a jirgi har garin aka kawo motoci aka dauki Amarya da Basonta ita kadai Ango yana motar Afif suka nufi gida wajen Mami,suna shiga kida na tashi duk angwayen su Sultana anyi hotuna sun tafi, Abokan Auta suna jiransa ga Motar Amarya a baya,suka shugo bayan anyi parking Auta ya fito da zugar abokai duk suka taho ga Kida na tashi ana Dj Auta ba kunya ya shige ciki ya dinga cashewa muna ta masa liki ana dariya,Baso ne ya fito da Amarya Shima ya shige cikin filin rawar yace a kashe,aka kashe kidan kuwa, yace bani kidan Na aurarta lafiya na huta da kaya,Dj da mutane aka dinga dariya ana tambaya waye haka akace ai shine ya kawo Amarya shi ya riketa,Kowa mamaki a haka ma Dan baiyi Shaye Shaye bane sosai,Baso yace ku sa min Kidan na jefar da kwallon Mangoro na huta da kuda,akace Shima Babu yace to wai sai Uban me Allah ya gani dama ba a so na taka,Nawaf ne ya jashi gefe yace zaka bata deal za ace ba tarbiyya please,yace chansa dai chansa dai na hakura ko Dan kudina su tsira,Wise ce ta budewa Salma mota ta fito da ita tana guda ga Amarya ga Amarya.

Kawai Baso mahaukacin ba Wanda ya bawa Amarya ba danginsu ya sulale ya fece,sai Nawaf yayiwa waya shi tuni ma fa yana hanya yabi mota,Nawaf yace to ya sake tura masa dubu talatin ya Kara kudin mota,Baso yayi ta godiya ya koma gidansa yana murna daga shi sai mahaukaci
Washe gari dare na yi Baso ya siyo manyan gasassun kaji da yogurt guda biyu ya bawa Mahaukacin guda da Madara shi ya dauki tasa yana ci yana cewa Alhmdllh na huta da jaraba haba ai na samu na Wala yarinya ta gallabeni da kyar na samu me siyanta sai shegen bakin jini.
Salma kuwa bayan Baso ya fece bata sani ba tana tsaye tana Shan kallon fitsarru muna ta rawa Auta rawa yake kamar me,Salma ta kalle shi tare da tabe baki tace kalle shi kamar Dan Iska aikin banza.

Zuwa dare aka Kai su Sultana Wise da Salma ta dinga tafiya sabo da taga bata da dangi,Mami ta dinga fada me yasa za mu dauki Amarya daga kawota mu tafi da ita Kai wasu Amaren,hakuri muka bayar.
Ranar Salma bata ga Ango ba Shima bai ganta ba a bangarenta suka kwana tare da Hamra,Sabreen da Iyamami sama sama suka yi bikin su ba ruwansu irin suna jin haushin su Mami,Iyamami Kuma wai an bari Auta ma ya auro musu bare ba yar dangi ba,gashi tana jin tsoron Auta wajensa ma baza ta je ba basa Shiri ko kadan gashi bashi da kunya wanke ta yake sol.
Yau duk Wanda Yazo biki na kusa da na nesa duk sun tafi sai iya Yan gidan,Hamra ita tasa masu aiki suka gyara part din Auta tsaf ko Ina yana kamshi ta hana Salma yin aiki ganin ta sawa kanta damuwa tunaninsu alhinin rabuwa da gida ne.
Mami har can taje tayi mata nasiha sosai karshe tace ki dauke mu Iyayenki Dan Allah ba babanci kuyi hakuri da juna aure sai hakuri,Idan ya Miki laifi kizo ki fada min kinji,Salma taji sanyi ko ba komai iyayen Nawaf mutanen kirki ne har mamakinsu take gasu masu kudi amma ba wulakanci,tana mugun son Wise da ni Rabi da su Star sabo da ta ganmu Yan harka ne har wasa muke mata muna tsokanarta.

Mami zata fice Salma tace ina matar Yayan me gidan nan? Mami tace waye megidan nan a kunyace ta kama Salma tana kasa da Kai tace Auta,Mami dariya tayi wai Auta ne ya zama me gida yanzu ta sake yin dariya tace tana gidanta,au ba a nan gidan take ba? Mami tace ae mana ku ma nan gaba zaku koma gidanku Idan an gama ginawa,Salma tace ina sonta wallahi ita da kawayenta da Wise take suna da kirki,Mami tace Wise Kanin Baffa take aure a takaice ta Dan bata labarin su,tace yanzu dama su Aunty Sultana sun girmi Me gidan nan,dariya ta sake kama Mami Idan tace wa Auta me gidan nan wani dariya ce take kama Mami,tace ai shine Auta,tace uhmm i see amma ya fisu girma ma kamar shine Babban, a ranta tace harda gemu da saje,Mami tace Dan Allah ku zauna lafiya,Salma tayi godiya sanye take cikin Atamfa super black and white tayi mugun kyau dama abinka da me kyau gata yar dagwas da ita matashiya.

Mayafinta ta gyara tare da rufe kanta ciki ta zauna a tsakiyar bed,Wise ce ta shugo tana mata turaren daki iri iri, Salma ita Baso ta tuna sai kuka take,Wise tace kyayi ma Kya gama Yan banzan Yara sai balagar zuci da Miji ya shugo za ajiku lakwas kuna karbar Antena, Salma tana kuka bata gane mene Antena ba.
Auta kuwa wanka yaci cikin wata Gezna ruwan Zuma ya tsula kyau yana kamshi ya gama Shiri ya zauna a bakin gado yana latsa waya a fili yace duk da cewar ba abinda zanyi wa Amarya amma da kunya yanzu kawai sai Mami taga na nufi part din Amarya ai da kunya sai da nace abokaina su rakani suka ce an Daina yayin raka Ango yanzu,Ina zan Saka kaina da kunyar Mami,yanzu Ina shiga shike nan ko banyi komai ba za ace nayi wani abu na zama Dan Iska,wayyo pillow ya jawo ya rungume yana cewa wayyo kunyar Mami waye zai rakani gashi ko kazar ban siyo mata ba ni ta Ina zan fara ne.
Tashi yayi yana gwada yanda zaiyi Idan ya shiga ya sha kunu ya bata rai ya furta kawai cewa zanyi Salamulaykum sannunki,da sauri yace nooooo Sallama zanyi da yanga na ajiye mata ledar kajin nace good night,a’a ai Kuma ba tsari kawai muyi fada tunda ba Sona take ba Nima haka,nooooo Auta nutsuwa zakayi Kaine fa namijin, mijinta a kasanka take behave well,yace uhmm hakane tabbas,yace yanzu zan fita Allah yasa kar na hadu da Mami,a hankali ya Bude kofar yana sanda yana lallabawa kamar barawo wai zai tafi part dinsa kar a Ganshi da kunya,da sauri ya dawo dakinsa kamar Wanda za a kama,sake gwadawa yayi har ya fita ya sake dawowa yana dariya yace wlh bazan je ba bazan iya ba,can Kuma yace haba karya ne Auta Kaine fa Dan zamani haba ka waye kunya ma tuni muka cillar da ita,kwanciya yayi a gadonsa ya ja pillow ya rungume

Mami ce ta banko kofar ta shugo dauke da katuwar ledar nama da kayan sha,uhm Auta Dan gata auren gata,Mami tace wai uban me kake Jira ne jiya fa baka je ba sai da Hamra suka kwana ko da matsala ne? kamar kana boye min abu,Auta duk zumudinka ka zauna jiya baka je ba yanzu uban me kake a nan ka bar yar mutane gashi har 10pm sai Wise na tura ta tayata zama,tashi ka tafi muje oya,Auta yace ni dai Mami wayyo yana yarfe hannu,dariya ya bawa Mami yace Mami zanyi kuka nima,muje Mami ta jawo shi ta rufe kofar tace kayanka an Kai can komai yana can muje,suka fito yana wani tirjewa yana sangarta,Mami tace zan mareka muje,suka tafi har bakin kofa ta kaishi tace kayi Addua ungo ta Mika masa ledar ya karba,ya juyo yana kallon Mami tace kaje,Rungume Mami yayi yace I love you Mami Babu kamarki,I will miss you gobe baza kizo ki tashe ni a bacci ba? Dariya Mami tayi tace ga matarka nan,mu kwana lafiya,tsokanar Mami yayi yace Mami ta juyo tace na’am yace hanyar ta Ina zan bi? zagi ta auna masa, ya shige ciki yana dariya har ya rufe kofa ya sake budewa yace Mami da karfi,ta juyo yace Good night kice Ina gaida Baffa,tafiyarta tayi,yana juyawa yaga Wise ta gama turaren tace Ango a bi yar mutane a sannu,Auta yace Mama karama karki bani kuka,Wise ta fice tana dariya ta musu sai da safe.

 

 

A dinga sharhi please shine godiyata ni

 

 

AsmaBaffa
08061929616
[8/15, 9:51 PM] AMINA KABIR CAPS: ‘YAR AIKIN KARUWAI 2
MATAFIYA

BOOK 2

 

Back to top button