Hausa NovelsYar Aikin Karuwai Book 2 Hausa Novel

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 51-55

Sponsored Links

Auta ciki ya shiga tare da haurawa sama direct dakinsa ya bude bata ciki ya dawo daya bedroom din ya tura kofar a hankali ya iske Salma tana uban kuka ita Baso take tunawa,Baki Auta ya tabe ya karasa ciki yace sannu da aiki ya bude ledar ya dauki abinda zai iya ci ya ajiye mata sauran yace ayi kuka lafiya,Salma wani takaici yasa tace sai anyi din Ina ruwanka dani, babu abinda ya shafeka da ni,juyowa yayi yace who even care about you kalleki Dan Allah ya ja tsaki, Salma kuma ta furta Karka sake ka shiga harkata,Ido ya tsura mata yace ni na Miki kama da ajinki? Salma ta juyo ta kalle shi tana yatsina tace Karka zo har dakina kace zaka fada min magana,dariyar yake Auta yayi yace Ina ya zama dakinki? Wa zai bawa irinki daki? Babu ni ba kai na fada maka Karka jawo Aljanuna su tashi na hada ma jini da majina, wani beran masallaci da Kai,Auta ya kalleta kawai wato tsabar lalacewa bera ne Kuma na masallaci ma.

Auta yace cikin fushi look at this dirty smelling local village girl, idiot ke Idan ban koma Santana naci ubanki ba shege nake useless girl yaja tsaki zai fice Salma tace Kai me nan wajen akuyarka ta kiyayi ramata wlh Nima tsagera ce Baso kawai nake wa biyayya,baki da aikin yi cewar Auta ya fice a fusace ya banko mata kofar kamar zai balla kofar, wani kallon banza ta bi kofar da shi ta ja tsaki ta mike tare da sawa kofar key tazo ta zauna ta baje kayan ciye ciyenta taci ta koshi,Alwala tayi da Sallah tana kallon dakinta a fili tace haduwa kuda a gefen gyambo Inama tare da Baso muke a nan wayyo Allah ta fada saman gadonta tana tunanin Basonta,Auta kuwa ya ja tsaki yafi goma yace Auta ka sa kudinka ka siyo problems da hannunka yace gobe Monday yana da lecture,Alwala yayi bayan yaci ya sha yayi Sallar Nafeela sannan yayi Shirin baccinsa cikin kayan bacci masu santsi Riga me dogon hannu sharara da ita da dogon wasu silver color,saman katon bed dinsa na alfarma ya haura ya jawo wayarsa ya hau Online,Nawwar yana kwance a jikin matarsa ni Rabiah muna danna waya dukkanmu muka ga Auta a Online yayi status ya rubuta Matata tafi ta kowa,Nawwar yayi dariya yace kaji Dan Iskan yaro a wajenka tafi ta kowa yo ta Isa ta fi miracle,nace never sai dai ta bi bayana,wani ya dora na biyu muka kunna muka ga yasa wasu suna chashewa an rubuta yanayi me Dadi,nace ba sabanba yau mun shiga uku,Nawwar magana yayi masa ta private yace Idan ana jin dadin a bar Online mana,Auta dariya yayi ya tura masa ya ranka mu babban Kai ne ba irinka ba an gama da Kai abu kadan sai ka rude mu kuwa sai an sha fama,Kai kuwa an wanke an baka ka shanye,Zanci ubanka wallahi cewar Nawwar sarkin masifa,Auta yayi voice yana cewa Yaya sai ya tsaya yace kashe light please sai Kuma yace sorry Yaya good night munyi can mu, waye yace kayi aure da wuri ka shanye dadinka kazo ka dameni ya kashe wayar gaba daya ya kwanta bacci abinsa..
Nawwar yana jin muryar Auta yace lallai yaron nan ya rainani yana magana da ni yana wani ce mata kashe light ya rainani na Daina wasa da shi,Nace chill man mene abin raini,dariya Nawwar yayi yace Allah Yan Makaranta abu kadan yanzu sai turanci nan gaba ma naga Alama Hausa Zaki daina,dariya nayi tare da makalewa a jikinsa,yace ga cikina yana ta girma Allah yasa a haifo min mace na fi son mace,Nace Ameen Allah ya bamu me albarka.

Washe gari da asuba Auta ya tashi mutumin da kullum sai an tasheshi ya tafi masallaci Sallar asuba indai Mami bata je ba bazai tashi ba sai rana ta fito yawanci yake Sallar safiya amma yau harda tashi da asuba,Light ya kunna yace to ya zanyi na zama Mijin wata Idan ban tashi ba ace banyi hankali ba,brush yayi da Alwala ya fito sanye cikin jallabiya harda rike carbi fari ya tako dakin Salma ya Murda handle kofar ta Bude ya Dan tura kofar a saman Sallaya ya isketa zaune yace cab duk sammakon ka wani a tafe ya kwana munafuka itama Dan tayi aure ne wai ita ta gari bayan mata da yawa basa Sallah akan lokaci wasu ma sai suce sai su gama ayyukansu suke hadawa,juyawa yayi ya rufo mata kofar tana jinsa domin a fili ya furta maganarsa tace Dan kawai Addua nake ne da na rama amma zamu hadu ne.
Yau Mami tana sa Ido ta Samanta ta leka part din Auta ta gani ko zai fito Sallah ko uban baccin nasa zaiyi sai kuwa ta Ganshi ya fito harda carbi da jallabiya,Baffa ta Kira tace zo kaga Auta me gida,window din ya karaso tare da rungume Mami ta baya suna kallon Auta suna dariya,Baffa sahu daya suka yi da Auta yau,sai da aka idar da Sallah ya tsaya harda azkhar sannan suna fitowa yace Baffa barka da asuba Ina kwana? Baffa yace sai kazo ma gaisa a hanya zaka gaishe ni,yace ni fa yau bazan zo ba bacci zan koma 12pm Kuma ina da lecture,au yau ma baza ka hakura da school ba kana Angon,yace me zan mata to shike nan sai na dinga zama,Baffa ya Kalli Auta yace Auta Anya kuwa kana son yarinyar nan duk mugun son aurenka,Ina sonta mana ya furta a ransa yana cewa karya nake bana sonta,sai da zasu rabu kowa zaiyi bangarensa yace ka gaida Mami,Baffa yayi dariya yace to zata ji ya tafi,Yana komawa bacci ya kwanta ya dinga bacci,Salma kuwa tuni ta koma bacci,sai 10am tashi tayi ta gyara gidan tace wallahi bazan gyara masa daki ba,wanka tayi taci kwalliya cikin leshinta na lefe brown and golden color tayi kyau,mayafi ta yafa ta fita taje part din Mami ta isketa a kitchen a kasa ta durkusa tace Ina kwana Mami,Mami taji Dadi taga hankalin Salma,ta amsa da fara’a,bayan nan ta fice tace zata je ta gaida Sauran tana mikewa Baffa ya fito cikin Shiri zai fita,ta sake zubewa a kasa guruf tace Ina Kwana ya amsa tace an tashi lafiya ya amsa da fara’a dama Baffa ya tsani gaisuwar zamanin nan da akeyi mussamman yaran yanzu ana ganin wayewa ce ko wacce Ina kwana wasu ma kafin ka amsa sunyi gaba Babu mutunci ba girmamawa Ina kwana kawai sai yarinya ta wuce ta barka nan,Baffa yace Honey zan fita,Salma kunya ta kamata a ranta tace bariki kan Uba tsofai tsofai a gabana cab wai honey,tana tsugune taga Mami ta rike hannayensa tana kwarara masa Addua,Salma tana satar kallon su ta mike sum sum ta fice kunya ta isheta ita Kam,part din wise ta shiga dauke da Sallama a bakinta Papa ya wani kwantar da Kansa a kirjin Wise suna Palo kuma,Baffa ganin surukarsa ce ashe ya tashi da sauri,Shima durkusawa tayi ta gaida shi ya amsa da fara’a ya tashi ya koma bedroom,tace Aunty Ina kwana? Wise tace ai ni kawarki ce yarinya tashi ta jawota saman kujera tace da Alama kalau kike wlh Auta ba abinda yayi gaskiya Ina Jira nazo gashi,Salma tana jin kunya tace sai kace wata kaza,bata Dade ba ta tafi wajen Iyamami Sabreen ta koma can da kwana ta gansu tare suka mata wani kallon banza suka watsar da kyar ma suka amsa gaisuwarta,Iyamami tace ashe da sauran hankalin da kika San kizo ki gaida manya Allah ya kyauta ko a Ina Auta ya kwaso Sabreen ta karasa da oho masa,Salma ta kalle su ta balla musu harara ta juya fiya fiya ta fice, Iyamami tace Iyye kaga yar iskar yarinya to dama tun kafin a aurota an zuga ta,lallai an sanar mata mune shegun gidan nan zata ci ubanta,Sabreen tace kyale banza can zata yanka.

Salma part dinta ta koma tana shiga ta samu Mami har ta Aiko musu da abinci,Auta ta gani ya fito daga shi sai wando 3qutr ya fito da mopper da tsintsiya ya gyara bedroom dinsa tsaf da toilet,tazo zata wuce yace dadin abin Allah ya mana hannu Kuma ya bamu lafiya mu bamu Saba kazanta ba,binsa tayi da kallo gaba daya ta shagalta da kallon surar Auta Dan dagwas har ta manta ma a Ina take ta shagalta ta tsura masa Ido,yace Hello,hankalinta ta dawo tace ai kasan ba Kai kadai bane a gidan da mutane to baka birge ba ka Maida rigarka ka Saka ya fiye maka na gaji da ganin muninka,Auta yace sannu uwata Mami ya ja tsaki yaje ya ajiye mopper ya dawo ya wuce sama abinsa wanka ya fesa ya sha kana nan kaya ya dakko yar jakarsa ya ratayota ta wuyansa ya fito Dan gaye anci swagg, Salma ta zuba abinda take so tana ci,ya fito ko kulashi bata yi ba tana Shan tea tana danna wayarta karama Vivo,cup ya dakko ya zuba tea ya hada abinda ya sha yaci chips kadan ya dauki chegum me tsada ya jefa a bakinsa,ta kalle shi ta tabe baki tace Iyayi mu ayi mana Iyayi mene bamu sani ba Mami Son kawai, komai sai an baka ai Kai a garin nan baza ka taba samun aikin yi ba,ga mate Dinka nan suna Neman na kansu kaje gari ka gani Yara kanana sun zama attajirai Kai kuwa sai dai a baka ka dogara da kudin Iyaye,a haka Zaka iya daukan nauyina,Auta yace Allah ya baki lafiya naga Alama baki da hankali,Salma ta mike tare da rike kugu tace Kai waye da zaka fada min magana,tsaki ya ja ya fice ya barta tana kwafa,cikin fushi ya fito a fusace yana cewa yarinyar nan naga Alama bata da hankali,Nawwar ne ya juya kan kan motarsa yayi parking ya iske Auta yana Shirin shiga motarsa da Baffa ya siya masa gaf da aure,yace Ango Makaranta Kuma? Auta ya kalle shi kawai ransa a bace,yace Auta kalau Ango Kai da za a ga kana nishadi,Auta harara ya zubawa Nawwar ya shige motarsa ya wuce,dariya ta kama Nawwar yace duk yanda akayi Amarya ta hana Auta kanta haka ya kwana Babu komai, haka nema ya furta tare da shiga bangaren Mami.

Mami tace Kai Kuma lafiya kake dariya Kai kadai yace ni da Auta ne kinga uwar hararar da ya min ya tafi fa school,Mami tace so soon haka har ya tafi? Yace ae Kuma yana fushi,tsokanarsa kayi maybe,Nawwar yayi dariya yace Anya kuwa Auta yana son yarinyar nan Mami,Mami tace Nima Ina ganin da wani abu kawai bazai fada bane sabo da Auta da aure amma ace gidan ma sai da na tasa keyarsa gaba yaje,Nawwar yace Allah? tace ae fa abin da mamaki wlh Kuma shi ya zabo abarsa bare ace mun takura masa,Nawwar yace lallaba shi zakiyi ya fada Miki ke Zaki iya jure iskancin Auta, kyale shi Idan haka yaci gaba da faruwa zan gane ai,Nawwar yace shi yasa na fada muku Auta ba wani hankali gare shi ba girman ne kawai kuka ki ji,da masifa Mami tace to munyi masa din kaji min yaro ka fa damu Autana,ai shi baya laifi dama,ae naji Dalla tashi ka tafi ni,Nawwar yace yau bazanje aiki ba fa Kuma Rabia na Kai Unguwa bata nan,Ina taje? Gidan Seraline wai zata yini a can,Salma tana gama karyawa ta wanke kwanikan ta yafa mayafinta ta taho part din Mami ko ta samu saukin tunanin Baso a ranta.

A hankali tayi sallama ta shugo ciki Nawwar ta gani taga suna kama da Auta tasan shine yayansa harda jin kunyar Yaya,a gaban Nawwar ta durkusa tace Yaya Ina kwana,ya amsa tace Ina Auntyn fa? Yace taje unguwa kuna lafiya? tace lafiya Alhmdllh, gaban Mami ta koma ta sake durkusawa tace Mami ga kwanikan Ina za a ajiye? Mami tana sani tace ya tashi kuwa? tace ae ya tashi,Nawwar yace wai wa? Salma tace me can wajen take nufi fa,Nawwar da hannaye ya dafe bakinsa dariya zata kamashi wai Auta ne me Can wajen sai kace tsohuwa ita baza ta fadi sunan Miji ba Babu kyau wai,dariyarsa ya boye yace ai ya tafi school tace ae,yace a gaishe ki Mami cewar Salma,Mami tace wa fa? tace shi din,Nawwar jaridarsa ya dauka tare da rufe fuskarsa yana dariya a boye,Doguwar kujera ta samu ta kwanta a kai sai bacci, Ya kwashe ta ta dinga bacci sai gani suka yi tana ta uban bacci sai da azahar tayi sannan ta tashi lokacin Nawwar har yaje masallaci ya dawo tana yin Sallah ta Kuma kwanciya a saman Sallaya sai bacci,Nawwar suna ta jira da Mami suna kallonta ta dunkule waje daya tana ta uban bacci,sai ga Auta ya shugo da Sallama ya ganta tana bacci,Mami ta kalle shi tace Yan Makaranta,yace Naam na dawo ya mikawa Nawwar hannu suka gaisa,ya nemi waje ya zauna yana satar kallon Salma yana Galla mata harara Mami tana kallonsa duk abinda yake Nawwar tayiwa signa da Ido Auta harda turo baki yana kallonta yana auna mata zagi a hankali,Nawwar da Mami suna ta masa dariya a boye har Salma ta Farka tana tashi taga Auta itama Ido ta faka ta zabga masa harara har da ce masa Yan Yan Yan kasa kasa a boye,ta murguda masa baki tayi fari ta masa wani up and Down,Mami suna ganin komai ga Auta ya nuna kamar baida hadi da Salma itama haka ba ruwan wani da wani,ganin Mami zata gane su sai Salma tace sannu da zuwa,Nawwar yace lallai yarinyar nan ta iya munafurci ta gama hararsa,Auta yayi murmushin dole sannan yace tashi mu tafi oya come come let’s go,ta mike tace Yaya ka gaida Aunty yace to,Auta harda sakalo hannunsa ta wuyanta suna fitowa ya hankadeta saura kadan ta fadi,ta juyo a fusace tazo ta hankade Auta da karfi ta wuce tana tsaki.
Mami kuwa tace ka gani ko ji yanda suke harar juna,Nawwar baki ya tabe yace matsalarsu ce ki kyale su kawai.

Salma kitchen ta shiga ta dakko juice zata sha Auta yace mayunwaciya look at you kinga banza ta fadi kin wani dakkowa mutane lemo ya fisge ya Maida kitchen,tace ai Kai Kam baka gaji iyayenka ba wlh marowaci akan lemo kalleni tsaf na maka kama da yar yunwa,Kai kana da kudin siya ne? Ba su Mami bane suka zuba maka komai ba ina kaga kudin ko zaka iya siye ne? baza ka iya siyan ko tissue da kudinka ba komai sai an maka Kai tafi can Kuma lemo ne sai na sha sai dai ka mutu,ta Koma kitchen ta dakko, sai ga abincin Mami an kawo musu ,tace nikam na shiga uku komai sai anyiwa me gida bashi da ko taro,Auta ya tsaya kawai yana kallonta sabo da ta buwaye shi ta rainashi da yawa, ta jawo abincin tace mutum komai sai dai ayi masa na zama matar ladan Noma,flask din ya fisge yace ai ba daga gidanku aka kawo ba,hannu tasa itama zata fisge ya rike gam ta kama hannunsa ta gartsa masa cizo,Kara ya saki ya saki flask din ta kwace tace sai na ci to Dan bakin ciki sai dai ya mutu,Auta yana yarfe hannu yace hungry girl mayuwanciya ko kunya bakya ji,tun Ina yarinya na siyar da kunyata ni Kuma a gidana ba Wanda ya Isa ya hana ni cin abinda nake so gidana ne dole inyi abinda nake so yawwa ehe sai dai ka mutu,Auta ya rasa ma me zai ce sabo da haushi yace na tsaneki,Nima haka ta furta tana cin fried rice dinta da kaza tana wani zukar kemo harda wani Jan lemon yana Kara zuuuu zuut tashi daya ta shanye karamin kwalin guda tace Dan jeka kitchen ka dakko min wani,yace baki da kunya ya juya haura sama,sai da yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya marasa nauyi ya fito yana zuwa ya samu taci iya nata ta kwashe komai ta maidawa Mami sauran,tace ya naga kadan aka ci? tace yace ya koshi shi yaci a waje,Mami tace Autan? tace ae yace yaci a school,shike nan cewar Mami ta juya ta tafi ta iske Auta a zauna yana latsa waya yace Ina abincin? Na mayarwa masu shi tunda Kai komai sai dai ayi maka baka San ka nemi na kanka ba,Auta baki Bude yake kallonta yace Amma dai wiwin Baso ta taba Miki kwakwalwa kema? Karka dameni bani da lokacinka,kwafa Auta ya ja ya fita tace yaro karami kusan sa’ana sai Iyayi da nawa ya girmeni ta gyara zama tare da harde kafafu tana cewa wahala ma sai ta sa ka sakeni na koma wajen baso na.

Auta bai je wajen Mami ba tunda ta Riga ta fadawa Mami ya koshi sai ya shiga wajen Wise yace wai abinda baya so aka dafa taliya,Wise ta zuba masa abincin ya ci ya koshi yayi tafiyarsa ya bar gidan gaba daya.
Bacci taci ta koshi, kamar taci kafar Kare haka yamma nayi tayi wanka ta shirya cikin shadda ta tafi bangaren Wise suna ta Hira tana rage tunani.

Washe gari ma haka suka yini fada da Auta ba ji ba gani,har suka kwashe sati biyu a haka fada baya karewa, basa Shiri Sam ganin haka Mami tana fahimta taji tsoro tunda Yara ne kar azo ayi saki, Auta ta samu Yazo gaisheta,tace fada min uban abinda kake boyewa wallahi ko na fita harkarka,yace me kuma Mami? Karka raina min hankali nifa na haifeka nafika sanin waye Kai wallahi Idan baka fada min dalilinka na auren wacce baka so ba to ba ruwana da Kai Karka sake zuwa inda nake,Auta badan ya so ba kawai yace kiyi hakuri Mami ya bata labarin Salma kaf ya fadi gaskiya,Mami tace Auta baka da hankali ashe,Matar da bata sonka kasan kuwa kiyayyar mace Idan ba ta son mutum,me ya kaika wani biyan kudi ka aureta bayan kasan wani take so,Auta yayi mukus Mami ta dinga zazzaga fada,yace Idan kin yarda nan gaba ai zan rabu da ita ma,shut up zaka Raina mana hankali mu ai wasa muka maka ba cewa mukayi zamu yi maka auren dole ba shine ai gashi Kai ka yiwa kanka auren dole Mafi Muni ma,wacce zuciyarta wani take so,to ko da wasa ba saki kayiwa kanka wlh baka Isa ka sake ta ba sai kuyi ta zama a haka matsalarka ce,Mami taji zafin Salma bata son danta dama,amma Kuma Auta shi ya jawa kansa.
Zuwa Mami tayi tace Salma ta dawo part dinta kawai aka kwaso kayan Salma na sawa aka bata dakinta a kasan Mami,Shima Auta ya dawo part din Mami da dakinsa,Mami tace kowa yayi harkarsa muga abinda Allah zaiyi.
Salma kawai sai ta mike kafa kamar gidan ubanta a gaban Mami ma fada suke yi da Auta.

Yau Auta yana zaune Mami tana gefensa tana Yanke masa farcen hannu, Salma ta biyo ta saitin kafarsa tayi fatali da kafar Auta,Mami ta kalleta kawai harda shagwaba kamar uwarta ce Mami tace a canja min channel,Auta yace wai gidan ku ne kin fa ishe mu kina gani Mami ta min ball da kafa Autanki guda kisa ta bani hakuri,Mami tace ke Salma ki Daina haka Mijinki ne fa,Salma tana dire diren kafafu tace ni Allah Allah…shike nan sorry ta zauna ragwaf a kujera,Auta yace bata da kunya fa Mami shame on you ya furtawa Salma,tace na karbe hakuri na Dana baka nafi karfin na baka hakuri,yace ke Dalla kucaka,tace ai gwara ni kaifa kwaila da Kai zaka iya siyen tv ne ko tv Kana da kudinta ta fisge Remote din,Mami tana jinsu bata ce musu kala ba dariya ma take a ranta ana mata maganin Auta,haushi Auta yaji yace Mami kina jinta ko garin kwace hannunsa Mami ta Yanke shi kadan da razor Auta kamar Wanda aka kwadawa Adda ko wani takobi haka yake yana yarfe hannu,Mami tace Kai Kam Allah ya sawwake maka kamar ba Namiji ba,tissue ta sa tare da danne masa wajen,Salma tana masa dariya tace sai kace ba Namiji mu kayi mana shuru.
Yace Mami bani ruwa na sha ko na ji salama,Mami ta mike zata dakko masa ruwa Salma tace Mami da kanki kamar wannan ya aikeki ki zamanki ya tashi da Kansa ya sha ya dawo,ke da uwata Zaki rabani marar tarbiyya ya ja tsaki,Salma ta dauke Kai taci gaba da kallonta.

Salma Allah ya yita da gasa sabo da yarinta da kuruciya Idan taga kusan sa’anta yana abu sai ta fara yi itama,Auta ta Raina an mata kananan kaya sunfi akwati biyu sabo da su can normal ne ana sawa bare Kuma matar aure,ganin Auta kullum cikin kana nan kaya yake sai itama ta koma sawa su normal ne amma sabo da ita ba a can ta taso ba tana ganin ko mace ce ta shugo sai taje ta Sako katon Hijab,komai Auta yayi sai tace sai tayi itama,Idan Mami ta masa abu itama fa sai anyi mata,daga gani Mami ta taje masa gashi,sai bayan kwana biyu tazo gaban Mami ta durkusa har kasa tace Mami kin iya kitso ki min Nima? Mami tace na iya,tace kalaba nake so,tace to bari ayi Sallar la’asar tace to,ita Salma tana birge Mami sabo da biyayyar ta da kunya sannan ga addini Sallah bata wuce,Auta 4pm ya dawo daga school ya shigo ya dora Kansa a cinyar Mami sai ga Salma ta fito ta bata rai tace matsa min,ko kulata baiyi ba,tace Mami kice ya matsa min ai kitso za a min tsaki ya ja ya tashi ya koma daya kujerar kasa kasa tace kwailan Miji kawai tana turo baki,Mami dariya ta kamata haka yake cewa Mata ko wacce yace kwaila ce yau gashi an ramawa su Omaira cikin ruwan sanyi,ran Auta Idan yayi dubu to ya baci kamar zaiyi kuka zaiyi magana Mami tace enough haba Enough of this nonsense ku kullum fada ke Salma Mijinki ne fa kike masa, haka kikaga anayi akan banzan tunaninki,sabo da bakwa son juna ku zauna lafiya mana,bana son rashin kunya Salma Mijinki ne fa ke ana lallaba Miji ana masa biyayya ke Banda ke kowa haka kika ga yana yi,Kai ma ba ruwanka da ita kowa yayi harkarsa, Auta yace dama matsalar da nake gudu kenan da auren kwailar yarinya indai ka hada harka da kwaila to ka shiga uku yanzu babba me hankali wacce tasan me takeyi zata yi abinda wannan sharar takeyi wannan tarkacen,indai mace ta mallaki hankalinta Ina zaka ga wannan shirmen,Ya Isa haka kayi hakuri kuyi hakuri da juna shi yasa fa na dawo daku nan gabana wato ban Isa ba ko bani da amfani,Salma zama tayi a kasa a gaban Mami tace kiyi hakuri Dan Allah tana so tayi kuka,Mami ta cire mata dankwalin gashinta dogo baki yala yala da shi ya bayyana yana sheki Mami tace Masha Allah Auta ya tabe baki tare da dauke Kai,Ita Kuma Salma dama ta Saba da kuka a gida tunda kullum sai tayi ita da Baso,Basonta ta tuna ta fashe da kuka wai an mata fada sabo da samun waje,Auta a ransa yace dama talaka bai iya samun waje ba,yarinyar da kullum sai an jibgeta na tausaya mata na aureta yau na zama kamar sa’anta ba komai kaima Allah ya Kara maka da Omaira ka aura da duk ba haka ba gadon soyayya tsaki ya ja yace a fili Wanda baiji bari ba ai yaji hoho rubbish ya tashi ya fice.

Nawwar ne ya shigo ni da shi cikina ya tsufa sosai,Mami tace daga Ina haka? Nace asibiti muka je muka biyo,Salma tana ta kuka,Nawwar yace lafiya take kuka? Mami tace gata nan tambayeta ta fada muku da bakinta,Salma tana kuka da shesheka tace sh…sh..shine…Nawwar yace shine wa? Shi….nace waye shi? tana goge hawaye tace Me can wajen, na kwashe da dariya nace Auta? ta daga Kai tace shine yake tsokanata har gori yake min,Mami tayi salati tace Salma kiji tsoron Allah Auta ba abinda ya Miki yana zaune kika ce sai ya matsa Miki ke Zaki zauna kina masa rashin kunya,kiyi ta kukanki tunda ke baza a fada Miki gaskiya ba,Nawwar yace to kiyi shuru za a masa fada kinji,ta goge hawayenta tace to,Mami tace bari na dawo ta nufi kitchen sai ga Auta yayi wanka ya dawo cikin 3qtr da Riga me gajeren hannu, hannunsa daya a aljihunsa daya Kuma wayarsa a rike yana latsata.

Salma tana ganin shine ta mike tsaye taga ya nufi kujera ya zauna komawa tayi wajensa tana kallon kitchen kar Mami ta ganta tace tasar min ni nan wajen nake so a nan zan zauna,Auta iya kulewa ya kule amma ya shareta ya tashi ya koma dayar ya zauna Salma ta zauna tayi irin zaman Auta ta harde kafafu ta fito da vivo dinta tana dannawa itama,yana cin chewgum kawai ita ba chegum a bakinta ta fara tauna itama,ni da Nawwar muka zuba Ido muna kallo kamar Film,dariya kawai suke bamu,Auta yana da abin hannu a tsintsiyar hannunsa na Samari Salma ta gyara nata na mata, juyowa tayi Shima ya juyo suka hada Ido gwalo ta masa,Hannu ya Kai zai dauki Remote ta Riga shi daukewa tana sani ta Kai tashar cartoon,Auta ya zuba tagumi da hannu Daya ya ajiye wayar a gefe ji yake kamar ya lakada mata dukan tsiya.

Nawwar ne ya Kalli Auta suka hada Ido Nawwar yace Matata tafi ta kowa ya rike hannuna,yasan da shi yake sabo da status dinsa ranar da ya shiga dakin Amarya,tashi yayi a fusace ya shiga kitchen yace Mami ki wa Yaya Nawwar magana tun dazu ya zuga matarsa sai Kallona suke suna min dariya,Mami ce ta fito tace waye yake taba min Baby,Nawwar yace ba ruwanmu daga nace Matata tafi ta kowa,Auta yace wlh da ni yake ai na sani, Mami tace ku tashi ku bar mana gida ta Kori su Nawwar.

Mami tana shiga kitchen ya zo ya zubawa Salma rankwashi tare da furta marar tarbiyya yar Namiji,dama tunda Baso ne ya rike ki Ina Zaki hankali,oho maka dai .
Bayan kwanaki kadan Salma ganin Auta yana ta zuwa school sabo da kwaikwayo sai da taje gaida Baffa bayan sun gaisa tace Baffa dama alfarma nake nema,yace Ina jinki,Salma tace tunda na gama secondary Kuma result Dina yayi kyau Dan Allah ko yar college ce ka sani,Baffa murmushi yayi yace ki kawo min takardun naki ta dinga murna,dama ta taho da abinta,Mami ta samu itama ta fada mata,tace kinyi hankali Salma Kuma kin birgeni,taje ta dakko takardunta ta kaiwa Baffa Wanda ya kamata a nema aka Nemo mata aka mata registration a Makarantar da Auta yake zuwa bai ko sani ba sai da zata fara zuwa Baffa ya sanar masa,ransa ya baci akace Kuma tare zasu dinga tafiya su dawo,amma department din Salma daban ita microbiology tace tana so shi Kuma Business time table dinsu kusan lokaci Daya ne,har waya Mami ta siya mata me tsada Samsung.

Yau Monday da wuri ta shirya cikin Arabian gown peach tayi rolling ta sa jaka arsh da takalmi me Dan tufu Arsh, 9am suna da lecture har Auta,ta fito da wuri ta tsaya a jikin motarsa tana waya da Baso yana masifa karki dameni da Kira fa haba jiya kin kirani yau ma haka wanne naci ne wannan ya kashe wayarsa,Nan take idonta ya cika da hawaye sosai ta kasa cire Baso a ranta sabo da Baso take ta yiwa Auta rashin mutunci ko zai gaji ya sake ta ko ya koreta amma yaki,Auta ne ya fito cikin wankansa na farin jean rigarsa silver yayi kyau ya sa glass me kyau a fuskarsa,ganinsa da Glass Salma hankalinta ya tashi da Mami ta bata kudin Makaranta taki karba amma ganin glass din Auta ta koma ciki da gudu,Sai da Mami taji tsoro tana haki tace Mami bani kudin school din na tuna zanga abin ci, Mami murmushi tayi ta bata dubu Daya,ta fito da gudu,Auta har yayiwa motarsa key ta Bude gaban motar ta shiga tana haki, tsaki ya ja yace da kin sani karki fito ki gani Idan zan jiraki,Salma tace ai dai motar ma siya maka aka yi baka da kudin siya,zaka iya siya ne? Ina kaga sana’a baza ka iya ba,Auta yace Mannerless kawai,ya fisgi mota suka tafi,suna zuwa school din taga Yan mata masu aji sai rububin Auta suke,suna cewa Nawaf kanwarka ce? Salma tana fitowa tace matarsa ce,sai lokacin suka tuna Auta fa yayi Aure suka dinga yabawa da kyawunta wasu Kuma suna kishi,Auta yace muje na rakaki bangarenku suka jera suka wuce suna tafiya yace ba tarbiyya kwaila dake sai jaraba duk kin gado jinin Baso mayya ya hankada keyarta ta kusa kifawa,tace kana wani girman Kai da fadi Kai ga me masoya wani Nawa….kasa karasawa tayi sabo da Baso yace sai taci ubanta Idan yaji ta Kira sunan Miji gatsal sai ta fasa cewa Nawaf tace sabo da Kai Kaine,yar kauye kina birni amma kamar a kauye kika girma foolish girl,har aji ya Rakata ya juya ya koma nasu,duk ajin yawanci kusan ba musulmi Allah yasa Makaranta me kyau tayi ta samu foundation me kyau,wasu suna ta Yaba kyanta suna tambaya amma ke Fulani ce? Itama da turanci ta basu amsa tace Kuma tana da aure,suka dinga dariya suna mamaki dama wai sun San Hausawa da auren wuri yar yarinya sai a ganta da Yara su sai sun tsofe a gida yawanci.

Suna gama lectures dinsu na yau ta fito ta sha yawo kafin taga Auta ta hango shi zagaye da mata suna ta duba littafi duk christian ne,Salma ko magana tana zuwa ta kutso ciki ta fisgo Hannun Auta tace tarbiyyar taka kenan harda rike kunnenta kunnenta wato baka jin magana ko muje to,fuska ya bata yace zan karyaki wlh nan ba a gida muke ba ya fisge hannunsa,juyawa tayi ta dinga zaga school tana kallo har ta hango masu Saida glass suna wucewa ta samu Dan fake fake ba me tsada ba Dan dari takwas ta siya ta kafta abinta itama a fuska harda yanga,ta fito waje taga masu siyar da agwalima da kwakwar manja ta siyi kwakwar manja ta wanke da ruwa ta Maida cikin Leda fara,Auta ne ya mata mahaukacin horn da mota ta juyo a fusace taga shine zagawa tayi ta shiga gaba yaja suka tafi tana cin kwakwar manjanta,ta dakko guda biyu ta mikawa Auta ungo ni badan halinka ba,ko kulata baiyi ba haka suka koma gida,ta Riga Auta shiga ciki Mami tace an dawo? tace ae Mami,ke kadai kika dawo? ta girgiza Kai tace a’a da shi muka dawo,Mami sai da tayi dariya again ita baza ta fadi ko Auta ba ma,Auta ne ya shigo ya zauna a gefen Mami Salma ta dawo daya gefen ta zauna suka sa Mami a tsakiya,Auta yana ganin kwaikwayo shi Kam yace wai ke babarki ce? baki ta turo zai kwanta a kafadar Mami Salma ta ture Kansa yace wai mene haka wanne irin iskanci ne wannan ni sa’anki ne wai,Salma tace to da nawa ka girmeni,kwafa ya ja, Mami tace haka kika je Makarantar kuna yi kenan,Salma tace Mami wallahi yayi watsi da tarbiyyarki kullum a cikin Yan mata yake zama bashi da abokai maza sai mata kowacce ta dinga yagula sunansa anyhow kowacce da tazo shi, shi,Mami tace me yasa bakya fadar sunansa ne? Salma tace fada aka min akace ba kyau, Mami tace to ga Auta,ga sunaye nan ki sa masa mana wani a ciki,Salma tace wannan zanwa suna ai sai dai na kirashi da mugun bawa kawai,Auta yace marar tarbiyya,Mami tayi dariya ta mike tace sai kuyi ai kunga tafiyata,Auta ya mike tace Mugun bawa, yace marar tarbiyya.

Cele ce ta duba riyal biyu dinta bata ganta ba Kuma a saman bed dinta ta ajiye fitowa tayi tsakar gida akan riyal biyu kacal tana cewa Allah ya tsiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiinewa Yan gidan nan shegu Yayan madugo,baza Kuga Annabi ba duk wacce tasan ta dauka ta fito da ita wallahi ko ta hadu da fushin Cele yar mutanen Kaduna,wacce tasan ta dauki riyal biyu ta fito da su ko ta hadu da Halin yar mutanen Kaduna,akan haka sai na tafi Ka’abah nayi dawafi,wallahi duk wacce bata fito da ita ba sai naje nayi dawafi cikin mace ya kulle ta mutu duk shegiyar data San ta daukar min riyal biyu ta fito da ita ba mutunci gumina ce ba haramci na aikata ba na samu,banyi madugo an lagudeni na samo ba,banyi kawalci ba,ba wajen boka naje ba sana’a nayi na samu gumina nace,Babu mutunci ba tsohuwa ba yarinya wallahi a fito min da kudi baza ku amfane ni ba, ‘ya’yan wata shegiya, ‘ya’yan wani Dan banza,wacce ta kawo Cele tana zaune duk suna nan kowa yayi shuru sai wacce ta kawo Cele tace Dan Allah dakko kayanki wallahi ni na yafe Miki kudin haya zan biya Miki zaman da kikayi hada kayanki ki tafi,Cele tana wani jingina da bango tana dagowa tana komawa tana fari da Ido da bala’i tace ba Dan Iskan,Babu yar madugon da ta Isa na bar gidan nan zama daram sai sanda Allah yayi tashina Ina nan,Kuma bance ki biya min kudi ba yawwa ficikarki ta haramci bazan ci ba, Yayan masu baki da kunu ma basu Isa ba,Raliya tace ke wallahi ki kiyaye mu ni tunda naga harkarki ba mutunci ba arziki a cikinta na fita shirginki bana kulaki karki sa Dani wallahi zuriarki kaf har na kabari sai na zage su tas.

Bazawarar dariya Cele tayi tace ai ni bari kiji bana cecekuce budawa nake da mutum in daka mutum in lugude shi, Allah na tuba bare ke da kike kamar karmami duwawu kamar kaskon soya manja,Idan kin Isa mu hadu a filin badar sai muyi yaki a can,sai da su Samira suka yi dariya,Samira tace fadan ma sai anje filin badar? Ai ta tabbatar ni bada wasa na fito ba,ke a yanda na fito nazo takari daidai nake da ko uban waye,ni ba a tabani ba ma ni kadai bala’i nake wa kaina bare an kulani an shiga gonata ,akan Riyal biyu ta billahillazi ji nake kamar zanyi aman wuta gwara ko wace ta kiyayeni,ji nake kamar na zama dragon na muku feshin wuta karku sake kaini bango wallahi yau baza ku runtsa ba tunda baku da mutunci abu ya hade muku biyu ga madugo ga sata wannan wacce masifa ce riyal biyu ta a dauke min a dake ni Kuma ace za a hanani kuka,mace daya ce ta min abinda bana so na kyaleta a garin nan Kuma itama na Riga na Mika karata wajen Allah,Meenal ce ta zaro riyal biyu tace indai akan wannan ne gata ni na baki kyauta,Cele ta tsani Meenal ta karba ta hada kudin da kan Meenal ta maketa sosai tace na tsaneki wallahi mayya bana so ai ni dake ba sauran mutunci mun kulla kenan tunda kika taba min dukiyar maza na wallahi bana sonki,Dattijan sukayi shewa suka ce au nono ne dukiyar maza, wannan jarabar nono sai kace an taba wata tsiya,ana kera shi ne a gidanku?Cele ta tambaya, Suka yi shuru. Cele bala’i take ba ji ba gani sai ga matar da Ahsan ya turo da botikin Awarar ta kwala Sallama

Suka amsa tace wacece Rufaida Cele? Cele ta daga hannu tace I’m ya akayi ko kece kika dauki riyal biyun yanzu ki karbi rabonki? Matar tace a’a ni wani ne ya aiko ni yace a kawo Miki wai naki ya fashe gashi,Cele ta karba sak irin na awararta,tana mamaki tace waye wannan haka ni ba mashinshini ba tunda nazo garin nan banyi masoyi ba sai Yan madugo,Matar ta bude baki tace Subhannallahi Allah ya shirya su ashe ba Neman kudi suka zo ba lalata suka zo yi kusa da dakin Allah wallahi irinsu ke bata wasu gaba daya ake mana kudin goro,duk sun bata gari ana kallon takari marasa daraja,Cele tace ai mutanen banza ne wallahi da dare haka suke lalubeni wata tsinanniya ma ta taba min albarkatun kirjina Ina bacci ai kuwa na tsine mata albarka zata gani Kuma,Matar tace Allah ya shirya wannan ba gidan zama bane in kin samu dama ki tashi,Cele tace so nake dukkansu na koya musu darasi gasu nan har tsofaffin banza.

Matar tace to ni zan tafi,Cele tace wai bakar fatar ne ya baki? tace ae baki ne yace a kawo Miki zaizo yace,Cele tace to maybe a masu siyen Awara ne na gode tsaya na baki tukwici mana ta zaro riyal biyar tace ungo tukwici,haba sai kace yarinya tace Kya ci ko Altuffa,ko Laban wa buskota wai biscuits,matar ta karba tana dariya da godiya ta tafi.

Washe gari Ahsan wanka ya sha cikin kana nan kaya yasa Driver ya kaishi inda Cele ke zama tana siyar da Awara,yayi parking yana mota yana kallon Cele tana zuba ciniki,kudi ya bawa driver yace yaje ya siye awarar duka ya rabawa masu siya kyauta,Driver ya fita yaje ya samu Cele da Hausa yace Hajiya nawa ne dukanta? Cele tace duka Kuma botiki biyu fa,yace ae sadaka zanyi naga ana siya zan rabawa alumma Cele ta fada masa ya bata kudin gaba daya ta tashi tana gyara mayafinta bata San da mutun a motar ba taje jikin mudubin motar da Ahsan ke ciki a zaune tana gyara mayafinta ta zaro lipgloss a jaka ta shafa ta gyara mayafinta da tayi rolling ta jingina da jikin motar tare da harde hannayen ta a kirjinta,Ahsan yana kallonta shi fes ta ciki bakinsa ya dora a jikin glass ta saitin bayan Cele yana ta zuba kiss bata sani ba ji yake kamar ita yake wa kiss din,sai kissing din glass yake.

 

Ayi hakuri chaji ne ya kare

A dinga sharhi yafi Godiyar nan

 

 

AsmaBaffa
08061929616’YAR AIKIN KARUWAI 2
MATAFIYA

BOOK 2

Back to top button