Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 5

Sponsored Links

Page5️⃣

 

Fada masa sunansu sukayi, doctor ammar gyara glass din idonshi yayi yace Muna dawani patient ne Wanda muke bukatar abashi special care Wanda yake cikin coma yanzu haka, so nayi bincike akan Wanda yakamata yakula dashi se bincike na yafado takanku yanzu dole ne mutum Daya nake bukata wacce zata dinga bashi kulawa dakuma attending nashi da wuri Banda letting, yanzu yakuka gani fanan nakokarin magana Amira tayi sauri tace am doctor Gsky sede abawa FANAN kura mata ido sukayi sunason Jin dalilin dayasa tafadi haka,kafin tadaura dacewa nide yanzu Gsky koda ace nice zanna kula dashi tofa Gsky bazanna zuwa da wuri ba saboda nasamu addimission a pen resources zanyi degree anan shisa nace abawa FANAN gyada Kai doctor Ammar yayi cikin gamsuwa da bayananta yace to FANAN yanzu gareki daga yanzu aikinki yafara saboda inada yakinin Zaki bawa patient dinki kulawa yanda yakamata.
Harga Allah fanan bataso haka ba har zuciyarta taji badadi domin tasan dole yanzu zatana takura fiyeda dah Amma haka ta kaqulo murmushi dole tayi tace to shikenan doctor allah yabani iKon kula dashi shikuma allah yabashi lfy amsawa sukayi doctor ammar nakara yaba hankalinta da nutsuwarta, kafin yace ke Amira Zaki iya tafiya sallama tamusu tafita juyowa yayi yakalli FANAN yace muje dakin nashi tafiya sukeyi Yana gaba tana binshi abaya harsuka Isa shiga ciki sukayi har gaban gadon nashi Yana kwance besan inda yakeba. kura masa ido doctor ammar yayi tabbas yasan wannan fuskan Amma yamanta, daure masa Kai abin yayi domin kuwa ba shakka yasanshi Kuma sani bana wasa ba sannan baya tunanin a Nigeria suka hadu. Ganin tunanin baze kaishi ba yajuyo Yanawa FANAN Dake bakin kofa magana karaso mana kintsaya awaje. Shigowa ciki tayi tana karewa dakin kallo, sauka idonta yayi akan wani kyakyawan balarabe idan kuwa ba Arab guy bane to tabbas half_cast ne domin kuwa kyaunshi yawuce misali, karasowa tayi tana kallonshi domin kuwa kyaunshi yatafi da ita, duk da akwai oxygen afuskanshi hakan behana kyaunsa bayyana ba, tubarkallah Masha Allah tafada azuciyarta.ashe doctor ammar nata mata magana ita batajishiba tana ta santin kyau din patient dinta, sunanta yakira da Dan karfi FANAN firgit tadawo hankalinta Naam murmushi kawai yayi domin yasan abinda yasa tashiga tunani yace your time Start from now on tace okay doctor. Fada mata Abubuwa masu amfani dazata dingayi yayi kafin yafita yabarta. Warm water tahada a bowl tasa karamin towel tajika tafara goge mishi jikinshi sannan tayi feeding nashi through vein Yi mishi abinda yakamata tayi har zuwa karfe 8:00 nadare kafin tagama komai fitowa tayi tawuce gida.

Tana shiga gida tasamu mama da baba awaje tambayarta suka shigayi meyasa tayi dare, bayanin duk abinda yake faruwa tamusu to shikenan allah yabashi lfy sannan kuma duk sanda zakiyi dare ki kirani awaya ko yayanki azo adauke ki karki Kara dawowa dakanki kinjini ko baba yagama magana Yana kallonta amsawa tayi da in sha Allah baba shiga cikin falo sukayi duk kansu anan tasamu taci abinci. Sannan tawuce dakinta tayi wanka tafito tasa kayan bacci ta kwanta tana tunanin wannan bawan Allah daga gani yayi matukar Jin jiki kudurtawa tayi aranta in sha Allah zatasashi a adduahrta . Ahaka har bacci yadauketa bata sani ba, karfe biyu nadare ta farka taga ashema bacci tayi lalle yau takwaso gajiya mikewa tayi tashiga toilet tayi alwala kasancewar tafara sallah shinfida sallaya ta tada sallah adduah tadinga Mishi nasamun sauki ta idar ta koma tayi adduah bacci ta kwanta.

Washe gari 5:40am ta tashi tayi sallah bayan tagama azkar ta mike taje ta gaishe dasu baba sannan tafara aikinta nayau da kullum tahada breakfast sannan Takoma taje tayi wanka tashirya fitowa tayi ta karya baba yabata kudin transport sannan Ya usman yakaita direct addimission ward tayi taje taduba patient’s dinta bayan ta sallamesu tawuce private ward kamar yanda tabarshi jiya haka tasameshi bayida maraba da gawa karasawa tayi inda yake tamishi duk wasu abinda yakamata.

Sannan tasamu waje tazauna tana hutawa.

Misalin karfe uku Narana doctor ammar yashigo yasameta tana feeding dinshi murmushi yayi yace dakyau nurse fanan aikinki nakyau yar dariya tayi tagaisheshi ya amsa Yana tambayarta yame jiki tace jiki da sauki duddubawa yayi yaga komai natafiya yanda yakamata kafin yafita. Yau da la’asar tafito tahadu da Amira suka wuce gida tana bata labarin yanda patient dinta yake dakyau kamar aljani. Amira da batama ganshi ba harta fara Santi lol .

 

Bayan 3 weeks.

Fanan ce zaune a dakin ta kura masa ido tana kallonshi yaude kimanin sati uku kenan Amma haryanzu bawani approving din da akasamu. Shikanshi doctor ammar abun nadamunshi domin yanda result yanuna baze wuce 1month ba ko kuma balallai yakaiba. Amma haryanzu bacigaba, fita fanan tayi adakin.

Abubuwane suka fara mishi flash a kwakwalwarshi magana yafaraji cikin sautin kuka ana fadin azaad abbanku yayi hadarin mota ahanyar dawuwarshi daga meeting da governor kayi sauri Yana asibitin medical center, Abubuwa ne suka fara tariyo mishi daga lokacin da yafito haryashiga mota har izuwa time din Daya fada Rami daga nan yabude idonshi Yana me rike kanshi dakarfi tsaban yanda yakejin kan kamar ze fashe mikewa yayi Yana karewa inda yake kallo anan yagane a asibiti yake. Mikewa yayi yaje gaban mirror Dake dakin yayi tsayawa yayi Yana karewa kansa kallo ganin yanda yazamane ya tabbatar mishi da yadade anan bincike yafarayi adakin karasawa jikin machine din Dake dakin yayi nan ne yatabbatar dacewa yashiga coma innalillahi wainna ilaijiraji unnn yanzu tsawon wani lokaci nayi anan ummina awani Hali take abba ya Salam. Sujjada yayi Yana Kara godewa allah dayasa yafarka yanzu. Kusada wata yar karamar system Dake ta nuna green din wuta da manyan rubutu yananu na awake ,awake,awake,awake alamun yafarka kenan tabbas in wayanda suke lura dashi suka shigo nanne zasu tabbar Daya farka kashe system din yayi, Jin kamar takun tafiya yasa yayi saurin komawa yakwanta kamar bashi ba. Shigowa FANAN tayi tasawa dakin key takaraso kusa dashi tadubashi sannan Takoma kan kujera tajire hijab dinta da dan kwali taja zib din riganta sbd gabadaya atakure take kayan sundameta bayanda ta iya ne kawai hankalinta akwance saboda tasan patient dinta baya cikin hayyacinsa. Shikuwa Bude ido yayi Yana kallonta, kallo Daya yamata yagane itace ke kula dashi Amma aitayi yarinya duk abinda takeyi akan idonshi jikintane yabata ana kallonta juyowa tayi dasauri rufe idonshi yayi tagama kallonsa kafin taci gaba dacin snacks dinta. Bude idonshi yayi Yana Dan murmushi bayan kamar 30 minute ta mike taje towel tadauko tazo zata goge mishi jikinshi tsayawa yayi Yana ganin ikon allah,mamaki cike aranshi yanzu yarinyar nan harda jikina take tabawa tana kallona shi damuwarshi ma karta kalle inda be kamataba duka duka nawa take, goge mishi jikinshi tayi Takoma tazauna tana haki. Jinjina irin karfin halinta yayi sbd yanda yake dinnan harta iya juyashi ta goge masa jiki tayi, afili tace wash allah na yau kam da wuri zankoma gida gyara jikinta tayi , kusa dashi taje ta tsaya tafara kwararo mishi adduah samun sauki sannan tatofa ahannunta Tashafa mishi afuska tanata murmushi kasa kasa yake kallonta bakaramin dadin adduahrta yajiba.

Bakin mirror ta tsaya ta kallon kanta dogo kanta tayi kawai taga mutum abayanta kamar aljani ihu tasaka tajuyo zata gudu ganin yanda ta tsoratane , taku biyu yayi yariko kugunta aikuwa atake yaji jikinta yasake duba fuskanta yayi yaga tasuma jinjina tsoro irin nata yayi domin kuwa shi bada niyyar yatsoratar da ita yajeba magana yakeso yamata Amma gashi tasume mishi Dan karamin tsaki yaja. Kwantar da ita yayi akan kujera, fridge yabude yadauko….

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story Written by MRS ISHAM

Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

__________________________________________

 

Back to top button