Hausa Novelskawali Ne Hausa Novel

kawali Ne 11

Sponsored Links

*KAWALINE*

 

 

*Zahra Surbajo*

 

 

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

 

*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

 

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

 

*07044600044*

 

 

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

 

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

 

 

*11*

 

 

 

 

Yunƙurawa yayi ya ɗauki maman hankalinsa atashe,da gudu rayhana ta riƙeshi tana faɗin”sauketa baƙin kare,ko itama fyaɗen zakaimata,ka ajiyemun ita nace!!!”ta ƙarasa cikin ƙaraji.

 

Da ƙyar bakinshi ya iya haɗa sunanta,yace”ray-hha-na tana buƙatar taimakon gaggawa pls trust me ba abinda zanmata”ya faɗi hawaye nabiyo idonsa.

 

Da sauri ya juya tana riƙeshi be saurareta ba har saida yasa mama a mota sannan ya shiga,gudun kar ya cutar mata da uwane yasa ta faɗa motar ba tare data san lokacin da akai hakan ba yaja suka bar ɗan lungun gidan nasu.

 

 

Gudu yake bana wasa ba,shiyasa suka iso kano cikin sauri,asibitin malam yakaita direct .

 

 

Duk abinda yadace akai mata sannan aka bata gado sai wajan sha biyu na dare aka gama komai,

 

 

Rayhana duk abinda rayhan yake ko kaɗan be burgetaba dan jitake kamar ta shaƙeshi ya mutu tunda shine silar komai.

 

 

Mota yaje ya ɗauko wata ƙaramar jaka ya dawo yaranƙwafa daidai setin fuskar rayhana yace a tausashe ta yadda bamejin abinda yake faɗin se ita.

 

 

“wannan rayhana milyan biyar ne ki ajiyesu agun ki sabida hidimar asibiti,dan Allah ki kula da mama da kyau,komai daɗewa zan sake dawowa in dubaku,ina me ƙara baki haƙuri akan abinda yafaru tsautsayine banayi da niyyar cutar da rayhana bane nayine dan rama cutarwar da siyama taimin,”ya ƙarasa maganar asanyaye.

 

 

 

Wata uwar harara ta warsa masa sannan tace”se gun rama cuta ka ɗauji abinda yafi ƙarfin kai cutar da akai maka kamaidani mara mutunci,agun mijin dazan aura banida wata daraja,ko nace na yafe maka ƙaryane wallahi bazan taɓa yafe maka ba.”

 

 

 

Murmushin ƙarfin hali yayi gamida runtse ido alamaun maganganun nata sunmasa nauyi,buɗe idanunsa yayi yace a sanyaye”kina da mutunci har yanzu rayhana,kuma dan Allah kici gaba da kama mutuncinki Allah ze shiga lamarin,na barki lafiya,in na shirya ki yafemin zan dawo neman yafiyar”ya faɗi yana murmushi yasa kai yafice”

 

 

 

Jakar kuɗin ta ɗauka da nufin binshi da ita tace basa so saita tuno kwandala basu da ita bare suyi magani da ita,haka ta koma riƙe da jakar ta zauna jijinta asanyaye hawaye na rugujewar rayuwarta na kwaranyowa.

 

 

 

Miƙewa tayi ta shiga toilet ta tsarkake jikinta,santa take tsarki taji irin badaƙalar da aka aykata mata sake rushewa tayi da kuka,da kyar ta rarrashi kanta ta kammala ta fito,ta rama sallolin da ake binta,bayan ta wanko inda jinin ya ɓata mata hijabi a toilet ɗin

 

 

 

********

 

 

 

Rayhan koda ya isa hotel dan ya kwana in gari ya waye ya tafi,kasa bacci yayi se safa yake da marwa a ɗakin,kyakkyawar fuskar rayhana da sunanta ne kawai ke yawp akansa da zuciyarsa,ra gefe ɗaya kuma tausayinta yake ji,shiyasa ya zaɓi yin nesa dasu dan tasamu ta rage jin zafinsa dan in ga zauna kullum cikin tsanarsa zata kasance .

 

 

 

 

Ranar yadda yaga rana haka yaga dare, dan ko kaɗan bejin bacci.

 

 

.

Washegari haka ya kimtsa ya fice daga jihar ta kani jikinsa amace yanajin kamar ya baro wani abu me muhimmanci arayuwarsa acikin garin na kano.

 

 

Be bi jirgi ba da kansa yaja motor zuwa Abuja,inda ya isa da misalin ƙarfe sha biyu na rana,direct be kula kowaba ɗakinsa ya wuce ya kulle ƙofar.

 

 

 

 

Daga mahaifiyarsa har ƙanwansa seda sukai mamakin yanayin nasa,amma se suka ƙyaleshi dan yasamu natsuwa .

 

 

Be fitoba se washegari,sanye da jallabiya milk color ya nufi falon gidan inda yake jiyo hayaniyarsu.

 

Yana shiga ƙanwansa tayo kansa tana faɗin”bross lafiya de kake ko jiya ka bani tsoro,”ta faɗi amarairaice.kallonta yayi na ƴan daƙiƙu,bazata wuce saar rayhana ba,danasanine ya ƙara mamaye zuciyarshi daya tuno inshi akaiwa ƙanwar tasa haka yazeji tabbas ya aykata babban kuskure me girma arayuwarsa.

 

“to ƙaraso mana katsaya kasata agaba kana kallo kamar gunki”cewar mummy.

 

 

A hankali yataka ya isa inda mahaifiyar tasu take ya tsuguna agabanta ya gaisheta sannan ya nemi guri ya zauna.

 

“Rayhan gaba ɗaya ka sauya,meke damunkane,gaba ɗaya ba yadda kasaba zuwar mana ba kazo”cewar mahaifiyarshi cike da kulawa.

 

Ƙasa yayi dakanshi yace”mummy bakomai yanayin kasuwancinane yakaini ga babbar asara”ya faɗi yayi shuru.

 

Murmushi tayi tace”in banda abunka rayhan fa dukiyar mahaifinku,kazo ka kula da ita kaƙi wai kai kana da naka business ɗin,gashinan an ɗora wasu se abinda kuka gani tunda baka nuna kadamu da ita ba”

 

 

“yanzu mummy na dena nawa kasuwancin zan dawo kan dukiyar mahaifinmu insha Allahu mummy”ya faɗi jiki asanyaye.

 

“to dade yafi maka kan dan baze yiwu ace akwaika agida amma dukiya na hannun wasu wannan ba tsari bane”.

 

 

“Komai ya wuce mummy yanzu insha Allahu Lagos ɗinma nadena zuwa zan zauna nan inci gaba da kulawa”

 

“Rayhan har yanzu kaƙi fitowa da macen aure ay maka ahuta kullum ƙara girma kake,Nusaiba yanzu ta dawo atafau kai take so last week hajiya takirani tana faɗamin yakamata kayi wani abun akai”

 

Shuru yayi yana kallon ta can ya nisa yace”mummy duk yadda kikace haka zaayi mummy in kinga auranmu yamiki kusa ayi kawai”ya faɗi asanyaye.

 

 

Kallon kallo sukayi mummy da ƙanwar tasa jin abinda yace,sauyawar tashi sosai ta basu mamaki.

 

COMPLETE ƊINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.

 

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

 

 

Surbajo for

Back to top button