Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 8

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*8* free page

Gida suka wuce da mutumin can bangaren baqi aka ajiyeshi cikin kankanin lokaci Dr ya karaso don an kirasa tun kan su karaso , allura ya fara masa sannan yayi dressing wajen raunukan ya saka masa drip yana bacci , dady ya kasa zama sai safa da marwa yake fatarsa shine Allah ya tashi kafadar mutumin. Aman da Ayman suka shigo tare sunzo masa snnu da xuwa da kuma jajanta masa kan abunda ya faru sabida Ammi ta sanar dasu, ya amsa cikin fara’a da sakin fuska yana tambayarsu ya school Aman ya b’ata fuska yace ” I don’t like it dady gaskiya state university fah kamar wani Mara gata ” ” hakuri zakayi haka Amminka take so bani da zabi akan choice nata, duk abunda take so shi zatayi babu yanda na iya sai hakuri, Ku dage kuyi karatu idan yaso masters sai ka zabi Inda kake son zuwa okay” OK dady ya na iya da Ammi ” murmushi dady yake ya maida kallonsa ga Ayman yace ” Allah taimaki yariman sennar, ya ksar tamu hope babu stress ko wani issues koh” cikin girmamawa yace ” babu komai dady sai godiya ” ” haka nake son ji ,Allah taimka ” ” ameen suka amsa daga nan Ayman ya masa sai da safe ya fice xuwa part nasu, ya gama duk abunda zaiyi ya dauki Qur’an mai translation yana karantawa babu littafin da yake so da kuma son karantawa irin Qur’an a rayuwrsa yana jin dad’in especially mai fassara, kullum sai ya karanta tare da fassarar yace babu labari mai dad’i a duniya irin tarihin dake cikin Qur’an mai girma, ya share 2 hours yana karantawa har ya fara gyangyadi shine ya rufe ya ajiye har ya kwanta ya sake tashi ya bude bag nashi na ciro letters din nan guda biyu ya karanta ya sake karantawa yana murmushi sannan ya ajiye a karkashin pillow ya kwanta yayi aduan bacci ya rufe ido.
Da safe mutumin ya bud’e ido yana kallon dakin kamar a mafarki nan ya tuna yana kokarin tsallaka titi wata mota ta bige shi ga cannular a hannunsa ya tashi ya zauna, wani bodyguard yaji motsi a d’akin shine ya leka yana ganinsa yayi saurin shigowa ” sannu malam ya jikin ” ” alhamdulillahi da sauki” ” Allah ya tsare ya baka lafiya bari a Sanar da alhaji ” bai jira amsa ba ya fice, bayan 15 minutes suka shigo tare da dady da Ammi sai wani yatsina fuska take dady ya zauna kusa dashi ” ya jikin naka bawan Allah, sannu kaji kayi hakuri tsautsayi ne Allah ya tsare ” ” ameen ” ya amsa Ammi ko kallon arziki bata masa ba bare tayi tunanin tambayarsa jiki, ” daga ina kake kuma yaya sunanka ” ” sunana Sule daga jahar Adamawa na fito ” murmushi dady yayi ya juya gun Ammi ” ikon Allah Amina kina ji Ashe dai d’an gida ne ” tamke fuska tayi don tasan halin dady da son mutane musaman idan tasan ka fito daga Adamawa ” wace unguwa kake da zama a nan Abuja?” Dady ya tambaya ” Alhaji jiya nazo bansan kowa ba ” gyada kai yayi yace ” i s OK Allah ya baka lafiya zansan abinda zanyi akai, ka ci abinci kayi wanka anjima Dr zai shigo ya kara dubaka , sannu Allah kara sauki ” daga haka ya tashi ya fita Ammi ta Mara masa baya. Suna zuwa falonsa tahau masifa ” wllhi kai ka fiye kwashe kwashe bakasan mutum ba don kawai yace yana Adamawa sai ka yarda, kasani ko karya yakema don kawai ansan kai Dan jahar yasa ya shirya wannan karya ” ” koma menene Amina ai motata CE ta bige shi kinga dole he is my responsibility ” naga kana kokarin cusa shi a gidan ne, Nide yana samun lafiya zai barmin gidana don banson ganin fuskarsa ” ” hakuri zkiyi ya zama dole na bashi kulawa okay ” fuu…tayi fushi ta tafi.
Aman yadau wanka cikin kaftan farare fat dasu sai daukar ido yake yayi kyau sosai kamar wani sabon ango , a balcony suka hadu da Ayman yayi wucewarsa wata mota daban ya shiga driver yaja nan Ayman ya gane zancen donhaka suka shiga dayar Wanda suka saba xuwa da ita dashi da fauzan.

__,_________________
Wata makobciyar su malama zata aurar da y’arta mace wata mai zuwa an kawo lefe mata na shiga kallon lefen matar tana islamiyar malama bayan sun tashi daga makaranta ne ta gayyaci inna tare da maman Nana xuwa kallon lefen, bayan azahar mmn Nana tace su shiga gidan saboda bayan laasar zata fita kasuwa . bayan sun gama kallon kayan suna xauna inna tace ” Allah sanya alheri ya nuna mana lokacin biki” ameen suka amsa maman Nana tace ” malama na hada turaren wuta da na tsuguno dasu tsumi da sabulun gyaran fata idan kuna bukata ” ” haba da gaske, ai bamu sani ba gara da kika fada mana, nawa kike hadawa malama ” inna tayi murmushi tace ” ya danganci irin hadin da kike so” ” toh malama kaman na nawa kike ganin zaiyi kinsan shawara ce ” ” ehh gaskiya bansan yanayin farashin kayan hadi a nan gari ba , ki shirya gobe sai muje kasuwar tare ” ” Allah ya kaimu nagode sosai Allah bar zumunci ” har kofar gida ta rakasu ta koma , maman Nana tace ” a haka ake fara kasuwanci malama , kinga yanxu duk Wanda yaji dadin nata zai nemi inda kike daga nan sai ki fara hadawa kina siyarwa ” hira suka cigaba dayi har suka shiga gida sun tarar da hajjo ta dawo daga makaranta ” ina yini inna , ina yini maman Nana ” ” lfiya lau yan makaranta an dawo” ” ehh na dawo dazu Nana tace kun shiga gidan mamn yusra ” ta nemi abinci shinkafa ce da wake da manja da yaji ta xauna taci ta koshi kafin tayi sallar azahar.da yamma suka fita talla as usual kowa na sha’aninsa busy kawai hajjo na rike da wasika tana Neman Dan gidan nata can ta hangosa yana xuwa murmushi ya fara da ya hangota nan ta mika masa ya karba yana murna saboda yasan zai samu mai tsoka a wajen mutumin, karfe shida saura Ayman ya iso wajen ya fito yana jiran sako can ya hango yaron yana xuwa ya karba ya mika masa 500 ya shafa kan yaron ya tafi. Bayan tafiyarsa da 15 minutes motar su Aman yayi parking ya fito cikin takun kasaita ya wuce wajen mai fruits ya gama siyayya bodyguard nasa ya karbo kayan ya wuce dasu Aman ko yana Neman inda zai hango hajjo, zata shiga shagon malam Dalha ta hangosa nan ta ruga xuwa inda yake tana hak’i ” kai alhamdulillahi yau dai Allah ya kawo ka , sati guda nake Neman ka amma shiru, wallahi inna ta tace dole a maida maka kudin bata so batasan…” Haba Aisha haka akeyi babu gaisuwa sai dogon surutu ” turo baki tayi tace ” ni waya fada maka sunana bayan Baba ne kawai yasan sunan sai fomasta na” murmushi yayi yace ” kin dace da masu sunan ne daz y, so yanxu kina nufin up to now baki daina talla ba ” ” up to yes me yes talla yes hajjo yes up” dariya yake harda tafa hannu ” iyye Ashe dai ke baturiya ce ” rufe fuska tayi cikin jin kunya sai kuma tace ” Allah yasa dai yaron bai fada maka ni nake turashi ya kai maka wasika koh?” ” wane yaron kuma wace wasika ” ” yauwa gara da Allah yasa baka tuna ba don kunya nake ji ” ta sake rufe fuska Aman ya girgiza kai , ” yawwa ka jirani a nan bari naje gida na taho maka da kudaden ” ” no no..u don’t have to kawai ki fadawa inna har yau baki kara ganina ba ” turo baki tayi ” toh ai inna tace babu kyau karya ” ” akwai karyar da zakayi ka kare kanka ai , anyway manta kawai ki bani lbari aji nawa kike a school” tabe baki tayi tace ” tabb.. ai ni yanxu ina pri 4 idan na gama sai inibasti daga nan na wuce saudiya na fara wa’azi kamar musti mai kyau din nan ka sanshi? Wani fari mai gemu yana da kyau sosai Allah yasa ya zama mijina ” dariya yaci karfin Aman ya rasa waye zai tayashi ” mufti menk sunansa, kina son ki zama Islamic scholar kenan, funny girl ” ya kura mata ido she is quite beautiful musamman idan tana magana ya shagala da kallonta wani yaro yace ” hajjo maman ki na nemanki tun dazu kina tsaye a nan ” da sauri ta kallesa ta marairaice tace ” shikenan bamu gama hira ba zan tafi, gobe zaka sake xuwa soyayya koh?” ” soyayya kuma? a ina ?” Ya zare ido yana kallon bayansa bai fahimci zncen nata ba ta ruga ta tafi yana smiling har ya daina hangota sannan ya juya ya fara tafiya.
Ayman yana rike da wasika yana murmushi ya bude ” zuwa ga MAsoyena bayan dubun gaisuwa mai yawa ina jiranka zama asebitin zuciya zan zama maganin bitamin lob mai Habib I lob u I mees u ples lob mai me u?” Murmushi Ayman yake he can’t control but to laf yayi dariya har ya gaji ya kwanta yana kallon ceiling still smiling he wish yasan yarinyar da zai nemi ganinta ko saboda ta debe masa kewa, Aman ya shigo yana dariya shi kadai Ayman ya xuba ido yana kallonsa yace ” bro kasan yau I met that girl wacce na taba marinta kwanaki, she is darn funny cewa tayi idan ta gama primary zata wuce university a Saudi kuma Allah yasa mufti menk ya aureta” smiling Ayman yake ba tare da yayi magana ba ,haushine ya kama Aman yace ” why am I even telling you mtww…mutum babu umm babu um um sai banzan murmushi kamar mara gaskiya mtsww” ya juya ya shige d’ayan d’akin Wanda yanxu shine bedroom nasa ya barwa Ayman d’ayan, murmushi Ayman yayi yace ” so funny just like my little girl ” lumshe ido yayi yana nazarin shekarun yarinyar dake aiko mata letters ko zata kai irin 15 to 16 haka maybe ,tana ss1 ko jss 3 murmushi ya cigaba da yi daga karshe ya kira ummarsa a waya suka sha hira ya tafi karatunsa. Malam Sule ya samu sauki sosai don yana samun kulawa na musamman gashi har ya fara sabawa da wani mai gadi sunansa Tanko ,yana harabar gidan suna hiran duniya akayi horn Tanko ya tashi ya bude gate dady ne ya dawo tare da wasu baqi bayan ya fito sai da ya tsaya suka gaisa ya kara tambayan jikin Sule kan ya wuce cikin gida, Sule yace ” gaskiya ban taba ganin mai kudi dake da saukin kan Alhaji ba , yana da kirki sosai Allah ya saka masa da alheri ” tanko yace ” in dai Alhaji ne baka ga komai ba wllhi ,da ace dukkan masu kudi suna da halayen kirki irin nasa da talaka basu sha wahala a duniya ba, yana karrama Dan Adam sosai yasan mutunci da taimako ga yawan kyauta” yayi kasa da murya yace ” amma mai samu mace ta gari ba Sam Sam …hajiya babu mutunci ga wulakanta mutane musamman talakawa, ga girman kai da son girma kai hatta yan uwan Alhaji bata barinsu su rabeshi yanxu yan uwansa duk sun daina xuwa saboda wulakancin hajiya ” Sule ya girgiza kai yace ” Allah sarki dama haka rayuwa take wani baiyi dacen mata ba wata kuma batayi dacen miji ba, yaransu nawa ?” Yaran shida ne maza biyu mata hudu, matan uku sunyi aure saura d’aya tana kasar waje, babban namijin yana can Italia yayi aure da yara autan nasu ko yana nan yana tsula tsiya kamar uwarsa ” ” kodai shine wannan fari jiya sun shigo tare da baban da wani kyakkyawa ” ” shine fari Sol haka kamar zabiya,wannan kyakkyawa Dan sarkin kasar wajene amma bansan ina garin nasu yake ba” yana magana kasa kasa kar wani yaji, haka suka raba Dare suna hira kafin Sule ya tashi ya koma masauki.

*Wasu na tambaya whether it’s a real life story, please is just fiction ni na kirkiro labarin Ku rufamin asiri maza su kaini ba mata ba lols, idan kina enjoying labarin mezai hana ki biya 300 naki if u know d story is worth paying please tuntubi 07030077024 for payment details just 300 not 3000 nasan baifi karfi ba show me you are all matured please, thank you, ina jin dadin comments naku but free pages yazo karshe hurry n patronize*

Back to top button