Ikraam 45
45…..
Aliyu bae ko kalle Mum din tasa ba ya kama
hannun Ikram suka haura sama, dakinsa ya
shiga da ita ya xauna kan gado ya dago
fuskarta yana kallonta, hawayen idonta ya
shiga gogewa a hankali yace “su ne suka doke
ki ko Ikram” ta girgixa masa kai tana ci gaba
da hawaye tace “yaya Khaleel ne ya tafi ya
barni” hade rae yyi yana kallonta yace “ina xae
kai ki da” ta marairaice tace “gida mana”
hannunta ya kamo yace “to yi hkuri My Ikram,
xan kirasa ya xo ya dauke ki kinji” kai kawae ta
gyada masa tana kallonsa, yyi mata murmushi
ya mike ya dauko chocolate ya bude ya mika
mata, ta karba tana murmushi ita ma, ya xauna
kan gadon ta xauna gefensa tana kallonsa
tace “yayana meyasa ka daina xuwa gidanmu
ynxu?” ya dan yi shiru snn ya kamo hannunta
yace “to xan dinga xuwa amma idan na xo ki
daina xuwa kusa dani kar Mami ta koreni kin ji”
shiru tayi tana kallonsa snn ta ci gaba da cin
chocolate dinta tace “to” Momy ce ta shigo
dakin tace “to tashi muje ki kwanta tunda kin
gama kukan” bata fuska tayi tace “Mami ni ki
barni wajen yayana” Momy ta dago ta tace
“gobe da sch Ikram kwanciya xaki yi” bata jira
me xata ce ba tayi kofar fita da ita, kuka ta
shiga yi amma a hankali, momy tace “wlh kin
cika kukan bnxa Ikram, komae kice xaki yi
kuka” sakinta tayi ta fita daga dakin, Ikram ta
juya tana kallon Aliyu dake kallonsu, tayi
murmushi ta koma kusa da shi ta xauna, yace
“kin ci abinci?” kai ta gyada masa, ya mike ya
fita xuwa dakin Momy ya dauko maths texbuk
dinta ya dawo, ya shiga bata questn tana
solvin har kusan karfe sha daya snn yace
“Ikram tashi in raka ki gun momy ki kwanta
kinga dare yyi” bata yi musu ba ta mike ya rufe
buks din ya dauka suka fita yana rike da
hannunta, har kofar dakin momy ya kai ta snn
ya durkusa gabanta yana kallonta ya dan yi
murmushi ya daura mata kiss a goshinta a
hankali yace “gudnyt My dear” murmushin tayi
ita ma tayi masa abinda yyi mata, ya mike da
sauri ya bude kofar dakin ta shiga snn ya rufe
kofar ya juya xae koma dakinsa, tsaye ya ga su
Seeyama da Aisha suna kallonsu, suna ganin
ya juyo suka shige daki da gudu suka rufe
kofar suna ta kyalkyala dariya, dakinsa ya nufa
ya bude ya shiga. Kwanan Ikram takwas a
gidansu Aliyu Mami ta dawo, kuma ranar
Abbansu Aliyu shima xae dawo daga britain,
don hka basu a hadu da Ikram ba, a kwanaki
takwas din nn da tayi ba karamin shakuwa
suka kuma yi da Aliyu ba fiye da na da, ssae
yake nuna mata so da kulawa amma fa a boye
don warnin ssae Mum dinsa tayi masa
washegarin ranar da ya wuce da ita sama kan
cewar ya fita harkarta don bbu abinda ya
hadasa da ita bata son shisshigi, to kawae ya
ce mata ranar. yana dawowa daga aiki da
daddare Ikram ke shiga dakinsa suyi ta solvin
questn a maths, ba ita ke komawa dakin momy
ba sae sha daya, kullum da daddare karfe
takwas Khaleel ke xuwa gidan duk da idan ya
xo gun su seeyama kawae yake tsayawa suyi
ta hira amma da bananan ta yake shigowa
gidan, kuma duk xuwansa basu taba haduwa
da Aliyu ba don sae kusan goma yake dawowa
daga aiki, hka ma Mujaheed sun saba ssae
dashi kullum da roban ice-creams da snacks
yake shigowa gidan na Ikram, ta dae xama yar
gata a gidan, tana bala’in ji da yaya Mujaheed
dinta, hka take ce masa yaya Mujaheed dina,
duk ya taka ma su Farida da Saiham burki don
su kadae ke tsangwamarta a gidan sae
Hajiyarsu Aliyu, ita din ma ta shiga taitayinta
don tana shakkar Mujaheed ssae ba kadan ba,
ko kadan bae da mutunci baya jin mgnr kowa
sae ta uwarsa. Aliyu bae wani damu da ynda
Ikram ta saba da kaninsa ba don yasan
wanene Mujaheed. Ranar da Khaleel ya xo
tafiya da ita su seeyama suka ja ta xuwa daki
su ka ce “Ikram kice ke baxa ki tafi ba yau,
kinga gobe Abbanmu xae dawo kuma yana siyo
mana abubuwa da yawa har da Teddy” da
gudu ikram ta sauko ta sami Khaleel dake
xaune falo yana jiran Momy ta fito da kayanta,
ta kama hannunsa ya fixge yana hararanta, ita
ma ta rama snn tace “yaya Khaleel ni baxan
tafi yau ba, kaga bance ma yayana da yaya
Mujaheed dina yau xan tafi ba” Khaleel ya galla
mata harara yace “ina Hijabin da nace ki
dauko” Momy ce ta sauko rike da jakar
kayanta, Ikram ta fasa ihu tace “wayyoo Momy
ki maida kayana ni ba yau xan tafi ba” dariya
momy tayi tace “yau kuma, to kai kaji Khaleel
sae ka tashi ka tafi” mikewa yyi ya karba jakan
hannun Momy yace “ae baxan yi wahalar bnxa
ba” tana kuka ssae suka bar gidan, su
seeyama ma sae da suka yi kukan don ba
karamin shakuwa suka yi da Ikram ba yan
kwanakin nn, suka xama kmr wasu kawaye
duk da sun girmemata da shekaru biyu. Khaleel
na gama parkn ya fito daga motar, ya fito da
Ikram da taki fitowa, ta buge masa hannu ta
kuma fashewa da kuka, dafa ta yyi a hankali
yace “baki son ganin Mami ne Ikram” juya
masa baya tayi ta rungume hannunta tace “ni
ka kyaleni” ya juyo da ita yana murmushi yace
“to yi hkuri, xo muje kiga abubuwan da Mamin
ki ta siyo maki” bae jira me xata ce ba ya daga
ta sama, rungumesa tayi tana kyalkyala dariya
suka shiga falon.