Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 13

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*13*
*thanks for patronizing love you much*

Hajjo ta sha fada gun inna ba kadan ba ta inda take shiga ba ta nan take fita ba kamar ta rufeta da duka tana tambayarta inda ta hadu da Aman tasan shi , kuka hajjo take tana bada hakuri Mann Nana na tayata bada hakuri a nan ta shaidawa inna cewa Aman ne ya bata kudi kwanaki nan inna ta karasa da nasiha ta bata shawara akan ta fita harkarsa hulda da masu kudi bazai haifar mata da komai ba sai nadama , ta fadi hakan ne saboda gudun wulakanci ta tuna aurenta da sule da kuma outcome din auren donhaka bazata so hakan ya faru da hajjo ba gara tun wuri ta rabata da Aman.ya zama dole ta nemi mafita tun abin nasu baiyi nisa ba, da wannan tunanin ta yini tana shirya shawarwari daban-daban a zuciyarta. Ledojin da suka kawo ta bude kayan tea ne da fruits sai kuma chocolates da turaruka masu tsada tagumi inna tayi ta tabbata Aman zai dawo ita kuma har ga Allah batason alakar tasu , mmn Nana ta nunawa kayan ta zayyana mata yadda sukayi da Amant, mmn Nana tace ” gaskiya ne malama nasan masu kudi ba kowa ke son hulda da talaka ba amma dai da kin tambayi ra’ayin hajjo ko tana sonsa ” ” haba mmn Nana me hajjo ta sani dangane da soyayya , Ni nafison ta rabu dashi saboda gudun wulakanci nan gaba” ” hakane kuma amma naga kamar akwai shakuwa tsakaninsu ” ” koma menene gara dai yayi hakuri yaje ya nemi dai-dai dashi don bamusan manufarsa a kanta ba , tana y’ar sha uku yaushe zai jira ta girma ” ” toh..Allah ya mata zabi mafi alheri ” ” ameen nagode ” .

________
Ayman ya kasa zaune ya kasa tsaye gaba d’aya yana Neman mafita akan abunda ke damunsa tabbas zuciyarsa bata masa adalci ba saboda yayi nisa cikin son hajjo baisani ba sai a yau daya sanyata a ido ta gama tafiyar da imaninsa amma ya tausaya musu da ganin halinda sike ciki , wayarsa ya cire ya kira fauzan yace ” ka samu abunda na sa ka?” Shiru yayi yace ” OK ku jirani a kofar gida gani nan zuwa ” ya kashe wayan ya fice.
Suna tsaye da wani mutum ya masa sallama suka gaisa yace masa ” yaya ake ciki ?” ” ranka ya dade na kammala duk wani shirin da ya dace saura ka bani go ahead kawai a gabatar da aikin ” ” OK na baka go ahead, ka turo account number zaka ga sako nagode ” godiya mutumin yake daga haka Ayman ya koma ciki. Fauzan ya raka mutumin ya tafi sannan ya dawo gida yana mamakin wannan lamarin .

***************

*Birnin sennar*

Gimbiya suhail ce tare da Gimbiya Asanti mahaifiyar Sabreena suna tattaunawa cikin private chamber din suhail ” haba y’ar uwa yanxu kina ji kina gani haka Sabreena zata cigaba da rayuwa da mutumin da bai taba nuna damuwa a kanta ba ” G Asanti tace ” toh ya zanyi , Sabreena ne akwai taurin kai kuma mahaifinta na biye mata duk abunda take so dole shi zaayi ya zanyi ?” ” ga nan yarima Aseem na mutuwar qaunar yarinyar amma ta nace ita dole sai wannan miskilin yaron da uwarsa bata gama sanin halayensa ba, da dai ki jarraba rabasu ko zaayi nasara” shiru Asanti tayi tana tunani , grapes ta dauka tajefa a baki ta cigaba ” idan zumunci ake so ba sai ta auri yarima Aseem ba, gashi yana da hankali da faraa ga tausayi ” ” zan jarraba amma nasan bazata saurareni ba, tayi nisa da son Ayman bata jin kira gashi bikin nasu saura wata hudu idan muna raye ” tabe baki suhail tayi ” hmm yanxu kina ji kina gani y’ar cikin ki zaki bari ta tafi inda zata sha wahala ” tagumi Asanti tayi haka G suhail ta cigaba da hura mata kunne gaba daya taji hankalinta bai kwanta da auren ba, Fulani na falo tare da had’imanta jakadiya ta shigo da sallama nan aka watse don basu guri ” Allah kara miki daraja da daukaka ,ina tafene da wani labari ” ” kunnuwana a bud’e suke a kullum ina mai jiran labari daga gareki ” ” Allah kara girma na samu labarin zuwan Gimbiya Asanti matar sarkin kush, tana bangaren Gimbiya suhail amma har yanxu babu labarin komai dangane da zuwan nata ” shiru Fulani tayi tana tunani daga bisani hannu ta d’aga mata ta fita, waya ta cire ta kira Ayman bayan suka gaisa take tambayarsa suna waya da Sabreena ne yayi shiru bai amsa ba nan ta gane cewa basu waya don Ayman baya taba mata karya , ” karka manta auren naku ya rage 5 months idan muna raye, ya kamata ku fara fahimtar juna kafin lokacin, nasan Sabreena bata da matsala yarinya ce mai saukin kai donhaka kada ka bari wani ya rigaka jan ta a jiki saboda kai kafi cancanta da hakan ” haka ta cigaba da masa nasiha da shawarwari daga karshe ta kashe wayar, yaron tausayi yake bata yana da zurfin ciki bazaka gane halinda yake ciki ba ga uwa uba ladabi da biyayya ga kuma tausayi da rikon addini .

*****************
*Abuja Nigeria*

Aman ya kammala shirinsa zai tafi ganin hajjo daga nan zasuyi magana da inna ta fahimtar juna yana cikin fesa turare Ammi ta shigo ” ina kake shirin xuwa , magana zamuyi ” ” Ammi sauri nake zan fita da friends dina , zamuje gaida Mara lafiya ” murmushi tayi ” koma menene dole ka saurareni, dama wannan yarinyar zee da take zuwa wajenka shine mukayi magana da mamanta , ka fara zuwa zance wajen.. ” ” what? Ammi bangane na fara zuwa zance ba, bafa Ni take so ba she is in love with Ayman not me ” ” baka da hankali ne , Ayman da aka saka ranar aurensa, koma mene yanxu ya zama dole ka fara tarayya da ita saboda ita zaka aura idan muna raye , maza ka gama shiri kazo ka wuce gidansu ana nuna muku hanyar arziki kana gocewa , toh yar gidan vice president ce idan baka sani ba ” “gaskiya bana sonta Ammi ina da wacca nake so ” ” zan mugun bata maka rai akan maganar wannan yarinyar ” ta juya ta fice Aman ya rike kai ya xauna cikin zuciyarsa wani haushi da takaici yake ji, yana xaune Ammi ta kirasa a waya dole ya fito falo ya sameta tace maza ya wuce driver ya saukeshi Asokoro gidan su Zee yana kunkuni ya fita . da mota biyu suka fita har suna xuwa gidan dama ansan da zuwan nasu sun samu kyakkyawan tarba wani katafaren falo aka saukesu , bodyguards na waje Aman ya xauna yayi crossing legs nashi yana danna waya nan da nan masu aiki suka cika gabansa da kayan ciye-ciye ko kallonsu baiyi ba, Zee ta shigo tana tauna cingam kas-kas ga wani uban takalmin high heels da ta saka tana rangaji kamar zata fado kasa ” Hi Aman ya kake ” zama tayi kusa dashi ta manna masa peck a kumatu ,a da can yafison mace wayayyiya irin haka amma bayan haduwarsa da hajjo komai na rayuwa da burinsa ya canza ” wannan wane irin rashin tarbiya ne daga ganin namiji zaki sumbace shi ” ” c’mon karka bani kunya , na Dade da saninka don nasha ganinka a parties da clubs but na fada tarkon son Ayman, but is OK mom naku ta min bayani Ayman is engaged kuma basu auren Wanda is not from a royal family as first wife so bani da choice, anyway kana da kyau n u r wise n educated so bani da problem I can love you ” wani kallo ya mata yace ” let me tell you, ina da wacce nake so gara tun wuri ki fadawa iyayenki baki son wannan had’in saboda bamu dace da juna ba ” wani dariya tayi tace ” haba Aman am not a fool , bakasan cewa da rashin uwa akanyi uwar daki ba, Ayman ya kubuce min bazan taba bari ka kubuce ba, saboda haka ina son ka sani cewa ina son ka kuma zan aureka. ita wannan budurwa da kake magana a kanta zan iya yin komai saboda soyayya da kuma masoyina donhaka ka kiyaye kada ka jawo mata matsala ” bakinsa ya mutu ya kasa bata amsa lallai yarinyar idanunta a bushe suke babu d’igon kunya a ciki, drink ta zuba masa a cup ta mika masa ya tashi ya tsaya yace ” ki kara tunani da kyau kiyi nazari , idan kin gama ki sanar dani ” ya juya ya fita tayi sauri tabi bayansa ” Aman Darling take care of your sweet self for me,bye ” tana d’aga masa hannu ya juya ya shiga mota wani shu’umin murmushi ” Aman zaka shigo hannuna, kwantar da hankalinka nida kaina zan kafa gwamnatin soyayyata a cikin Birnin zuciyarka” ta juya ta shige part din mom nata tana bata labarin yadda sukayi, momy tayi dariya tace ” kwantar da hankalinki nasan Hajiya Amina idan tana son Abu ko mijin nata bai is a yahana ba , kedai ki saka ido kan shiga da fitarsa don gane inda matsalar take , Allah ya bamu sa’a auren ya tabbata ” ” ameen momy Ni kaina ina son shiga familyn nasu babu raini ” haka suka cigaba da tattaunawa.

*Ki/ka biya 300 naira kacal don samun cigaban wannan labarin tuntubi 07030077024 for payment details thank you*

Back to top button