Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 66

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*66*

Fulani na zaune cikin falonta tana cikin farin ciki saboda yau y’ayan nata duk suna tare da ita , Gimbiya Alia babbar y’arta tazo tare da y’ayan ta sai Kuma gimbiya Kafeela wacce take aure a can Switzerland tazo da yarinyar ta d’aya gaba d’aya sunzo ganin autan nasu Wanda ya kasance Abu Mafi soyuwa agaresu bare Kuma abar kaunar tasa wacce Fulani ta gama Basu labarinta . dayake jirgin yamma suka biyo sai magariba motocin da sukayi convoy don daukarsu daga airport sukayi parking saboda akwai dan tazara tsakanin airport da masarautar , Failuzaa na gefensa na hagu Hajjo na gefen dama ya sakasu a tsakiya Fauzan na gidan gaba tare da driver har yanzu Failuzaa fushi take dashi akan fadan da ya mata donhaka ne yasa tace masa suna isowa zata wuce masarautarsu ta Singa shi kuwa gogan Bai hanata tafiya ba, ta kira masarautar tasu tun kafin ta iso masu daukarta sunzo suna jiran karasowarta Sennar.
Bayan sun fito Kai tsaye bangaren Fulani suka shiga saboda magariba ta gabato sultan zai tafi Masallaci, kuyangi sai diban gaisuwa suke wajen yarima hajjo tayi mamakin yadda ya canza cikin kankanin lokaci ya koma asalin yarima Ayman miskili mara son magana saboda duk gaisuwan da Ake musu baya amsawa sai dai ya d’aga Kai Fauzan ne ke d’aga musu hannu har suka samu suka shigo bangaren Fulani, kallo ya koma sama wai aljannar duniya kenan Hajjo tunda take Bata taba ganin falo Mai irin wannan haduwar ba sunkuyar da Kai kasa tayi saboda gudun Kar tayi kauyanci, lallai Ayman dan gata ne gaba da baya Allah ya bashi komai na rayuwa sai dai ya tsaya ya nemi lahira kawai . Alia ce ta fito ta rungumi Hajjo cike da fara’a ta fara fillanci irin nasu na Sudan , Failuzaa kuwa tabe baki tayi ta nemi waje ta zauna Ayman na murmushi yace ” Gimbiya ita wannan Bata Jin fullancin najeriya ma bare na Sudan ” murmushi Alia tayi tace ” laifin ka ne da baka koya mata ba gashi mu Kuma bamu iya Hausa sosai ba ” tana magana cikin gurbatacciyar hausar nata, Fauzan ya gaisheta cikin girmamawa ta amsa tana fara’a daga haka mazan suka fice zuwa Masallaci sai a wannan lokacin Alia ta Kalli Failuzaa tana mata barka da zuwa ta amsa tana fara’an munafunci.
” Taso muje kuyi sallah , Fulani tana ciki sallah take ” Failuzaa tace ” nidai zan wuce ana jirana gobe zan dawo mugaisa ” cike da mamaki Alia tace ” Ina Kuma zaki ?”
“Singa zan wuce driver Yana can Yana jirana”
“Allah ya tsare ” “Ameen ” ta amsa Alia tabi bayanta da kallo sannan ta Maida kallonta gun Hajjo tace ” kodai matsala suka samu da mijin naku”
“Wallahi nidai bansani ba ” murmushi Alia tayi tace ” taso muje koh ”
Wani d’aki aka shigar da ita Mai Karen kyau komai na d’akin light purple ne har hasken lantarkin d’akin, toilet ta nuna mata nan Hajjo ta ajiye bag nata ta shiga wai… dakyar ta gane inda Ake kunna fanfon ruwa tayi alwala ta fito ta samu har an shimfida mata dardumar sallah, dama doguwar hijabi ne a jikinta sabo fil donhaka ta tada kabbara tayi sallar ta.

tana zaune bayan ta idar akayi sallama aka shigo Kafeela ce kana ganinta kasan y’ar uwar Ayman ne don tsabar kamannin da sukayi amma ta fisa haske kadan fuskarta dauke da murmushi ta farawa hajjo magana da turanci ” sannu da zuwa amaryar yarima ya hanya ”
“Lafiya alhmdllh dafatan mun sameku lafiya”
tana nan zaune kuyangi suka fara shigowa da abinci sunkai mutum 5 kulolin kansu abin kallo ne sai daukar Ido suke ga fruits shake a tray kaloli daban daban wasun Bata taba ganinsu ba tayi saurin dauke Ido, Kafeela ta Yaba da ita sosai cikin zuciyarta kuwa dadi takeji da alama kanin nasu yayi dace
“Bismillah kici abinci”
“Ina son gaisawa da Umma ” murmushi Kafeela tayi tace ” da dai kinci abincin kafin nan ”
“A’a ba matsala zanci anjima ” haka suka jera zuwa Wani falon daban inda fulanin ke zaune bisa dardumar sallah, falon yafi wancan kyau sai dai Bai Kai na farkon girma ba, murmushi ne ya bayyana a fuskarsa hannunta rike da carbi tace ” lale marhaban da mutan Abuja barka da zuwa y’ata”
Zama tayi a kasan kafet da sauri Fulani tace ” A’a koma kan kujera”
“Nan din yayi Umma Ina yini ” “lafiya ya hanya ya kika baro mutan gida ”
“Duk suna lafiya suna gaisheki” “Ina amsawa nagode ya wajen naku”
“Alhamdulillah”
“Masha Allah y’ar uwar taki ta wuce gida ashe ”
“Ehh dazu ta tafi ”
” Allah ya kaisu lafiya da dan tazara tafiyan ai zuwa garin nasu ”
“Allah Sarki ‘” shiru ya biyo baya Fulani ta kalleta tace ” kije kici abinci kafin Akai ki wajen sultan ku gaisa ” shiru tayi cike da kunya Kafeela ce tazo ta rike mata hannu Fulani tana murmusawa tana Jin dad’in samun suruka irin Hajjo , d’akin dazu aka shigar da ita sannan ta juya ta ja mata kofa.
Kallon kulolin take sun gwanin Bata sha’awa tana nan zaune wata kuyanga ta shigo da sallama ta rusuna tana tambayan me za’a zuba mata, hajjo tace ta bari zata zuba da kanta ba yanzu zata ci ba daga nan kuyangar ta fice ta rufe kofar.
Ayman ya shiga suka gaisa da Fulani nan yake tambaya Ina matan nasa suke Alice tace ” ita wancan fada kukayi ne daga zuwa har ta wuce garinsu Bata tsaya ta gaisa da kowa ba ”
Ware Ido yayi ” kina nufin Bata tsaya sun gaisa da Umma bah ?”
“Ko minti 10 batayi a gidan nan ba inaga ”
Fulani tace ” Kai gimbiya bana son tsegumi ”
tabe baki tayi tace ” dama ke Baki ganin laifinta ai Umma komai tayi daidai ne awajenki shiyasa ta raina mutane, idan ba raini ba ya za’ayi tazo har falonki ta kasa tsayawa ku gaisa ” sauke numfashi Ayman yayi yace ” zata Gane kuskurenta ”
“Kul…nasan halinka bana son Neman magana don Allah ka bari yadda kuka zo lafiya ku koma lafiya yarima karka jawo mana abin fada bakin mutane ” Fulani ce take magana in a serious note, cike da bacin rai Ayman ya tashi yace ” bari naje na watsa ruwa ”
“Ok ka duba yarinyar nan ko tana cin abincin kar ta zauna da yunwa nasan halinta da kunya” lumshe Ido yayi gaba d’aya ransa a bace yake har ya manta Bai nemeta ba, gyada Kai yayi ya juya ya tafi . Apple take taunawa a hankali tana jingine da gado har yanzu hijabin nata Bata cire ba ya turo kofa tare da sallama a hankali ta amsa , ya karasa inda take” baby girl ya gajiya ”
“Babu Wani gajiya am ok”
“Masha Allah taso kici abinci I’ll feed you ”
“Um..ni banjin yunwa fah”
“Umma tace na tabbata kinci kin koshi kafin na bar d’akin nan ” kauda Kai gefe tayi ya jawota jikinsa yace ” please kizo kici abincin gidanmu Baki taba ci ba”
Babu gardama suka koma inda aka Shriya kulolin ya budesu abinci ne kala daban daban harda tuwon shinkafa da miyan ganye , biryani rice din tace zata ci ya zuba mata kadan da hannunsa yake Bata tana ci kamar Bata so a yangace take ci abincin yayi dadi wannan dandanon spice din da Failuzaa ke using tajishi cikin abincin, taci half tace ya isheta , ruwa ya Bata Tasha sannan ta kallesa tace” what about you ”
Murmushi yayi ” am ok ”
“Tell me waya Bata Maka rai ” da mamaki yake kallonta juya idanu tayi tace” yes I know idan ranka a bace baka iya cin abinci ”
Wani gauron numfashi ya sauke” don’t worry bari naje nayi wanka zan dawo muje wajen sultan ” “A’a nidai ka zauna a nan karka tafi ”
“Please hearty I want to be alone for some moment please ”
“Um..um I need you here”
“Idan na zauna me zaki bani” ya fada Yana kallonta tana karantar yanayinsa tabbas Yana cikin bacin rai toh me zata masa ta faranta masa, gira ya d’aga mata
” am listening me zaki bani idan na zauna ” murmushi me kayatarwa tayi tace” abubuwa dayawa ” lumshe Ido yayi
“Ok am waiting…”
Babu zato ta manna masa peck a kumatu runtse Ido yayi yace ” bahaka akeyi ba ”
“So kake Wani ya shigo ya samemu a haka ”
Jawota yayi ya hada goshinsa da nata suna kallon juna ya hada hannayensu waje d’aya Yana wasa da zarazaran yatsun hannunta ” yanzu zan koya miki yadda ake ” “um..um nidai bana son Wani ya shigo kasan…
Bata karasa ba aka turo kofa tare da sallama Kafeela ce tana ganinsu haka tayi saurin ficewa daga d’akin , hajjo ta kwace kanta tana tura Baki ” kagani koh..yanzu da wane Ido zan kalleta ”
“Kinga tashi mu koma part namu Babu mai shiga ”
” Don Allah Yaya ka bari zaka sani Jin kunyarsu wallahi” riketa yayi Yana son d’aga ta, kwankwasa kofa akayi Ayman ya saketa ya juya yaje bakin kofa Kafeela ce tana kallonsa ta fara murmushi tace ” sultan ke son ganinku sorry for interrupting”
hararinta yayi yace ” bayan kin Bata min komai ” hajjo dai kanta na kallon kasa bataji me suke cewa ba sai da ya Mika mata hannu
“Let’s go Sultan na son ganawa dake”
Make kafada tayi taki Mika masa hannun Yana dariya yayi gaba yace da Kafeela ta taho tare da Hajjo.

Sultan na can private parlor dinsa inda yake ganawa na musamman da manyan baqi a nan suka samesa ya karbesu cike da fara’a nan suka gabatar da gaisuwa cikin girmamawa Yana kama da Ayman sosai kyakkyawan dattijo Mai cikar Kamala ga fara’a da sanin darajar dan Adam haka ya zauna Yana taba hira dasu Yana Jan Hajjo da hira tamkar ya Dade da saninta Yana dan Bata labarin rayuwar Ayman na baya yadda yaki yin karatun Boko ya dage akan sai Arabic ashe da rabon a Nigeria zaiyi karatu har yai arziki, daga karshe ya dora musu da nasiha da fatan alheri ga rayuwar auren nasu, suna gurin har aka kira Isha sannan suka tashi kuyangi suka raka hajjo bangaren Fulani Ayman Kuma ya tafi Masallaci tare da sultan.
Gimbiya Suhail na d’akin baccinta tare da Jakadiya wacce ta gama Bata labarin komai , numfashi ta sauke tace ” yanzu aikinmu zai fara akanshi saboda gobe da sassafe ki tabbata sakona ya iso gun amaryar tasa Kuma ki tabbata komai yayi yadda ya kamata saboda bazan jure ganin wannan arzikin da yaron nan yayi ba, ke jakadiya kina ganin dalleliyar motar da ya Siyawa sultan ai kinsani arziki ya zauna masa, toh ki tabbatar anyi komai yadda aka tsara don yanzu ta wannan hanyar kadai zamu samu mafita don na samu labarin cewa Yana balain kaunar yarinyar Kinga ko faduwa tazo daidai da zama ”
“Hakane uwargijiyata Allah ya Kara Miki lafiya ya biya Miki dukkan bukatunki” ” jakadiya idan har aikin ya tafi yanda aka tsara toh na Miki alkawarin gida”
“Ayuriri…sai ke gimbiya Suhail y’ar sarkin yamma a kasar Sudan y’ar sarki jikar sarki matar sarki Kuma uwar sarki Maijiran gado Kuma kakar sarakuna ”
“Kai jakadiya na Kara Miki da rakuma 10 ”
“Allah ya ja zamanin sarauniyar birnin Sennar ” haka suka cigaba da kulle kullensu har zuwa Wani lokaci.

Check Also
Close
Back to top button