Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 67

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*67*

*Wanda ban samu damar musu replying mssg ba kuyi hakuri a mini uzuri mssgs din suna dayawa ne insha Allah I’ll do d needful thanks for d love n support*

Bayan tayi sallar ishah aka hadata da hadimai mata suka rakata bangaren yarima bayan an shirya mata ruwan wanka na musamman me dauke da furanni da kayan qamshi irin na al’adun masarautar tasu a cewar Fulani yau ta fara shiga masarautar dole a mata duk abinda ya dace, sun fita falo suna jiranta bayan tayi wanka ta fito duk motsin da tayi qamshi ke tashi tana tsaye tana kallon d’akin Kai duniya labari arziki na inda yake, kwankwasa kofa akayi tace a shigo daga ita sai towel a tunaninta Ayman ne sai wata kuyanga ta Gani rike da Madara cikin kwarya ta risina cikin girmamawa tace ” ranki ya Dade idan kika bani dama zamu gabatar Miki da wankan al’adar masarautar Sennar”

tabe baki tayi tace ” toh har wanka sai an mini, ni bazan iya ba gaskiya sai dai nayi da kaina ”
“Angama ranki shi dade da izinin ki zan kawo abubuwan da zaa bukata ” tabe baki tayi nan kuyangar ta ajiye kwaryar Madaran ta juya ta fita bayan mintuna kadan ta sake dawowa dauke da tray toilet ta nufa ta ajiye ta dawo ta dauki kwaryar ta shigar kafin tazo ta risina tana cewa ” idan kingama zan dawo na kimtsa bayin ranki shi dade ” daga haka ta fita hajjo ta shiga toilet din tana son ganin mene a cikin tray din, kurkum aka kwaba cikin wata y’ar kwano me ban sha’awa sai qamshi ke tashi ga Kuma Wani abu kamar kuka Shima ankwaba shi Yana fitar da Wani qamshi na musamman, kwaryar Madaran ta d’aga ta duba Wani qamshi ne still me ratsa kwakwalwa, kurkum din ta fara shafawa bayan ta cire towel ta ajiye gefe tana mitsissika jikinta saboda ta tuna irin gyaran da aka mata na Maiduguri kusan hakan ne, bayan mintuna kadan ya fara bushewa ta dauki d’ayan abin ta shafa ta shige jacuzzi ta kwanta daga karshe Madaran ta dauka ta wanke jikinta dashi kafin ta hada Wani sabon ruwan dumi ta dauraye jikin, ya ilahi wannan wane irin hadine haka gaba d’aya hajjo sai shafa skin nata take yayi Wani mugun laushi ga Wani qamshim dake tashi akowane kusurwa na jikinta.

Bayan ta fito ta dauki hijab ta saka ta koma bakin gado tana bin d’akin da kallo sallama akayi daga bakin kofa kuyangar ta dawo dauke da kaya ta risina ta ajiyesu bisa gado sannan ta shiga toilet din ta wanke ta dauki abubuwan daga nan ta mata sai da safe ta fita, kayan Hajjo ta d’aga Wani qamshi ya daki hancinta har sai da ta lumshe Ido ta budesu wata doguwar riga ce shara shara kamar net ga duwatsu agaban rigar Bismillah tayi ta saka dama Babu komai a jikinta kallo d’aya tayiwa jikinta ta dauke Kai Wani kunya ya lullubeta wato wannan rigar Idan Ayman ya shigo ya sameta shikenan ta gama Jin kunya , gaban mirror ta koma ta tsaya tana karewa kanta kallo rigar ya kama jikinta sosai Kuma dashi da Babu banbanci kadan ne kwalliyar gaban rigar ne ya birgeta ta dauki turaruka ta fesa ta ajiye , Ina kayanta suke gaskiya dole ta saka undies idan bahaka ba… turo kofa yayi tare da sallama saura kiris ya zube a wajen yayi irin ta Maza ya karasa inda take yace ” muje mu kwanta dare yayi” sunkuyar da Kai kasa tayi ta kasa motsi saboda duk taku d’aya jikinta sai ya motsa cikin wannan shu’umar riga. Zuwa yayi ya rungumeta ta baya Yana shakar qamshin dake tashi a jikinta Yana kallonta through mirror sai faman lumshe Ido yake he can’t resist the scent, fuskarsa ya dora bisa kafadunta gashin kanta ya rufe masa fuska Yana yawo da fuskar bisa fatar kafadarta da yayi Wani irin laushi kamar auduga ga Kuma qamshi na musamman Mai ratsa kwakwalwa , bugun zuciyarta ya tsananta ta kasa d’aga Koda dan yatsane saboda abinda yake mata a jiki . ganin komai zai iya faruwa inda suke tsaye yasa yarima d’agata cak! Yana tafiya a hankali ta boye fuska bisa faffadan kirjinsa ya rada mata a kunne yace ” kina da nauyi baby girl” tafiya suke cikin wannan yanayin har ya karasa asalin bedroom nasa Wanda ba kowane mahaluki yake shiga ba sai bisa Wani kwakwaran dalili, Kai tsaye bisa gado ya direta rub da ciki tayi tana kulle Ido batasan cewa babban kuskure ne Hakan ba saboda halittun bayanta yadda suka bayyana daga shi sai singlet da 3quater ne daman haka ya haye gadon tare da kashe wuta ya jawota tana kankame jikinta, murmushi yayi cikin zuciyarsa kuwa cewa yake yau dole ayita ta kare gashin kanta ya fara shafawa gaba d’aya a tsorace take ya dawo fuska Yana yawo da yatsun hannunsa bisa fuskarta in a circular motion, lokacin da yatsarsa na biyu ya shige kunnenta tamkar tace wayyo Allah saboda Wani irin yanayin da ta tsinci kanta a ciki ganin ta fara reacting yasa ya hade bakinsu wuri guda ya fara aika mata da sakonnin da batasan kalansu ba, gaba d’aya yarima ya rikikta y’ar inna ta manta wace duniyar take ciki a wannan lokacin ya maidata cikakkiyar mace Wanda sai da ya gama rikita mata kwakwalwa kafin Mai aukuwa ya auku hawaye Wani na bin Wani babu bakin magana, yarima ya kankameta tamkar zai maidata cikinsa Yana Jin sonta da dada karuwa lallai Allah ya mata baiwa iri iri saboda Bai taba Jin irin abunda yaji agareta ba mata suna suka tara, ya taimaka mata suka tsabtace kansu kafin suka dawo ya sake kankameta sukayi bacci .
Ya makara wajen sallar asuba Wanda rabon haka ya faru dashi har ya manta yayi sallah ya tasheta tayi alwala Babu hijab sai da ya koma d’akin ta ya dauko bayan ta idar ta kasa hada Ido dashi ta haye gado ta kwanta, ya kalleta Yana murmushi yace ta tashi ya cire bedsheet din kauda Kai gefe tayi tana tashi kuwa ta fice daga d’akin bayan ya sauya bedsheet din ya koma d’akin nata tana kwance ya dawo kusa da ita ” morning hearty ”
“Good morning” ta amsa a gajarce, ” me zakici a kawo Miki yanzu ?”
“Tea kadai zan Sha sai Kuma pain killer ”
“Ok am coming..” sai da yakai bak’in Kofa tace ” da kayana please”
“Owk..” Yana fita ta runtse Ido tanajin azaban da gurin ke mata kawai daurewa take Bata son nuna masa gazawarta amma tanajin radadi, bayan like 30 minutes da fitarsa aka kwankwasa kofa jakadiya babba ce ta shigo da sallama wasu Yan mata kuyangi biyu na dauke da kaya suka ajiye cikin girmamawa suka gaisheta ta amsa, fita sukayi ya rage daga ita sai jakadiya ” sannu gimbiya Allah ya Miki albarka ya Baku zuria dayyaba, ga wannan tashi ki Sha sakon Fulani ne tayi matukar farin ciki da wannan lamarin, tashi ki zauna ” sunkuyar da Kai hajjo tayi tana Jin Wani bala’in kunya na ratsata wato yanzu sai da Fulani tasan meya faru kenan , Wani traditional bowl jakadiya ta Bude take qamshin ya cika d’akin farfesun kafan shanu ne Wanda ya samu dahuwa na musamman da kayan qamshi gashi da kaurinsa, jakadiya sai da ta tabbata hajjo Tasha farfesun me dan yawa kafin ta Bata hadin shayi irin nasu ba Madara sai kayan qamshi Yana da dan zafi haka tace ta shanye a hankali take sipping har ta shanye fiye da rabi tace ya isheta sannan ta Mika mata pain killer ta hadiye tace ta tashi suje ta shiga ruwan zafi, jakadiya Bata bar d’akin ba sai da ta gama duk aikin da Fulani ta sakata har kayan sawa sai da aka kawo mata daga bangaren Fulani wasu Arabian gown me kyan gaske da Yan kunnen gold set nasa kyautace ta musamman.

Bayan fitan jakadiya hajjo taji dad’in jikinta gashi an tattara d’akin an rufe mata kofa take ta fara Jin Wani bacci , ta gyara kwanciya kenan aka kwankwasa kofa guntun tsaki tayi ta tashi ta Bude wata mata kakkausa tana tsaye dauke da wasu kaya masu bala’in kyau sai daukan Ido suke ” barka da fitowa ranki shi dade Sako na musamman daga bangaren Fulani ” murmushi tayi tasa hannu ta karba ” nagode”
“Babu komai da son samu ne ki cire na jikinki sai ki saka wannan zatayi farin cikin ganinki dasu idan kika fito ”
“Nagode ” ta furta cikin kaguwa haka matar ta juya ta tafi, hajjo ta ajiye kayan gefen gadon ta zauna tana kallon na jikinta toh shin fulanin biyu ne ko Kuma yayane? ko minti 20 batayi ba da saka wannan sababbin kayan sannan a sake kawo Wani a ce ta saka gaskiya al’adun masarautar dayawa yake, rike Kai tayi kan na mata ciwo sallama yayi ya shigo ya rike hannayenta ” Yaya dai any problem naga kin rike Kan ”
“Ciwo yake min ”
“Baki Sha maganin da Umma ta aiko bane ?”
“Nasha…” “Ok sorry kwanta kiyi bacci yanzu zan Hana kowa shigowa ok ” Bata fuska tayi tace ” yanzu Kai don baka da kunya shine zakaje ka fada musu komai ”

“C’mon ban fada musu ba kawai dai it’s just a coincidence ” hararinsa tayi”ni ba yarinya bace ”
“Toh naji kwanta kiyi bacci is part of our tradition Kuma laifinki ne da kika wahalar dani tun daga Abuja ” kyabe Baki tayi ” ni gaskiya bazan Kara zuwa wajen Umma da Abbu bah da wane Ido zan kallesu gaskiya ni gobe zan koma Allah ”
“Duk naji ya yarda kwanta kiyi bacci ok… sorry my baby girl ” peck ya manna mata Yana Kara kallonta ” gaskiya kayan sun Miki kyau u really look like a princess ” “Umma ce ta bani su ”
“You look gorgeous Allah ”
“Thanks ga can wasu ansake kawowa ”
Ya juya yana kallon kayan ” waye ya kawo?”
“Wata ta kawo dazun tace sakon Fulani Kuma am even confused ” kallon tuhuma yakewa kayan yace ” shin wacce ta kawon ya siffanta yake?”
“Uhmm… doguwa haka so giant ” murmushi yayi Yana gyada Kai daga haka ya dauki kayan ya fita ba tare da yace mata komai ba, tabe baki tayi ta haye gado ta gyara kwanciya saboda bacci takeji nan da nan kuwa baccin yayi gaba da ita.

Bangaren Fulani yayi da kayan nan ya mata bayanin komai ta girgiza kai tace ” ta Allah ba tasu bane Allah ya kare y’ar mutane don Allah gobe ka dauketa ku tafi bana son a cutar da yarinyar nan yarima ” ” dama nace sati zamuyi amma yanzu ita kanta tace kunya takeji bazata iya hada Ido dake ba tace zata koma ” murmushi Fulani tayi ” don ma anrage wasu abubuwan al’adun naku ai da kunya kuwa bansan ya zatayi ba, Allah dai yayi albarka dazu waziri ya kirani Yana tambaya akan kyautar da ya aika ko ya iso wajena nace ni Babu abunda aka kawo ”
“Rabu dasu Umma ni Babu abunda iyalina suka rasa donhaka Wanda ya boye kyautar shiya sani ”
“Allah ya rufa asiri ya kareku da sharrin Makiya” “ameen ya rabbi Umma nah” ya tashi yabar part din Yana zuwa ya Bada directives akan a Hana kowa shigowa bangarensa kowanene sannan ya wuce fada wajen sultan.

Back to top button