Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 65

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*65*

Falon kasa suka sameta nan suka tare ta shirya musu kayan marmari da kunun aya da zobo bayan suka gaisa Hajjo ta Bata labarin sabuwar mota da ta samu adua sosai in a tai tana Sanya musu albarka Ayman yace ” haba inna don Allah ki daina irin wannan godiya bana so wallahi ai ita din kanwata ce ”
“Allah ya Kara arziki da rufin asiri”
“Ameen nagode inna aduar nake bukata a Koda yaushe” Hajjo ta mike ta tsaya ” inna muje ki gani motar tana waje ”
ta fada cikin Jin dadi, hijabi inna ta saka suka fito tare Ayman Yana waya ya koma gefe ya jingina jikin motar inna ta zagaya ta kare mata kallo tana musu adua da fatan alheri daga haka suka koma ciki shi Kuma yaci gaba da wayar da yake, suna shiga inna ta bude baki tace ” ke hajjo Kinga mota kuwa..Kai Masha Allah don Allah ki rike dan nan tsakani da Allah karki yarda ki cutar dashi ” murmushi tayi “insha Allah inna , ga Kuma sabuwar waya da ya kawomin sai Kuma jiya ya turo min kudi 5 mil suna cikin account dina ”
“iKon Allah…Allah ya Kara rufin asiri ya Baku zaman lafiya, yanzu zanyi magana da anty Balqis sai asan me za’ayi da kudin ”
“Toh shikenan inna dama shine nace sai nazo asan yadda za’ayi”
“Ki adanasu sai munyi waya duk yadda Ake ciki zan sanar dake bana son siye siyen banza da wofi”
“Ni Babu abunda zan Siya yanzu haka bana bukatan komai ”
“Ahtoh nasan Hali ”
Murmushi take ta dauki ayaba tana ci yayi sallama ya shigo ya zauna yace ” inna zamu tafi, sannan Kuma dama na kawota ta Miki sallama don jibi zamu wuce Sudan jirgin yamma insha Allah”
Bude Baki hajjo tayi tana kallonsa yace ” wat…me kike kallona ban gaya miki cewa idan kingama test zamuje Sudan bane?”
“Toh ai gobene zan gama” ” ni Kuma naje jibi zamu tafi bance Miki gobe ba right” Kai ta gyada ya tashi Yana saka hannu cikin aljihu ya zare bandir din 500 notes ya ajiye gaban inna yace “inna a mana adua ”
“Kai dai baka gajiya da dawainiya Allah ya Bada sa’a ya kaiki lafiya ya Kuma dawo daku lafiya”
“Ameen ya rabbi”
ya juya ya fice don Basu damar yin sallama da juna , inna ta Kara ja mata kunne akan ta kula da mijinta sosai ta Kuma Yi taka tsantsan da abokiyar zamanta haka sukayi sallama ta tafi.

Kai saye Sahad stores ya nufa branch dinsu dake women center batayi magana ba sai da yai parking sannan ya Kalli bangaren da take yace ” idan akwai abinda zaki bukata na tsaraba u can pick anything”
Fitowa tayi tana kallonsa ya kulle motar ya fito hannunta ya rike kamar zaa kwace masa ita suna tafiya a jere gwanin sha’awa duk Wanda ya kallesu yasan nice couples ne haka kurum Hajjo ta tsinci kanta cikin wani farin ciki she feel safe with him around her, ita dai ta rasa me zata dauka donhaka ta dauki turaruka dayawa toh batasan kalan suturan da suke sakawa ba a Sudan bare ta debi zannuwa kawai she decided to pick abayas ta dauki abayas dayawa da Kuma shaddodi masu tsada sai chocolates saboda yara da Kuma spices ita she is not good in shopping da ya fada mata da wuri zata nemi shawara gun inna Amma is late, haka suka gama siyayya ya Bada ATM card nasa aka cire kudin masu daukar kaya suka dauka zuwa mota Yana gaba suna biye dasu a baya, Yana fitowa wajen entrance din akwai wajen snacks da kaji ya tambayeta me zata ci tace pizza aka Sako musu 5 a leda da Kuma shawarma sai kaji 3 sannan ice cream da yoghurt daga nan suka wuce mota.
Ana Kiran magariba suka shigo gida aka dire kayan a falonta ya wuce Masallaci, itama sallah ta shiga tana idarwa ta fada wanka a gurguje ta shirya cikin wata English gown me tsagu ta gaba har guiwa sexy gown ce me shegen kyau , eyeliner ta saka sai lipgloss me sheki falo ta koma ta shirya kayan ta kawosu bedroom nata ta adana tana jiran shigowarsa shiru har akayi Isha tayi sallah ta saka hijab nata , abinci ta shirya bisa tray da Kuma pizza da shawarma din da suka Siya sai ice cream da yoghurt din ta dauka zuwa part din Failuzaa ta shiga da sallama fada yake mata muryarsa Bata fita sosai Amma kallo d’aya zaka masa kagane ransa a bace yake, ajiye abincin tayi ta juya ta fice saboda yanayin da ta samesu idanun Failuzaa cabe da hawaye ga meenal na zaune tana kallonsu, fitan hajjo Shima ya koma part nasa wanka yayi ya fito ya shirya cikin black jallabiya me kauri sai zuba qamshi yake.
Wani indian series take kallo yayi sallama ya shigo ya zauna Yana kallonta she looks sexy gown din yayi fitting nata komai na shape nata ya fito lumshe Ido yayi ya koma ya jingina jikin kujera, ta dan kallesa tace ” a kawo maka abinci”
“No..Wanda naci in d afternoon ya wadatar tanx ” “amma dai bahaka zaka kwanta ba koh”
Lumshe Ido yayi Yana cikin bacin rai har yanzu bayason hayaniya, ta fahimci hakan donhaka ta tashi ta dawo kusa dashi ” ya Ayman na kawo Maka tea?”
ya zuba mata sexy eyes nasa yace ” hearty bana Jin dadin jikina ne kaina ke ciwo ” murmushi tayi cikin tsigar wasa tace
“Kasan yarima bayason hayaniya yanzu dan magana da kayi shine yasa ka ciwon kai, sorry bari na kawo Maka shawarma dinka”
Bata Jira amsa ba ta tashi ta nufi table inda ta ajiye abubuwan, ta shirya komai cikin plate ta siyaya yoghurt cikin Wani glass cup ta dawo kusa dashi ” don Allah Kaci ko da kadan ne kasan baka jure yunwa , kada ka bari bacin rai ya rinjayeka ya hanaka cin abinci please”
Kallonta yake Yana Jin dadin yadda ta nuna kulawarta gareshi ” thanks I’ll eat but ke zaki bani da hannunki ”
Murmushi tayi sai Kuma tace “okay.. accepted”
nan da nan ya sauko daga kujera ya dawo kafet ta jera komai a gabansa shawarma din ta fara basa ya Bude bakin kadan Ya gutsira Yana taunawa a hankali batasan cewa ta kura masa idanu ba sai da yakai hannu ya shafa fuskarta, numfashi ta sauke cike da Jin kunya tace “sorry hankalina yayi Nisa ”
Cikin zuciyarta kuwa godiya takewa Allah da ya mallaka mata wannan bawan me cikar halitta Wanda Allah ya azurtashi da kyau kamar shi yayi Kansa ” tunanin me kike hearty?”
“Umm.. nothing” ta Mika masa Yana ci Yana kallonta ta sunkuyar da Kai cike da kunya bazata jure wannan idanun nasa ba, kadan ta ci pizza din ta tattara komai bayan sun gama ta fitar da KAyan da suka Bata zuwa kitchen. Toilet nata ya shiga ya Bude sabon brush yayi using ya dora da alwala sannan ya haye lafiyayyan gadon nata ya kwanta gaba d’aya Failuzaa ta canza masa mood nasa yau, Jin shiru baifito ba yaza tayi zamanta maybe he needs to be alone wata zuciyar na ce mata taje ta duba halinda yake ciki Wani bangaren Kuma Yana gargadinta haka ta zauna taci gaba da kallon film din sai 10 ta kulle kofar falon ta shiga d’akin bacci yake cikin kwanciyar hankali kamar Wani jariri haka yake sauke numfashi ta tsaya tana kallonsa tana murmusawa daga bisani ta shige toilet tayi brush tayi alwala ta fito ta kashe fitilun d’akin ta haye gadon ta kwanta. Sai around 3 Ayman ya Farka ya hangota can gefe tana bacci ya koma kusa da ita ya jawota jikinsa kamar zata Farka ya fara bubbuga bayanta taci gaba da baccinta Yana Jin Wani sonta har kasar zuciyarsa.

Yau sun gama test din gaba d’aya sai nan da wata d’aya zasu fara exams sun fito kenan hajjo take shaida musu gobe zata tafi Sudan Ummeey tace ” Kai how I wish da na biki besty Ina son zuwa Sudan ban taba zuwa ba bare Kuma masarautar Sennar anty zee ta yabamin al’adunsu wallahi tace komai nasu gwanin sha’awa ga Wasu dazuka masu kyau da ban sha’awa gaskiya ta Yaba Sennar city sosai,, murmushi hajjo tayi tace ” toh gashi ni ban Wani shaku dashi ba bare na rokesa mu tafi tare Kinga da Nima zaki debe min kewa saboda bansan kowa a can ba sai mahaifiyarsa ” Ummeey tayi carab tace ” ki kirasa yanzu ki fada masa nasan zai amince ”
Ba tare da ta kawo Wani abu a rai ba ta Bude jaka ta fito da sabuwar wayar tata Ummeey tace ” kanbu…waton kinyi sabon waya shine ko a nuna mana lallai besty ”
“Afuwan wallahi mantawa nayi ” Naima ta murmusa tace ” Amma dai Baku da tunani, yanzu da gaske Kiran nasa zakiyi Aysha wallahi karki kirasa yanzu ne fa farkon zuwanki shine zaki jajibo wata ku tafi tare, ki bare man asan ki a gidan kafin nan ki…
“Munafuka y’ar bakin cki waton bakison a tafi Dani toh wallahi sai naje idan kin Isa ki hanani ”
“Nidai ba munafuka bace sai dai ke” “dama na Dade Ina kula da irin hassadan da kike min Kuma karki manta tare kika ganni da Aysha Kuma haka zaki barmu tare ” hajjo tace” haba besty meyayi zafi haka don Allah ku daina ”
Naima tace” gaskiya Kam ya zama dole na fada tunda ba tsoronki nake ji ba hassadan me zan Miki me kike dashi Wanda ni na rasa”
“Ahayye .. abubuwa dayawa kuwa ke Naima wallahi kinsan cewa ni ba sarar ki bace kawai dai… ” Haba Ummeey haba Ummeey meyasa kike haka don Allah ki daina Babu kyau nidai bansan ki da wannan Halin ba ”
Naima tace” ai gara ta nuna miki tun wuri ki sani don wannan da kike gani macijin sari ka noke ne , idan ita Bata da hankli ai ke kina dashi donhaka karki yarda ki biye mata kice zaki fadawa mijinki ku…. Bata karasa ba taji saukar mari Ummeey ta ajiye mata Mari tana huci kafin kace me Naima ta rama tace ” kinyi kadan wallahi ”
“Ni zaki mara Naima wallahi sai kinyi nadama ”
“Babu nadamar da zanyi Ummeey yau ko ubankine shugaban kasa kinyi kadan ki mareni ban rama ba Kuma…
“Haba don Allah haba meyasa kuke haka don Allah ku bakuji kunya ba ” hajjo ce tayi wannan furuci
tsaki Ummeey ta ja ta gyara Jakarta tayi gaba , hajjo na kiranta taki dawowa Naima ta Kalli Hajjo tace ” wallahi ki biye mata ta kashe Miki aure don naga Yan kwanakin nan sai hiran mijinki take kidai bi a hankali ni bazan shiga tsakaninku saboda tare na ganku amma wallahi Ummeey batta da hali ” jikin hajjo yayi sanyi me hakan me nufi kenan, suna nan tare da naima Fauzan ya iso daukarta tacewa Naima tazo su tafi tace ” no yau nazo da motata dama wancan ta samu matsala ne aka bani wata ”
“Ok ayya toh ki gaida momy please”
“Zataji insha Allah sai munyi waya Allah ya kiyaye hanya” “Ameen nagode” daga haka suka rabu Hajjo ta wuce gida ta fara Shirin tafiya Sudan.

**********

*Sennar city Sudan*

Ankawata fadar kana Gani kasan baqi za’ayi saboda yadda makadan fada suke faman aikinsu sai bushe bushen kayan gargajiya Ake abinci kuwa baa magana an gyara bangaren yarima Ayman tsab hadimai sai Kaiwa da komowa suke Fulani kuwa kana ganinta kasan tana cike da farinciki

Back to top button