Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 9

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*9*
second to d last free page hurry n pay ur 300 saura kiris free page ya kare, thanks to all

*Birnin sennar*

Fadar Abu Hanifah na cike makil da jama’a ana fadanci anan magatakarda ya karanta sakon da ya fito daga masarautar kush cewa Sultan zai karbi bakoncin sarkin kush gobe idan sulatn ya bada izinin hakan, nan aka rubuta amsa cewa sultan na marhaba da xuwan nasa kuma yana godiya. Babu b’ata lokaci aka fara shirye shiryen tarban sarkin kush ta bangaren masauki da duk wani abunda zai bukata, washe gari kuwa aka kawata fada da kayan ado na zinari da lu’u lu’u da yakutu Wanda ababen tarihine tun kaka da kakanni ga makadan fada suna aikinsu hadimai kuwa babu zama an shirya private chamber na sarki da kayan abinci da na motsa baki kala kala dangin y’ay’an itatuwa da ababen sha , turare kuwa ba magana saboda kana doso bangaren zaka fara jin wani ni’imataccen qamshi ya buga maka hanci. Sultan ya shirya tarban baqo kuma aminin nasa saboda sun dade suna zumunci da juna , motocine sunkai 30 suka shigo fadar da tambarin kush a jiki nan fadawa suka fito saboda girmama wannan babban sarki don yana daga cikin sarakunan kasar Sudan , sultan da kansa ya fito yana tsaye har aka bude motar da sarki Kamaluddeen bn Rauf ke ciki dogarawarsa suka tare gaba saboda babu mai ganin fitar sarki daga mota , manyan rigunansu suka rufe ya fito bayan sun shimfida kafet yana rike da sandarsa mai daukan ido nan ya karasa kusa da sultan suka rungumi juna , falonsa na ganawa da baqi na musamman Wanda ba kowa ke shiga ba suka wuce, dogarawa a bakin kofa suka tsaya babu mai shiga ciki sultan na kishingide bisa lallausan karagarsa ga y’ay’an itatuwa a Gabansu hadimai maza shida ne suka shiga suka xuxxuba abinci da duk wani abunda ya dace mai dandana abinci ne yazo ya zuba kadan a cikin filet ya saka a baki yaci kansa na kallon kasa don bisa ka’idarsu bazaka hada ido da sarki ba, ya gama hadiye abincin sarki ya daga musu hannu suka fice daga falon Wanda girmansa yakai wani babban hall , suna cin abinci babu mai magana cikinsu sai bayan suka gama suka sha ruwa da tea irin na masarautar tasu cikin wasu kananun kofuna masu kyau da daukar ido.
Sarki kamaludden ya gyara zama hannunsa rike da inibi ya fara magana ” Allah baka nasara sultan ,wato nazo maka da wata magana mai muhimmanci ” ” Allah taimkeka ina sauraronka ” ” dama zancen auren y’ay’an nan ne wato Gimbiya Sabreena da yarima Ayman shine nake so a sanya musu rana don yarinya ta girma Allah taimakeka, bana son y’ay’an sarakuna su fara kawo mata hari gara ayi maganar auren nasu ” murmushi sultan yayi yace ” hakan yana da kyau zan shirya zuwa gabatar da abubuwan da suka dace na al’ada amma kuma yarima yanxu ya fara karatu a can kasar Najeriya, zamu d’aga lokacin biki zuwa karshen shekara kafin nan ya kammala shekara ta farko ” ” Allah ya nuna mana lokacin cikin masu rai ” ” ameen ya Allah ” haka suka cigaba da tattaunawa akan harkar siyasar kasar tasu da harkar kasuwanci. Gimbiya suhail na safa da marwa a falonta ta kasa samun sukuni ta rasa meyasa gabanta ke faduwa Allah yasa ba zarginta ne yazamo gaskiya ba idan hakane kuwa burinta zai wargaza na son cusa qaunar Gimbiya Sabreena a zuciyar Aseem saboda shi yafi dacewa da aurenta domin tana zumunci da mahaifiyar Sabreena sosai, a takaice zuwan Sabreena Hutu a wajenta ne sanadiyar haduwarta da yarima Ayman har ta fara nuna masa so da kauna duk da cewa shi bai damu da ita ba amma tana wani mahaukacin sonsa . jakadiya CE ta shigo dakin cikin girmamawa ” Allah ya taimaki sarauniya kuma Gimbiya ,na kasa samun cikakken labarin da ya kawo sarkin kush saboda dukkan masu kawo mana rahoto basu samu hanyar shiga ba, amma sarkin kofa yayi alkawarin kawo miki labarin kafin faduwar rana ” buga table tayi cike da bacin rai tace ” duk hanyar da zaku bi Ku tabbatar an kawo min labarin da nake son ji saboda ina cikin tsananin tashin hankali ” cikin rawar jiki tace ” Allah ya huci zuciyarki da yardan Allah dukkanin bukatunki zasu biya ” tsaki taja tare da d’aga mata hannu alamar ta fita nan ta sulale ta fice.

******************
*FCT, Nigeria*

Dady na falonsa ya aika kiran Sule yana xuwa ya risina cike da girmamawa ya gaidashi ya amsa cikin sakin fuska ” ya karfin jiki malam Sule ” ” Alhamdulillahi jiki ya warke nagode sosai Alaji Allah kara girma da arziki ya rufa asiri ” ” ameen nagode malam Sule, yanxu wace Sana’a kake ganin zaka iya?” ” ranka ya Dade duk aikin da na samu zanyi da izinin Allah ” ” da can menene Sana’ar ka a gida ?” ” ni tsohon direba ne kafin na tafi kamaru kasuwanci ” ” Allah sarki ba damuwa daga yau ka zama direba na amma sai an nuna maka gari ka San duk inda ya dace kafin mu fara fita tare, a can dakin d’ayan driver zaku kwana tare ” ” nagode alaji nagode sosai Allah kara arziki ” ameen zaka iya tafiya ” ya tashi ya tafi yana murna kai tsaye ya wuce wajen tanko ya bashi labari nan ya xauna suka kama hiran duniya.
Ammi ce ta shigo part nasu Ayman ta sameshi yana shirin fita lectures don yau bashi da class din safe sai 12 yake da class, zama Ammi tayi ya ajiye turaren dake hannunsa ya dawo kusa da ita ” Ammi wat is d matter u look tensed ” ” Ayman am worried about you, jiya da dare Umma ta kirani she was saying that ankai sadakin aurenka a masarautar kush ” cikin kaduwa yace ” what..as young as I am, meyasa zazu mini haka , meyasa bazasu daina wannan al’adar tasu ba, ya Allah gani gareka ” rike kai yayi yana jin wani irin bakin ciki a zuciyarsa , ” sorry son kayi hakuri Allah yasa hakan shine mafi alheri ” ” Ammi ba alheri bane bana son wannan auren bana son sarauta shiyasa nafi son na nisanci kaina ga masarautar I hate everything about it ,baka da freedom komi naka atakure bana son irin wannan rayuwar nafison nasarar rayuwata ya kasance ba karkashin masarautar ba , ina son nayi rayuwa as a normal human being not as a royal Prince Ammi ” kafadarsa ta rike tana bubbuga bayansa , daga karshe ta tashi ta fita kwanciya yayi don gaba baya bayajin fitan yafison ya kwanta a gida ko zai samu saukin abunda yake ji , letter ne ya fado masa a rai idan baije school ba waye zai kawo masa wasikar? tashi yayi ya xauna yana lumshe ido nan da nan ya karasa shiryawa ya dauki jaka ya fita fauzan na ganinsa ya karbi jakan suka shige mota suka wuce.
Yau hajjo zazzabi take tana kwance a gida tasha pcm taji dan dama bata samu zuwa school ba inna na zaune tana hada sabulun mmn yusra, sallama akayi mmn Nana ce ta dawo daga chefane ta xauna tana cire hijabi ” sannu malama ana nan ana aiki ,ya mai jikin ” ” alhamdulillahi gata nan ta samu sauki, ya rana ?” ” hmm ana zafi a garin wllhi talaka na shan wahala komai yayi tsada yau pure water naira talatin ina zamu koma ne jama’a ” murmushi inna tayi tace ” Allah zai kawo mafita ,amma dai kinsan cewa baa mugun sarki sai mugun bafade, mutane basu gane cewa laifin ba daga shugabanmu ne mutanen da suke tare dashi sune suka aikata wannan abubuwan don bata gwamnatinsa amma idan muka tashi sai zagi da tsinuwa kuma hakan haramun ne a addini babu kyau zagin shuwagabanni , idan bazaka musu adua ba kayi shiru ko ka roki Allah ya yaye mana ” girgiza kai mmn Nana tayi tace ” Allahu Akbar! Kai ilimi yayi a rayuwa, shiyasa malama kike birgeni wllhi kina da nitsuwa ga kuma aiki da ilimi” murmushi tayi tace ” dama amfanin ilimi aiki dashi , Allah ya ganar damu ya kawo mana sauki cikin lamuranmu ” ” ameen ya Allah, wannan sabulun amaryar ne , malama wannan me dame ne aciki naga yayi ja yayi yellow ” ” ta kawo sabulan da take amfani dasu sune na daka, nidai Zuma kurkum dilka majigi lemun tsami man zaitun rosewater da madara ta gari na hada mata a ciki, sai sabulun Ghana da sabulun salo da lallen gargajiya kadan saboda kashe kuraje sai kuma madarar turare kadan saboda qamshi ” ” lallai wannan hadi yayi, da a ce mijina na nan da kin hadamin jikina yayi luwai luwai ” mmn Nana ta fada tana dariya ” haba mmn Nana yanxu fisabilillahi bazaki gyara jiki ba sai saboda namiji, idan ya dawo bazata ya sameki haka kuma ai bai dace ba, ita mace yar gayu ce yana da kyau ki kasance cikin tsabta ko kina da miji ko babu domin tsabta cikon musulunci ce, koda bakiyi ado mai nauyi ba ki kasance kullum akwai Abu uku a tare dake.wannan Abu uku sune kwalli ko tozali, turare da kunshi idan baki rabuwa da wannan abubuwan wllhi karyan namiji yace zai raina ki ko ya miki kallon ballagazar mace , amma shi turare idan zaki shiga cikin jama’a ya haramta wani yaji qamshin turaren saboda hakan babban laifine musamman ida n ya yaba da turaren tamkar kin aikata zina ce ” ware ido tayi ” tabbas kuwa laifin zina zaa rubuta miki saboda an haramta mana hakan, dama shi zina ba sai kayi fasikanci ne kadai zina ba zina tana dayawa akwai zinan ido akwai na hannu akwai na baki da sauransu Allah dai yasa mu dace amma wllhi muna da babban aiki a gaba aljannar bahaka kurum zamu shigeta ba sai mun dage da nemanta ” jikin mmn Nana yayi sanyi tace ” malama Allah ya barmu tare ya baki lada, lallai mata muna cikin kalubale zaki ga matan unguwan nan dayawa sai idan zsu biki suke cin uban kwalliya amma a gida sai zani da t shirt ,idan zaa biki kuwa turare daban daban ga Jan baki da aishado toh kice duk zina ce , kowacce tana son nuna ita wata ce ” ” Allah yasa mu gyara ,amma dai kayiwa mijinka kwalliya ka samu lada da yardan Allah da mala’ikunsa ya fiye maka burge yan Adam ” ” wllhi har jikina ya mutu saboda ni kaina lokacin da bbn Nana na nan yakan ce ke ko yar kunshin nan da mata keyi bakison yi sai zama da daurin kirji a gida babu kwalliya ” dariya inna tayi cikin zolaya tace ” toh kice ke kika korosa bawan Allah yatafi Neman mai lalle da Jan baki da turare ” ” ah ah malama talauci dai ya korosa ga uban y’ay’a da ya ajiye ” dariya suke hajjo tayi shiru tana sauraron hirar tasu lallai dole itama ta dage da kwalliya don ta burge farin masoyin nata Wanda bata samu daman sanin sunansa har yau, sai yanxu ta tuna dashi Allah sarki yau bata samu an rubuta Mata wasika ba ” inna zan tafi talla anjima koh” ” a’a yau dai ki huta sai kin kara samun sauki ” ” inna na warke tuntuni ” ” nace bazaki ba sai gobe ko jibi insha Allah ” turo baki tayi ta koma ta kwanta .
Aman ya fara xuwa wajen ya gama dube dubensa bai hango ta ba ya gaji ya tafi shagon malam Dalha ya tambaya aka ce masa yau batazo ba haka ya juya ya tafi yana murmushi, Ayman kuwa har wajen 6 ya karasa ya fita ya gama yawonsa shiru babu letter ya juya zai koma kenan ya hango dan aiken nasa yaron yazo da gudu yana murmushi ” ina wuni Alhaji ” shafa kansa yayi ” ya kake,yau baka kawomin sako na ba why?” ” ni kaina Neman ta nake amma wata yarinya tace min batazo ba , shikenan yau bazan samu kasuwa ba ” murmushi yayi ” dama kasuwanci ka maida aikan?” ” ehh mana ba kudi kuke bani ba kai da ita ” ” haba nawa take baka? ” ” wataran goma wataran ashirin ” ” abokina meyasa kake son kanka dayawa,kullum ina baka 500 ko dubu d’aya bai isheka ba sai ka karbi nata,daga yau kada ka sake ni zan na baka kullum kaji aboki ” ” ai shikenan nagode, dama tunda na hadu da kai na daina bara don kana bani kudin da ko a kwana uku bana samun hakan, da sai na kwana biyu banci abinci ba amma yanxu gaskiya ina jin dadi ” hawaye ne ya fito masa yayi saurin sharewa yace ” alhamdulillahi dan abunda nake baka har ya wadatar da kai, kaga ina da lada a wurin ubangiji sai kayi kokari ka taimaki abokanka Wanda basu da abunda zasu ci kaji koh, kullum zan baka dubu d’aya ka raba da abokanka OK ” kai ya gyada masa ” yaya sunanka ?” ” sunana Sale ” ” OK sale ga wannan ka rike, idan kaga abokiyata kace ina gaisheta kuma nayi kewanta a yau kadai da bansamu sakonta ba na kasance cikin bakin ciki, sannan ina son Ku tayani da adua Allah ya min mafita kan lamurana ” gyada kai sale yayi , nan ya cire 1k ya mika masa ya karba yayi godiya ya tafi cike da murna, girgiza kai Ayman yayi yana tausayin yaron wannan rayuwar da muke ciki akwai damuwa sosai yanxu Allah kadai yasan mutum dubu nawa suke kwana da yunwa a kullum, tabbas duk halinda bawa ya tsinci kansa sai ya godewa Allah saboda kafi mutane dayawa wadata wasu kuma sunfi ka, har ya shiga mota yana tunanin rayuwar talakawa musamman wannan yaran almajiran he wonder meyasa wasu iyaye ke turo y’ay’ansu almaniranci Wanda baqar wahala kadai suke sha , wani lokacin yunwa zai hana yaron karatu Allah yasa mu dace a wani bangaren zuciyarsa kuwa tunanin secret lover din nasa yake kome ya hana ta rubuta masa oho gaba d’aya yana jin yayi kewarta duk da cewa baisanta ba bai taba ganinta ba.

*Nasarar rayuwata is not for free , ki tuntubi 07030077024 for payment details @ 300 naira only, if you really enjoy d story please don’t be stingy 300 baifi karfi ba a min adalci for my time n knowledge thank you*

Back to top button