Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 58

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*58*

A bangaren nata suka kwana washegari Basu tashi da wuri ba Failuzaa kuwa kafa 3 tana zuwa part nasa baya ciki gaba d’aya ranta a dagule yake taso ta buga musu kofa anty Maryama sun hanata dole ta hakura, Hajjo ce ta fara tashi tun bayan baccin da suka koma da asuba wanka tayi ta shirya cikin kananan kaya riga long sleeves brown shirt da palazo golden n brown ta zuba kitson nata har gadon baya tayi light makeup da nude lipstick tayi kyau sosai, kitchen ta nufa a nan taci karo da Failuzaa wacce numfashinta kamar zai dauke ayayinda taci karo da kyakkyawan fuskar hajjo.
“Ina Kwana” hajjo ta furta a fusge daga haka ta wuce bangaren da kayanta suke, daidaita nitsuwarta tayi ta kirkiro murmushi
“A’a amarya da kanki zaki shiga kitchen ai da kin bari yanzu zan hada mana breakfast din ”
“Babu komai ke da kika dawo jiya ke yakamata ki huta na girka mana ” tana magana tana Bude drawers ” A’a kije kihuta ki kula mana da miji wannan aikina ne ”
Murmushi hajjo tayi haka Failuzaa ta dage sai ta tasa hajjo fita ta koma part nata cike da bacin rai gaskiya bazata iya hada kitchen da wannan matar ba.
Zama tayi a falonta ta rasa me zatayi gashi ta tashi da yunwa , chin chin ta tuna donhaka taje ta hada tea me kauri ta koma kitchen ta dauki plate Failuzaa na fere dankalin turawa murmushi suka sakarwa juna hajjo ta dauki abunda zata dauka ta koma part nata, kasan kafet ta zube tana Shan tea nata cikin kwanciyar hankali ya fito ya tsaya bakin kofa Yana kallonta Yana faman murmusawa
“Good morning baby girl”
Juya idanu tayi kafin ta amsa ” morning my Yaya”
Murmushi yake ya karasa kusa da ita ya zauna
“Chin chin at dis hour”
Marairaicewa tayi ” toh ni yunwa nake ji”
“Ba dole ba jiya rigima ya hanaki cin abinci”
turo Baki tayi ta juya masa baya, ya zagaya ta gabanta ya zauna tare da rike hannayenta
“Tell me what do you want to eat yanzu zansa a siyo Miki don wannan kwalliyar ba na shiga kitchen bane ” rausayar da Kai tayi “ni ka kira inna kace ta aikomin da breakfast ”
“Angama hajjajo ” dariya ya Bata ta murmusa tana masa fari da idanu
“Kinsan me..idan kika cigaba da min irin wannan kallo komai zai iya faruwa ”
hararinsa tayi”komai kamar me kenan ”
“Komai as in anything..”
“Yaya nah! ” ta furta sunan cikin Wani irin salo Wanda Hakan ya saukar masa da kasala , yarinyar nan zata jefasa cikin matsala batasan cewa Yana d’aga mata kafa bane ,
“Yaaya…”
“Uhmm..Ina jinki baby girl” “Yaya Ina son zuwa school yau please…” Wani kallo ya mata kafin yace ” ok ..by what time?”
“10 am ”
“Ok bari na shirya idan na fito sai muje kiyi breakfast gidan inna daga nan sai na saukeki ”
“Thank you Yaya ” murmushi yayi ya tashi ya fice daga falon tana kallonsa tana Jin Wani irin yanayi Ayman akwai saukin Kai ba laifi bashi da problem ko kadan.

Yayi wanka ya fito cikin kananan kaya body huck Black n white sai black rubber jean Wanda ya kama jikinsa ya gyara sumar Kansa sai daukar Ido yake agogon Dior Jordan ya saka da Dior sneakers gaskiya yayi matukar kyau Mai daukar hankali, bangaren Failuzaa ya shiga suka gaisa da Yan uwanta suka shaida masa tana kitchen meenal ce ta fito yarinya me kama dashi sak sai dai haske ta fisa tana ganinsa ta makale Dady Dady haka suka wuce kitchen, Failuzaa na kwashe potatoes da ta soya suka shigo ta kura masa Ido Babu ko keftawa Yana murmushi ya d’aga mata gira
“Madam u r doing something, please kar ki Kona kanki concentrate”
Murmushi tayi ” morning Qalbee ”
“Wannan sunan belong to somebody, morning ya kika tashi ” ” not fine gaskiya ” ta fada tana yatsina fuska , ya ware Ido” meke damun ki ?”
“Ina missing din mijina so much ” murmushi yayi yace ” yau zan dawo gareki ” ta murmusa tace ” I can’t wait..”
dariya suke dai dai lokacin hajjo ta shigo zata ajiye plate , sai zuba sauri take kamar zata Fadi Ayman yabi ta da kallo Failuzaa kuwa tana ganin hajjo ta fara narkewa ” Qalbee kasan me, jiya fa har mafarkin ka nayi don Allah yau ka dawo da wuri saboda Ina bala’in missing naka kasan mun Saba kullum Muna makale da juna all these days da nayi ni kadai jina nake tamkar wata mara lafiya ”
Juyawa tayi ta fice daga kitchen din , Ayman Yana bin bayanta da kallo Failuzaa ta murmusa tace” Qalbee am talking ”
“Yes..Ina ji ai ”
“Ina zan ajiye mana abin breakfast din idan na gama?” “No..ni fita zanyi yanzu so don’t include me ” Bata rai tayi “kamar Yaya Ina Kuma zakaje bakayi breakfast ba ”
“Fita zanyi somewhere important ” daga haka ya juya ya fice meenal na makale dashi Yana son ya mata dabara yaje gun hajjo ya rasa ya zaiyi donhaka part nasa ya shiga ya dauki chocolate ya Bata sannan ya sauketa bakin kofar falon Failuzaa yace ta jirasa Yana nan dawowa a haka ya samu ya rabu da ita.
Hajjo tana kwance bisa 2 seater zuciyarta na tarfafasa tana Jin haushin kanta meyasa zata shiga ta samesu , wata zuciyar Kuma na ce mata ke me naki a ciki mata da mijinta dama can masoya ne ke kika shigo kika samesu Ina ruwanki da rayuwarsu, da haka ta samu ta rarrashi zuciyarta har ta rage Jin radadin da takeji. Sallama yayi ya shigo ya tsaya Yana kallonta Yana son karantar yanayin da take ciki Amma ya kasa gane komai” are you ready Qalbee nah ”
“Don Allah Yaya sunan nan ya fita daga bakin ka” ” but why..haka nake son kiranki ”
“Ni Kuma bana so bana sharing din abubuwa dayawa a rayuwata Wani abin dolene yasa nake sharing amma Ina son ka gane Hakan ka Kuma kiyaye ” Wani Kayataccen Murmushi yayi ya Gane inda maganar ya dosa wato saboda Failuzaa ta kirasa da Qalbee a gaban idonta , ya zuba hannaye cikin aljihu Wanda ya Kara masa kyau yace ” fine…idan kika ce haka is ok, idan kin shirya tashi mu tafi banason meenal tazo ta sameni ta cika rigima kamar Antin nata ” murmushi tayi ta tashi ta shige bedroom ta barsa tsaye a falon, girgiza kai yayi wato cikin Yan kwanakin da sukayi tare ya gane lallai tana da kishi amma ita Bata farga cewa kishinsa take ba shi Kuma Hakan ba karamin dadi yakeji ba da alama tarkonsa ya fara kama kurciya.

Bayan Yan mintuna ta fito cikin hijab dogo har kasa cikin hijaban da ya Siya mata a gida kafin aure Bata taba sakawa ba sai yau, bag nata dauke da books sai Kuma waya shikenan. Kallon Jin dadi ya bita dashi dama irin shigar da yake son ganinta ciki kullum kenan, yayi gaba tana baya ta kulle part nata da key lokacin 9 ne da Yan mintuna Kai tsaye mota suka nufa. Fauzan na Jin karar mota ya fito suka gaisa Ayman yace Yana nan dawowa idan Bai dawo da wuri Kuma Fauzan ya shirya yaje office saboda yau shi bazai samu daman zuwa ba, ya saka key ya tada motar hajjo tana kallonsa tabe baki tayi kamar baza tayi magana ba sai Kuma tace ” saboda kana dokin komawa gun uwargidan naka shine zakayi skipping din office, kar ka manta Yan uwanta suna nan dai ” murmushi yayi ya juya Yana kallonta a dai dai lokacin da suka fita daga harabar gidan kenan ta turo Baki tace ” ni ka daina kallona ka Kalli titi ”
” Wannan bafulatana ba dai kishi ba, kin manta jiya nace Miki am tired yau zan huta a gida shine zakimin Wani sharri ”

“da banji da kunne na bane sai ka Musa amma ai naji abunda ta fada that Kuna missing din juna blah..blah..”ta karasa maganar tana juya idanu, dariya ne ya kubcewa Ayman har Yana buga steree hararinsa tayi tace
“Ni kada ka yadamu kan hanya please ”
Yana murmusawa idanunsa na bisa titi Yace ” my jealous Ayshah” tabe baki tayi tace ” am not jealous ni Ina ruwana da soyayyar ku da matarka tare na sameku ” lumshe Ido yayi ” u are also my wife Ayeeshah” kwanciya tayi bisa kujera Bata sake magana ba ya dauki hanyar zuwa Apo.

Failuzaa ta gama girkin ta fito ta Kai nasu part nata ta dauki na hajjo zata Kai anty Sailuba ta tabe baki tace ” sai Kuma kiyi ai , tana can makale da miji sun fita tun dazu ke kina nan zaki Kai mata abin Kari ”
“Tare fa kika ce anty, yanzu dama saboda ita ne Qalbee yaki tsayawa yayi breakfast yace min akwai inda zashi very important” “toh da me kike tunani ga important nan agabansa me yafi amarya important yanzun, kedai ki dage kiyi abunda aka ce Miki idan bahaka ba zaki tattara ki koma Singa ahtoh ”
“Kissan nan dai kissan dai ki rike shi hannu biyu ki dora maganin Akai sai a samu zaman lafiya idan bahaka ba kina ji kina gani zata rabaki da mijinki don naga yarinyar tana da mugun wayo da kirsa ” tagumi Failuzaa tayi zuciyarta na raya mata abubuwa dayawa dole sai ta daura damara.
Inna tana falo tare da Nana tana baya Sadeeq custard sabuwar Mai aikin da ta kawo tana mopping a kasa aka danna door bell ta Bude hajjo ta shigo a guje Ayman na tsaye Yana murmushi ta haye sama , da sallama ta shigo falon inna tana kallonta cike da mamaki tace ” ke lafiya da sassafe haka ?”
turo Baki tayi”wato inna ni bakiyi kewata ba koh ”
Ayman ne ya shigo cikin takun kasaita tare da sallama inna tana kallonsa ya karasa ya zauna bayan sun gaisa yace ” gata nan ta dameni tace tana son karyawa da girkin innarmu shine na kawota” girgiza kai inna tayi “yau naga shiririta, shine ka biye mata ka kawota , aure ko sati ba’ayi ba har Kun fara sintiri bisa titi ”
Tashi hajjo tayi ta wuce kitchen bayan mintuna ta fito rike da plate din shinkafa da wake da stew a sama, Wani kallo inna ta biyota dashi saboda ganin spoon d’aya da ta dora bisa abincin ” ke kadai zaki ci abincin koh” inna ta tambaya a bukace, murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yace ” inna kinsan yanzu tare muke ci shiyasa ta kawo spoon d’aya” kunya ne ya rufe hajjo ta Kalli Nana tace ” kawo min spoon please” haka suka ci abincin cikin plate d’aya inna ta tashi ta Basu waje, Sadeeq sai Shan kununsa yake sai da ya koshi kafin ya dawo kusa da hajjo ya zauna.

Back to top button