Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 56

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*56*

Ayman Yana wanka Yana faman murmushi Yana lumshe Ido Yana tuna kiss din da ya mata he needs more , haka ya gama shiri a gaggauce saboda lokaci ya tafi cikin wasu blue suits ya fito Yana rike da dan briefcase nasa sai zuba qamshi yake tana nan bisa kujera ya shigo kallo d’aya ta masa gabanta ya Fadi don Wani irin cool kyau da yayi zai iya Sace zuciyar duk macen da suka Hadu Koda a hanya ne , murmushi ya sakan mata ya dawo kusa da ita ya zauna saitin fuskarta ya kawo Kansa yace
” zan tafi Qalbee ki min adua ”
Wani ajiyar zuciya ta sauke kafin tace ” Allah ya tsare ” “Ameen tanz I’ll surely miss you” sauke idanu tayi Batason ya Gane halinda take ciki Yana jefa zuciyarta cikin matsala a duk lokacin da yake mata irin wannan abubuwan, hannunta ya rike tare da narke fuska ” yanzu ke baza kiyi missing dina ba haba mana is not fair…”
ta shagwabe fuska tace ” ya Ayman don Allah ka tashi kaJe sai ka dawo ”
“Um..um ni sai kin min good bye kiss ” juya idanu tayi tana furzar da iska ita dai tana ganin jaraba ashe dama haka yake tana ganinsa shiru shiru din nan, batayi aune ba taji lips nasa cikin nata sai da yayi kissing nata son ransa ya saketa Yana Maida numfashi ya juya dakyar ya ja kafa ya fice , daskarewa tayi inda yabarta jitake tamkar komai na jikinta ya daina aiki lallai Ayman Yana gab da zautar da ita da nasa salon soyayya dama haka so yake , ta share 30 minutes tana tunani iri iri akan Ayman Kafin ta tashi ta kulle kofa ta koma bedroom nata bacci takeji ta kwanta tunaninsa ya cika mata zuciya tana tuna ranar da suka fara zuwa dubata a asibitin Aso haka dai ta cigaba da tuna rayuwarta na baya har bacci yayi gaba da ita.

Failuzaa kuwa tana gidan Ammi kullum waya take da Yan uwanta na Sudan suna Kara kwantar mata da hankali haka nan zee sukanyi chat ta mata hudubar tsiya saura kwana biyar Yan uwan suzo gaba d’aya tayi kewar mijinta daurewa kawai take don Babu yadda ta iya Amma idan dare yayi dakyar take bacci Gani take Yana can makale da amaryarsa duk da cewa har yau batasan dalilinsa na auren yarinyar ba Amma gaba d’aya ta tabbata munafukar uwar yarinyar ce ta lika masa ita dole tadauki mataki zasu raina kansu ita kuwa zata gwammace da baayi auren ba ita amaryar , kudaden da ya Bata 5 million duk gida ta tura zasu mata shiri na musamman da kudaden dole ta tashi tsaye ta kwaci mijinta a hannun kowace y’a mace don bazata iya barin Ayman ya rabi wata mace bayan ita ba saboda shi din na musamman ne samun namiji da ya hada komai irinsa sai an tona.
dA yamma Fulani ta shirya zuwa ganin amarya tayi tayi suje da Ammi firr tace Babu inda zataje donhaka suka shiya da anty sofy da kuyangi biyu Yan rakiya driver yakaisu gidan, Hajjo taci kwalliya da yamma dama sunyi waya da inna tace mata ta fara girki yau shiyasa ta dafa tuwon shinkafa da miyar kubewa danya sai Kuma dambun couscous me hade da vegetables, sai kunun aya da ta hadà ta shirya komai bisa table tana kallo taji alamun door bell tana mamaki toh ya manta da key ne ko yau Kuma salon da yazo dashi kenan, hijab ta dora kan doguwar Egyptian abaya da ta saka sai qamshi ke tashi don ta tuna gargadinsa na ranar kan fitowa Babu hijab .
A hankali tasa hannu ta Bude kofa nan taci karo dasu murmushi tayi tana musu barka da zuwa ta musu iso har zuwa falonta , a kasa ta zauna bayan Fulani ta zauna bisa kujera kuyangin suka zube kasa kusa da ita ganin haka hajjo ta Gane kowacece don inna ta fada mata cewa shi Dan sarki ne, cikin girmamawa ta gaisa dasu anty sofy kuwa sai kallonta take tana Kara godewa Allah da ya raba mijinta da wannan yarinyar kyau kamar ita tayi kanta.
ruwa ta kawo musu cikin tray ta ajiye Fulani na Sanya mata albarka daga nan ta tashi ta fara sakko da kulolin abincin suka bi bayanta da kallo har ta gama shirya komai ta musu Bismillah murmushi Fulani tayi tana Jin dad’in tarban da ta samu tabbas yarinyar ta cancanci so saboda tana da halayen kirki, kuyangin ne suke tambaya ko akwai abunda Fulani ke bukata daga cikin kayan abincin tace a zuba mata kunun aya zata Sha anty sofy kuwa ta Bude kulolin ta zuba tuwon kadan ta fara ci tana lumshe Ido miyar tayi yauki sosai ga kayan qamshi a ciki ga Kuma daddawa abin ya Bada ma’ana, Fulani kuwa dambun aka zubo mata tana fara ci Hajjo ta tashi ta fice zuwa bedroom don Basu guri.
Sai bayan wasu mintuna hajjo ta fito ta samu kuyangin sun tattara komai sunkai kitchen har sun wanke plates din da aka Bata, zama tayi Fulani na godiya cikin zolaya tace ” mun cinye abincin maigidan idan ya dawo me zaici ”
Murmushi tayi ” A’a ba komai akwai Wani tuwon dama dayawa nayi ”
“Allah yayi albarka sai hakuri zaman tare zomu zauna ne Kuma zomu Saba,…” Nasiha sosai ta mata hajjo ta mata godiya suka tashi tafiya ta zubo chin chin dasu alkaki da sassafa da dublan dayawa cikin babban cooler ta mikawa kuyangan suna godiya ta rakosu har bakin mota, suna Shirin shiga aka wangale gate motar Ayman ta danno Kai Fauzan ke Jan motar shi kuwa Yana gidan gaba. Fulani ta fasa shiga mota sai da akayi parking suka fito fuskarsa dauke da murmushin ganin ummarsa ya karasa Yana rike hannunta ” Umma nah barka da zuwa”

“Barka da dawowa ango ” murmushi yayi”Umma harda ke ”
“Munzo ganin amarya Masha Allah tubarakallah Ina tayaka murna yarima Allah ya Sanya alheri ”
“Amin nagode Umma nah ” ya fada Yana kallon Hajjo wacce ta sunkuyar da Kai kasa , Fauzan ya gabatar da gaisuwa wajen Umma sannan ya juya ya gaisa da hajjo
“Munyo tawaga munzo mun cinye girkin da amarya ta ajiye Maka ”
dariya yayi Wanda ya Kara fito da kyaunsa yace ” ba matsala Umma sai ta girka min Wani nasan Bata da ganda ai ”
“Toh Allah yayi albarka mu zamu wuce magariba ta gabato ”
“Nagode Allah ya kiyaye hanya ” hajjo ta musu sallama ta juya ta koma cikin gida.
Cikin zuciyar Fulani fes taji dadin yadda ta samu hajjo haka take mafarkin samun suruka Allah ya amsa aduarta sai murmushi take tana murna Allah Allah take suje gida ta kira sultan ta zayyana masa wannan albishir din.

Fauzan ne ya shigar masa da jakar can ya tsaya bakin kofa Yana sallama ta fito ta karba kafin ta gabatar masa da abinci Wanda ta zuba masa nasa musamman ya karba Yana godiya ya juya ya tafi, part nasa ta shiga ajiye jakar can bedroom ta Kai masa ta fito kenan suka kusa yin karo bakin kofa, hannaye ya Bude mata ta sunkuyar da Kai kasa Yana murmushi ya jawota ya rungumeta Yana cewa
” Bakiyi missing din mijinki bane Qalbee..” lumshe Ido tayi tana Kara labewa bisa faffadan kirjin nasa ,
” Muje ki min massage am darm tired, sorry I was busy shiyasa I didn’t call to hear from you”
batace komai ba ya juya hannunsa na bisa kafadanta suka koma bedroom yasa hannu ya zare hijabin Yana kallonta daga sama har kasa, runtse Ido yayi ya tuna lokacin da siyo rigar a Madina Yana kiyasta yadda zata karbi jikinta ashe da rabon shi zaigani a hankali ya furta
“Alhamdulillah bini’imatillah”
Kallonsa take salonsa daban yake , zama sukayi bakin gado ya Mika mata kafafunsa ya kwanta yace ” ki taimaka ki cire min takalma da socks din kinsan ni dan gatan ki ne dole ki koyi yadda zaki kula dani”
Babu gardama ta cire masa ta ajiye sannan ta yace ” saura massage” tabe baki tayi ita dai Allah ya hadata da Dan rigima , kamar ya tuna Wani abu ya tashi zaune ya fara cire botins din suit nasa ta sauke Kai tana kallon kasa ya gama cirewa ya Mika mata sannan ya cire tie din daga nan ya cire shirt daga shi sai singlet ta kasa hada Ido dashi ya juya ya fara zare belt tayi saurin kauda Kai gefe murmushi yayi Yana kallon duk Wani nokewa da take ya gama ya ajiye bisa gado ya juya ya shige toilet, motsin ruwa da tajine ya tabbatar mata da cewa wanka yake tashi tayi ta shirya kayan inda ya dace ta fice daga d’akin.
Ya gama wanka ya fito Bata d’akin ya shirya cikin jallabiya ash color me kauri lokacin ana Kiran magariba dama yayi alwala ya fesa turare ya fito ya leka Bata falo daga nan ya wuce Masallacin Dake layin nasu, Bai dawo gidan ba sai bayan Isha ta sake canza kaya mini top da notch skirt ta saka me fadi ya matukar fito da tsarin jikinta tana danna waya tana murmushi ya shigo da sallama ta amsa , zama yayi Yana kallonta hankalinta na kan waya yasa hannu ya karbe wayar ta d’aga Ido tana kallonsa
“Yanzu lokacina ne ba lokacin waya ba, Baki bani abinci ba kina hira da wasu a waya ”
“Sorry ” ta furta daga haka ta tashi tana tafiya cikin salon Jan hankali Wanda ita kanta batasan dalilin yin Hakan ba, ta dauki tray din da ta shirya masa tazo ta dire agabansa Yana kallonta Babu cire Ido ta gama ajiye komai ta Bude warmer cikin sanyin murya tace ” me za’a zubo Maka ”
“Tuwo nake so ”
Kulli biyu ta since ta juye cikin plate sannan ta zuba Miya cikin bowl hade da nama ta ture kusa dashi , ruwan wanke hannu ta ajiye masa Yana kallonta sai da ta gama zata tashi yace ” wait…ai Baki gama aikin ba ko kin manta a Baki zaki ban ” sunkuyar da Kai tayi yace ” wallahi am serious yau dai sai kin bani ”
Shiru tayi tana zaune kamar wacce taje Neman gafara , ya sauko ya dawo kusa da ita ya zauna yace ” Bismillah Qalbee nah”
kamar zatayi kuka ta wanke hannu ta fara basa tuwon Yana ci Yana zuba Santi yana mata shiririta da rashin kunya iri iri har ya gama yace ya koshi , tana wanke hannu yace ta zubo Wani tuwon haka ta zuba ya jawota yace ” is ur turn ”
Ware Ido tayi ” nifa a koshe nake”
“A’a dole sai kinci ” narke fuska tayi yaki sarara mata dole ta Bude Baki Yana Bata tana ci kamar Bata so taci rabo tace ya isheta, ta tattara komai ya tayata suka Kai kitchen ya wuce d’akinsa itama toilet ta wuce tayi brush sannan ta fito.

tana zama ya shigo yace ” oya kizo mu tafi , kinsan da Rana Ina tayaki hira a part naki dare Kuma part dina zamuje” hararinsa tayi kasa kasa Yana murmushi ya d’agata Bata Musa ba suka wuce ya sauketa bisa 3 seater ya kunna TV ya dawo kusa da ita ya kwanta Kansa na bisa cinyoyinta yace ” toh a bani labari ”
Shiru tayi Bata kulasa ya gyara kwanciya Yana kallonta kamar daga sama yaji tana cewa ” tun yaushe ka fara Sona ?”
“Tun ranar da kika fara turamin wasikun soyayya” ware Ido tayi
Yana murmushi yace “yes…tun kina y’ar kwaila I love me you…wash Kash kibiyar sonka ya tsokeni ” dariya hajjo tayi harda kyalkyalewa ya zuba mata ido Yana kallonta she look so cute idan tana dariya , tayi minti 2 tana dariya kafin tace ” are you serious ni na taba turo maka wasika ”
“Uhmm toh…I don’t know ko it’s not meant for me amma Allah ya kaddara hannuna zasu shigo shiyasa tun a wannan lokacin ya fada tarkon son y’ar yarinya Ayshatul Humaira uwar muminai ” murmushi tayi yace ” tashi muje ki gani ”
Yana gaba tana baya suka shiga bedroom nasa ya Bude sif ya Ciro wata karamar bag ya fara fito da wasu takardu cikin Wani file ya dauko letters din ya Mika mata, ta Bude tana karantawa cike da mamaki haka abin ya dawo mata tiryan tiryan tana tuna lokacin da take ba sale naira 10 kullum akan ya isar mata da sakonta wajen Aman ashe Aman Bai taba karanta sakon nata ba ko sau d’aya, Wani guntun hawaye ne ya fito tayi saurin sharewa Yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi komai nata burgesa yake shi Kansa baisan irin kaunar da yake mata ba Kuma yayi alkawarin sai ya cusa mata sonsa cikin zuciyarta Wanda sai ta furta da bak’inta. rayuwa kenan kana naka Allah na nasa yau gashi sun Rabu da Aman rabuwa ta har abada , ta gama karanta letters din yasa hannu ya dauke ya Maidasu inda suke ya mayar ya rufe sif din ya koma gado ya kwanta ta tashi zata fita yace “Ina Kuma zaki Qalbee nah”
Shiru tayi ta dawo ta zauna.

Back to top button