Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 8

Sponsored Links

️8️⃣

Inna sai numfarfashi take, nishinta na fita ta kwanta lifet da ribda ciki, kawai jiran tsammani take, dan duk tunaninta aljanin ne ya shigo kawai neman inda take yake yi.

“Allah ka gani ZAMAN WANKA na zo, hanyar zumunci ne, idan kuma ba aljani bane mala’ikan mutuwa ne Allah ka yafe min kura-kuraina, ka haɗa mu a aljanna da Malam, ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla” Cewar Inna a zuciyarta.

Gabaɗaya ta sanya hannunta ta riƙe ƙafar gadon, duka hannayenta a jikin katakon suke, dan gudun kar aljanin ya ɓanɓarota daga ƙasan gadon. Har aka fara kiran assalatu Inna tana ƙasan gado Sadiya kwa bata falka ba, saboda kwana da ta yi ta waye tana gwagwarmayar naƙuda hakan ya sanya ta gaji bare haka nan ma nauyin bacci gareta.

“`IMRAN“`

Tun da ya buga ƙafarsa a jikin kujera ya ƙara razana Inna, jin ɗif a ɗakin babu motsinta hakan ya sanya ya gane ta mugun tsorata dan haka bai ma san lokacin da bacci ya ɗaukesa ba. Sai dai lokacin sallah ya yi alerm ɗin wayarsa ya fara masa sallama, tashi ya yi ya kunna fitalar falon ya fara kiran Sadiya sau boyu kawai ya kirata dama ba dan ya tasheta ya yi kiran ba dan Inna ta jiyo muryarsa ya san tana nan har lokacin a tsorace dan haka ɗakin ya nufo ya zo ɗaukan kayansa dan ya yi shirin tafoya masallaci. Daga setin da Inna take a ƙasan gado daga nan drower kayansa take, haka ya buɗe ya sanya kayan da ya yi amfani da su wajen tsorata Inna ya ɗora musu wasu kayan ya ɓoye su yadda ba za a gani ba ya ɗakko wami yadi riga da wando, ya juyo ya fito daga ɗakin sai dai ya yi matuƙar mamaki da Inna ta ji shigowarsa amma bata fito ba, kuma ya tabbatar idonta biyu, dan babu yadda za a yi bacci ya ɗauketa dan bata cikin kwanciyar hankalin da bacci zai ɗauketa.Sosai abin ma ɗaure masa kai da ya ga bata kan gadon, yana tunanin inda za ta ɓuya a ɗakin sai da ya je zai buɗe drower ne ya hangi rigarta a ƙasan gadon aikuwa kamar dai ya yi ta ƙyaƙyata dariya.

“Ashe ma abin naki tsoro ne ba dai ke MAI ZAMAN WANKAN da za ta addabi mutane ba ma ji ma gani wai an rufe tsohuwa da ranta” Ya faɗa a zuciyarsa ya fito falo ya sanya yadin da ya ɗakko ya fita domin yin alwala ya tadi masallaci.

“`INNA“`

Tun da Inna ta hangi hasken fitilar falo gabanta ya shiga faɗuwa dan duk tunaninta aljanin ne.

“Ya Allah ka makantar da aljanin nan kar ya ganni, idan kuma shi ba aljani bane mala’ikan mutuwa ne ka sa in cika da imani, ka haɗa ni a aljanna da Malam Allah ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla” Ta faɗa hawaye na gangarowa daga idanunta.

 

Har sai da ta ji Imran ɗin yana ƙwalawa Sadiya kira hakan ya tabbatar mata ba aljanin bane Imran ne ya tashi. Ta san jin Sadiya bata amsa ane ya taho ɗakin. Amma sai ta ƙyaleshi har ya gama uzurinsa ya fice.

“Babu abin da zai sa na faɗa maka akwai aljani a bayi, sai ka je kaima kun yi ido huɗu da shi ka gan shi ra’ayal aini, sannan in ga ƙarshen kurmanci dan na san yau in ka rinƙa ƙwanzama uban ihu sai duk maƙota sun ji ka sai ka gwammace kiɗa da karatu, dan yaro bai san wuta ba sai ya taka, yau za mu ga ƙaryar rainin wayo” Inna ta faɗa a ranta tana hasashen yadda Imran ɗin zai yi idan ya ga aljanin.

Shiru -shiru bata ji ihun Imran ba, abin ya bata mamaki dan ita mugunta ce ta sa ba za ta faɗa ba ma bare ya fs zuwa bayin, tana a haka sai ƙaran buɗe ƙofar gida ta ji ya fita masallaci, sosai ta girgiza da hakan.

“To ko dai aljanun gidan ne basa yiwa masu gidan komai si baƙi, ko dai tun da ya ɓace lokacin da na waiwaya bai ƙara fitowa ba shi sa Imran ɗin bai ganshi ba?” Ta rinƙa saƙa-da warwara zuciyarta.

Har sai da gari ya ɗan fara haske sannan ta ji ƙaran ƙofar gida alamar Imran ya dawo daga masallaci, kamar jiran dawowarsa yaran ke yi, uka tashi suka fara kuka a tare. Hakan ma ya yi dai dai da shigowarsa ɗakin ya fara tashin Sadiya daga bacci, haka ta tashi tana ɗan yatsina fuska tare sa murza idanu irin na wanda ya tashi daga bacci.Haka ta ɗauki Hassan ta yi bismillah ta sanya shi a nono, shi kuma Imran ya ɗauki Husainin yana jijjigashi a kafaɗarsa. Sai bayan yaran sun ɗan yi shiru ta lura Inna bata kan gadon.

“Inna har ta tashi sallah kenan” Ta tambaya tana kallon Imran.

“Sa’adiyya, Sa’adiyya” Inna da ke ƙasan gado ta shiga kiran sunan Sadiya.

“Ikon Allah daga ina nake jiyo muryar Innar ne?” Ta faɗa tana ɗan waiwaye -waiwayen ɗakin dan ta ni muryar a ɗakin ne.

“Halima kin ganni nan” Cewar Inn jin bayanta ya tokare da jikin katako ta ma kasa ko da yinƙurin fitowa daga ƙasan gadon dan ta san dai yanzu aljanin ko yana nan dai, ba zai zo a tun ba ga masu gidan a nan kuma gari ya waye shi kuma zuwan dare ya yi jiya.

“Ina kike Inna?”

“Ko a cikin drower take” Cewar Imran a fili a ransa kuwa sai dariyar ƙeta yake yiwa Inna.

Hannu Inna ta ɗauke daga riƙon da ta yiwa katakon, ta sanya a jikin filankin gadon ta shiga bugawa da hannunta.

“Ƙasan gado kuma, Inna?” Sadiya ta faɗa da mamaki, ta miƙa Hassan kan gadonsa ta kwantar dashi ta tashi cikin sauri dan ta san tun da Inna har ta shiga ƙasan gado to ba lafiya ba lallai akwai lauje cikin naɗi.

“Wai kina nufin daga ƙarƙashin gado muryar ke fitowa?” Imran ya tambaya da nuna alamun mamaki.

Cikin sauri Sadiya ta gewaya ta leƙa aikuwa idanunta suka sauka a kan kakarta da ke kance magashiyan da rubda ciki ta kama katakwaye ta rirriƙe kamar wanda za a ƙwace mata su.

“Inna garin yaya kika shiga bakya ganin ma wurin ya yi matsi, ya miki kaɗan gabaɗaya a takure kike” Sadiya ta ce tana durƙusaw dan taya Innar fitowa.

“Taimaka mata mana, ko a magagin bacci ta shiga” Ya faɗa yana jin tamkar ya kwanta ya yi ta dariya tsabar yadda dariyar ke cinsa.

“Haba ɗan nan kamar wata ɓera zan shiga ƙasan gado, kuma ko a sume nake ba bacci ba ai ba na shiga ƙarƙashin gado ba” Inna da ke ta nishi ta faɗa a fili dan bakinta bai mutu ba, da ta ga gari ya waye. A zuciya kuma ta ce.

“Kai dai da Allah ya tsallakar da kai baka yi angamo ba amma ba haka na so ba na so ka ganshi muraran yadda na ganshi ai ni na ga ta kaina yau”

dashi ta tashi cikin sauri dan ta san tun da Inna har ta shiga ƙasan gado to ba lafiya ba lallai akwai lauje cikin naɗi.

“Wai kina nufin daga ƙarƙashin gado muryar ke fitowa?” Imran ya tambaya da nuna alamun mamaki.

Cikin sauri Sadiya ta gewaya ta leƙa aikuwa idanunta suka sauka a kan kakarta da ke kance magashiyan da rubda ciki ta kama katakwaye ta rirriƙe kamar wanda za a ƙwace mata su.

“Inna garin yaya kika shiga bakya ganin ma wurin ya yi matsi, ya miki kaɗan gabaɗaya a takure kike” Sadiya ta ce tana durƙusaw dan taya Innar fitowa.

“Taimaka mata mana, ko a magagin bacci ta shiga” Ya faɗa yana jin tamkar ya kwanta ya yi ta dariya tsabar yadda dariyar ke cinsa.

“Haba ɗan nan kamar wata ɓera zan shiga ƙasan gado, kuma ko a sume nake ba bacci ba ai ba na shiga ƙarƙashin gado ba” Inna da ke ta nishi ta faɗa a fili dan bakinta bai mutu ba, da ta ga gari ya waye. A zuciya kuma ta ce.

“Kai dai da Allah ya tsallakar da kai baka yi angamo ba amma ba haka na so ba na so ka ganshi muraran yadda na ganshi ai ni na ga ta kaina yau.

Imran ganin Sadiya ta kamo hannunta tana janyowa amma ta kasa taimakawa Innar, hakan ya sanya ya kwantar da Husainin jin ya yi shiru ya nufi wurin ya durƙusa ya leƙa, da idanun Inna ya ci karo sun yi wani ƙwala -ƙwala, ga bayanta tokare da saman jikin ƙasan gadon.

“Wa ya ga ido ya ƙwallin wake, sai rarraba ido take ya na mujiya” Ya faɗa a ransa yana dariyar zuci.

Hannu ya sanya ya kamo ƙafar Inna ya riƙe wajen idon sawun ya ja.

“Haba Imirana, baka ganin yadda ka riƙe min ƙafar da ƙarfi kamar ka riƙe ƙafar raƙumi, son dai ka karya min ƙwauri ko ka girɗa ni” Cewar Inna tana sauke numfashi dan da ɗan ƙarfi ya janyo ƙarfar.

 

Ai jin ta kira shi da Imirana nan da take kiransa hajan ya sa wani haushi ya ƙara turnuƙeshi, a haɗa ƙafar duka biyu ya shiga janyosu.

“Wayyo Allah, ashe Halima kina ganin rashin imanin da mijinki ke min sai ja min ƙafafu yake kamar mai ɗakko ruwa a rijiya, ni ba guga mai igiya ba a ce ana jana ta ƙarfin tsiya”

“Bari in ɗauke katifar sai a ɗauke filanki sai ta fito” Cewar Sadiya dan ita ma ta tausayawa Innar amma har yanzu tana mamakin dalilin shigar Inna ƙasan gadon. Jin abinda Sadiya ta faɗa yasa Imran sakin ƙafar Innar amma ba a hankali ya saki ba jaɓas ya yiwa ƙafafun.

“Ta Allah ba taka ba Imirana, in Allah ya yarda da ƙafafuna zan mutu, in ma taƙamarka ka gurgunta ni”

“Ga aljani nan mai fararen kaya, na ciki bayi yana tsaye a samanki” Imran ya faɗa a ransa.

Sai da aka fitar da duka filanki Inna Azumi ta lallaɓa ta fito tana jin jikinta gabaɗaya yana mata ciwo kamar wanda aka mata dukan tsiya.

“Ubangijn mutane da aljannu, Allah saka m…”Inna da ta fara ƙoƙarin neman sakayya ta ja bakinta ta yi shirun gudu ko aljanin na wurin ma dan su b ganinsu ake ba.

 

Sharaf ta zauna a tsakiyar ɗakin tana sauke numfashi.

“Inna wai mai ya kai ki shiga surƙuƙin ƙasan gadon nan, ko duk kunyar gadon ce ta sa kika ƙi kwana a ka, kuma sai ki shiga ƙasan gado san ki jiwa kan ki ciwo” Sadiya ta faɗa cikin jin tausayin Innar ganin ta yi wujig-wujiga, ji yadda rigarki ta jiƙe jigif”

“Haba Halima yo in har kunyar gado nake ai bana shiga ƙasan sa ba, sai in kwanta a tsakiyar ɗaki”

“To mai ya ki ki shiga ƙasan gadon?” Imran jin an jefowa Inna wannan tambaya sai ya yi saurin barin ɗakin ya koma falo dan ya yi dariyarsa ta ishe shi.

“Wai na ce Halima bayi nawa gareku a gidan nan?”

“Inna ana ga yaƙi kina ga ƙura, bayin me kuma amma dai na ga ba yau kika fara zuwa gidan nan ba bare ki ce baki sani ba”

“Ke kar fa ki min rashin kunya ki bani amsa kawai”

“Guda ɗaya ne”

“Mara ta gabaɗaya a cike take ina zuwa” Ta faɗa tana miƙewa ta fito daga ɗakin, gabanta na ɗan faɗuwa, tana zuwa falo ta ga Imran zaune a kujera ya ɗora ɗaya kan ɗaya baki ta taɓe ta ce

“To Allah ya yi dare gari ya waye” Ta faɗa tana yin gaba ta fita daga falon.

“Gata nan aljani” Cewar Imran zuciyarsa ya fara dariya har da riƙe ciki yana mamakin ƙarfin hali irin na tsohuwar nan wai ita ala dole ba za ta nuna karayarta ba. ” Amma dai mu je zuwa” Ya faɗa yana sake sakin wata dariyar.

 

Dai dai nan Sadiya ta leƙo, ganin Imran na dariya sai abin ya bata mamaki mutumin da ganin dariyarsa m aiki ne sai ya ga dama amma yake dariya haka har da riƙe ciki amma dariyar ba mai sauti ba.

“Inna a ƙasan gado” Ya yi saurin faɗa dan Sadiya ta ɗauka ganin Inna a ƙasan gado ne ya sanya shi dariya, dan kar ta yi zaton akwai wani abu a ƙasa ta yi saurin harbo jirginsa.

“Haba kuma menene abin dariyar ni wallahi tausayi ta bani na san haka kawai ba za ta shiga ƙarƙashin gado ba”

“Hakane amma ki tuntuɓeta”

“To” Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin ɗakin.

 

“`INNA“`

Tana fitowa gabanta na daɗa tsananta bugu, gani take kamar za ta sake ganin aljanin nan, hango takalmanta a wajen hanyar bayin kowanne ya kama gabansa, hakan ya sa ta nufesu ta ɗakko ta sanya a tsorace dan gani take kamar aljanin ya sa takalmin.

“Wallahi dama da ba takalmina bane na ado, da ba zan ɗauka ba in je in saka kofato ya fito min”

 

Haka dai a tsorace ta sanya takalmin ta je wurin wanke -wanke ta kunna famfo ta yi fitsarinta ta yi tsarki, ta wanke cinyoyinta zuwa ƙafafunta da fitsarin daren na ganin aljani ya ɓata mata, haka ta ɗaura alwala cikin sauri ta baro tsakar gidan, sai gata bidik ta faɗo falon kamar an jefo ta, duk da Imran ya san dalilin saurin nata sai da ya kalleta da mamaki. Amma Inna ta wayance ta fara tafiya a hankaliyadda take tafiyarta, ta buɗe jakarta ta ɗauki abin sallah da wasu kayana ta wuce bedroo.

Sadiya na kallonta ta ce

“Inna akwai ruwan ɗumi fa kika yi dana sanyi” Banza Innar ta mata har ta gama canja kayan ta tada sallah ita kuma lokacin tana baiwa Husaini ruwam zam-zam ɗinsa.

Sai da ta idar ta kalli Sadiya ta ce

“Ni Halima baku da mansileta ko roob, ko ma aboniki ne ki bani”

“Me kuma za ki yi da su Inna

“Ni na ji yarinya da neman dalili in da akwai ki bani mana , yo ni da na ƙarasa kwana na a ƙasan gado tamkar wacce take a ƙasan gadar legos har a tambayeni mai zan yi da man zafi, jikin nan nawa ban da ciwo babu abin da yake, ga wani wurin ma duk na kuje wallahi, kai in da ranka ka sha kallo”

“Akwai kin gan su can a kan mudubi, amma Inna wai dan Allah me ya kai ki kika shiga ƙasan gado?”

Har za ta faɗawa Sadiya abin da ya faru sao kuma wata zuciyar ta ce mata

“Kar fa ki bada labari yana jinki ke da ba ganinsa kike ba, ya ke ya ƙara tsorataki cikin dare in har yana zuwa ita ma za ta gan shi wata rana”

“Yo me zai sa kwa na shiga ƙarƙashin gado in ba sanyi ba, kin san ɗakinmu na ƙasa da banbanci da na siminti sanyi ne kawai ya sanya na shiga ƙasan gadon haba ina zan iya da sanyin nan naku na birni mutum ya rasa inda zai sa ransa, yake jinsa kamar a cikin ruwa” Ta faɗa tana shafa aboniki a jikinta.

Shiru Safiya ta yi tana sauraron Inna tana ammaki wane irin sanyi Inna ta ji da har ta shiga ƙasan gado.

“Allah kyauta”Cewar Sadiya.

“Ina kwana Inna, ba mu gaisa ba”

“Lafiya lau, ya kwanan ƴan samarin?”

“Lafiya ƙalau”

“To madalla bari in tashi in ɗora ruwan wanka tun da gashi har gari ya waye tangararau” Cewar Inna ta tashi ta fita.

“To”Inna

 

Haka ta fito ta ga Imran yana kan katifar ya sanya filo ya jingina da jikin kujera yana latsa waya. Ko kallonsa bata sake yi ba ta fita , wajen da aka tanada tukunya da ita ce ta nufa ga wani ƙaton murhu wanda zai ɗauke tukunyar.Kallon tukunyar kaɗai ya sanya Inna zaro idanu tana tunanin ta yadda za ta ɗor tukunyar haka ta sassaka itacen a murhun ta hura wutar tana ta ɗari-ɗari da tsakar gidan sai take ganin kamar aljanin nan zai fito, har dai ta kammala ta shiga kokawa da ƙatuwar tukunyar dakyar ta ɗorata a kan murhun sannan fa ta je take ɗakko ruwa tana zubawa a ciki sai da ta cika sannan ta rufe ta dawo ɗaki.

“Ina kwana Imirana”Inna ta gaishe da shi jin bai gaishe da ita ba.

“Lafiya ƙalaw” Ya faɗa idanunsa na kan wayarsa.

 

“Idonka da kunya nangaisheka ka amsa Imirana, dan rashin kunya in zo gidankanZAMAN WANKA in kwana amma a ce ni zan gaisheka?”
Shi dai bai ƙara cewa wani abu ba.Haka ta rinƙa komawa tana iza wutar har ruwan ya yi zafi, ta kwalfa ta kai bayin tana ta addu’a ba dan Sadiya ba za ta iya kai ruwan ba da a ƙofar bayin za ta ajiye. Haka ta yiwa Sadiya wankan nan da ruwa mai zafin tsiya sii tururi yake amma haka ta laflafta mana da tawul, sai da ta gama sannan ta haɗa mata ruwan da za ta shiga ciki wanda aka zuba dettol a ciki, dakyar Sadiyar ta yarda ta zauna.

“Yo wannan har wankan jego ne Halima wanka da tsumman tawul, mu lokacin mu da runhu ake yin wankan ruwan kan tafasa har sai ya yi ja, sannan a sanya ka tsugunna a kan garwashi”

“Garwashi fa Inna”

“Eh mana a sanya turaren gabgab a ciki har sai ya ƙone za ka tashi, amma ke yanzu da wannan jikin duk faci wa zai sanyaki tsugunna ɗinkin naki ya farke bayan ruwan da za a shiga ma cewa suka yi marar zafi sosai”

 

Haka dai ta fito ta bar Sadiya a zaune a cikin ruwan ta zo ta haɗa wanda za ta wanki Hussaini dan bata ma san yadda za ta wanki Hassan ba dan bata so ma ta ga bayansa bare har ta masa wanka, dan duk maganar nan da ake fa bata yi ido biyu da bayan Hasan ɗin ba.Husssimin ta wanka ta gasa wa cibiya ta shirya shi tsaf, haka dai ta zubar da ruwan ta ƙara haɗo wani na Hassan ɗin danbata so ma dai amma haka za ta daure saboda ita ta ce ta ji ta gani za ta yi ZAMAN WANKA. Bayan ta ajiye ruwan dama Hussainin Imran ta baiwa da yake a bedoom ɗin take musu wankan.Har lokacin Sadiya bata fito daga bayi ba.Inna hannu na karkarwa ta ɗakko Hassan da ke ta bacci haka ta shiga rabashi da kayansa zuciyarta na lugude, shi kwa ya shiga yantsara kuka jin an tashe shi daga baccinsa.Sai da ta tuɓe shi tana ɗauke idanunta sannan ta kalli yaron wani irin zabura ta yi ganin yadda bayansa yake.

 

“Lahaula wala ƙuwwata illah billahi aliyal azim” Ta faɗa hankali tashe.

“Imirana! Imirana!Imirana!!” Ta shiga zabga masa kira hannunta riƙe da yaron jikinta sai rawa yake…

 

Masu son grp na zaman wanka 09030283375.ƳAR ZAMAN WANKA‍

(KWANA ARBA’IN)

NA

 

MAMAN AFRAH

 

Back to top button