Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 55

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*55*

Bathroom din Kansa abin kallo ne haka ta cire rigarta ta shiga jacuzzi tub ta hada ruwa ta shiga tayi wanka sai qamshin shower gel nasa ke tashi ta gama wankan ta dauki bathrobe nasa ash color ta saka turarukansa take kallo ta hango sense body splash da Resonance ta fesa a jiki ta Bude kofa ta fito , Yana zaune bak’in gado Yana waya yabita da kallo hannu ya Mika mata ta dalla masa harara ta nufi kofa taku biyu yayi ya cafkota ta callaraa Kara ba shiri ya kashe wayar . Bubbuga kafa ta fara masa
“Ni ka barni kaya zan saka ” Ina da kaya a nan d’akin ”
“Um..um ni banson kayan matarka ” ya jawota ya matseta da jikinsa ” tell me meyasa kike kishin matata ”

“Ni bana kishinta ni ka kyaleni ”
“Bazan iya kyaleki ba har abada Ina tare Dake Qalbee ” lamo tayi a jikinsa tana Jin Wani shaukin na kamata, Ayman ya iya lafazi ba laifi ya iya Sace zuciya cikin kankanin lokaci. Kankameta yayi tamkar zai maidata ciki Yana Jin Wani sonta na dada shigar kowane jijiyoyin jikinsa , zaunar da ita yayi bisa gado ya Bude wardrobe nasa ga mamakinta sababbin kayan bacci ne a jere cikin ledansu masu dumbin yawa Yana daddagawa har ya hango kalar da yake so black n red ne da kwalliyan flowers Riga ce da guntun wando iya guiwa , ya bare ledar ya cirosu ya fesa turaruka 3 sannan ya ajiye mata ya juya ya Bata baya yace ” am waiting…ki saka wannan ” turo Baki tayi”ni..ni ka fita ka ban waje ”

Murmushi yayi ya fice daga d’akin, a hankali ta tashi ta zame rigar wanka Dake jikinta tanayi tana kallon kofa tamkar mara gaskiya har ta gama sakawa wow…Masha Allah kayan sun matukar karban skin nata tayi kyau sosai a ciki abunka da farar fata, qamshin turarensa ya mata dad’i.

Haye gadon tayi ta kwanta Batason fitowa falon ya kare mata kallo, ganin Shirun yayi yawa ne yasa Ayman ya shigo tare da sallama tana kwance ta Bada baya kare mata kallo yayi Yana saurin dauke Kai ya karasa bisa gadon, rufe Ido tayi tamkar tana bacci murmushi yayi yasa hannu Yana taba dimple nata murmushi ne ya kubce mata ya mirgino ya koma kusa da ita tafin tasa ta rufe fuska yasa yatsun hannunsa Yana shafa zanen fulawar da aka mata yace ” Ina son abin nan Yana matukar birgeni ”
Ya cigaba da shafa lallen nata Yana kallon kyakkyawar fuskarta yace “tashi ki zauna magana zamuyi ” ko motsawa batayi ba
“Kina kina Qalbee…”
tana son amsawa amma kunya take Gani take is too early ta sake dashi haka amma duk laifinsa ne daya like mata ya hanata samun sukuni …
Saukar hannayensa bisa gashin kantane ya dawo da hankalinta ” please Qalbee don Allah ki bani hadin Kai mu zauna lafiya bana son matsala ta bangaren ki please, duk da nasan cewa is not easy amma please ki daure ki jure ki boye kiyayyar da kikemin please…” Ya karasa maganar tamkar zaiyi kuka da sauri ta Bude fuska tana kallonsa tace ” Yaya Ayman ni ban taba tsanar ka ba please don’t misunderstand me, ni na karbi auren a matsayin kaddarar rayuwata ”
Lumshe Ido yayi ” wallahi auren nan shine the best thing that ever happened to my life , please ki daukeshi da muhimmanci ki sama min farin cikin da nake mafarki don Allah” shiru tayi jikinta yayi sanyi ya cigaba da cewa ” nasan Kuna matukar kaunar juna dake da Aman ni bazan ce ki ciresa daga cikin zuciyarki ba cos nasan is not easy at all Amma Ina rokon ki da ki boye kiyayyar wannan auren Hakan shine zai samar min da kwanciyar hankali da nitsuwa” hannayenta ya rike
“Ina son kasancewa dake har karshen rayuwata Ina son idan na mutu ki min takaba a gidana a matsayin matata ”
Hawayene ya taru a idanunta nan ta kife kai da pillow ta fara rusa kukan da batasan dalilinsa ba, ya rude ya dauka kalamansa sun tuna mata da Aman ne da sauri ya jawota Yana Bata hakuri Bata sauraresa ba ta cigaba da kuka .
” Am sorry Qalbee if my words hurts you in any way please kiyi hakuri ki yafemin please wife…”

rungumeta yayi Yana bubbuga bayanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ya fara hura mata iska a kunne taji tsigar jikinta na tashi tana lumshe Ido nan da nan ta fara gyangyadi kafin kace me bacci me dadi ya kwasheta, Jin saukar numfashi ya tabbatar masa da cewa tayi bacci ya Kara jawota bisa jikinsa Yana gyara mata kwanciya, adua ya mata ya tofa kafin ya kashe switch din zuwa dimm.. light haka suka kwanta tana bisa jikinsa ya dora habarsa bisa kitson nata har bacci yayi gaba dashi Yana rungume da ita tamkar Wani zai Sace masa ita.

Da asuba ta tashi ta koma part nata bayan ya tafi Masallaci ya tasheta tayi sallah key ta saka don batason ya dawo ya sameta ya takura mata , wanka tayi kafin tayi alwala tayi sallah ta zauna tana azkar har zuwa 6 ta dauki Qur’an tana tilawa har zuwa 7 tayi adua ta ajiye. Gyaran d’akin tayi yau batajin bacci donhaka ta fito ta gyara falonta duk da cewa Babu Wani datti daga nan ta kunna bunner qamshi ya mamaye part din, kitchen ta nufa an kawo kulolin abincin jiya da aka bawa maigadi donhaka ta wankesu ta tsabtace kitchen din ta koma falonta ta mike lokacin karfe 8:15 , sanye take da lace riga da skirt kayan sun balain Yi mata kyau Bata daura dankwali ba TV ta kunna tana kallon channels, bayan like 30 minutes akayi knocking kamar a mafarki taji muryar inna tana sallama cike da murna ta tashi ta Bude kofa Yana tsaye cikin shirt mara nauyi da blue jeans ya gyara gashin Kansa sai qamshi ke tashi, inna ta kalleta tace ” kodai bazaki bamu hanya mu shiga bane ”
Cike da Jin kunya ta karasa ta rungumi innar saboda ita harga Allah batasan ta tsaya kallonsa ba. ” Inna kece da safiya haka ”
“Toh ko bakison nazo ne”
“A’a, Ina kwana ”
“Lafiya ya zaman kadaici”
tabe baki tayi “banason asan nazo wajenki shiyasa na buga wannan sammako haka ” ya ajiye basket din hannunsa Wanda inna ce tazo dashi ” inna Ina Sadeequ nah ”
“Yana bacci baisan na fita ba , ai ba dadewa zanyi ba dama shiya matsa wai dole sai nazo naga gidanku ” murmushi yayi Yana kallon Hajjo ya kasa cire Ido tayi kyau sosai, ita kuwa ta kasa mishi magana kunyan inna takeji, ya juya yace ” inna minti 5 Ina zuwa bari nayi waya ”
daga haka ya juya ya fice, inna ta karewa falon kallo ta gyara zama tace ” ki bani Aron hankalinki kafin ya dawo don yanzu zan tafi, kina ji …Ina son ki kwantar da hankalinki Ayman mutum ne Mai saukin Kai ki saki jiki dashi ki manta da komai na baya kiyi facing future, na tabbata Allah ne ya Miki wannan zabin Kuma insha Allah baza kiyi nadama ba, wannan yaron tun bayan haduwarmu dashi yake ta dawainiya damu har ila yau, ina son kisa a ranki cewa Ayman shine nasarar rayuwar ki saboda duk makarantar da kikayi a baya da na yanzu shiya biya Miki kudin ….”
“Wat…inna are you serious ” ta fada cike da mamaki, ” tabbas Ayman shiya biya Miki na secondary har university da kike ciki yanzu idan kina tantama ai kina da number y’ar Mrs Juliet sai ki kirata ta Miki bayani , yaron nan ya cancanci so da kauna a gareki yasan mutunci da darajar ki donhaka na rokeki daki rike wannan auren tsakani da Allah ki cire Aman a cikin zuciyarki don Allah…” ta karasa maganar tare da damke hannun y’ar tata , jikin hajjo yayi sanyi tace ” toh Amma inna meyasa tun farko kuka boyemin Hakan, ko godiya ban taba masa ba , Kuma ya akayi aka daura auren dashi ?”
“Allah ya riga ya rubuta cewa shine mijinki tun farko shiyasa Aman da Kansa ya janye yabar masa ke aka daura ” hawaye ta share ta Kalli inna tace ” shikenan ni Kuma nayi alkawarin faranta masa iya gwargwadon yadda zan iya insha Allah ”
“Allah ya Miki albarka Allah ya Baku zaman lafiya ki masa ladabi da biyayya ki bashi girma ki rike masa amana a kullum Kuma ki kyautatawa kowa nasa , abokiyar zamanki Kuma Babu ruwanki da fada da ita ki zauna da kowa lafiya kedai ki rike adua Allah ya tsare ki da sharrin masu sharri ”
“Ameen nagode inna ”
“Maza share hawayen kar ya shigo ya sameki haka, ki rike tsabtar nan da na sanki dashi Kuma ki kasance me yawan fara’a agaresa da duk Wani Wanda yazo gidan nan , Banda rowa ki kyautatawa kowa ki rabu da kowa lafiya banason naji akasin haka ”
Gyada Kai tayi tana share hawayen da ya zubo mata a fuska , shiru sukayi can ya shigo da sallama inna ta tashi tace” yawwa dama jiraka nake ni zan tafi ”
“Haba inna daga zuwa Kuma sai tafiya ”
“Kai dan inna yanzu ma saboda dagewar da kayi ne yasa na taho ”
“Toh nagode innata ni kadai ” ya fada Yana kallonta murmushi tayi ta sunkuyar da Kai gaba d’aya kunyarsa takeji yanzu dama shi yake sponsoring karatun da take ita ta dauka uncle Yusuf ne ashe bahaka bane, inna ce ta katse mata tunani ” yaushe uwargidan naka zata dawo ?”
“Ni ban hanata dawowa ba inna kawai cewa tayi zata Jira sai Yan uwanta sunzo kafin ta dawo, zasuzo next week shine Umma tace a barta ta huta tana can gidan Ammi ” “toh..dafatan ka mata kayan fadar kishiya” “kudi ta bukata Kuma na Bata duk yadda take so, yanzu wanna ce zan Baki kudi a hado mata lefe” ya fada Yana kallon Hajjo, inna tace ” wane irin lefe Kuma bayan ga wancan na Aman yace ya yafe ”

“Aman kika ce koh inna, wannan Kuma Ayman ne ” shiru inna tayi daga bisani tace” toh ai gata nan sai ku tattauna idan tace tana so ai shikenan sai kuje ku Siya ni karka hadani da Wani aikin” murmushi yayi dai dai nan suka kawo bakin entrance din gidan, ya juya ya kalleta yace” ki koma ciki Baki da hijabi bana son ki fito haka ” sallama ta yuwa inna ta koma cikin gida.

A bakin mota ya tsaya bayan ya Bude mata tare da mata godiya Fauzan ne dama ya daukota shi zai maidata gida ya rufe mata kofa Yana d’aga hannu kafin ya koma ciki , falonta ya nufa tana zaune ya shigo ya zauna dab da ita sunkuyar da Kai tayi cikin siririyar murya tace ” Ina kwana Yaya ”
“Waye yayan naki, nifa yanzu na wuce wannan matsayin ” peck ya manna mata a kumatu yace ” Good morning my love, haka zakimin every morning am no longer your Yaya ” wasa take ta yatsun hannayenta ya d’aga habarta suna kallon juna yace ” kinsan me..ni bana son wannan kunyan please feel free with me am ur husband after all not your in-law ” murmushi tayi ya lakuto hancinta Yana dariya yace ” mijin naki baya wasa da yunwa yanzu, ki taimaka ki sama masa abinda zai saka a Baki ”
tashi tayi ta Bude kulolin da inna ta kawo farfesun kayan ciki ne sai kosai da Kuma bread Wanda aka soya da kwai , ta shirya komai ta ajiye sannan ta wuce kitchen ta hada ruwan zafi a boiler bayan few minutes ta juye cikin tea flask ta dauki plates ta shirya bisa tray ta koma part nata dashi, ta ajiye Yana mata sannu ta sake komawa ta dauki kayan tea da cups ta dawo ta ajiye, ita ta zuba masa komai ta ajiye agabansa ya b’ata rai yace ” gaskiya ni sai dai ki bani a Baki ”
Marairaicewa tayi ” don Allah Yaya kayi hakuri u feed urself ”
“Um..um bazan iya ba bahaka matata take min ba gaskiya ni a Baki ta Saba bani ”
hada rai tayi tare da kauda fuska gefe tace ” toh kayi hakuri ka kirata tazo ta baka ” murmushi yayi ya dauki waya Yana dannawa can ya Kara a kunne Yana kashe murya
“Hello baby nah..kina ganin amaryata taki bani abinci a Baki koh..”
Hajjo tashi tayi ta shige bedroom nata kwanciya tayi bisa gado tana Jin Wani irin radadin cikin zuciyarta, batasan lokacin da hawaye ya fito mata ba tana gogewa dama wannan shiyasa mata suke gudun kishiya, tabbas kishiya Babu dadi Niko nace hajjo wasa farin girki tun baa fara komai ba kenan.
A hankali ya turo kofa ya shigo fuskarsa dauke da murmushi ya karasa bakin gadon ya zauna tayi saurin juya masa baya, zagayowa yayi ya dawo gabanta hannu ya Mika mata ” taho Qalbee nah duk duniya bani da wacce nake so Kuma nake kauna sama dake am sorry wallahi wasa nake Miki, ni waye nake dashi da zan kira baby bayan gakinan a gabana taho my baby ” kulle Ido tayi Kai Ayman shu’umi ne zai jefa zuciyarta cikin rudani ya iya lafazi da tattalin mace , goshinsa taji bisa nata goshin suna gugan juna ya furta
“Tashi muje I’ll feed you my Qalbee sorry ok ”
runtse Ido tayi tanajin duk ilahirin jikinta Yana mutuwa tamkar wacce aka tsoma cikin kankara , kissing nata ya farayi Babu space Bai Bata daman ta numfasa ba Wani salon kiss ne Wanda batasan Yana existing ba a duniya, gaba d’aya ta fita hayyacinta har ta Bada Kai tana Maida masa martani Ayman ya fara fita hayyacinsa yayi sauri tashi daga jikinta tamkar Wanda ya tuna Wani abu ya juya gefe Yana sauke numfashi. Kunya ya gama lullube hajjo saboda ya saceta ya mata bazata Bata taba tunanin zata Bada Kai a saukake haka ba donhaka ta kasa hada Ido dashi, hannunta ya rike Yana fitar da numfashi a hankali” let’s go n eat ” tashi tayi suka koma falon, a kasa suka zauna suna ci a hankali Babu Wanda ya sake magana cikinsu kowanne da tunanin da yake cikin zuciya.

Bayan sun gama yace mata zaije ya shirya zai fita Yana da aiki a company daga haka ya wuce part nasa , huduban anty Balqis ta tuna na cewa ta taimakawa mijinta ya shirya idan zai fita aiki Hakan na Kara shakuwa da soyayya Amma gaskiya she can’t yanzu Gani take ya gama da ita bare Kuma tace zata biyosa zuwa part nasa ai zai dauka she needs him more ne , kwanciya tayi tana kallon pop din falon gaba d’aya ya saukar mata da kasala dakyar ta tashi ta tattara kwanukan takai kitchen ta dawo ta kwanta tana tuna moment dinsu na dazu.

Back to top button