Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 50

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*50*

Anty Dada tare da sauran matan sun samu tarba Mai kyau abin ya matukar burgesu sosai ana Raha da dariya tamkar sunsan juna aka Bude akwatuna nan anty luba ta fara guda sauran mata suka tayata kowa na Sanya albarka tare da musu fatan alheri har aka gama nunawa, sunyi sallama zasu tafi nan aka rakasu da tukuici Mai tsoka tare da kayan ciye ciye da aka tanada musu da drinks aka rakasu dashi har mota sukayi sallama suna godiya, cikin gida kuwa ana zuba santin wannan uban dukiya da aka kawo ana ta musu adua. Haka dai aka fara Shirin biki tirya tiryan inna Babu zama sai shiga da fita Ake yau kasuwa gobe nan jibi can tare da anty Balqis da anty luba , Baban Hajjo ya siyar da shanayensa ya aikawa inna kudi yace a Siya duk abubuwan da suka dace Wanda akewa Yan gata a siyawa tilon y’ar tasa, Aman ango sai rawan Kai yake tamkar yanzu ne zaiyi auren fari ko bin takan matarsa bayayi tana can tana haukar ta yaki kulata sai gayyatan mutane yake Ammi kuwa kamar yadda ta fada ta zame hannunta daga lamarin bikin Babu Wanda ta gayyato amma fulani ta taso daga Sudan tazo saboda matsalolin gidan y’ar uwar tata, dangin mahaifin Aman kuwa sai zuwa suke kamar da gayya saboda Ammi ko magana batayi yanzu.

Saura kwana 3 daurin aure kowane bangaren baqi sun fara hallara Failuzaa tana tare da Zee da wasu kawayen nata suna Kara zugata akan irin abubuwan da zatayi bayan auren , wata kawarta tace ” amma dai zamuje programs nata koh ” ” chabdi…uban me zamuje muyi , so kike ta raina mana wayo” Failuzaa ta fada a harzuke , zee tayi murmushi me ciwo tace ” ni gaba d’aya kaina ya kulle brain dina ya daina aiki please someone should cheer me up”
“Wallahi tausayi kike bani sis Ina Jin abin har cikin raina na tsani kishiya a rayuwata duk da cewa gidan sarauta na taso gidan kishiyoyi amma I hate it wallahi ” Failuzaa ce ke magana wayar ta ya fara ringing ganin Ayman ne yasa ta tashi ta koma gefe

“Hello Qalbee ”
“Kina Ina yanzu ?”
“Ina gidan Aman wai har Kun sauka kenan welcome gani nan zuwa yanzu ”
“No..kiyi zamanki kawai zan wuce wajen Umma mugaisa ” diff..ya kashe wayar, murmushi tayi tana kankame tamkar shi take gani tanajin sonsa na Kara shiga cikin jijiyoyinta .
Fauzan na driving suna tafiya a hankali sun gama waya da Aman kenan yace yakai wasu abokansa guest house yanzu zai dawo, hanyar gidan inna suka kama bisa umarnin Ayman Yana son ya mata kallon karshe da Baiyi niyyan zuwa yau ba sai Kuma zuciyarsa ya tsananta da begen son ganinta shiyasa ya Siya ticket yazo, sun shigo estate din kenan sunzo kusa da gidan suna Neman wajen parking saboda motocin dake wajen kamar daga sama ya hangota sanye da jalbab light pink ya matukar haska fatarta tayi kyau matuka tana waya sai faman murmusawa take , parking Fauzan yayi ya fito Yana tunkarar inda take a yayinda Fauzan ya tafi neman wajen parking Mai kyau don Yana kan hanya.
Sallama yayi ta juya suka hada Ido ta kashe wayar ta amsa cikin Sakin fuska da Bai taba ganin irinsa ba ” Ina wuni Yaya ”
“Amarya baki laifi ”
rufe fuska tayi da tafin hannu haka ya kura mata Ido Babu ko keftawa cike da Jin kunya tace ” don Allah Yaya ka bari ”
gyara tsayuwa yayi bugun zuciyarsa na karuwa Yana son ya tona sirrin dake cikin zuciyarsa amma ya kasa , kura mata Ido yayi ya kasa magana ta d’aga Kai idanunta suka fada cikin nasa a karo na biyu Wani faduwar gaba ne yazo mata ba shiri ta juya ta shige cikin gida dama Mai lalle tana can tana Jira Kuma yaune za’ayi Fulani day.
Ayman ya juya ya fara tafiya Kansa na tsarawa Fauzan ya karaso inda yake nan ya nuna masa hanyar mota Yana shiga yaja mota suka fara tafiya, sunkuyar da Kai yayi Yana Jin Wani radadin cikin zuciyarsa a zahiri kuwa idanunsa ne ska canza launi sun kada sunyi ja , Fauzan ya dan saci kallonsa Yana son yayi magana amma baisan me zai ce ba don sanyaya zuciyar uban gidan nasa maimakon gidan Ammi Kai tsaye suka wuce gidansa dake Asokoro saboda ganin baya cikin hayyacinsa.
Suna zuwa gida kuwa ya kwanta kamar da wasa zazzabi ya rufesa Fauzan ya fito ya Nemo masa magani ya kawo gashi matarsa Bata gida yaso kiranta ta dawo Ayman ya hana dole su biyu kadai suka zauna kowanne da abunda yake tunani cikin zuciyarsa,

Hajjo Bata gama lalle ba sai 4pm gaba d’aya ranta a bace yake gashi 5 yakamata a fara Fulani day mutane har sun fara hallara an gama shirya wajen da zatayi event Amma lalle Bai bushe ba, 5 nayi dole kawayenta suka tafi da Yan uwa aka fara taro Babu amarya an kunna fanka saboda zanen ya bushe gaba d’aya taji event din ya fita kanta Batason zuwa, Aman ya kira wayarta har ya gaji Bata picking sai wajen 6 ta wanke lallen ta shiga wanka ta fito dama Bata sallah ta shirya cikin kayan Fulani amma gaba d’aya tana Jin zuciyarta Babu dadi dole anty Balqis ta tisata gaba sukaje wajen event din inda Tasha ruwan kudi ango da abokansa da dangi sun nuna mata kauna ita dai hajjo tana Jin zuciyarta Babu dadi ta rasa dalili, sai wajen 9 aka gama program din suka koma gida. Washegari da yamma akayi walima a wannan lokacin dangin Babanta suka iso saboda gobe ne daurin aure wasu Kuma suna can Kano zasu bi motocin daurin aure sutaho, Ayman dai Yana kwance har Ammi da fulani sukaje suka duba jikin nasa.

Ranar daurin aure aka shirya motocin da zasu tafi Kano saboda kwaso Yan biki ango da tawagarsa kuwa jirgi zasubi Ayman da karfin Hali ya tashi duk da baya Jin dadin jikin nasa amma haka ya daure yace zai halarci daurin auren Fauzan na kusa dashi saboda yanayin jikin nasa, cikin jirgin Aman sai raha yake da abokasa bini bini yakan juya ya Kalli Ayman su sakarwa juna murmushi har suka iso Kano ta dabo tumbin giwa karfe 11am daurin auren, sun karasa cikin convoy zuwa gidan bappa dake unguwar Rimi nan aka fara Shirin daurin aure aka gabatar da Dady a matsayin waliyin ango Yaya Yusuf Kuma shine waliyin amarya an ajiye sadaki 500k nan aka ambaci sunan amarya Aisha (Hajjo ) Suleiman tare da angonta Muhammad Ayman bin Sultan Abdoo , Fauzan yayi sujada Yana hamdala a yayinda Ayman yayi mutuwar zaune shin kodai kunnensa Baiji da kyau bane kamar sunansa aka ambato kodai mafarkin aurenta yake shiyasa yaji tamkar sunansa aka kira , Aman ne ya dawo dashi daga tunanin da yake ta hanyar Mika masa hannu ” congratulations man Allah ya Sanya alheri ya Baku zaman lafiya Kai Kafi cancanta da ka mallaketa am happy for you” Ayman ya d’aga Ido Yana kallonsa wani hawayene a idanun Aman Yana kokarin boyewa Ayman ya rungumesa hawaye Wani na bin Wani shin ba mafarki yake ba kuwa , kallonsu ake abokan Aman suka fara tambayan meke faruwa sai dai Aman ya murmusa Amma ya kasa magana cikin zuciyarsa Wani radadi yakeji ko a mafarki Bai taba tunanin zai rasa hajjo ba Amma Babu yanda ya iya dama ance matar mutum kabarinsa.

Back to top button