Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 48

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*48*

*Team Ayman kuyi hakuri karku dakeni wannan hayaniya tayi yawa ku Kara hakuri a mini uzuri dai haka labarin yazo, kudai cigaba da bi a Sannu zaku Gane kan zaren nagode da soyayya love you all*

Dady yayi shiru Yana sauraron malam Sule kafin yace ” Haba malam Sule nifa tamkar dan uwa na daukeka , don Allah kayi hakuri ka cigaba da zama gashi har ansaba an shaku , auren yaran nan bazai rabamu ba hasali ma nayi farin ciki sosai da samun wannan labarin, Allah ubangiji ya Basu zaman lafiya Kai Kuma insha Allah Babu inda zakaje Muna nan tare sai dai zan canza Maka sana’a tunda yanzu ka zama suruki agareni ”
“Nagode Alaji Allah ya Kara girma amma kayi hakuri gida nake son komawa dama tun farko na fada Maka dalilin zuwana wannan garin yanzu Kuma gaba d’aya garin ya fita kaina , dama Ina da niyyan ajiye wannan aikin na koma gida na cigaba da noma ”
“Shikenan malam Sule ni bazan tursasa Maka ba Allah ya mana zabi Mafi alheri” Ameen ya rabbi nagode Allah ya Bada Ladan abubuwan da ka mini a rayuwa tabbas bazan manta dakai ba “.

Bayan fitarsa Dad ya tashi yaje ya zayyanawa Ammi komai ta tashi tsaye tace” wat…dama y’ar malam Sule ne toh Alhamdulillah dama tun farko ba son auren nake ba yanzu Kuma ga Wani babban dalilin da na samu, Kai a tunaninka zan yarda Aman ya auri y’ar direban ubansa” ran Dad ya baci sosai yace ” ke wace irin mutum ce Amina, na dauka zakifi kowa farin ciki da wannan labarin saboda halayen Sule nagari na manta cewa ke din kin tsani talaka a rayuwar ki shin ko kin manta Allah ne ya halicci maikudi Kuma shiya halicci talaka ba don baya qaunarsa ba sai….”
“dakata ni ba wa’azi zakamin ba , Aman d’ana ne ni na dauki cikinsa har na wata Tara Babu Wanda ya taba tayani donhaka Babu Wanda ya Isa…” Ke…! ya daka mata tsawa ” ya Isa haka nan Amina ya isheki nagaji da wannan halayen naki, kullum magana d’aya nagaji Ina son ki tattara yanzu kibar min gidana yanzun nan na Baki 10 minutes” ya tashi fuu… Ya fice daga gidan, don tsabar kaduwa ko motsi Mai kyau ta kasayi a wannan lokacin yau ita Ake cewa ta fita tabar gidanta, auren shekara 40 shine yau zai koreta saboda wata fakirar yarinyar tabbas a duniya Bata da makiyi irin wannan yarinyar wutar tsanar yarinyar ne yake dada ruruwa cikin zuciyarta , daga ita sai handbag nata me dauke da ATM da wayoyinta sai car keys ta fice Kai tsaye wajen parking lot ta Bude motar ta tana shiga Dad Yana isowa ya Mika mata hannu ” bani makullin motata ai Bada shi kika zo gidan nan ba ”
Bude Baki tayi tana kallonsa ya hada rai
“Bani makullin” Wani kuka ne yazo mata ta fashe da kuka
“Yau ni zaka wulakanta saboda wata fakirar yarinyar Alaji, tabbas yau na gaskata cewa namiji ba dan goyo bane , duk irin zaman da mukayi baka Duba ba zaka koreni ka wulakanta ni”
“Ke Baki Duba zaman namu ba kika kafe akan bakan ki, toh Ina son ki sani ni Dan talakawa ne gaba da baya Allah ne ya d’agani a lokaci guda nayi arziki har kika yarda kika aureni, na tabbata da Ina matsayin talaka ko kallo ban isheki ba Amina donhaka zabi ya rage naki ko ki zauna ayi bikin Aman ko ki tafi ayi bikinsa saboda Allah ya riga ya kaddara sai anyi wannan auren Babu fashi sai dai ko Wani iKon Allah daban ” ficewa tayi daga cikin mota ta nufi gate maigadi da malam sule suna mata kallon mamaki Kai tsaye ta Bude kofa ba tare da ta kula kowa ba, jikin malam Sule yayi sanyi ya gano kan zaren lallai ma ya zama dole ya gaggauta barin gidan don bayason ya zama silar tarwatsa farin cikinsu.

Aman na rike da waya Yana safa da marwa cikin office nasa yanzu ya gama call da zee ta shaida masa Ammi na gidansa tayi yaji, shiya rasa meke damun Ammin nasu tana Abu tamkar karamar yarinya Kuma ya rasa waye zai kira yakai masa kukansa ga auren na gabatowa Babu Shirin da ya fara gudana , Ayman ne ya fado masa a rai Allah sarki dan uwa rabin jiki yasan shi kadai zai iya tunkarar Ammi ya shawo kanta saboda Allah ya masa baiwar iya lafazi nan kuwa ya fara Neman layinsa na saudiya Bai d’aga ba sai ya tuna da d’ayan layin sai Kuma ya fasa kira ya koma Whatsapp call, zama yayi bisa kujera ya danna video call bayan Wani lokaci Ayman ya dauka suka gaisa ” Kai bro gaskiya Anya bazan biyoka Jeddah ba , kaga Wani fresh kake ka Kara kiba wato hankalinka a kwance ka barni nan Ina fama da tension”
Murmushin nan nasa na kasaita yayi kafin yace ” u are welcome duk lokacin da ka shirya dawowa ” toh shikenan sai bayan biki ka min booking 5 star hotel zamu zo honey moon dani da sweedie ” lumshe Ido yayi ” ok , ni yanzu ka bani list din abubuwan da kake bukata na lefe I’ll handle it ” ware Ido Aman yayi “really… My billionaire bro bana son dora Maka dawainiya ”

” Banson rashin kunya Kai ba kanina bane ” murmushi Aman yayi ” sannu babban yaya ”
“Ehen ko ka manta ask Ammi na baka 2 years ”
” Toh 2 years Wani abu ne anyways na yarda but please ka kira Ammi ka mata magana ta daina wannan behaviours din da take please ”
” So kake ka hadani da ita koh ”
“No…kasan Kai din ne bro Allah ya Maka baiwan iya lafazi ka iya sarrafa harshe ” murmushi yayi haka suka cigaba da hira ,
hira sosai sukayi har Aman ya manta da matsalolinsa kafin sukayi sallama ya kashe waya.

Ayman ne ya kira Ammi Yana Bata hakuri akan ta amince da batun auren ta koma d’akinta taso tayi fada amma ya kwantar da murya Yana mata dad’in Baki har ya samu ya shawo kanta ta amince akan zata koma gidan mijinta amma Babu ruwanta da lamarin bikin nasu ta zame hannunta daga lamarin gidan Aman gaba d’aya, haka dai tayi ta masifa Yana Bata hakuri. Kawayenta ta kira ta sanar dasu halinda Ake ciki kafin kace me gidan Aman ya cika da kawayen Ammi sun zube a falo zee ta haye sama ta bar musu falon saboda hayaniyar tasu tayi yawa tamkar suna gidan biki, anty Balqis ce ta shigo last bayan sun gaisa taji abunda ya faru murmushi tayi ta kallesu d’aya bayan d’aya tace ” yarinyar da Baki son Aman ya aura y’ata ce jinina ce Amina ”
“Waat… Me kike nufi kina da wasu y’ayan dama bayan su Samira ?” Wata daga cikinsu ta tambaya ”
“Y’ar kanwata ce uwarmu d’aya ubanmu d’aya da mahaifiyarta Kinga kenan y’ata ce, idan kina ganin ubanta talaka ne toh uwarta Bata gaji tsiya ba kinfi kowa sanin Koni wacece Amina , idan kina tinkaho da mulki ko arziki toh Babu abunda zaki nunawa yarinyar nan Amma kin dauki karar tsana kin dora mata I don’t know why ” kallon kallon suke kowacce tana raba Ido , Ammi jikinta yayi sanyi ta kasa furta komai ganin haka yasa anty Balqis ta dauki handbag nata tace ” toh nidai na barku lafiya Ina da abubuwan da zanyi dayawa Muna can Muna shirye shiryen bikin Allah bamu alheri ”
daga haka ta juya tayi tafiyarta, falon yayi tsit tamkar an kulle musu Baki Ammi sai kada kafafu take tana ta tunane tunanenta cikin zuciya daga karshe ta Yanke hukuncin komawa gidan Dady ayi bikin da ita tunda Babu fashi ta tabbata ko Bata gidan sai anyi idan yaso bayan bikin sai daga baya ta nemi mafita.

Back to top button