Aci Yau Aci Gobe Hausa NovelHausa Novels

Aci Yau Aci Gobe 17-18

Sponsored Links

17 & 18
Tunda yake a rayuwarsa yau ne rana ta farko daya taɓa riƙa 35k nasa nakansa,saida shagon mai sayar da kanyan fruit da kayan miya ya tsaya saida ya kashe 2500 a gurin harda su Nama saida ya siyawa yan gida

Dacewar sa kowama yaci daɗi tunda shima yaji dadi

Aekuwa Luba nata murna da jin daɗi ganin Audu ya fara sanin ciwon kansa baida aeki sai zaman ɗaki yanzu kuma ansamu cigaba yana fita nemo.

Ranar dai anci mai daɗi kuma ansha mai daɗi gidan Tukur,luba sai wasar baki akeyi

Domin Tukur kalar mazan nan ne wadan da basu iya siyawa gida kayan saidai su susiya a waje suci

~~~~~~~~08143322386~~~~~~~~~~~~~~~~

Bintalo tunda taje gidansu Raihana sukasha fira ta fahimci abu buwa da dama game da Raihana

Kamar Raihana na buye mata wani abu kamar kuma tana cikin damuwa,haka ta manta gaba ɗaya dacewa Lantana tace taje ta dauko ƙannanta.

Saida tayi sallar magrif kafi tayiwa Hafsa sallama dacewa zataje gida

Gaba ɗaya abunda sukeyi da firarda sukeyi Aliyu najinsu kuma sosai abun ya ɓata masa rai wanene wannan Audu ɗin zaici ubansa

Idan yashigo hannunsa zaisa sasa a jail saiya gaya masa dalilinda yasa yake latsa Fateema

Bakin ƙwarido yaja ya tsaya yana jiran fitowarta duk inda ranshi yakai ga ɓaci ya ɓace gaba ɗaya yaji maganar ta dagula masa lissafi

Hafsa ta rakota har bakin ƙwarido tace mata saida safe ita kuma ta juya takoma cikin gida,

Yana ganin lokacin da Raihana ta juya ta koma ciki shikuma ya kashe light din gidan baki ɗaya

Ita kuma taringa tashigo ƙwaridon wata ƙara tasaki wayooooo Allahnah bata karasa rufe makiba taki an fizgo ta ta faɗa jikin mutun

Aekuwa ta ƙara tsurewa tashigs mutsumutsu gashi yasa hannunsa ya rufe mata baki

Jin hawayenta sun fara sauka a hannunsa yasa yace ki nutsu kinji Aliyu Magana zanyi dake kuma ki buɗe kunnuwanki kijini da kyau kuma kiji abunda zan gaya miki

Waye Audu kuma yakuke dashi,shiru tayi masa gashi yariga ya bude mata baki jintaƙi cewa komi yasa yadaka mata tsarwarda tasata gigicewa hade dacewa wayooooo Allahnah nashiga Uku.

Dan uwanki ne kowaye shi a gunki,Fateema akwai taurin kan tsiya still tayi shiru taƙi yimasa magana duk inda Aliyu ke kaiwa ya kai

Kyawawan maruka ya sauke mata jere da jiuna hade dacewa Dan Ubanki badake bake magana bahwata ƙara tasaki yaji karar har cikin ƙashin zuciyarsa

Fizgo ta yayi ta faɗo jikinsa ya mata wata muguwar matsa tare dacewa why Fateema miyasa miyasa zaki yimin haka miyasa zaki bada jikinki miyasa baki gayawa kowaba miyasa kikayi shiru

Fateema️ya faɗi cikin muryar lallashi saboda yaga bata tsoron tsawar kuma bazata gaya masaba idan ba lallashinta yayiba

I just wanna ask you plz tell me the truth I abeg you,kiji tsoron Allah ki gaya min gaskiya bayan romancing dinki dayayi yayi amfani dake

Bintalo taji tambayar kamar saukar Aradu a kanta,shiru tayi ya kara maimaita mata tambayar
Ta noƙe kanta ƙasa tashiga girgirza masa kai tana zamewa daga jikinsa a hankali harta raba jikinsa da nata

Ƙara fizgo hannunta yayi tare da bude motarsa dake fake a bakin gate ya jefata yasa lock yakoma yashiga yaja motar idonsa sun ƙaɗa sunyi jajjajir kamar wuta sai huci yake

Kamar wani zaki, jan motar yake da matsiyacin gudu kamar wanda zai tashi sama,gaba ɗaya jinsa yake cikin ƙunci

Gaba ɗaya Bintalo a tsorace take, jikinta kawai ke rawa yana karkarwa,sosai yake gudu da ita ya dauki hanyar fita garin Kano harya wuce BUK NEWSIDE

Kafin taji yaja burki ƙuuuuuuuuu ihuuuuu tasaki tayo gaba kaɗan ya rage forehead dinta ya daki gaban motar da sauri ya kara hannunsa goshin ya daki hannunsa

Wata Uwar ajiyar zuciya ta sauke murya na raga tafara Magana Dan Allah hamma Ali kayi haƙuri wallahi bazan ƙara making mistake ba Dan Allah ka mayar dani gida,idan Abba yadawo baiganni a gidaba zaidake ni, duk Maganar da takeyi tana yine tana jan majina.

Kinaso ki koma gida? Da sauri tashiga ɗaga masa kanta kamar lizard okay share hawayen ki yanzu nan aekuwa ta rarumo Hijab dinta zata goge ta sauri ya riƙe tare da miƙa mata tishu saida ta goge fuskarta gaba ɗaya

Kafin yace A You ready to tell me the truth? Ehhh tafaɗa da sauri okay waye Audu nan tashiga basa labari bata boye masa komiba

Har ruwanda yabata a kwalba tasha tun lokacin bata ƙara sanin mitakeyi ba kawai taji yanayin jikinta ya canza

Ya isa yafaɗa da karfi yana dukan sitiyarin motarsa,jikinta yashiga rawa yana ƙyarma kamar ace Arr ta ruga a guje.

Okay da hakan yafaru wakika gayawa, “bakowa” miyasa baki gayawa kowaba miyasa kikayi shiru

You means kinji daɗin abunda yayi miki kenan,shiru tayi masa tana kuka ƙara ƙasa

Bakuka nace kiyimin ba, dago idonki ki kalle ni tana ɗagowa yace “Zahra kinason aure ne” idan aure kikeso kigayamin zangayawa Abbanku kuma nizan aureki”

Ƙasa tayi da kanta batace masa komiba ajiyar zuciya ya sauke

Ya tayar da mota yana magana a hankali “if you need anything just tell me”kinji koki gayawa Raihana zata gayamin kinji Okay ta faɗa lips dinta kawai yaga sun motsa amma kwata kwata baiji Muryar ta ba

Murmushi yayi yana shafa zajensa, soyayi ya mayar da ita gidansu amma saiya canza shawara ya mayar da ita gida suna isa ƙofar gidan dai-dai ana fitowa daga masallaci angama sallar “Isha” nashiga uku tafada azuciyar ashe maganar tafito fili

Lafiya Fateema a ɗimauce tace Hamma Abba yadawo

Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa ina Abban yake nunamin shi yafada yana tsareta da dara daran idanunsa hannunta na rawa ta nuna masa shi,yana tsare gefen masallaci suna magana da wani mutun

Aedama Abba nakeso yaganmu nidake da sauri tashiga girgirza masa kai tana A’a Hamma Aliyu wallahi Abba zai iya yankani

Aekuwa ya ƙara hadiye rai yana cewa kina tsoronsa kika shiga ɗakin Audu harya baki ruwa kikasha ya latsar miki nono da sauri ta noƙe kanta ƙasa

Magana nake kinyi shiru runtse idanunta tayi gamm, hannu biyu yasa ya ɗago da kanta yana kallon kyaykyawar fuskarta, zahra miyasa yaki yimin haka kin kuwa san burinda naci akanki

Fuskar sa yakawo daidai tata fuskar yana sunsunarta, gaba ɗaya tsoro ya gama kamata gabanta kawai ke faɗuwa

Lips dinsa ya ɗora a han yana kafin a hankali ya fara shan lips din cike da mugunta yake jan lips din yana tsotsarsu kamar yanashan nono

ƙanƙamesa tayi tana rige masa gefe da gefen riga tana ƙoƙarin ƙwace labɓanta dataji sun fara yimata wani sululi da azabar zafi

Samm Aliyu bada niyar yaji daɗi yafara sha mata lips ba saboda ya hukunta ta yayi hakan amma daya fara tsotsa sai yaji bazai iya denawa bah Wannan shine first kiss daya taɓa yiwa mace da sauri ya saki lips din

Tana ƙoƙarin buɗe ƙofa tafita ya riƙota tare dacewa am sorry plz yana dafe goshinsa, shiya fara fita ya zagaya domin buɗe mata ƙofa amma gaba ɗaya sai yaga hankali su Tukur da Tanimu mahaifinta da sauran magidanta suna akan motar

Dumm yaji gabansa ya yanke ya fadi ganin sutaso gaba ɗayansu sun nufosa gadan gadan sai watsar haƙori suke, Tukur ya fara magana yana cewa wanake gani Kamar Doctor Aliyu Haidar Allah sarki ashe kuna sane da unguwarmu dama san cewa zaku kawo mana taimaka kamar yadda kuka saba bisimilla ƙaraso mana ga masallaci

Okay ya faɗa yana sosa ƙeyarsa (kansa) nan take Tanimu ya fahimci akwai wani abu a ƙasa da sauri yace Aa malam Tukur kabari mana muji ta bakinsa kasani koba aekinda ya kawosa kenan bah

Sosai wannan maganar tayiwa Aliyu daɗi da sauri yace Ehhh Abba dama inason magana dakai ne da sauri Tanimu yace ni kuma, Ehhh Abba kai kosamu dan keɓe idan ba damuwa, to shikenan babu komi Wallahi

Gefe suka koma saida ya ƙara gaishesa kafin yashiga gaya masa duk abunda Bintalo ta gaya masa baiɓoyewa Malam Tanimu komi ba kuma

Hmmmm Aliyu ka tabba Fateema ce tagaya maka waɗannan maganganu Ehh Abba to shikenan aekuwa zatagane kurenta kuma zata haɗu da fushina da bata taɓa fuskanta ba

Da sauri yace Abba Dan Allah kayi hakuri ban gaya maka dan ka daketaba kokayi fushi da ita Abba nagaya makane saboda ka ƙara tsananta kulawa akanta

Kuma Abba Dan Allah ina neman wata alfarma guda ɗaya daga gunka…..Abba inason kabani auren Fateema Aliyu aure fah kace Fateema zaka aura Aliyu kasan mutun nawa Fateema ta bawa jikinta ko Kanada tabbacin cewa Audu kawai ne samarinta

Aliyu kaiba ɗana bane amma bazan yimaka ƙwaɗayin auren mata kalar fateema bah,Abba Dan girman Allah ka dena fatar waɗan nan kalaman akanta kuma ni inason Fateema kuma tun bayau ba nakesonta, Hmmmm naji Aliyu na baka Fateema tazama matarka ko bayan raina

Amma abu ɗaya nakeso na gaya maka wallahi wallahi wallahi saina ɓata mata rai kamar yadda tayi ƙoƙarin ɓatamin suna a idon duniya

Ina Fateema din take jikin Aliyu na rawa yace tashiga gida Abba tun ɗazu Okay toh, Ngd maka Allah ya tsare hanya kaji

Kagaishe da mahaifinka baitsaya jin abunda Aliyu zai faɗaba yashiga gida fuuuuuuuu rigarsa nabin iska…………

*Maman Ekram ce*✍

*ACIYAUACIGOBE*

Back to top button