Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 49

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*49*

Baban Hajjo yayi sallama da Dady cikin mutunci Daddy ya basa kudade masu yawa Kai tsaye Kano ya wuce gidan dan uwansa a can Kano za’a daura auren, Aman ango ganin Ammi Bata sake d’aga magana yasa ya fara Shirin biki gadan gadan don saura sati 3 ya samu Wani gida a wuse zone 5 a can Hajjo zata sauna.

Hajjo sun iso Maiduguri lafiya tare da anty Balqis suka tafi bayan sunhuta nan aka fara mata gyaran jiki Babu b’ata lokaci da halawa aka fara mata kamar ta kurma ihu saboda zafin da yake mata, idan aka gama a shafa dilka me hade da kurkum da turaruka masu kama jiki, from day one ta fara ganin canji tattare da jikin nata. da dare aka dafa mata kaza dahuwar Amare ga tsumi da gumba kamar tayi kuka yadda ake dura mata abubuwa, Bata samu kanta ba sai 11pm a bangaren yakumbo take ta gama Shirin bacci kenan mutumin nata ya kira, “Aman darling ya kake ”
“am not fine am cos missing you dearly ”
“Allah sarki nawa Nima haka but it’s a matter of few days insha Allah ”
“Allah ya nuna mana wallahi sai counting days nake iswear ” “uhmm …su darling Ango ” dariya yayi harda kyakyatawa haka suka cigaba da hira har 12 kafin suka rabu kamar zasu hadiye juna.
Washegari aka cigaba da mata gyaran jiki sai zuwa yamma anty Balqis tace ” ki shirya zamuje kauye wajen Wani kakanki ” hajjo ta amsa mata haka suka shirya suka dauki driver da motar Hilux suka tafi Wani kauye can wajen dambua amma cikin daji ne, kofar Wani gida ginin gargajiya driver yayi parking suka fito anty Balqis na gaba hajjo dake sanye da jalbab brown color tana biye da ita a baya, can cikin gidan aka musu kyakkyawan tarba da ruwan randa kafin aka jera musu abinci dasu kunun gyada anty Balqis tace ” kawu Bakura Yana nan kuwa ”
” Yana ciki ai yasan da zuwan naku ku Isa ”
Nan suka wuce Wani part na cikin gidan Wani bukka ne me karamin kofa Wanda sai ka sunkuya kafin ka shiga , suka shiga da sallama Yana zaune bisa abin sallah Yana Rike da Wani qaton carbi dattijo ne me tarin gemu ba fari bane Yana da dan haske amma ba sosai ba, ya amsa suka zauna bayan sun gaisa anty Balqis tace ” yakumbo tace a gaisheka sosai ”
“Masha Allah dafatan tana lafiya ya Mai martaba da jikin nasa ”
“Alhamdulillah.. da sauki sosai duk suna gaisheku ” toh Alhamdulillah wannan itace y’ar wajen Aminatu ” ehh itace kawu ” murmushi yayi Yana kallon Hajjo ta sunkuyar da Kai kasa ya Kalli anty Balqis yace ” jeki cikin gida ki karbo min kwarya da na bama yakaka ta ajiye ” tashi tayi ta fice daga d’akin, ” Aishatu baiwar Allah, rayuwar ki na dauke da abubuwa dayawa akwai sauran gwagwarmaya a rayuwarki amma idan kika jajirce kika daure zaki ga ya wuce kamar baayi ba, ke dai ki zauna da kowa da zuciya d’aya karki cutar da kowa zaki ga haske cikin lamiran rayuwar ki, ki yarda da kaddara a duk yadda tazo Miki , adua da hakuri da juriya shine zai magance Miki matsalolin da zaki fuskanta nan gaba, akwai taurari biyu cikin rayuwarki na fili da na boye suna bibiyar rayuwar ki, na boyen zai rinjayi na filin amma Wani duhu zai tare haskensa Wanda hakuri da adua ne zai Kara fito da hasken nasa amma sai kin daure , shine yafi dacewa da rayuwar ki kinsan wasu lokutan abubuwan da mukafi so zai zamana ba alheri bane agaremu amma sai Kiga munfi Maida hankali akansa toh haka rayuwar duniya take , idan ka rike Allah ka Mika masa dukkan lamuranka sai kaga Yana tsara Maka komai yadda ya dace, kedai a Koda yaushe ki roki zabin Allah kibar komai a hannun ubangiji zakiga rayuwar ki na tafiya dai dai, karki cuci kowa gara a cuceki akan ki cuci Wani Ina Miki fatan alheri Allah ya Miki zabi Mafi alheri Allah ya mana Mai kyau ”
“Ameen ” ta amsa cikin sanyin murya don ita ko za’a kasheta Bata fahimci me tsohon yake nufi ba , tana nanata kalaman nasa amma ta kasa gane komai har anty Balqis ta shigo rike da wata kwarya sabuwa ta ajiye a gabansa, Wani rubutu ya dauko cikin galon ya zuba cikin kwaryar ya dauko Wani garin magani ya zuba ciki

“Karbi wannan kiyi Bismillah ki shanye duk da cewa Baku sanar dani zuwan naku da wuri ba, da na shirya mata abubuwa da dama saboda akwai kalubale nan gaba sosai sai adua ku tayata da adua ku karfafa mata guiwa zabin Allah shine yafi dacewa a kullum ”
“Meya faru kawu.. akwai Wani abu ne ”
“Toh Balqisu ai baza’a a rasa ba kedai kuyi abunda nace Allah yasa mu dace ” “Ameen ” ta amsa jikinta yayi sanyi domin tasan Halin kawun nasu haka yake komai sai dai ya gaya Maka a dunkule, hajjo tana Bata rai haka ta shanye ya sake kwaba Wani da Zuma ya Bata ta shanye ya hado mata Wanda zasu tafi gida dashi na wanka da na shafawa, anty Balqis tana zuba godiya tare da ajiye masa alheri Mai yawa dakyar ya karba sukayi sallama bayan an sauke musu tsarabar kayan abinci da aka kawo musu.

Sati guda sukayi a Maiduguri ana gyara hajjo ciki da waje ta murje ta canza ta Kara kyau na fitan hankali, ita kanta idan ta Kalli mirror sai dai tayi murmushi lallai Aman zai rikice mata duk ranar da ta koma Abuja, qamshi kuwa duk inda ta zauna ko ta wuce sai ta bar musu qamshinta donhaka ne aka hanata shiga mutane tun yanzu nan aka hado mata sauran magungunan da kawu Bakura ya bayar tayi amfani dasu suka fara Shirin komawa don biki saura 2 weeks Kuma za’a kawo lefe wannan satin dole anty Balqis ta koma a fara Shirin tarban baqi.

Kamar yadda Ayman yayi alkawarin hada lefe shiya Siya komai da kudinsa da kansa yaje Dubai ya Siya duk abubuwan da yake tunanin zasu dace da hajjo Yana Yi Yana danne zuciyarsa saboda Wani radadin rashinta da yake ji tun yanzu, Fauzan kuwa mugun tausayi uban gidan nasa ke basa akwatuna set 2 shake da kaya Babu abunda Babu da zuciya d’aya ya hado lefen ko na aurensa bazai wuce haka ba, bayan ya gama yace Fauzan ya nemawa Failuzaa ticket su wuce da kayan shi Kuma sai ana gobe daurin aure zai shigo, Fauzan tamkar yayi kuka idan ya tuna da zancen auren shikenan yanzu duk soyayyar da yakewa hajjo ya tashi a banza kenan duk dawainiya da rainon da yayi ya tafi kenan , cikin kwana biyu suka wuce Nigeria da kayan Ayman kuwa sai lokacin biki zaije. Aman yayi mamakin ganin wannan uban kaya har ya rasa bakin godiya yace a Kai kayan gidan Dady Ammi ta Gani, ana zuwa Ammi tace me nata a ciki su anty sofy ne suka Gani suna yabawa Ammi kuwa tana d’aki bakin cki na cinta wannan uban dukiya duk za’a Kaiwa wancan matsiyaciya y’ar direba har kuka sai da tayi ta kira Fulani tana shaida mata abin arzikin da Ayman yayi Fulani taji dad’i sosai tana zuba masa albarka tace haka Ake son su hada Kai , Yan uwan Dady 3 sukazo daga yola sai Kuma anty Dada wacce take Kano sai anty faty dake Abuja sune zasu Kai lefen sai anty sofy da tace zata bisu don ganin gulma kar ayi Babu ita.

Zee uwargida anbuga an raya shiru kakeji malam na suleja yace mata baza’ayi auren ba amma gashi ana ta shiri ga uban kayan da Failuzaa ta mata video ta nuna mata hankalinta ba karamin tashi yayi ba don kayane na kece raini hardasu gold da diamond cikin Yan kunnayen , ta rame ta fita hayyacinta mom nata tayi fada ta gaji ta kyaleta Ummeey kuwa sun raba gari don ko magana ta daina mata saboda itace babbar aminiyar amarya.
Tun bayan dawowarsu Maiduguri anhanata fita Kuma anhana Aman ganinta ya shiga matsala sosai kullum sai dai suyi waya ko video call Kuma kullum cikin katuwar hijab take ciki ta daina zuwa lectures Babu Halin fita inna tace sai bayan biki tunda ba Wani serious Abu Ake a school din ba, yau za’a kawo lefe gidan inna ya cika da kawayenta na cikin estate din da abokan business sai Yan uwansu biyu daga Maiduguri anty Falmata da yakoko sai anty Balqis da aminiyarta sai Kuma maman Nana da suka dawo , matan Aso biyar sukazo saboda maman Nana ta fada musu a takaice dai gida ya cika makil ana jiran isowar lefe anyi girke girke na zamani da na gargajiya abin dai sai sambarka.
Hajjo amarya tana can gidan anty luba Wanda gida uku ne kadai tsakaninsu tana tare da Humaira y’ar anty luba can Ummeey ta samesu suna tattaunawa kan program din da za’ayi na biki suna rokon hajjo da ta Kara musu programs don su cashe hajjo taki tace Fulani day ma kamawa tayi da bazatayi ba sai walima Wanda inna ta shirya za’ayi a Masallacin estate din.

Check Also
Close
Back to top button