Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 43

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*43*

Duk yadda Aman ke daukan zancen amincewar Ammi Abu yaci tura Yana kan bakarta na cewa zancen auren Babu shi donhaka yayi deciding ya kira anty Dada wacce take kanwa ce gun Dad ita kadai ce mafita don yasan Bata shiri da Ammi Kuma ita kadai zatayi tijara a tsaida magana ko anaso ko baa so saboda ya kirata a waya ya zayyana mata halinda Ake ciki tayi murna sosai bare da ta samu labarin cewa y’ar Adamawa yake so nan da nan ta fara Shirin zuwa Abuja daga Kano.
Bangaren hajjo ma the same problem ne saboda inna taki Bada goyon baya kan wannan lamarin ga masoyan kuwa soyayya sai abunda ya karu zee kuwa tamkar zatayi hauka saboda har yanzu Aman be sakko ba Babu wani shiri tsakaninsu, ranar da anty Dada ta iso kuwa da yamma ta kira Aman tace ya sameta a gida. Bayan ya taso daga aiki ya wuce gidan suna falo tare da Ammi kowacce na danna wayarta yai sallama ya nemi waje ya zauna kafin ya d’aga musu gaisuwa Ammi Bata amsa ba, tabe baki anty Dada tayi tace ” toh ke anty Amina duk wannan fushin na menene, kawai saboda yaro na Neman raya sunnar ma’aiki ”
dariya Ammi tayi harda shewa tace ” ai dama Ina ganinki nasan da biyu kika zo saboda Baki Saba kawo mana ziyara ba, wato gaki nan uwata koh ankai karata wajenki toh idan kin Isa sai ki daura masa auren mugani ni Ina dai dai da duk Wani munafuki ” tashi tsaye anty Dada tayi tace” ke Aminatu naga Baki gaji arziki ba, ke har kin Isa ki Kalli tsabar idona ki kirani munafuka toh idan Kinga baayi auren nan ba shegiya nake tunda abin naki Babu mutunci cikin lamarin ”
“aikuwa ki shirya komawa shegiyar saboda aurene Babu Wanda ya Isa … ” Wallahi ki kiyayeni dama Ina dauke da cikin ki, karki ga kina abunda kika ga dama a gidan nan ana barinki , kinyi sa’a lokacin aurensa na fari bana kasar kinyi abunda ranki ke so , idan bahaka ba ke har kin Isa ki Hana danginmu zama cikin wannan gidan… ” Toh Dada tunda gashi yanzu kinzo ai sai ki dauki mataki idan ke kika haifamin Aman don Allah na rokeki kisaka a daura aurensa gobe gobe ” Aman ya rike Kai yace ” haba mana meyasa kike haka Ammi ”
“Rufemin Baki tsohon munafuki Ina ce Kai ka gayyato ta tazo ta kwatar Maka y’anci koh , toh ai sai ka canza uwa ”
ganin abin nasu ba na karewa bane Aman ya kama hanyarsa ya fita daga cikin gida ya wuce mota don bayason tashin hankali, Yana fita yaci karo da convoy din Dady wuta kawai ya haska musu da Kuma horn ya wuce don bayajin zai dawo gidan.

A falo Dady ya samesu a hargitse masu aiki na faman Bada hakuri amma sai musayar kalamai suke ya zauna anty Dada tace ” barka da zuwa Yaya ” “Dada yaushe a garin ”
“da Rana na iso wallahi yaron nan ya fadamin abunda ke faruwa shine nace bari Nazo da kaina ”
“Kin kyauta ai gata nan nayi iya bakin kokarina ta kasa fahimta ” tamke fuska Ammi tayi tana faman Harare Harare tace ” aurene nace bana so ba sai a bar zancen ba tunda Babu wacce ta haifamin Aman ”
“Ke kika haifi kayan ki amma ubansa yafiki Iko dashi Amina aurene Kuma Babu fashi Ina nan gobe zaaje Neman auren da izinin ubangiji ”
“Zamu ga uban da zai tsaya masa kuwa ”
Dad yayi murmushi yace ” Gani nan ni ubansa ni zan tsaya masa ba Wani ba ”
“Yanzu Alhaji saboda kawai…” dakata Amina, sai dai ki zaba idan bakison d’anki ya Kara aure ni ubansa zan Kara Kuma da wannan yarinyar zan Kara donhaka zabi ya rage naki ” Yana gama magana ya tashi ya wuce sama , ragwaf ta zube bisa kujera tana son daidaita nitsuwarta tana son Gane me Dad yake nufi dama yayi amfani da wannan Kalmar ne saboda yasan weak point nata , a duniya Amina ta tsani kishiya yanzu yasan dole Bata da Wani option zata amince da wannan batu kowa ya huta.
Anty Dada ta nemi waje ta zauna tana buga shewa tsaki Ammi taja ta tashi fuu..tabar falon ta koma d’ayan falon, wayarta ta dauka kira layin Fulani ta fashe da kuka ” lafiya Ammi meke faruwa?” Yanzu duk zaman da mukayi da Alhaji sai yanzu da muka girma da jikoki shine zaici mutunci na ”
“Cin mutunci meya faru” Fulani ta tambaya cike da son Jin meya samu y’ar uwar tata.
” Aman ne zai Kara aure da na hanasa shine Alhaji yace shi zai Kara yanzu ya kyauta kenan ”
” Toh in Banda abinki Ammi ke me naki da auren Aman, meyasa kike son shiga lamarin yarane wai, yaro Yana son aure sai ki bari ya Kara ki tayasa da adua Allah yasa alheri ne Amma ki…” A’a gaskiya ni ban yarda ba saboda yarinyar nan y’ar manyan mutane ce ya zai tozartani gaban iyayenta ”
“Toh shikenan sai ki bari ubansa ya Kara ” tana gama fada ta kashe wayar cike da takaicin halayen y’ar uwar tata Wani lokaci tana da abin haushi, Ammi ta kira anty Mami ta zayyana mata komai take anty Mami ta Bata wata shawara da hankalinta ya dauka donhaka ta samu relief take ta kira zee ta sanar da ita abinda take bukatan su aiwatar ta zauna da shiri gobe zasuyi aikin.

Washegari Hajjo ta tafi school inna tana bedroom aka shaida mata tana da baq’i ta fito cikin shiga ta alfarma suna falon kasa donhaka ta sakko zuwa kasan ta samesu a zaune , kallo d’aya ta mata ta shaidata kallon kallo sukewa juna Ammi ta nunata da yatsa ” ashe dama kece dangin matsiyata, na dauka gidan wasu hamshakai ne ashe gidan sadaka yalla ya shigo, toh wallahi nazo ne na fada Miki ki jawa y’ar ki kunne ta rabu da d’ana ko na dauki mummunar mataki akanta ” murmushi inna tayi” hajiya barka da zuwa ashe dai kece, toh naji abunda kika fada amma Ina son na tunatar Dake cewa mace Bata likewa namiji sai dai namiji ya like mata donhaka shawarar da zan Baki shine ki koma ki jawa d’anki kunne kice ya rabu da y’ata saboda shiya fara cewa Yana sonta ” ” haka kika ce koh toh shikenan ki zuba Ido zaki Sha mamaki ”

“Babu abunda zangani sai alheri insha Allah ” zee tace ” wallahi idan kina son y’ar ki gara ki gaggauta rabasu don tana Shirin jefa rayuwar ta cikin fitina da bala’i ne ” murmushi inna tayi tace” I guess kece matarsa koh, Allah sarki da alama Baki rike mijin naki da kyau ba tunda har ya iya hango wata ya fara bibiya ” Ammi tayi caraf! tace ” ke dallah! Y’ar matsiyata ana Baki shawara kina biyewa son zuciya saboda kwadayin abin duniya ”
“Abin duniya Kuma? Ki Kalli gidan nan Hajiya daga sama har kasa shin Kinga munyi kama da masu bukatan abin duniya, da kike cewa matsiyata kuwa ai kece babbar matsiyaciya saboda Bakisan darajar dan Adam ba Babu abunda kika iya sai tutiya da nuna ke wata tsiya ce Wanda komai a nan gidan duniya zaki bari, shi Allah Babu ruwansa da arkizi ko kyaunka innallaha ta’ala layanzuru ila ajsamikum Wala ila siwarikum Walakin yanzuru ila qulubikum , Koda yake ba lallai kinsa fassarar ba Allah madaukakin sarki baya duba sura ko jiki face zuciya donhaka Ina Mai Baki shawara da ki aikata alheri ki daina tinkaho da arziki a nan zaki mutu kibar komai ” tsaki Ammi taja tare da rike hannun zee tace ” taho mutafi idan kunne yaji jiki ya tsira” Wani guntun murmushi inna tayi” Ina muku albishir da cewa yanzu y’ata zata fara soyayya da Aman da can duk shirme suke ” Bude kofa sukayi suka bangaje suka fice , girgiza kai inna tayi tana dariya tace ” muje zuwa yanzu aka fara wasan , da can bana bukatar auren Amma yanzu ya zama dole ayi auren muga abunda zakuyi “

Back to top button