Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 42

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*42*

Kai tsaye zee taje ta fadawa Ammi abunda ya faru take Ammi tana huci ta kira Aman tace tana son ganinsa idan ya taso daga aiki zee cikin jindadi ta shirya ta koma gida , da yamma Aman yaje ya sameta a falo suka gaisa yace ” Dad Bai dawo bane Ammi?”
“Bansani ba wane irin iskanci ne auren 4 years har ka fara zancen Neman wata, toh bari kaji idan neme nemen mata zata fara ban yarda ba idan Kuma da gaske kake toh na tsoke zancen ” kallonta yake cike da mamaki yace ” Ammi waya fada Miki wannan zancen ” toh ita zee din hauka take da zata zuba Maka Ido ka wulakantata , kaf zuriyarsu Babu me kishiya donhaka bazaka fara a kanta ba bari kaji da kyau” amma ni ai ba matan banza nake nema ba tsohuwar budurwa ta ce nake son na aureta Kuma har Ina son na tura gidansu ” mene? Ka tura gidansu ayi me? Toh wallahi tun wuri ka janye wannan batun don ni banson fitina ana zaman lafiya zaka tada rigimar karo aure akan wane dalili? Yarinyar nan ciki ne da ita so kake ka hanata kwanciyar hankali?” “Gaskiya Ammi ni auren zan Kara Kuma zee Bata isa ta hanani ba ehen ” “idan Bata Isa ba ai ni na Isa koh, toh Babu wannan zancen ” hada rai Aman yayi ya tashi Bai sallameta ba ya fita tabi bayansa da harara ” shashasha kawai Ina Kai Ina mata biyu dududu nawa kake “. Aman Yana kokarin shigar motarsa yaji anbude gate da alama SGF ya dawo kenan donhaka ya fasa shiga ya juya motar Dad dinsa ne ya shigo tare da security nasa , bayan anyi parking cikin girmamawa aka budewa Dad ya fito Yana waya Aman ya karasa kusa dashi yasa hannu ya jawosa suka jera zuwa cikin gida. Ammi ta masa barka da zuwa Yana waya har ya zauna Bai gama wayar ba , Ammi ta kawo tray dauke da drinks don Bata wasa da kula da mijin nata, ya gama wayar Yana kallon Aman ” auta dan Amminsa ya akayi ” Ina yini Dad ya aiki ” “Alhamdulillah ya naka ana can ana ta investigations koh ” guntun murmushi yayi saboda har yanzu ransa a bace yake, ya Maida kallonsa gun Ammi ” uwargida sarautar mata ya gida” barka da dawowa mijina ya aiki ” Alhamdulillah” nan ta Mika masa cup din juice ya karba Yana kurbawa nan ta tashi tana cewa ” bari a hada Maka ruwan wanka kafin ka fito cin abinci” “ehh a hada ruwan Amma abinci sai bayan magariba” ok angama ranka ya dade” murmushi yayi Yana Maida hankali gun Aman.
” Ya akayi naga mood naka somehow” dad dama Ina son nazo muyi magana, dama …” Shiru yayi don baisan ya Dad zai dauki zancen ba, ” continue Ina ji ”
“Dady aure nake son karawa ” murmushi yayi yace” Masha Allah yaro ya girma , kasan ance idan mutum yace zai Kara aure toh da alama yaji dadin na farkon ne Yana Neman doubling na Jin dadin hakane?” Sunkuyar da Kai yayi ” umm..dama my first love ne tun wancan lokacin…”
“Ok nagane , Allah yayi jagora yasa Hakan shine alkairi , y’ar Ina ce ?” ” Mutanen Adamawa ne Amma suna zama a nan ” Masha Allah kace gida zaka koma toh ba matsala idan ka gama magana Kun ajiye lokaci sai ka sanar dani” Ammi da take shigowa tace ” lokacin me kenan ? ” Murmushi Dady yayi ” yaronki ya girma zai ajiye mata biyu ” “yanzu Alaji don’t tell me har ka amince masa, Kai da kake mahaifinsa baka da mata biyu, sultan babban wansa bai ajiye mata biyu ba sai Aman dan 32years yace zai ajiye mata biyu haba don Allah..” Kai mata ku dai baa rabaku da silly things, yanzu wannan din reason ne ?” Wani mugun kallo ta jefawa Aman tace ” tashi ka bani waje mara hankali kawai ” ah ah ya kike haka Kuma…” Kaga dakata wannan zancen bazan yarda ba Kuma bazan taba amincewa ba don Aman baikai rike mata biyu ba” Aman ya Kalli dad nasa yace ” Dad sai munyi waya” ya juya ya fice daga gidan. Dad ya tashi ba tare da ya sake magana ba ya haura zuwa bangarensa, Ammi ta zauna tana kwafa tace ” wallahi duk zakuyi ku gama zancen auren Babu shi ban Isa ba Azo a rabawa d’ana hankali ya kasa samun nitsuwa cikin gidansa.
Hajjo tana rike da wayar ta kura masa Ido tana tunanin yadda Aman yace dole ta fadawa inna a Basu ranar da zai turo magabatansa, gaba d’aya ta rude ita Batasan inda zata fara ba tunda Bata taba fadawa inna cewa Aman ya dawo suna soyayya ba. tagumi tayi daga bisani ta tashi zuwa d’akin maman Nana da sallama ta shiga suna kallo saboda kowane d’aki akwai TV a gidan , zama tayi tace ” maman Nana magana zamuyi” rage volume tayi ta Kalli Nana tace ” dauki Abba kuje falo ” tashi Nana tayi ta rike hannun kanin nata Wanda yanzu yakai 8 years suka fita zuwa falon. Hajjo ta gyara zama tace ” don Allah taimako zakimin, dama Aman ne ..amm yace zai turo iyayensa Ina son ki fadawa inna ” wane Aman? Aman din da na sani wannan dan masu kudi da yake zuwa wajenki lokacin da muke zuwa maraba ” ehh ..shine dama Muna tare ya dade” hmmm tashin hankali, Amma inna batasan da zancen ba koh ” ” ehh shine nake son ki fada mata sai ta basu lokacin da zasu zo ”
“Allah yasa a dace amma nasan da kamar wuya, kinsan kwanaki taje wajen maman Ayman ita mahaifiyar Aman ta wulakanta ta dama can Bata son tarayyan naku Amma ba komai zan mata magana yanzu kuwa tunda Alhaji baya gari ” tagumi hajjo tayi tana tunanin yadda inna zata karbi zancen.
Inna tana bedroom nata maman Nana tayi sallama a bakin kofa ta Bata izinin shiga, zama tayi kasan kafet ” Baki bacci ba malama ”
“Wallahi yanzu nayi shafa’i da witiri zan kwanta kenan ” “dama magana zamuyi akan hajjo ” ok ince kodai lafiya ba Wani laifin ta Miki ba ” ” aa ai tsakanina daku malama sai fatan alheri Allah ya biyaki da irin dawainiyar da kike damu ” “Babu komai ai Nima kin mini a lokacin da nake bukata Allah dai ya barmu tare kiyi kokari ki saka rana kije wajen dangin ki, Nima nan Ina Shirin Kai yarinyar nan Adamawa kafin mu wuce Maiduguri da Yaya ” Insha Allah karshen shekara idan akayi Hutu zamu tafi don jarabarsu Nana nake Jira ” “ehh itama hajjo tace min sun kusa fara jarabawar Kinga zata gama aji 3 idan muka dawo zasu shiga ajin karshe ” Allah ya nuna mana, yanzu ma zancen da ya kawoni kenan wannan yaron Aman zai turo iyayensa Neman aure shine…” Aman Kuma kodai Ayman kike son fada? Murmushi maman Nana tayi ” toh malama shi Ayman ya taba furta cewa Yana sonta ne? ke kinsani Aman ne ke soyayya da ita ” A’a nidai bansani ba yanzu dai nake ji a bakin ki, kodai Wani Aman din ta samu ” shidai Wanda kika sani yace zai turo iyayensa a nema masa auren hajjo ” tabe Baki inna tayi” wato a makarantar suka sake haduwa koh, toh ki fada mata ban amince ba ” haba dai malama yaran nan suna son juna da dai kin bari ya turo ” ” maman Nana kenan, kin manta halayensa ne ko kin manta yadda na Baki labarin abunda uwarsa ta min da naje gidan? Gaskiya y’ata bazata je gidan da zaa wulakanta ta ba Allah ya kawo mata Wani Wanda yafisa ” shiru inna tayi haka ta dauko Wani hira daban sai 10:30 ta mata Saida safe ta koma d’akinta, hajjo na zaune tana chatting fuskarta dauke da murmushi, nan ta zayyana mata yadda sukayi jikin hajjo yayi sanyi haka ta juya ta koma nata d’akin ta kashe data tayi Shirin bacci gaba d’aya ta kasa baccin sai faman juye juye take dakyar bacci ya saceta.

Aman kuwa a wannan daren fada sosai sukayi da zee har yakai sai da suka raba d’aki, zee ta kira yayarta tana kuka tana Bata labarin abunda ya faru yayar tayi shewa tace ” ahayye lallai damu yake zancen, a Ina ya taba Jin kishiya a familyn Armani toh wallahi karya yake, kwantar da hankalinki ki bincika mana lambar budurwa munemi address nata muje a mata warning idan taki rabuwa dashi sai abi bayan fage ”
Share hawaye tayi tana cewa ” yanzu nasan wannan magana idan ya fito dariya zaa Mani cikin family”
“Karki damu auren nan bazai taba yiwuwa bah , tashi ki koma wajen mijinki ki lallaba abinki idan bahaka ba yanzu dole zai kirata a waya ya samu nitsuwa tunda ke kin Bata masa rai” hakane Kuma wallahi ni tunanin baizo min nagode anty sai da safe ”
“Yawwa ko ke fah, tashi ki shirya kibi mijinki baa fushi da miji akan kishiya, kedai gobe zan Miki bayani ” kashe wayar tayi ta shirya cikin kayan bacci dama Fahad wajen me Reno yake kwana , Kai tsaye ta wuce bedroom din Aman ta tura kofar tajishi a kulle ta kwankwasa shiru Bai Bude ba haka taci gaba da knocking yaki budewa dole ta hakura ta koma d’akinta tana Mai tsinewa yarinyar nan daga zuwa ta fara samun matsala da mijinta auren da ko shekara 10 Baiyi ba, taci kuka sosai a wannan daren tana kiyasta abubuwa da dama cikin zuciyarta ya zama dole ta dauki mataki gashi tun Abu Baiyi Nisa ba har Aman ya fara juya mata baya dama ya Yaya akayi bikin lallai dole sai ta tashi tsaye.

Back to top button