Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 27-28

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*27&28*

 

 

……….So what idan kafad’a masa wacece ita?”nace sai me?yafad’a Aharzuk’e yana jan doguwar tsuka, ya yanke wayar cikin zafin rai tun kafin mus’ab yasami damar furta masa wani abu”sai huci yakeyi yana jin ko Dr mansoor zai iya rasa ransa sbd Amaan bazai tab’a taimaka masaba dan ta soshi balle harya mallaketa”sbd Aganinsa wannan Ai cin Amana wa matarsa ne Dr Mansoor yayi! duk yadda yaso ta sukayi Aure shine yanzun harya hararo wata”idan taji maganar Ai bbu dad’i”shiyasa da yawan mata ke cewa wa” mazan basuda tabbas ,kuma maciyan Amana ne mayaudara”da wannan yanayin suka iso Airport”ko a be cewa body quards nasaba da PA d’insa da driver, yayi gaba ya shige jirgi sbd ransa Ab’ace yake”ko break fast d’in da yayi tunanin zaiyi a cikin jirgin k’inyi yayi”sai wajen 11 am ya sauka….saida yafara zuwa masaukinsa yayi wanka ya huta,yyi waya da Ammi”yasanar mata sun sauka lfy”yanaso ya tambayeta ina Amaan? Amma yakasa”sai bayan sallar Azahar sannan yafito yatafi yayi Abinda yakawosa garin”be samu Aka gama solving problem d’in ba saida yamma hakan yasa dole Anan zai kwana”yana ganin kiran Dr Mansoor dana mus’ab duk ya musu banza yak’i d’agawa”yakuma sha Alwashin muddin Dr mansoor zai damesa game da zancen Amaan zai rufe Ido yamasa Abinda zaiyi matuk’ar mamakinsa…..bayan sallar isha’i yana kwance saman wani luntsumemen bed da yaji shimfid’u na Alfarma “yana sanye da wondo 3 quarter da t shirt me gajeran hannu”kasancewar sucan garin ba’a musu sanyi”pillows guda biyu na rungume Atsakkiyar k’irjinsa”yayinda kyawawan idanuwansa ke A lumshe yana sauke Ajiyar zuciya Anutse “wayoyinsa guda 3 na zube saman bed side drower sai ringing sukeyi yamusu banza”gaba d’aya kewar Amaan ce Aransa “duk yadda yaso yabasar ya manta da ita Amma zuciyarsa tak’i yarda hakan”sai koma bujuro masa da tunaninta takeyi”kunnuwansa na juyo masa sautin siririyar muryarta datake masa surutu”gaba d’aya Abinda yafaru daren jiya game da ciwon da yaji shine ke yawo a k’wanyarsa”sai yaji kamar yakira Ammi yace Abama Amaan”sai kuma yaji bazai iyaba….can yaja tsaki Akaro na bbu Adadi yana mik’a dogon hannunsa me cike da zara zaran gashi bak’i ya d’auki baby nokia d’insa”contact d’in Abdallah ya lalibo…k’arfe 8:47pm kiran shariff yashigo cikin wayar Abdallah dake zaune a parlourn yana kallo”sai Amaan dake zaune can gefe”Ammi kuwa tana d’akin ta”bugu biyu Abdallah ya d’auka yana fad’in yaya d’azun na kiraka dan naji lafiyanka shine kak’i d’auka ko?”shariff ya yamutsa fuska yana fad’in kasan bana son yawan k’orafi ko?”hakane Ina wuni?”lafiya qlau “Ina Ammi?”tana d’akinta”d’an jim yayi sai kuma yace” “Amaan fa?”gata nan zaune tanata fushi sbd taga baka dawoba”shine ta tambayi Ammi kana Ina? Akace mata tafiya kayi”shine tasha kuka kamar wata yarinya, sannan tanata fushi ko Abinci bata ciba….. Ayya maza bata wayar”yafad’a batare daya san yama furta d’in ba”Abdallah ya kalleta yaga hankalinta bama wajensa da wajen TV yake ba”Anty Amaan!yakira sunanta” d’ago kanta tayi ta kallesa batayi mgn ba”ya mik’e tsaye yana fad’in ga yaya yace abaki kuyi mgn”wai hamma nah?”shariff dake sauraran y’ar muryarta yasaki d’an murmushin gefen baki yana jiran yaji meye zatace idan Ance shine”Abdallah yace Eh shine”kukan shagwab’a tasaka tana Amsar wayar”Abdallah dai na kallonta yana tunanin to ita meyasa batada waya?….Amaan kuwa k’in mgn tayi sai k’ananun kuka irin na zallar shagwab’a takeyi”can shariff dake sauraronta ya gyara zamansa yana fad’in ya Isa haka sarkin rigima! ko wani abun kikeso ne?”cikin yarinta tace”hamma bakai bane katafi kabarni ko?”karki damu gobe fa zan dawo”shine kuma ni baka sanar mun zakayi tafiya ba?”Amaan dama haka kike da k’orafi?”yanzun fad’amun me kikeso gobe na siyo miki tsaraba?”komai dai inaso hamma nah”Amma ka siyamun kayan wasana kaji?”murya can k’asa yace” duk zan siyo miki”to harda irin turarenka nakeso”zan siyo miki Amma da sharad’in kije yanzun kici Abinci saiki kwanta ko?”to hamma kai yanzun kana Ina?”shiru yayi yak’i mgn “Abdallah ga wayarka tunda bazaiyi mun mgn ba”duk shariff najinta kafin yayi wani abu Akai ta mik’ama Abdallah wayar tanufi dining area “jin Abdallah na fad’in hellow yaya! yasaka shariff ya yanke wayar “gaba d’aya jin zuciyarsa yakeyi tana son cigaba da jin muryar Amaan….da wannan tunanin yayi bacci”washe gari kuwa yana gama kimtsawa ya wuce yima Amaan shopping “kaya yashiga jidar mata na ban mamaki”harda kayan kwalliya da irin turarukan dayake Amfani dasu”ya zab’armata wata teddy me kyau”koda yaje sashen da y’an kunne da sark’a suke haka yadinga jidar mata da set d’in kayan gyaran gashi…… k’arfe 2:45 pm shariff ya iso katafaren gidansu”yaransa na rik’e da ledojin kayan Amaan da tsarabar kayan fruits dayayima Ammi Ahanya”yaran suka fara shiga da kayan shi kuma ya shigo yana waya….jummai me Aiki ce da Amaan zaune Acikin parlourn suna kallo”ihun murna Amaan tasaki tana tasowa ta nufesa tanata dariya had’e da murmushi”saida ya rintse Ido sbd jin ihun nata”ta k’araso gefensa kamar zata shige jikinsa tana fad’in oyoyo hamma nah! Allah har na d’auka sai wata goben zaka dawo”ta k’are maganar tana bin kyakykyawar fuskarsa da kallo”shima ita kawai yake kallo”k’asan zuciyarsa yana jin dad’in yadda take shiga ta mutunci tana rufe jikinta”dan Ayanzun ma mini hijab ce Ajikinta da sabuwar doguwar riga ta Atamfa”ganin yak’i yimata mgn saidai yayi tsaye kawai yanata kallonta yasa ta kwashi fili zata kama dire dire gashi yana lura jummai me Aiki nata kallonsu”hakan yasaka ya d’aure fuska tamau yana fad’in koki nutsu ko kuma Allah na b’ata miki”wuce ki d’auki ledojin can farare”nawane hamma?”kansa ya gyad’a mata “jummai ta matso ta duk’a tana gaidasa had’e dayimasa sannu da zuwa”ya Amsa Atak’aice,Amaan dai ta matsa wajen ledojin tana d’auka da k’yar sbd sun mata nauyi “hakan kuma yayi daidai da fitowar Ammi daga cikin kitchen”tana sanye da kaya na Alfarma Ajikinta”fuskarta d’auke da murmushi tace “koda naji nasan kaine kadawo tunda naji murnan Amaan”Shariff na d’an murmushi yakarso yaduk’a yana fad’in Ammi Ina wuni?”nasameku lafiya? Alhmdllh shariff”tafada tana zama yafara yimata bayanin yadda yashawo kan matsalar”yana satar kallon Amaan da farin ciki yak’i b’oyuwa saman fuskarta”tana d’auke da leda guda”da nufin taje takai tadawo takoma d’auka”Ahaka Abdallah yashigo dawowarsa kenan daga skul”bayan yayima shariff sannu da zuwa yanufi dining area da nufin zaiyi lunch”Ammi ta kallesa tana fad’in Akwai dambun nama da Amaan ta Ajiye karka tab’a mata”to Ammi meyasa bata ciba ta Ajiye?”nidai gaskiya idan yamun zan d’iba…..meye zaka d’iba?”yaji muryar Amaan data fito daga cikin d’aki ta tsintsi maganar”dambun nama mana”b’ata fuska tayi ta kalli shariff da ita yake kallo yana ganin zata kallesa ya janye idanuwansa Akanta “hamma ka ganshi ko?”jeki kwashe tsarabarki yaje yad’iba idan zai iya”cewar shariff fuska a gimtse”to dama hamma kaina Ajiye mawa danaga Ammi bata Ajiye maka ba saina hak’ura na Ajiye maka ko?”kasa mgn shariff yayi dukda k’asan zuciyarsa mamakin yadda yarinyar kullum ke k’ara damuwa dashi yakeyi”ita kuwa jin beyi mgn ba saita wuce ta d’auki gudar ledar ta koma d’aki “Abdallah kuwa yanata d’acin rai yaje yazuba Abinci yadawo cikin parlourn ya zauna”yayinda uban gayyar ya mik’e tsaye ya d’auki tarkacensa ya haye samansa…..Amaan na zaune tsakkiyar carpet ta baza kayan shopping d’in tanata dubawa”teddy d’in na rungume Ajikinta tana fad’in nasamu y’a! sai kuma ta d’auki turarukan tanata faffesawa Ajikinta “Ahaka Ammi ta shigo tana kallon ta tana kallon kayan tayi shiru kawai”saidai tasha Alwashin yimasa mgn yarage wannan facakar dayake mata da kud’i “bayan bata hayyacinta ,wasu Abubuwan ma batasan yadda ake Amfani dasuba…. Ammi kinga hamma ya siya mun?”nagani Amaan”kingode sosai”yanzun ki tashi kimayar a wardrobe duk idan zakiyi Amfani dasu saiki d’auka ko?”Amma ki cire kayan kwalliyar ki Aza kan mirror da socks d’in idan zaki saka saiki d’auka “dato ta Amsa komai ta fidda sannan ta mayar dasu cikin ward rope”Anan taga teddy d’in da shariff yatab’a siya mata a kwanaki”Ammi dake lura da ita tana kallon teddy d’in sai cewa tayi”ki had’a da ita duk nakine”sosai Amaan farin cikinta yak’i b’oyuwa “bayan tagama Adana komai ta d’auki teddy d’in guda ta fito main parlour ta zauna ta azata saman cinyarta tana mata wasa harda surutu……Anutse yake sakkowa down stairs d’in”yana sanye da bakar shadda wacce akayima Aiki da golden d’in zare”ya Aza golden d’in hula me zanan bak’i saman kansa”yayi wani irin kyau kamar Ango”hannunsa guda na zube cikin Aljihun rigarsa”tunda yafara doso parlourn yalura da Amaan da Abinda takeyi”ita kuma daddad’an k’amshin turarensa ne yakaima hancinta ziyara”ta juyo da sauri idanuwanta danashi na sark’ewa”hamma! Uhmm”kaci Abinci?”kansa ya girgiza mata”to meyasa?”wanka naje nayi sarkin tambaya”yafad’a yana zama kan 2 seeter “Amaan ta taso ta zauna gefen sa har saida yad’an matsa sbd kusancinsu yayi yawa”hamma kayi kyau sosai”shiru yayi yana dai sauraron ta”kaji?”kema kinyi kyau *Amaan shariff* Amaan Shariff?”ta tambaya”kansa ya gyad’a mata yana tab’e baki yace”koba ita bace?”uhmm! To shikenan thank you! daga haka be koma mgn ba yana maida hankalinsa a waya yana kallon yadda mutane keta post d’in Alh yahaya da Alh Isa a face book”Anata kace nace game da hukuncin da aka yanke musu”Ibtihal da fareedah nata zage zage….hamma ! tashi muje kaci Abinci na baka dambun naman”kansa yad’ago ya kalleta yace”bazan ciba”meyasa hamma?”sbd k’azama ceke bakya wanka sosai”saufa 3 nakeyi kullum”tab’e baki yayi yak’i mgn saiya mik’e tsaye yanufi wajen dining table”ita ma saita biyosa taja kujera ta zauna”kinci Abinci?”uhmm uhmm! be tambayeta dalili ba yazuba mata plate guda yatura mata gabanta yana fad’in oya kici Abinci”to hamma zakaci dambun naman?”oh my God! zanci Amaan dan Allah”yafad’a yana d’aukar spoon yayi bissimillah yafaraci”itama Abincin takeci Amma jikinta Asanyaye yake”shine yarigata gamawa yaci dambun naman rabin bowl d’in ya Ajiye mata sauran sbd zai tafi yayi sallar la’asar….itama Amaan data gama sallar tayi”bayan ta idar ta kwanta saman bed itada teddy d’inta..…. Ammi ce zaune kad’ai cikin parlourn”shariff ya shigo ya zauna beyi mgn ba”dama inaso muyi mgn dakai game da Amaan! saida yaji fad’uwar gaba Amma saiya dake yana fad’in to Ammi”Abinda nakeso dakai shine karage wannan siye siyen dakake yawan yimata”wasu Abubuwan batasan yaya Akeyin Amfani dasuba”bawai na hanaka kamata Alkhairi bane koka k’i kyautata matane bane”shikenan Ammi zan kiyaye”ya jikin naki?”Alhmdllh da sauk’i”bece komai ba yamik’e tsaye yafita….

*Bayan kwana 2*
tun bayan shariff yadawo daga Abuja shak’uwa me k’arfi ta koma k’aruwa tsakaninsa da Amaan”dukda yana d’an dojewa had’e da basarwa”Amaan kuwa ta maida hankali wajen wasa da teddy d’inta”ta gogeta ta goyata….mus’ab kuwa yakasa gane kan shariff tunda sukayi wannan wayar” dan yanzun iyakarsa dashi gaisuwa idan sun had’u office”Ayau yakama week end”kuma masu Aikin Ammi duk suna ganin gida”itace ta had’a break fast yau”tun bayan ta gama ta d’an kwanta Amaan ce ta gyara d’akin da main parlour “sannan kuma tace itace zatayi wanke wanke “tana tsaye gaban sink tana sanye da dubai abaya light green me zanen bak’i da Adon stones”ta yane kanta da mayafin tamkar wacce ta saka Acuci ,haka gashinta yayi Atsakkiyar kanta”yau harda red d’in lip stick ta shafa”teddy d’in ta na zaune saman dining table d’in dake cikin kitchen d’in ita kuma tana wanke wanke “Ahaka shariff ya shigo da nufin zai d’auki ruwa”wanda a bad’ini bbu wasu ruwan dazai d’auka “kawai tunda yashigo yaga began taba yanaso yace tana Ina Amma zafin kansa ya hanashi”can yaji Ammi dake kwance a parlour tana cewa Abdallah Amaan na kitchen tana wanke wanke shine yafake da zaisha ruwa yashigo”yana sanye da farar shadda kansa bbu hula”Ammasa Aski da gyaran fuska”Anutse yayi sallama be Ida shigowaba yana kallonta k’irjinsa na bugawa”sai yaga tamasa kamar Aljannah sbd irin kyan datayi yau”juyowa tayi ta kallesa tasakar masa murmushi tana dariya har wushiryar dake a tsakkiyar hak’oranta ta bayyanah”hamma nah baka fita ba?”uhmm”dama kin iya Aiki?”na iya mana kawai Ammi ce bata son sakani nayi ne”ta fad’a tana dauraye hannunta sbd ta gama”gefenta shariff ya matso yana fad’in yau bakyajin sanyi ko?”yak’are maganar yana deb’o ruwa yawatsa mata gefen fuska murmushi me ban sha’awa na sub’uce masa”wanda tunda take dashi bata tab’a ganin yayiba ko kuma ta tab’a zaton ya iyaba”shine zaka jik’ani hamma?”nima saina rama Allah”ta fad’a cikin shagwab’a itama tana deb’o ruwan da hannayenta guda biyu yana k’ok’arin tsaida ita ta watso masa gaban rigarsa da saman fuskarsa “nidai ko Amaan?”gwalo ta masa ta koma deb’o wasu ruwan ta watsa masa tana dariya”tsaye kawai yayi yana kallon ta tanata murmushi cikeda burgewa ta matso gab dashi tana fad’in kaga nasaka saika canza kaya gashi zakaji sanyi ko?”tafad’a tana masa gwalo”shidai ya kalleta ya kalli jikinsa yana kuma tunanin idan yafito Ammi ta gansa da kaya Ajik’e yace mata me?be gama wannan tunanin ba Amaan ta d’akko teddy d’in ta tana fad’in hamma muje ka canza kaya saina zab’ar maka masu kyau irin kalar kayana ka canza ko?”kuma Allah ni yau sai nashiga d’akinka”kullum sai kace karna biyoka…shiru dai yayi yak’i mgn”nifa hamma kaine kake ja Ina fushi dakai sbd sai nayi mgn kamun shiru”beyi maganarba sai matsowa yayi by surprise taji ya d’alli pink lips nata……✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button