Nasarar Rayuwata 32
*Talented writers forum*
*32*
“Sunana Muhammad but they call me Sultan nice meeting you” ” nice to meet you sir, how may I help you” kin manta dani already, last time I said I want to be your friend ko kin manta , mun Hadu a office din uncle Mansoor ” “awn…dama kaine , yanzu na tuna ya gida ” “lafiya Alhamdulillah ya school ” lafiya Alhamdulillah” good..so wat do you think ” sorry am too young for that” murmushi Mai sauti yayi yace ” look just friends fah nothing else, or zaki iya daukana as ur bro ko kina da Yaya?” No..ni kadai innata ta haifa ” wow .I can see shiyasa kike ta zuba mata shagwaba dazu Ina kallonki ” ware Ido tayi Wanda hakan ya Kara mata kyau tace ” da gaske kana kallona , are you stalking me” no no… please kinsan I can’t do that kawai dai it was just a coincidence” ” ok fine.. tell me mekake Yi a school namu ?” “Ni..am aiki nake nema shiyasa nake yawan zuwa ” “toh ka samu ?” “Bansamu ba ko zaki samamin a Wani guri daban ” tabe Baki tayi tace” ni Kuma ..tab Babu Wanda na sani wallahi Allah ya taimaka” Ameen nagode” shiru sukayi suna zaune wayarsa ta fara ringing sofy ce Baiyi picking ba ta sake kira kamar bazai d’aga ba yayi answering” hello beb how far ” ta narke masa hajjo na Jin voice nata tana cewa ” haba beb wia have you been tun dazu baka dawo ba I’ve been waiting for you kasan bana son kayi Nisa dani ga su Dady duk suna nemanka ” ta karasa maganar tamkar zatayi kuka , tabe Baki hajjo tayi ya dan saci kallonta yace ” am ..uhm am sorry na danyi Nisa ne but yanzu zan dawo sorry ok..” nidai ka dawo da wuri please” alright I’ll be there soon” “take care toh bana son mata suna kallonka ” murmushi yayi Wanda ya bayyana kyaunsa hajjo ta kura masa Ido ya kashe wayar suka hada Ido ya mata signal yace ” how far .. akwai matsala ne wannan kallo haka ” tabe Baki tayi” matsalar me kawai Ina mamakin wannan wacce take Wani narkewa kamar zata fasa wayar tazo ta sameka ne ” murmushi yayi” ohh.. really ta Baki mamaki saboda me, kishi take Batason yan mata su kalle mata miji ” “au yanzu ita din matarka ce, lallai ” “meaning? Bankai bane or what?” ta tashi tsaye tace ” aa ni Ina ruwana wannan ku ta shafa da Kai da ita ” Ina Kuma zakije Muna magana” “nagaji zan shiga dom na kwanta sai anjima ” “wait! taja ta tsaya ba tare da ta juya ba , ya karasa kusa da ita ya cire kudi a aljihunsa ya Mika mata” gashi kiyi amfani dasu” “no nagode innata ta kawomin bana bukata ” daga haka ta juya tayi tafiyar ta ya tsaya Yana kallonta da mamaki this is the first time a rayuwarsa ya Bada kyauta aka ki karba, ya Dade a tsaye Yana kallonta har sai da ta bace masa da Gani sannan ya Sauke numfashi ya juya ya koma inda yayi parking motarsa cike da damuwa ya Bude ya shiga ya kama hanyar gida.
___________
Shirye shiryen biki Ake Babu kama hannun yaro Ammi tana son bikin ya zama one of the best cikin garin Abuja, a bangaren gidan su zee kuwa Babu magana gidan vp da minister ai karshen kudi kenan, ankai lefe akwatuna 12 Aman Babu zama ana ta shiga da fita Yana arranging wajen saukar baqi saboda shi mutum ne Mai jama’a ga Kuma dangin Ammi tun yanzu sun fara zuwa dangin babansu kuwa sai da aka Nemo masu gidan da zasu sauka har ayi biki a gama don tsabar rashin jituwa tsakaninsu da Ammi. Yau Ya shirya zuwa Jin labarin hajjo wajen inna donhaka ya fita shi kadai , inna tana harabar gidan tana kwashe shanya akayi sallama kofar gida kamar ta shaida me muryan ta amsa , Aman ya shigo Kai tsaye inna ta masa sannu da zuwa inda ta shimfida masa dardumar maman Nana Bata nan ita kadai ce a gidan sun fita tare da nana, ya zauna suka gaisa ta kawo masa zobo da ruwa yaki Sha ya gyara zama sannan ya fara magana ” inna ya labarin hajjo , dama kwana biyu banzo ba shine nace ko tazo Hutu” ” Allah sarki tana nan kalau dayake hutun nasu ba yawa shiyasa Bata zuwa nan ” ” inna don Allah karki hanani aurenta Ina sonta please ” murmushi inna tayi tace” idan tana sonka ai shikenan ni bazan hanata aurenka ba idan da rabo ” ” insha Allah nasan tana Sona duk da dai umm..” ya fara Susa Kai inna tace ” duk da me kayi magana Ina jinka ” um..dama ansaka ranar aure na next week tare da y’ar gidan Armani ” Allah sarki Ina tayaka murna Allah yasa ayi a sa’a ya Baku zaman lafiya ” ” Amin nagode inna Amma Ina fatan Hakan bazai sa ki canza ra’ayi ba ” kamar yadda nace Maka tun farko idan har tana qaunarka ni bani da matsala da Hakan ” shikenan nagode zan tafi Amma Ina fatan zakizo bikin nawa ga katin gayyata , idan zakizo zan tura driver ya daukeki ”
“Allah ya kaimu lokacin nagode da karamci ” daga haka ya mata sallama ya tafi. Yana fita inna ta girgiza kai tace ” iska na wahal da Mai kayan Kara yaushe Hajjo zata iya kishi da y’ar gidan Armani Allah shi kyauta, gara ta Kara nesa da ku” tana magana ta dauki waya ta kira Mrs Juliet ta fada mata cewa idan akayi Hutu hajjo ta zauna summer dama hutun 3 weeks ne ta bari sai hutun second term kan tazo gida. tana gama wayar ta koma aikin hada turaren wuta Wanda zata tafi dashi, maman Nana suka dawo nan take labarta mata abunda ya faru tace ” ai sai ki shirya kije bikin malama ko don darajar dan gidanki Ayman ” inna tace ” hmm wannan uwar tasu mara mutunci toh bari muga yadda Allah zaiyi ” malama duk Wanda suka dace na sanar dasu na fada musu yanzu dai da shawarata zaki ba da ana daura auren kawai ki tare me batun mara sati biyu ” “haba maman Nana sati biyun ai ba Wani yawane dashi ba, da nawa ra’ayin ne ai da sai na Kara wata d’aya Amma sai faman azalzakata yake ” dariya tayi harda shewa tace ” ai wannan ogan naki ba wasa zaa Sha soyayya a gidan naki, nidai bazanje ba sai kin share watanni Kun gama soyewa ” murmushi inna tayi tace”haba maman Nana abin Kuma harda sharri wane irin soyayya kamar wasu Yara ” ai wannan mutumin naki yadda yake Miki ko a bainar jama’a na tabbata idan aka daura Babu inda zai bari kiyi Nisa dashi don wallahi ba karamin sonki yake ba ” murmushi inna take Bata Kara magana ba ita kanta tasan Halin yayan nata ita dai burinta ayi auren taje gida gun dangi da iyayenta saboda tayi kewarsu ba kadan ba, ga Balkees da suke gari d’aya ma ta kasa zuwa wajenta sai nan gaba.
Ummeey ta buga tagumi da trolley agaba tana kallon hajjo tace ” yanzu da gaske besty bazaki min Kara muje bikin nan bah, haba besty y’ar uwata fah uwa d’aya Uba d’aya shine zakimin haka ” kiyi hakuri best kinsan na fada Miki banjin dadi ne da munje ai me a cki ” karya kike wallahi nasan Hali idan bakison Abu kin dinga kawo excuse na karya kenan, kawai dai bakison shiga family dinmu ne ”
Murmushi tayi ” haba best kiyi hakuri mana kije kawai sai kin dawo Allah ya Basu zaman lafiya” “mtsww…aikin banza bayan kingama batan rai, toh sai kizo ki tayani jiran ya mahruf yazo kan ki tafi ki barni ni d’aya, bayan kin saka na roqi uncle Mansoor ya rubuta cewa tare zamuje wllhi ke banza ce y’ar duniya” dariya ta kyalkyale dashi ” kin manta y’ar lahira ce ” mtsww ..aikin banza ba don Kinga na damu dake ba, Allah ya kaimu Ina dawowa zan nemi wata besty zanyi quiting naki ” ta marairaice “haba chief best yanzu duk son da kike min ashe wasane zaki iya rabuwa dani ” hararinta Ummeey tayi ” shegiya ga iya narkewa mutum ga wulakanci ” juya mata baya hajjo tayi nan da nan Ummeey ta rike hannunta “haba mana besty kinsan wasa nake Miki waye ubana a garin nan da zan rabu Dake ” ubanki Armani ” kema ubanki Suleimanu” suka kyalkyale da dariya suna makale da juna inda sukabi motar da tayi parking da kallo , wata farar Mercedes AMG ce tayi parking sai sheki take ya fito Yana tafiya cikin sassarfa har ya karasa kusa da ofishin principal, Ummeey tace ” lahh ya Mahfouz ne fah wallahi shine ..Yaya nah ” ta ruga a guje ta tafi wajensa hajjo na dariya ta jawo trolley din tabi bayanta. Hannunsa ta rike tana murna ya harareta yace ” kin wahalar dani dakyar na gane address din using map ” “toh bro laifinka ne baka taba zuwa visiting ba Daz y ” naji ki jirani Ina zuwa ” daga haka ya shige office din principal inda ya karbi Exit permit ya fito kenan ya samesu da hajjo, kallonta yake Babu keftawa hajjo cike da kunya ta sunkuyar da Kai”Ina yini Yaya” Ina yini Yaya! Yana kwaikwayon muryar ta kafin ya dora da cewa ” Ina kika samu wannan pretty girl din sis ” “she is my best in this school yaya I love her so much” me too..zan tayaki kula da ita dafatan zaki tayani campaign” Kara sunkuyar da Kai hajjo tayi, ya sunkuyar da Kai Yana leken fuskarta yace ” amaryata ki daina Jin kunya am not the type ok, ” dariya Ummeey tayi ” kin shiga uku indai ya Mahfouz ne wallahi agaban kowa zai iya furta Miki Kalmar so ” gaskiya sis Muna zuwa gida zan fada musu na samu mata a fara Shirin bikina ” dariya Ummeey take hajjo kuwa kunya kamar ta nutse. Mahfouz mutum ne Mai barkwanci bashi da girman Kai ko kadan Kuma halinsa bazai bari ka gane when he is serious ba Amma har zuciyarsa he mean what he said wato Ya kamu da son Hajjo, ya cigaba da tsokanarta ko a ce nasa salon soyayya kenan daga karshe sukayi sallama ya ja mota suka tafi hajjo ta koma cikin school dayake yamma ne lokacin , tana Mai Jin kewar Ummeey don tunda sis khairiyya ta hadasu daga wannan lokacin suka shaku kullum Basu rabuwa ajinsu ne kadai daban Amma gadonsu d’aya komai tare suke ci da Sha da wanki wanka da komai a tare suke shiyasa shakuwan tayi yawa har basuson nesa da juna sai gashi auren yayar Ummeey ya tashi duk da taso su tafi hajjo taki ba don komai ba sai don tsare mutuncinta da tsayawa inda Allah ya ajiyeta Bata daukan rayuwa da zafi tana bin komai a sannu.