Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 35

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*35*

Ranar dasu Hajjo zasu koma gida sukayi hotuna suna sallama da mates nasu Bless kuwa harda kuka saboda ita Bata rubuta jarabawa ba sai next year Hajjo tana jiran Ummeey don tare zasu tafi gida amotar gidansu,. Ummeey tazo ta rada mata a kunne ta juya ta tafi tsaki taja sai da ta share mintuna goma kafin ta tunkari motar , Yana sanye cikin wasu ash jacket n pants da takalmin half cover yayi matukar kyau ga qamshin turarensa na Miata sai tashi yake ya kura mata idanu Yana lumshesu a hankali, ta Bude gidan baya ta shiga ta zauna tana kallon window ya kafe ta da idanu ta mirror har na tsahon 5 minutes kafin ya juya Yana kallonta ” Hi bae ” Hi! ta furta tana daure fuska , ” ko zan iya sanin wannan fushin na menene ?” Kai zan tambaya tunda ka iya kashe min waya while am talking ” kura mata idanu yayi ta kauda Kai gefe don bazata juri wannan kallon ba, ” Bae don’t tell me bakisan cewa kin Bata min rai ba, I deserve sorry from you ” da sauri ta juya tana kallonsa ya cigaba” yes ko bakisan kin b’ata min rai bah ” rausayar da Kai tayi ta cigaba da kallon gefen window, shiru ne ya ziyarci motar Babu Mai magana sai Karan AC da bugun zuciyoyinsu. ” Ok am sorry Aysha ” ” ni zan tafi sai anjima ” wait…yanzu idan kika tafi kina fushi dani ya kike so nayi ” Nima bansani ba ” ta Bude murfin mota ta fito nan ya Bude nasa yasha gabanta ya tsaya idanunsa sun fara canza launi , kallo d’aya ta masa ta kauda Kai ta sunkuyar da kan tana wasa da yatsun hannunta ” ki fadamin da wane yari zan fahimtar dake halinda nake ciki, it’s over a year now ya kamata ki Gane komai but naga kina son nesanta kanki daga gareni Wanda bazan iya jurewa , please karki hukuntani ta wannan hanyar please am so sorry ” Bata tanka masa ba tasa Kai ta wucesa Yana tsaye yabi bayanta da kallo Yana Mai Jin haushin zuciyarsa da ta bari ya kamu da son wata Wanda Bai taba tunanin Hakan zai faru ba. Ummeey ce ta hangota da sauri ta karasa tana cewa ” alhmdllh dama yanzu ya Mahfouz ya tsareni da tambayoyi Ina kika tafi na rasa amsar da zan basa nace kina can kina pic da friends namu taho mu tafi har na fidda kayanmu ansaka mota ” ta rike hannunta suka wuce inda Mahfouz yayi parking suna zuwa Ummeey ta Bude gidan baya ta Kalli Hajjo tace ” ki shiga front seat ni Ina daga nan ” Hajjo batace komai ba ta Bude ta shiga, Yana kallonta kamar Wani mara gsky, a hankali ta furta ” good morning Yaya ” how are you my beauty ” am fine ” daga haka ya ja motar suka fita daga harabar school din. Shara gudu yake kamar zasu bar garin ya kure volume din wakar da ya kunna Babu Wanda yayi magana har suka iso Apo domin sauke Hajjo , Ummeey ce ta fara sauka hajjo tasa hannu zata Bude yace ” wait beauty…” ta dakata ba tare da ta juya ba yace ” just tell me what’s on your mind about me ” shiru tayi ya sake cewa ” beauty please ki gayamin gaskiya shin kina Sona ko aa ” shiru ta sake Yi sannan tasa hannu ta Bude kofa tace ” thanks ” ta juya ta fice. Iska ya furzar ya rasa meke masa dad’i a duniya Bai taba tunanin cewa akwai macen da zatayi rejecting nashi ba sai yau Kuma karamar yarinya for that matter.
A can cikin gida kuwa inna sai murna take tana musu adua ta fatan alheri Ummeey ta baje tana zuba sai da Mahfouz ya kirata a waya kafin ta fita suka tafi, maman Nana wacce ta dawo gidan da zama tare da y’ayan ta duk sun canza sunyi Kyau alamar Hutu ya fara bayyana ga inna tana fama da laulayin ciki ta fada tayi fari Amma ta Kara kyau tayi fresh sosai, ya Yusuf sai tattalinta yake kamar kwai ya Bata kudade masu dumbin yawa ta fara business din kayan qamshi har ya kama mata shago a wuse market Wani Yana zama inna kuwa ta hada kayan ta bayar a Kai ana ciniki sosai, ga Kuma makota sun Saba da ita saboda ta iya muamala da mutane suna shiga har gida su Siya humra da turaren wuta dasu kulaccam. Hajjo ta koma d’akin ta tayi wanka ta kwanta sai bacci yayi gaba da ita Bata Farka ba sai bayan azahar nan tayi sallah ta shirya ta fito falo ta samesu suna kallo ta nemi abinci tana ci suna dan taba hira da Nana tana Bata labarin sabon school din da ta shiga. Abba (uncle Yusuf) ne ya shigo tare da inna tana rike da briefcase dinsa da alama yanzu ya dawo , sannu da zuwa suka masa ya amsa cikin Sakin fuska Yana kallon Hajjo yace ” y’ar gatan inna congratulations” thank you Abba ” ya exams din dafatan ba problem” Alhamdulillah mungama lafiya Babu wata matsala ” Masha Allah haka nake son ji yanzu wane school kike son zuwa ” ta sunkuyar da Kai tace ” kowanne na samu zanje Abba” ok zamuyi magana da Fav zamu Duba Wanda ya dace ” nagode ” daga haka suka haura last floor inda dakinsa yake , Hajjo ta Kalli maman Nana tace ” wai mmn nana inna ciki ne da ita ” dariya maman Nana tayi tace ” ehh zaki samu kani Ina tayaki murna” chabdi wallahi ni kunya nakeji a ce innata ta haihu yanzu da girmana ” ” wallahi bari taji ba ruwana ita kanta kunya take amma idan taji kina furtawa zaki Gane kurenki ” dariya sukayi suka cigaba da hirarsu.
Da dare bayan sallar Isha Nana ta shigo ta sameta a d’aki tace ” Abba yace ki samesa afalonsa na sama ” ok Gani nan zuwa ” hijabi ta dauka ta fice , Yana zaune inna tana gefensa Yana yanka mata apple tana ci Hajjo ta sunkuyar da Kai kasa , Wani kwali ya tura gabanta yace ” ga gift dina sai a kula ayi amfani dashi ta hanyar da yafi dacewa bana son TikTok” da sauri ta d’aga Kai taci karo da iphone XR Wani murna ta fara Yi tana murmushi sai zuba godiya take , inna tace ” kindai ji me akace Miki Banda TikTok wallahi kika kuskura kika fara Hawa TikTok kina rawa ko posting na hotunan toh kinbar waya kenan har abada ” insha Allah zan kiyaye nagode Allah ya Kara lafiya da arziki Abba ” Ameen dota tashi kije abinki a kashe lafiya” murmushi take ta mike cike da farin ciki ta koma d’ayan falon tana nunawa maman Nana sun tayata murna suna Yaba halayen Abba da irin karamcin da yake musu. Hajjo Kai tsaye d’aki ta wuce ta hada wayar ta jona chargy sai zumudi take yau ta fara rike wayar kanta dama tana tunanin ya zasu na communicating da Ummeey. Wajen 11pm ta kunna wayar akwai sim da credit ciki ta saka number Ummeey ta kirata anyi sa’a kuwa batayi bacci ba nan ta daka tsalle tana tayata murna sunsha hira daga karshe tace su Hadu a Whatsapp . Haka rayuwa ta kasance suna Hutu kullum Hajjo na makale da wayarta sun shirya da mutanen nata ita ta kirasu ta Bada hakuri suka cigaba da zumuncin nasu Babu Wanda ya sake kawo mata zancen soyayya saboda sungane abin nata harda yaranta.
Bayan wata biyar inna ta haihu ta samu d’a namiji murna wajen uncle Yusuf baa magana tamkar yanzu ya fara haihuwa , lokacin yaje Maiduguri wajen d’ayar matarsa nan take ya shirya ya dawo Kuma har wannan lokacin danginsu Babu Wanda yasan cewa yayi aure. Ranar suna yaro yaci sunan Abubakar mahaifin inna Babu Wani taro da akayi Amma makota da aboka arziki sun shigo anci ansha, Ummeey kuwa kwana tazo tayi tazo da kayan jarirai dasu pampers tamkar ita akawa haihuwar. Inna taci gaba da rainon sadeeq nata Wanda kullum Yana wajen maman Nana ko Hajjo , Hajjo ta fara zuwa Baze university bayan result nasu ya fito ance ta samu scholarship a jami’ar Baze dake can Nnamdi Azikiwe express way Jabi kusa da EFCC head office. Ummeey ta dage sai da aka sama mata Baze din saboda aminiyar tata inda Hajjo ke karanta Geography Education Ummeey kuwa tana computer science, Idan Hajjo ta koma gida Bata da aiki sai wasa da Sadeeq duk da cewa Baiyi wayo ba Amma haka zatayi ta masa wasa tana kaunar yaron tamkar ta hadiyeshi. Inna kasuwanci ya bunkasa yanzu kowa yasan shagon *Hajjo Gidan qamshi* a cikin kasuwar wuse haka Kuma cikin Amina court tayi suna kowacce idan zatayi aure sai suje wajenta ta hada musu kayan qamshi na musamman, kana shiga gidanta kasan lallai kazo gidan qamshin ne ga Kuma zobo da kunun aya tanayi maman Nana ke kula mata dashi kullum ana zuwa Siya cikin gida, donhaka hankalin inna a kwance yake har wata y’ar kiba tayi ta Kara haske tayi kyau , ga uwa Uba soyayyar da take samu gun mijinta baa cewa komai kullum cikin kwalliya da gyara inna take ta koma Amina gimbiya y’ar Mai Borno ga lalle kullum cikinsa take ga tsabta ga Kuma tattalin da yayan nata yake samu shiyasa ya sake mata ragamar komai tana ja sai yadda ta juyashi.

Back to top button