Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 2

Sponsored Links

️2️⃣

Tun da ɗan acaɓan ya kaita tasha, ta biya shi kuɗinsa har gaban mota ya ajiye mata jakarta tana ta zabga masa godiya kamar wanda ya kawo ta kyauta. Mota na cika suka kama hanyar Kano, Inna Azumi ta samu wata tsohuwa mai shegen surutu irinta aikuwa suka rinƙa zuba kamar daman sun san juna, tafiya ta yi tafiya Inna Azumi ta fara gyangyaɗi a haka suka ƙaraso Tashar ƴan kaba ɗan sahu ta samu unguwa uku zai kai ta, suna cikin tafiya ta tuna cewa bata sanar da Mamar Halima ba dan dama ƙarya ta yiwa Malam a kan cewa ta ce ta taho, kawai dai Inna Azumi ta kira su gaisa sai take ce mata suna asibiti Sadiya na naƙuda shi ne fa ta shiryo ta taho ba tare da ta sanar da ita ba.

Ganin wayar babu caji ta mutu ta taɓe baki a zuciyarta ta ce

“Yo ya za a yi da ni, ni da gidan ɗana duk da dai ya mutu amma ai babu mai korata daga gidan jikokina, dole na je na tabbatar kar na fara zuwa gidan Halima(Sadiya) Na tarar an bar ta a gidansu saboda wankan jego, ko da kuwa ma hakan ta kasance dole na mayar da yarinyar ɗakinta na mata zaman wanka dan ba kasafai wasu mazan ke son matansu su je gidan iyayensu wankan jego ba” Tana cikin saƙar zucin ta lura sun kusa layin da za a ajiyeta, dan haka ta shiga nunawa ɗan sahun inda zai bi har dai suka ƙaraso ƙofar gidan, idanu ta ƙwalalo lokacin da ta yi tozali da danƙareran kwaɗo a ƙofar gidan ɗan sahu bai ankara ba ya ji ta ce

“Na shigenge ni Azumi”

 

“Lafiya dai Baaba” Ya faɗa yana kallonta da mamaki, ganin ta dage sai zabga salati take kamar an ce wani ya mutu.

“Yo ba dole ba na yi salallami ɗan nan ka ga gidan da na zo a rufe”

“Haba Baaba ya za a yi da ki taho baki sanar da mutanen gidan ba, gudun haka ne ya sa ake faɗa, gashi na ga da alama ma kamar ba a gari kike ba dan na ga lokacin da kika sauka daga mota”

“Wallahi kuwa ɗan nan ba a gari nake ba daga wani garin nake, amma na san inda zan same su, mu je tarauni”

“To Baaba” Haka ya juya kan napep ɗin suna tafiya tana ta faman surutu har suka kawo ƙofar gidan da ta nuno masa zai ajiyeta tun kan su ƙaraso.

“La’ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W, yau dai na ga ta kaina wannan wane irin abu ne kamar an haɗa baki” Ta ƙarasa faɗa tana tafa hannuwa.

Ɗaga ido ɗan sahun ya yi aikuwa ya sauke a kan ƙofar gidan ashe nan ɗin ma a kulle.

“Gakiya Baaba kin taka fawul a ce ko ina babu kowa kamar basa son zuwanki” Ya faɗa yana tuntsurewa da dariya.

“Kai ɗan nan ka kiyayeni ni nan da kake gani can gidan ɗana ne nan kuma gidan jikata kuma na san inda suke suna asibiti jikartawa za ta haihu zatona duk sun dawo shi ya sa”

“To ki musu waya mana” Bani sa caji kai bari dai ka ga” Ta faɗa tana fitowa daga napep ɗin ta lissafa kuɗinsa ta biyashi kamar yadda ya faɗa, ya fito mata da jakar kayanta kamar yadda ta buƙata.

“Baaba ziyara kika zo ko ƙaurowa kika yi?” Ya faɗa cike da sheƙiyanci lokacin da ya ɗaga bakkon ya ji wani uban nauyi.

“Ka ji ni da ja’irin yaro to ina ruwanka” Ta faɗa tana juyawa ta shige gidan da ke maƙotaka da gidan Sadiyar, shi kuma ya ja ya tafi yana ta dariya dan hatta yadda take magana dariya yake bashi, ga wani uban gwaggwaronta kamar bututun zuba kalanzir.

Tana shiga suka gaisa da matar ta sanar da ita gidan Sadiya ta zo a rufe, nan matar ta ce suna asibiti tun da sassafe. Matar ta ce ta zauna kafin su dawo dan ta gane kakar Sadiya ce ta taɓa zuwa gidan sun haɗu lokacin ita Inna Azumin ta zo, cewa ta yi bari ta samu ko almajiri ne ya ɗakko mata jakarta.

Imran ne tafe a kan machine ɗinsa roba -roba matashi ne matashi ne dan ba zai haura shekara 26 ba ɗan gayu ne dan yanzu ma yana tafe a machine ɗin sai wani dube -duben jiki yake, lokaci zuwa lokaci yana sanya hannu ya karkaɗe rigarsa duk da ba komai a jiki amma saboda kawai tsabar tsafta da ƙyanƙyami yake karkaɗewa. Imran bashi da son mutane gashi da ƙyamatar ya ga an kusanci inda yake sai wanda ya yi niyya sai kuma wanda jininsa ya haɗu da nasa. Ba ya son duk wani abu da zai shiga tsakaninsa da farincikinsa wato matarsa Sadiya yana son ta sosai saboda auren soyayya suka yi hakan ya sanya ba ya son duk wani abu da zai sa ya yi nesa da ita ko ya nesanta shi da abar ƙaunar tasa. Ya fi so koyaushe idan yana gida ya kasance tare da matarsa, gashi mutum mai yawan buƙata, shi ya sa ko yaya ba ya son wani abu ya haɗashi da Sadiya bare ta yi fushi, idan kuwa hakan ta kasance to ya kan yi iya ƙoƙarinsa ya shawo kan ta dan kar ya rasa biyan buƙatarsa dan bashi da haƙuri ko kaɗan a wannan harkar, sai ya samu matar tasa ita ma mai burin faranta masa bata so ko kaɗan ta hana shi kan ta.

Ya kusa ƙarasowa gidansa ya hango wata ƙatuwar jakar bakko a ƙofar gidan, cikin mamaki yake kallon jakar da kuma neman dalilin ajiyeta a ƙofar gidansa.

 

Cikin sauri da azama ya ƙaraso har yana neman faɗuwa a machine ɗin dan ba ya ƙaunar abin da zai haɗa shi da kayan wasu, dan shi akwai tsare gidan ko maƙota iyakarsu gaisuwa tsakaninsa da su dama shi ba wani yawan magana yake ba bare zaman majalissa in har ba wurin aiki ya tafi ba to yana gida tare da iyalansa, sai ko idan ya je gaishe da Hajiyarsa. Yana faka machine ɗin ya ƙanƙance idanu yana kallon jakar, kallon da ya mata ma sai ya ji yana tsantsaninta dan sai ya ga duk ta yi wani ƙura, ko kuwa dan bai yarda da jakar bane oho ya ɗago kai yana son gano yadda aka yi jakar ta zo ƙofar gidansa sai ya ji wata murya tamkar daga sama an ce.

“Shikenan ma na huta ga Imirana nan” Shiru ya yi tare da runtse idanunsa da ƙarfi, jin an kirashi da sunan da ba ya so kwata-kwata, kuma ma duk duniya ya san babu mai kiransa da sunan nan sai kakar Sadiya wato Inna Azumi ita kaɗai ke kiransa, kuma ya shaida muryarta dan ko daga bacci ya tashi ba zai kasa shaida muryarta ba.

 

Shi ya rasa me yasa matar nan take son takurawa rayuwarsa, sam ba ya son wannan nuna ƙoƙon usulin da take nuna masa dan yana auren jikarta, shi ko ƴarta yake aure ba ya son takurawa amma ita ta kasa ganewa, sannan duk miskilancinsa na ƙin son magana da mutane sai da ya daure ya faɗa mata cewa Imran ake kiransa dan idan ta kirasahi da Imirana nan ji yake kamar ta kwaɗa masa gudum a kan sa.

“Ashe ma kana kusa har nake bin gidan maƙotanku ka ganni nan saukar yanzu tsal ɗin nan” Ta ƙara faɗa tana ƙarasowa wajensa ba tare da ta jira ya ce wani abu ba, cije gefen lips ɗinsa ya yi yana ji da a ce wani ne da ban ba tsohuwa ba yake damunsa kamar yadda tsohuwar nan ke damunsa da sai ya ɗau mummunan mataki.

“Eh” Kawai ya ce hakan ma dan ta kasa kunne ne ta gane me ya ce amma da gungune ya yi maganar.

“Allahu akbar Imirana har yanzu dai kana nan da wannan mugun halin naka, kai wane irin mutum ne da baka sakewa da mutane ku yi magana ma ta fatar baki kawai ni fa kakar ka ce ba sirikar ka ba” Ta faɗa tana kallon fuskarsa da ya haɗe ta murtuk kamar zai saki kuka.

“Sauri nake” Shi ne kawai abin da ya ce, shi ma dai da ƙunƙunen ya faɗa.

“Oh Allah na shiga aljanna na maƙale, yanzu baka ce min Inna ina wuni an zo lafiya ba sai ka zauna kana min magana kamar mai ciwon haƙori, ko kallon arziƙi na kasa samu daga wajenka”

Banza ya mata ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan.

Inna Azumi kuwa baki ta taɓe, dan ta lura in ta ce za ta ga yadda take so to zuciyarta sai ta yi bindiga bata samu yadda take son ba, gwara ta lallaɓashi a rabu lafiya, bare ita da ta zo dandalar arziƙi.

“Sa’adiyyar ta sauka ne?” Ta faɗa tana kallonsa yana cire kwaɗo daga jikin ƙofar gidan.

Bai bata amsa ba a take ta tuna da katoɓarar da ta yu, dan dama Sa’adiyya take kiran Sadiya amma saboda kwainane irin nasa ya ce wai ta fiya ɓatawa mutane suna ganin baya iya faɗar Sadiya sai Sa’adiyya sai take cewa Halima saboda jarabar Imran ɗin dan duk ranar da ta zo gidansa haka zai yi ta mita a ƙunƙunen nan har dai ta ɗan canja sannan ta samu salama.

“Na ce Halimar bata sauka bane?” Ta gyara sunan dan ta matsu ta ji halin da jikarta ke ciki.

” Ta sauka” Ya faɗa a takaice yana tura ƙofar gidan ya shige ya bar Inna Azumi a tsaye baki sake, da ya shige ma sai da ya ɗan turo ƙofar.

“Yau na ga abin da ya isheni, a haka zan yi har kwana hamsin ɗin, ana wannan zaman doya da manjan, taɓɗi aikiwa duk abin amarya sai an sha manta wallahi ko me za ka yi sai na zaina ZAMAN WANKAN nan dan ban ga abin da zai sanya na fasa ba dan kana wannan fisfigar” Ta faɗa a ranta tana tura ƙofar ita ma ta shiga gidan tare da jan jakarta ta shigar da ita dakyar saboda nauyi, Imran da ya dawo domin ya ɗakkowa Sadiya zani saboda zannuwan sun yi kaɗan yana cikin sanya zanin a leda ya jiyo ƙaran jakar Inna Azumi tana janta ƙiiiii.

“Me yasa matar nan ta shigo min da ƙazamar jakarta gidana” Ya faɗa a ransa, ya yi sauri ya fito daga ɗakin ya dawo falo ya sanya hannu ya fusgi labule da ƙarfi ya fito daga ɗakin tare da rufo ƙofar dan ma kar ta yi gigin shigar masa da jakarta ɗaki dan ba ya jin zai iya bacci ma idan jakar tana ɗakin saboda ƙyanƙyami.

Baki sake Inna Azumi ke kallonsa har ya gama kulle falon, yana wani ɗaɗɗaga kai kamar ya ga kashi ya ce.

“Asibiti zan koma” Sai da Inna Azumi ta saurara da kyau sannan ta gane me ya ce.

“Yo ni ma ina na ga ta zama, ai ba zama wai an ɗaurawa karya zani, mu tafi sabitin in je in gan su dan can ma gidansu na fara zuwa a rufe, na zo nan ɗin ma ashe dai basu dawo daga asibitin ba”

“Eh” Kawai ya ce dan shi kamar mai ciwon baki haka yake ba ya son magana ko Sadiya sai ita ta yi ta masa hira shi dai sai umm da um, um kawai ko da zai yi maganar ma to ba wata mai yawa ba sai dai kuma ranar da ya ga dama sai ya yi maganar amma ba sosai ba.

Yana fitowa ita ma ta fito ya rufe gidan, aikuwa sai ga wani mai napep zai wuce ya tsayar da shi ya ce ya ɗauketa sai ya biyo bayansa.

“Wannan yaro da mugun hali yake” Ta faɗa tana taɓe baki ta shiga napep ɗin suka bi bayansa. Maƙociyar Sadiya kuwa da ta leƙo ganin Innar bata dawo ba, ganin Imran ya sa ta juya ta koma gidanta dan ita ko gaishe shi ta yi banza yake yi in ma yana amsawa to ita bata ji, sai ma ta daina gaishe da shi ganin rainin wayo da rainin hankalinsa dan ita tana mamakin yadda Sadiya take zaune da mutum kamar gunki.

Tun da suka fara bin Imran yake zabga uban gudu kamar zai tashi sama, da yake kuma unguwar kwana -kwana ta yi yawa ga ƙurunƙusai sai ya zama na Inna Azumi tana ta tangal-tangal a cikin napep ɗin saboda yadda ɗan sahun shi ma ke zuga gudu abinsa. Inna Azumi hannu ta sanya ta kama ƙarfen napep hagu da dama ta ƙanƙame dan ji take gabaɗaya kamar juyata ma ake yi. Idanu ta ɗaga ta sauke a kan me napep ɗin fa bai wuce shekaru sha tara zuwa ashirin ba, ga wani uwar suma a kan gashin ya yi cibir-cibir har da matajin kai a soke a jikin gashi, ga wani uban kiɗa da ke tashi a napep ɗin tamkar ma kiɗan jijjiga napep ɗin yake.

“Wai ni kai kwa yaro bahaushe ne?” Inna Azumi da bakinta baya shiru ta tambaya tana mai ƙuga maganar da ƙarfi yadda zai ji..

“Ke tsohuwa da wane yare na miki kama”?” Ya faɗa yana sakin wani uban fito da duk ƙaran kiɗan amma bai hana fitowar fiton ba.

“Ai tambayrka na yi dan na ga alama hausa bara ganka ba”

“Inyamuri ne ni, ko na miki ne, kina ciki”

“Amma wannan yaro an yi shegen yaro yanzu ka dubeni tsofe-tsofe da ni ka ce ina sonka? Amma gidanku ba manya”

“Sun ƙare” Ya bata amsar yana sanya hannu ya ciro matajin ya ɗan taza kan ya mayar ya soke.

“Baby kin yi shiru”

“Uwarka ce baby, wallahi tsakani na da kai Allah ya isa, ni Azumi na ga ta kaina.

“Ba dai shaƙa kika yi ba Hajiya, ban da ƙauyanci dan na ce baby ba wai yarinya nake nufi ba, wasan kaka da jika ne fa”

“Ƙauyancin uban wa? Na ce ƙauyancin uban wa, to tun kafin a haifi uwar mai sabulu farfela take da farinta” Ta faɗa tana jin kamar ta saki fitsari dan gabaɗaya an dagula mata lissafi ga yunwa ga wani fitsari da ya cika mata mara ga wannan jijjigar da napep ɗin ke yi sai ta ji a ranta ta fara ɗan da na sani kaɗan ba da yawa ba na tahowa ZAMAN WANKA, da tana gidanta da yanzu ta ci ta ƙoshi tana bacci ko kuma tana kama ƴan kuɗaɗenta daga masu zuwa siyan mai da ƙuli amma wani ɓangaren na zuciyarta sai ya bata ƙwarin gwiwa.

“Kar ki karaya bayan wuya sai daɗi, daga yau ne fa wahala ta ƙare za ki fara cin kayan daɗi” Wani murmushi ne ya suɓuce mata har sai da ta ɗan rausaya kai.

“Ka daina zabga wutar nan haka gudun ya yi yawa”

“Bakya ganin yadda wanda muke bi yake gudu kamar zai tashi sama.

 

 

“Rabu da Imirana mugun hali ne da shi ka yi tafiyarka a hankali ka ji”

“In ya ɓace mana ke zaki kaimu wajen da za ku je?”

Shiru ta yi bata ƙara magana ba, wata kwana Imran ya shiga dai dai wani gida ya faka machine ɗin ya sauka ya faka machine ɗin ko kallon su Inna bai yi ba ya tura gidan ya shiga.

“To ki fito mana tun da mun zo ashe ma babu wani nisa sosai”

“Nan ne asibitin?”

“Asibiti kum?”

“Eh mana asibiti za mu je”

“Haba Hajiya nan ya miki kama da asibiti nan ai gida ne”

“Gida kuma, wai ni me ya sa Imirana ya raina mutane ne haka, ya za a yi ya shige wani gida ya bar ni ko bayani ba zai mini ba” Ta faɗa tana saurin sakkowa daga napep ɗin ta ce mai napep ɗin ya jira ta, a fusace ta tura ƙofar ita ma ta shige tana shiga ta ga wani ɗaki da ke a farkon shiga gidan, bata yi wata- wata ba ta bankaɗa labulen kawai sai ganinta suka yi bakam ta shigo kamar an jefo ta.

Wani kallo da Imran ya jefawa Inna Azumi shi ya sanya ta wayance ta ce

“Ikon Allah ashe ba mu zo asibitin ba, wallahi duk zatona ɗakim haihuwar ne nan” Ta faɗa tana saurin juyawa ta fito da sauri dan shi da wani da alama abokinsa ne ya miƙo wa Imran ɗin zamzam a robar zamzam. Abokin kuwa yadda Inna ta yi ya matuƙar bashi dariya, Imran kwa tsaki ya yi ya fito ya hau machine ɗin.

Inna kuwa mai napep ganin ta fito da sauri sai abin ya bashi mamaki har ya so bashi dariya.

“Kin masa magana?” Ya tambayeta lokacin da ta fito ta shiga napep ɗin.

Inna da gabaɗaya take a ruɗe ba wai kallon da Imran bane ya sa ta gigice ba, abokin nasa ne babu kaya a jikinsa daga shi sai ƙaramin wando wanda ake kira inpant, to har ga Allah bai san ya yi wawan zama ba ashe Inna ta hango abu ya leƙo ta ƙafar wandon wannan ne abin da ya ruɗa ta dan ita yaushe rabonta da ta yi ido huɗu da bananar ma ta manta, dan su yanzu an tsufa, ganin bananar abokin Imran ne ya ruɗa ta, hakan ne ya ruɗa ta ta dawo da sauri har tana neman yin tuntuɓe. Dan da alama ɓa abokin nasa gwauro ne dan ɗakin nasa a bakin ƙofar gidan ne daga ciki kuma tana jiyo hayaniyr mutane daga cikin gidan.

 

” Ashe ruwa zai kama” Ta faɗa dan ta waske amma a ranta sai salati take ko idanu ta rufe sai ta ga abu kawai. Da haka dai har suka iso asibitin bayan sun sha uban gosulo. A wurin da aka tanada dan ajiye napep a nan ya sauke Inna haka ya yanka mata uban kuɗi ta bashi, dan Imran ko tsayawa bai yi ba bare ta sa rai zai biya kuɗin napep ɗin.

Tana bawa mai napep ɗin kuɗi ta fara sauri-sauri gudu-gudu dan ta tarar da Imran dan machine ana iya zuwa da shi har ƙofar ɗakin da mutum zai je da ke asibitin na gwabnati ne, ashe da ɗan tazara zuwa ɗakin haihuwar dan haka kafin Inna ta kawo ta gama jigata dan ma tana iya hango Imran ɗin da yake wurin babu kwana bare ya ɓace mata.

“Oh ni da bani da kuɗi yau da na tagayyara, wannan yaro ko kaɗan bai san mutunci ba, uwarsa kwa ba haka take ba lallai albasa bata yi halin ruwa ba, na ɗauka shi zai biya min kuɗin tun da shi ya tsare ɗan sahun amma sai ni na biya, ko ma ya tsaya idan ma ba zai biya ba, sai ya ce Inna ki biya kuɗin amma shiru maƙatau babu niyya wai ango ya kwana da wando” Take ta zancen zuci har ta ƙaraso wurin ɗakin haihuwar.

 

ƳAR ZAMAN WANKA‍

(KWANA ARBA’IN)

NA

 

MAMAN AFRAH

Back to top button