Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 11

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*11*

*thanks for d love guys Allah barmu tare*

Ayman ya kasa bacci a wannan daren gaba d’aya tunanin hajjo yake ya rasa dalili yana jin haushin Aman saboda ya hangosu tare suna hira cikin nishadi ,letters nata ya fitar yana sake karantasu d’aya bayan d’aya ya rasa meyasa letters din ke kwantar masa da hankali phone nasa yayi ringing ya duba new number ce har ya katse bai d’aga ba aka sake bugowa har na ukun ya d’aga ba tare da yayi magana ba ” hello my Prince ya kake ” muryarta ya gane zee ce donhaka ya kashe call din da wayar baki d’aya dama he was tensed zata kara bata masa rai a banza, haka ya cigaba da lallaba kansa har bacci yayi gaba dashi d next day ya sake xuwa da yamma ya tsaya yana kallon yadda suke hira cikin nishadi da shakuwa ya share 40 mins yana kallonsu kafin ya shiga mota suka koma, Aman da hajjo kuwa wata shakuwa ce ta shiga tsananinsu har shi kansa Aman yakanyi mamaki meyasa idan yana tare da hajjo yana manta da kowa da komai a duniya duk da karancin shekarunta amma yarinyar tana da wayo da kaifin basira na ban mamaki ,kuma duk yadda zeyi bata karban abun hannunsa idan ya wuce chocolate haka ya gaji ya zuba mata ido . har bakin mota ta rakasa tana d’aga mishi hannu yana murmushi ya shiga ya tafi , tana komawa gida yau ta fara wani ciwon ciki tun tana boyewa har ta fara kuka nan ta sanar da inna tana fada inna ta fahimci kwanan zancen donhaka ta fita chemist da kanta ta hado mata magunguna da always guda d’aya ta dawo gida, tana shigowa ta sameta tana birgima a daki mmn Nana na bata hakuri ga kayanta sun baci inna ta hada ruwan zafi ta kai mata bayi ita da kanta ta taimaka mata sannan suka fito ta shiryata cikin wasu kayan gwanja Riga da wando iya guiwa tayi kyau sosai, kiran sallan magrib ake donhaka suka gabatar da alwala inna ta kalli hajjo dake alwala tayi murmushi bayan ta gama ta dauki hijabi inna tace mata ” ki sameni a daki ” ta shiga da sallama ta xauna ” hajjo kin manta da babin wankan tsarki da nake koya miki kwanaki tun kafin mutaho nan garin ?” Shiru tayi daga baya tace ” na tuna inna,akwai wankan gawa na biki na haila da janaba sai..” murmushi inna tayi tace ” toh alhamdulillahi yau Allah ya kawo ki lokacin girma kin fara jinin haila, saboda haka ki maida hankali sosai girma yahau kanki ki nisanci kanki ga kowane d’a namiji , Allah ya tsare bari nayi sallah ki xauna kiyi istigfar da salati ina xuwa ” daga haka inna ta fita waje don dama ta ajiye dardumar sallah a waje ta tada Kabbara hajjo tayi shiru tana nazarin kalaman inna, bayan inna ta idar da sallah ta gama lazimi ta dawo kusa da hajjo ta cigaban da mata nasiha na sanar da ita hukunce hukuncen haila ta dora da cewa ” wasu mata ko kuma nace mafi yawan mata idan jinin al’ada ya ‘dauke musu suna jinkirta wanka da niyar ko jinin zai qara dawowa. Wasu sukan Qara kwana ‘daya zuwa biyu bayan haila ya ‘dauke.
Wasu kuma idan suka ga alama guda ‘Daya na ‘Daukewar jinin, sai suce zasu jinkirta wanka domin su jira zuwan sauran alamomin. Misali: Mace taaga bushewar gaba amma bata ga Farin ruwa ba, wanda ake kiransa da larabci Qaswatul biyadha’a,daga nan sai tace bari ta bari sai farin ruwa yazo sannan tayi wanka ta cigaba da sallah da azumi.duk Wannan kuskure ne babba abinda yake wajibi shine: Da zarar taga jini ya tsaya ko taga alamomin Daukewar Jinin haila, toh wajibi ne tayi wanka nan take ta cigaba da ibadar ta. Qin yin wanka har lokacin sallah ya wuce babban zunubi ne.Allaah ya tanadi Azaba mai tsanani ga masu wasa da sallah.
Allaah yace:- fawailul lilmuswalleena allazeenahum answalatiheem saahuun,
Allaah ya qara da cewa:- Fakalafa min ba’adi him khalfun adha’us salata wattaba’u shahawati fasaufa yalqhauna ghayyan suratul maryam aya ta hamsin da tara da ayoyi masu yawa cikin al-Qur’ani. daga lokacin da jini ya dauke, ibada ya wajaba ga mace, idan mace ta jinkirta sallah toh sai ta rama su bayan tayi wanka, sannan tayi istigfarin jinkirin sallah, idan kuka xauna da kawayenki a makaranta kiyi kokarin sanar dasu domin yada ilimi yana da daga cikin abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci donhaka ki kula ki maida da hankali kuma akan shiga cikin maza” nasiha ta cigaba da yi mata mai shiga brain da jijiyoyi. Mmn Nana ta shigo ta samesu tana zolayar inna tace ” malama sai a fara tanadin aure y’armu ta girma” murmushi inna tayi tace ” hmm da saura dai ” ” malama ke kuwa me zai hana ki mata rajista ta rubuta jarabawar shiga sakandari ” shiru inna tayi “. Allah da kin daure kin biya mata don naga tana da ilimi ga kokari kuma tana da tsayi da saurin girma ” ” hakane tana da tsaho gaskiya, gobe insha Allah zamuje sai naji nawa suke biya idan baifi karfi ba sai a biya mata ” “masha Allah haka ake so malama Allah ya taimaka, abinci suka ci sannan suka cigaba da hira.

_______________

Aman da yazo ya aika kiran hajjo tazo bata xauna kusa dashi ba murmushi yayi ” yau kuma me na miki ” turo baki tayi tace ” babu komai ina wuni ” ” lafiya ya innarmu ” ” aa inna ta dai don Ni kadai ta haifa ” ” Allah sarki bazaki bani aronta muyi sharing ba ” um um bana so” dariya yake yace ” laifin me na miki bakison zama kusa dani yau?” “Inna tace babu kyau zama kusa da namiji ” gaskiya ina son inna saboda akwai tarbiya, shiyasa nakejin dadin hira dake domin a kullum sai na qaru ” ” toh kai meyasa baka koyamin abubuwa” me kike son na koya miki? ” turanci nake so kaga nan garin kowa ya iya turanci amma Ni ban iya ba, zaka koyamin koh” murmushi yake yana kallonta tana matukar burgeshi komai nata abin sha’awa ne d way she talks her smile n everything ” meyasa kake son yawan kallon mutum nifa banson haka ” ” am sorry toh ” ta juya masa baya ” please besty please… ” murmushi tayi tace ” kasan bazan iya fushi da kai ba ” da gaske?” Bansani ba” ta harareshi yana dariya phone nasa ya fara ringing ya duba Ammi ke kiransa yana d’agawa ” kana ina maza ka dawo gida ina son ganinka ” ” okay Ammi ” kit ta kashe waya , murmushi yayi yana kallonta ” sorry zan tafi Ammi na kira ” ” toh ka gaida gida sai gobe ” ya tashi ya tafi , motarsa na tashi Ayman ya bude tasa motar ya fito sale ne ya hangosa yaje da gudu yana murna ya mika masa hannu suka gaisa nan ya cire kudi ya bashi tare yake da abokansa nan Ayman ya fara raba musu kudi kan kace me masu baran dake wajen suka taru haka ya rarraba musu kudi dakyar ya samu hanya ya fita yana Neman hajjo bai ganta ba cikin jin haushi ya shiga mota driver yaja suka wuce gida. Bayan sallar isha Ammi ta tarasu a falonta suna zaune ta kare musu kallo sannan ta fara magana ” yanxu ko kunya baku ji, kai dan sarki ne kai kuma dan SGF amma a ce kuna shiga cikin talakawa kuna intermingling dasu , wannan wane irin shashanci ne haka, toh daga yau sai yau idan na kara jin labarin Aman kaje gindin gada kana zama da wannan yar almajirai sai na mugun tsaba maka wllhi, kai kuma idan sadaka kake son yi ka wuce masallaci ba sai can wajen masu zaman banza da sunan mabarata ne zaka ba sadaka ba donhaka Ku kiyayeni wllhi,daga yau babu ruwanku da tsayuwa under bridge hope am communicating ” shiru sukayi Aman ya fara kunkuni ” toh Ni duk inda mutum yake sai anturo masa yan sa ido wannan rayuwar har yaushe , gaskiya… ” ” ka shiga hankalinka dani wllhi, idan kayi wasa zan turaka wata uwa duniya can kayi nisa da gidan naga ta tsiya ” shiru yayi da bakinsa don sanin hali zata iya aikatawa ” kiyi hakuri Ammi zamu kiyaye ” yana gama fada ya tashi ya tafi. Aman yace ” sorry Ammi ” daga nan ya wuce part nasu tabi bayansu da harara tana cewa ” sakarkaru kun dauka bansan me kuke ciki bane , duk abunda kuka aikata yana cikin kunnena ” tsaki taja ta tashi ta shige ciki. Washe gari Aman ya wuce yana kallon gurin zaman nasu yasan halin Ammi zata aikata duk abunda taga dama donhaka ya zama dole ya kiyaye don Neman zaman lafiya, karo na farko a rayuwarsa yaji yana son ganin wata mace bayan uwarsa lallai shakuwarsa da hajjo yayi nisa baisan hakan ba sai yau da bai sanyata a ido ba gaba d’aya ya shiga damuwa da tashin hankali har suka wuce yana kallon bangaren, Ayman kuwa da suka zo wucewa yana kallon bangaren nasu ya hangota xaune kusa da mmn Nana tana cinikin pure water tana magana da dariya tana murmushi duk idanunsa na kanta bugun zuciyarsa na dada k’aruwa amma yana son karyata zuciyar tasa , har suka wuce yana kallonta sannan ya sauke numfashi ya kwanta. Hajjo sai faman leka shagon malam dalha take ko zata hango Aman amma shiru har magrib haka ta koma gida cikin rashin walwala tana jin babu dadi a cikin zuciyarta, a wannan dare mutane uku duk sun kwana da damuwa wato hajjo , Aman da Ayman Niko nace love circle kenan asuba ta gari tarkon qauna.

Wasa wasa hajjo ta share sati 2 babu Aman babu labarinsa tun tanasa ran ganinsa har ta gaji ta cire abin a zuci takan tuna dashi wasu lokutan idan ta xauna shiru, a haka har lokacin zana common entrance exams nasu ya gabato ta rubuta kuma taji dadin jarabawar sai fatan alheri da samun sakamako mai kyau, Aman kuwa kullum sai ya duba wajen zaman nasu wani zubin kamar ya sauka amma yana tsoron hukuncin Ammi kuma kamar da wasa ya gane cewa ya fada tarkon son hajjo saboda a kullum da tunanin ta yake kwana dashi yake tashi haka nan yake dannewa a zuciyarsa don gudun matsala, yau yana xaune a balcony da yamma yayi jugum yana tunani Baba sule da tanko ne ke hiran duniya Tanko yake shaidawa Sule zaije gida karshen sati gun iyalansa, Baba sule yayi murmushi mai ciwo yace ” Allah sarki ka godewa Allah kana tare da iyalinka kana ganinsu suna ganinka, Ni nawa iyalin bansan ina suke ba ” ” haba Baba sule me kake nufi ” ” Amina baiwar Allah mace mai karamci da mutunci ta mini halaccin da bazan manta ba, iyayenta masu tarin dukiya amma ta rabu dasu ta auroni har muka haifi ‘ya mace sunanta Aisha mamana baiwar Allah, Allah ya sadamu da alheri ” kuka ya fara yi Tanko na bashi hakuri , jikin Aman yayi sanyi ya tausayawa Sule nan hajjo ta fado masa a rai anya zai iya rabuwa da hajjo kuwa? gaskiya dole ya nemi mafita yau zai tafi ganin hajjo a sace babu Wanda zai sani bare a fadawa Ammi, dole ya nemi inda zasu na haduwa ba a cikin kasuwa ko gefen titi ba ya zama dole , haka ya cigaba da tunani daga karshe ya figi makullan mota ya fita ba tare da ya sallami kowa ba.

*Ku biya 300 naira kacal , wannan littafin amana ne duk Wanda ya fitar toh tabbas yaci amanata na barka/ki da Allah, tuntubi 07030077024 for payment details thank you*

Back to top button