Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 83

Sponsored Links

83
Kwanciyarsu sukai hankalinsa na kwanciya da dawowan su Bena rayuwarsa da sumayyah sbd idan har yanda wasu likitocin suka fada ne dawowar wainda ta rasa rayuwarta zai iya dawo mata da hankalinta daidai cikin qanqanin lokaci koma lokaci Daya yasaka yake Jin damuwarsu da quncinsa na rashin lafiyarta tsawon lokacin Dan haka a yanzu kam yakejin lokacin warkewar matarsa yayi.

Gyara mata kwanciya yayi a jikinsa kafin ya miqa hannu ya kashe musu wutan dakin Yana lumshe idanuwansa tareda kokarin Tina gwarwarmayar daya Sha a baya daga lokacinda ya bar gida.

Babu wanda ya farka a cikinsu kaf wainda sike gidan sai da safiya tayi sosai,

Bena ce tafara farkawa ta Bude idanuwanta dasukai mata nauyi sosai tana Jin kanta na Dan juyawa ta dafa ta tashi zaune daga kwancen datake tana kallan inda take.

Lumshe idanuwanta da sukai nauyi da ja tayi tana kokarin motsawa ta sauko Amma jikinta gabaki Daya ya mutu batajin karfinsa ko kadan kaman wadda akaiwa duka ko Wani allura.

Qafafunta ta zira qasa ta saukar tareda kokarin miqewa tsaye ta daddafa bango ta Isa bakin kofar dakin ta Bude ahankali ta fito tana tafiya kanta da Dan juyawa.

Motsin dataji a hanyar dining ta nufa batareda tasan inane take nufar ba.

Sumayyah ce da momyn Abdul ke zubawa ruwan tea Dan baa barin tana hada tea da kanta sbd ruwan zafin kada ya mata illa dokan Bilal ne.

Sumayyah dataji motsi tahowa itama dago kanta tayi ta Kalli hanyar idanuwanta a Bude hakama fuskarta dauke da murmushi da farin ciki duk tinanin Bilal ne ya fito.

A cikin idanuwan junansu idon kowaccensu ya sauka,

Cak Bena ta tsaya rawan qafafunta na qaruwa kaman yanda bugun zuciyarta ya tsaya cak wannan lokacin.

Sumayyah kuwa kafe idanuwanta tayi kan Bena tana Dafe kirjinta ahankali dataji Yana harbawa kadan kadan yana qaruwa.

Bena na ganin Hakan take ta fahimci halinda sumayyah take ciki sbd a duniya ita kadaice tafi kowa Gane lafiyan sumayyah da Anne hakama rashin lafiyansu.

Wasu zazzafan hawaye ne da tinda masifun rayuwarta suka fara saukan mata jiya Bata samu ko digon hawaye sun zo mata ba sbd radadin masifun sai wannan Karan dataji suna gangarowa daga idanuwanta tana rasa Gane wane yanayi ne a cikin zuciyarta,
Zallan farin ciki ne ko tsoro da fargaba ne¿

Takowa ta ringa yi ahankali tana nufo sumayyahn wadda hawayen Bena suka sauya buguwan zuciyarta kwata kwata sbd tini kanta ya fara juyawa fuskar Bena na dawo mata cikin Kai da hawaye kala kala da kukansu na baya.

Benazir na qarasowa Bata tsaya komaiba ta rungume sumayyahn data miqe itama tana kallan Bena har lokacin kanta na juyawa sosai.

Cikin tsananin Kukan Daya tarwatsa zuciyarta me qunci da tsima Rai ta ambaci sunan sumayyahn Wanda yayi daidai da fitowan Anne itama daga dakin tana dafa bango ahankali ganin inda take da Neman Bena.

Ganinsu ya sakata tsayawa cak itama tareda tsirawa fuskar sumayyah idanuwanta tana tinanin kenan jiya a hankalinta da gaske taga sumayyah,
Ta dauka cikin haukarta ne taga sumayyahn na mata gizo kaman yanda taga Safnah tai mata gizo shekaran jiya da jiya a gidan Ababa.

Sumayyah Datake rawan jiki sosai tana Neman rikicewa da runguman da Bena tayi mata tana ambatan sunanta suna hada Ido da Anne ta qarasa rikicewa gabaki Daya tafara jijjjiga tana kafe idanuwanta akan Anne benazir na Jin Hakan itama nata jikin ya hau rawa, Anne data farka cikin hayyacinta itama kansu tayo tana Taya Bena taro sumayyahn jikinta sbd zubewan Datake Neman yi.

Fitowan Bilal ya ga Abinda yake faruwa da sauri ya qaraso tareda daukan sumayyah wadda ta zube jikinsu kaman ba Rai jikinta idanuwanta a rufe koina jikinta na rawa sosai.

Kai tsaye dakin dake kusa Wanda Anne ta kwana ciki ya nufa da ita ya Kwantar sai alokacin ya lura da yanda jikinta ke rawa sosai da sauri ya fara girgiza ta Yana Kiran sunanta da karfi Yana cewa ta Bude idanuwanta.

Momyn Abdul dataga halinda sumayyahn take cikin damuwa da tashin hankali ta kallesa tace yayi mata alluranta mana.

Girgiza Kai yayi Yana kallan Bena da Anne da Suma suke cikin girmamammen tashin hankali da tsoron Abinda yake faruwa yace bazai mata ba yau tinda wainda take shiga wannan halin sbd su yau din suna tareda ita Yana fatan qarshen wahalansu ne yazo yau din.

Benazir ce ta hawo gadan itama ta kamo fuskan sumayyahn tana Kiran sunanta da qarfi muryanta na rawa,
Anne gabaki Daya ta kasa yarda da duniyar dasuka tsinci kansu a yanzu,
Shin duniya suke kokuwa lahira suka hade dasu sumayyahn,
Ita dai a halin yanxu data ganta tareda yaranta biyu a gabanta ko lahirar ne batada damuwa bare baqin ciki Dan kuwa rayuwarsu ta duniya sai dai suce Allah ya Basu ladan Ibadan daukan qaddarorin da sukaita Yi.

Bilal da duka zuciyarsa da kirjinsa suke tsalle Yana kallansu Yana jira da fatan daga yau idan ta gansu kada hankalinta ya sake juyewa ya tsaya daidai Dan bazai sake mata allura ba inshallah ahaka yakeson ta samu sauki da ganinsu.

Anne ma hannu takai ahankali ta dafa sumayyahn tareda Jin hawaye sun gangaro daga idanuwanta na farin ciki da tausayin kansu batasan lokacinda ta zube jikin sumayyahn ba ta rungumeta da qarfi ta qanqameta tareda fashewa da kuka me sauti tana Jin tsananin so da kaunar ‘yarta na dawo mata sabo fil sbd sun cire Rai daga rayuwarta tintini.

Kukan Anne ya saka sumayyah bude jajayen idanuwanta da suka sauya take ta Kalli Anne hawayen nason ciko idanuwanta Wanda ya saka Bilal Jin zuciyarsa na Neman bugawa sbd fargaba da matsuwan son ganin reaction nata sbd tsawon shekarun Bata taba Kuka ba bare hawaye Wanda Hakan ke nuni da Bata hankalin nata Amma yau ganin hawayenta na Neman sakasa Kuka Kai tsaye.

Momyn Abdul ma ganin hawaye idanuwan sumayyah ya sakata fashewa da kuka kawai tana kallan Bilal Wanda hawayensa ke gab da gangarowa.

Benazir ma datake Gane sumayyah ta dawo daidai tin Abaya idan taga hawaye a fuskarta ne tana ganin hawayen ta batasan lokacinda itama ta fashe da kuka ba Wanda ya saka sumayyah fashewa da kuka take itama tana kallansu har lokacin Bata gama dawowa daidaiba Amma tabbas Bena da Annenta ko da can ko a halin ciwonta Bata mantasu Bata Dena sonsu Bata Dena jinsu tsakiyan ranta.

Fashewan kukan sumayyah ya saka Bilal fashewa da kuka mara sauti Wanda ya saka momyn Abdul zuwa gurinsa ta dafasa tana Dan bubbugasa alaman rarrashi da taya murnar farin cikin wannan Rana me dinbin tarihi a rayuwarsa sbd soyayyan sumayyah a ransa Wani Abu ne da momyn Abdul Bata taba Gani ba, mutumin dazai iya baro gida,iyaye da danginsa da gata da daulansu ya zo ya Gina tasa rayuwar daban sbd kawai kulawa da macen dayakeso Kuma duk shekarun Nan a cikin rashin cikakken hankalinta.

Duk Wanda ke dakin Kuka yakeyi tsawon lokaci kowa baya iya magana suna kukan rage baqin ciki da quncin rayukansu na baya tareda farin cikin rayuwar dazasu sake ginawa a tare yanzu.

Sumayyahn ce tafara shiru daga kukanta jikinta na Neman sakewa sai alokacin suka saketa suna kallan Bilal Wanda ya fita ya dauko mata Wani magani da sauri ya dawo ya saka mata bakinta tareda zuba mata ruwa daqyar ya samu ta hadiye maganin ta silale jikinsa idanuwanta na rufewa.

Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu a tare kowa idanuwansa na kanta cike da so da kauna da kulawa.

Bayan tayi baccin sai alokacin suka zazzauna jigum jigum kafin Bena da qyar ta lallaba ta shiga toilet din dakin tayi wanka sbd ciwo da tsamin da gabobinta sukai na wahala Dan haka tana shiga toilet din ta sakarwa kanta ruwa ta fashe da sabon kukan Datake riqewa cikin ranta na tata quncin zuciyan.

Wane tsaka me wuya ta samu kanta aciki?
Menene makomar tata rayuwar data auren Dayake kanta?
Ta Ina zata fara tinanin kowace iriyar rayuwa batareda shi da Amnah a cikinta ba?
Wannan sabuwar qaddarar tata me nauyin gaske ce data hadata auren miji Daya da Safnah,
Gashi idan ta lissafa daidai itace ta haramta garesa Koda su Safnah da Ababa Basu koreta ba sbd ta tabbatarda zamansa da Safnah bayan tarewan bikinsu sunyita samun muanalan aure….

Rintse idanuwanta tayi tana durqusawa qasa kukanta mara sauti da tsananin qunci na qaruwa.

Ta jima a cikin toilet din kafin ta fito tana sakawa ranta cewa dole ne yanzu tayi kokarin yakicesa daga zuciyarsa sbd yariga ya haramta gareta matiqar ‘yar uwarta na Raye.

Bayan fitowanta Anne datai zugum itama cikin Nisan tinani dagowa tayi ta Kalli benazir din wadda taqi barin Annen taga fuskarta sbd yanda yanzu take daidai zata iya Gane quncin Datake ciki me tsananin gaske Wanda zata buqaci Jin dalili wanda idan har hankalin Anne ya manta da Abinda ya faru Bata fatan tinatar da ita ko sanar da ita Safnah da Abinda sukai din na korarsu akan suna auren miji Daya,abarsa akan Annen ta Dade da dangana da sakawa ranta cewan Safnah ta mutu,
Gwara ta zauna akan maganar Safnah bata Raye datasan Abinda yar tata takoma abin ya zo ya taba zuciyarta dasuke fatan samun sabuwar rayuwar aminci a yanzu matiqan suna tareda junansu.

Sallah tayi wadda duka Basu samu sunyi ba sbd ficewa hayyaci.
Itama Anne wanka tayi momyn Abdul ce ta kawo musu kayan sawa masu kyau duka acikin tarin kayan sumayyah dake cike da closets na kusan dakinsa Dana dayan bedroom din Dayake matsayin nata duk sitirar Dayake Siya mata ne kala kala baya damuwa da wasu ma bata sakaba yake siyo wasu.

Bayan sun shirya sunyi sallah abinci aka kawo musu har dakin Dayake babu sauran qunci bayan Wanda Bena ta danne cikin ranta haka sukaci abincin sama sama suka gama aka tattara gurin sai suka sake komawa zaman jigum jigum suna jiran farkawar sumayyah
Itakuma Bena kebe kanta tayi dayan dakin tareda zaunawa qasa ta cusa kanta cikin qafafunta zuciyarta na mata Wani irin ciwo da radadin datakejin kaman ba bazata iya rayuwaba ahakan.

Har yamma Bata fito daga dakin ba ko abinci takasa ci Annenta hankalinta yayi mummunan tashi Nan tafara tambayarta Yaya mijinta da Amnah.

Wannan tambayar ta Anne ta saka Bena kasa riqe kukanta Datake ta riqewa idanuwanta sunyi jajir da nauyi ta fasa kukan Mai ciwo tana fadawa jikin Anne.
#MAMUH#

 

_Masoya masu goyan bayanmu a da yaushe, masu san shek’e masge kwarkwatar idanunsu, da san kwakwale damuwarsu, da sanya bak’in cikin su facewa, su kwamaso sink’i-sink’in dariya, annashuwa da sassanyan murmushi kan fuskarsu, su antayawa ruhinsu salama, su sanbad’awa zuciyarsu yalwa, masu san farin ciki wajen karatun littattafan Hausa? to ku matsu kusa, dan nesa tazo kusa, ga shahararriya, hazik’a, fasihiyar, mai san kasancewar ku cikin annuri, wacce ta saba kawo muku nagartattun litttattafanta masu dad’i, wacce ta kware wajen rubuta dad’ad’an labaru tun daga kan wanda ya k’unshi nadama, kuku,tausayi, cin amana, da nagartacciyar soyayya mai yalwa mai sanya tsoho ko tsuhuwa su tuna da jiya samartakarsu da ‘yan matancinsu ya motsa,_
_ta sake dawo muku da wani sabon salon littafinta mai k’unshe da abubuwan mamaki, al’ajabi, kala-kala, wa’azantar da ban tausayi gami da sanya zuciya tsinkewa, wanda zai nishad’antar daku, ya d’ebe muku kewa ya sanya masu hawan jini, sauka, masu ciwon zuciya darawa,_ _*BAK’AR SHUKA…2 shine sunan littafin, wanda *HAUWA A USMAN JIDDARH* tayi bajakulin fasaharta da basirarta wajen antayo muku dashi, *BAK’AR SHUKA…BOOK2*_
_zaku biyu naira d’ari hud’u (400) kacal domin samun labarin da karantashi akan 400 kacal da k’arin bayani sai ku tuntub’i wannan number 08037649871 ko ku tura ta 0153259310 Gt Bank Hauwa Auwal Usman_

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button