Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 10

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E10_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

 

A Kwance ya ke saman shimfiɗeɗan gadonsa, Kamar kullum cikin shigar larabawa, hannun shi a ruƙe da wayarshi, Ya ƙurawa Hoton wallpaper ɗin shi ido, ko ƙyaftawa bai yi sam baya gajiya da kallon hotonta, Yanayin fuskarshi Ya nuna tsantsar damuwa, a hankali ya ɗaura yatsun shi saman hoton kan wayar yana shafa fuskarta, lumshe idanuwanshi Ya ɗanyi kafin a hankali ya ware su kan hoton, waƙar larabci ya soma rairawa da daddaɗar muryarsa duk akan hoton wadda ya ke kallo, ya dage yana yi mata waƙa mai nuni da ƙaunarta da yake yi, Tunawa da bata a raye yasa shi dakatawa da raira waƙar, Ya jefar da wayarshi gefe ɗaya saman mattress ɗin, haɗi da kifa kanshi saman pillow, kamar ƙaramin yaro ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, abun ne yana damunshi ya hana rayuwarshi sakat.

“Shureim, Ka yi haƙuri Ka daina sanya damuwa aranka, I know it hurts you, but worrying won’t make anything better, it’ll only make things worse kuma ka tuna Allah yanasan bayinsa masu tuba, Kana fa da ilmin ka ba sai na tunasar da kai ba,”

bai tsammaci jin muryarta ba, A hankali Ya ɗago da idanuwanshi Waɗanda su ka kaɗa jawur da su, ya ɗaura su kan fuskar Zainab.

Tana a tsaye cikin shiga ta riga da skirt, kanta sanye da hula, ga dukkan alamu daga kitchen ta fito.

“Babu wanda yasan nashigo shureim, Satar hanya nayi don nasan idan hajiya layla ta sani ba za ta bar ni in zo wurin ka ba…….” numfasawa ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa”Tuntuni na so mu samu lokaci muyi magana sai dai ban samu damar yin hakan ba saboda baka nan, till today” har cikin zuciyarshi ba ƙaramin sanyi yaji ba, yunƙurawa yai tare da miƙewa ya zauna ya jingina bayansa jikin headboard din gadon Yana kallonta, Still hawaye basu daina wanke fuskarshi ba, Zainab ta damu dashi sosai, har mamaki ta ke yi yadda wasu iyayen Allah ya basu damar haihuwar ƴa’ƴa nagartattu amma suke watsi da su, basu damu da damuwar su ba, yayin da wasu neman ƴa’ƴan su ke yi ruwa Ajallo, tana matuƙar jin takaicin haka.

“Aunt Zainab, Kin tabbata ba wanda yasan kin shigo? Ina mommy da daddy ne”
“Layla tana a palour, mahaifin ka kuma Yana a garden shi da kawunka Musa” Jin hakan Yasa shi saukowa daga saman gadon shi Ya nufe ta, tsayawa yai suna fuskantar Juna.

“Ka faɗa min wani taimako ka ke so In yi maka? in sha Allahu babu abunda zai gagara, a shirye nake da in share maka hawayen ka”

Hannayen ta biyu ya ruƙo a cikin nashi gabanta sai faɗuwa ya ke yi, tsoronta kada wani daga cikin Iyayenshi ya faɗo ɗakin, muddin hakan ya faru zata ɗanɗani kuɗarta ne.

“Aunt Zainab I feel in my heart that she’s still alive! Tun bayan da abun ya faru I’ve never dreamed of her as dead, I’ve always seen her alive in my dreams.” tun kafin ya ƙarasa maganar ta katse shi “How could that be possible, Shureim? Mutumin da ya mutu ai baya dawowa and the dreams you’re having aren’t real Don’t believe what you see in your dreams.”

Fuskarshi a yamutse ya ke dubanta

“Amma ni inaji araina bata mutu ba!” kafe mata yai akan zancen shi
Ta fahimci ya fara zaucewa, Zaifi ta lalla6a shi don ta kwantar mashi da hankalin shi”shureim, idan ma tana araye da buƙatar mu shirya plan don mu tabbatar da abunda muke zargi,”

Jinjina mata kai yai alamar yana fahimtarta.

“Dole Ka bi duk a bun da zan faɗa maka,” amsa mata yai da in sha Allah, mu zauna sai muyi magana” girgiza mashi kai tayi”a’a ina tsoron Mahaifiyarka ta faɗo dakin nan, Just A tsaitsaye zan faɗa maka matakin da zaka ɗauka domin mu ci nasara akan binciken da zamu yi” zame hannunta tayi daga cikin nashi da sauri ta nufi ƙofar ɗakin ta leƙa tana duban ko’ina don kada wani ya faɗo masu, ganin bakowa yasa ta gyara labulan ɗakin nashi, ta juyo da sauri ta nufe shi Yayin da take cigaba da yin maganarta”mataki na farko shine Dole ka tanƙwashi zuciyarka, ka danne raɗaɗin da ka ke ji ka daina sanya damuwa aranka”

“Mataki na Biyu Ka daina gudun Iyayen ka, Ina nufin Ka koma masu tamkar yadda ku ke da su Ada, Biyayya sau da ƙafa, ka nemi yafiyarsu akan 6ata masu rai da ka ke Yi…..” tun kan ta kai ƙarshen maganar ta lura da canzawar da yai, a marairaice yace da ita”Aunty zainab taya zan iya yin hakan? Ni bana jin zan Iya sakar masu fuska mu koma kamar yadda muke ada” murmushi ta ɗan saki kafin tace”Shureim kenan, Nafi so ina magana kana fahimtata, ta wannan hanyarce kaɗai zamu Iya gano meke wakana a tsakanin Iyayenka” jinjina mata kai yai alamar ya fahimta.

Har ya buɗe baki zai yi Magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa

“Me ka ke buƙata in kawo maka? nasan kana jin Yunwa”

A ruɗe ya ke kallonta da mamaki Akan fuskarshi, Me ya kawo zancen yunwa acikin maganar su.

“Ko dai kana buƙatar chips in haɗo maka da shi”? Ta wutsiyar idon shi Ya hango Layla A tsaye bakin ƙofar, Ta kifa ɗaurin ɗan kwalin atampa akanta, Riga da skirt ne sun bi shape ɗin jikinta, duk da alamun manyantaka atattare da ita, hakan bai 6oye kyawun surarta ba.

Wahalallan Yawu ya haɗiya haɗi da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, aranshi ya ayyana ko yaushe tazo bakin ƙofar! Sai yanzu ya fahinci dalilin canza maganar zainab, ita tun kafin layla ta shigo tajiyo takun takalmanta saboda bata sanya takalmi idan ba mai tsini ba, Ba don Allah yasa taji motsinta ba da ko ta yabawa aya zaƙin ta

“Aunty zainab wai meyasa ki ke son takurani akan dole sai naci abinci, nace maki bana jin yunwa ki tafi kawai, Ni bana buƙatar ganin kowa akusa da ni, ana dole ne” Ranshi a matuƙar 6ace yai maganar, tare da Juya mata baya, Ya ruƙe qugu da hannu ɗaya, Zainab dake kallon bayanshi tace”Shureim zama da yunwa zai Iya haifa maka wata matsalar, abunda bama fata, Ni bari naje na faɗawa mahaifiyar taka kaƙi cin abinci wataƙil idan ita tayi maka magana ka ci” Har zata Juyawa shureim Ya juyo a sukwane Ya daka mata tsawa”Karki Kuskura ki ce zaki haɗani da ita, Ko kin faɗa mata abanza, matar da bata damu da ci na ko sha na ba…..” Sai da yai wannan maganar, Layla ta kai hannu ta ɗan kwankwashi Jikin Ƙofar ɗakin nashi Don hankalinsu ya dawo kanta, tamkar basu san da zamanta ba suka ɗago suna kallonta, Fuskarta tasha uban make up, gashinta baki wulik har mid back ɗinta, Cikin takun izza da nuna isa Ta nufo su tana magana”Zainab Nagode da kulawarki akan ɗana, ki ƙyale shi, shureim ya daina jin maganar kowa a yanzu bansan laifin me mu ka yi mashi ba da yake gudun mu,’ tun da ta fara magana Zainab take sauke ajiyar zuciya, jin bata gano me suke tattaunawa ba, shureim ko sai ƙara ɗaure fuskarshi ya ke yi kamar zata fashe saboda tsabar nuna fusatarshi.

Idanuwan mahaifiyarshi akan fuskarshi, Cikin girmamawa zainab tace”Shureim har yanzu yaro ne, tun da yana a ƙarƙashin kulawarku, sai ana haƙuri dashi ana kuma lallashin shi da jan shi a jiki ta hakanne zamu iya sanin meke damun shi” jikinta na ɗan kerma tayi maganar, gyaɗa kai Layla tayi”is Okey, ba sai kin koyamin yadda zan Kula da ɗana ba, Ni da na haife shi ni nasan kayana, Zaki Iya tafiya ki bamu wuri” ta yi maganar tare da nuna mata ƙofa da hannu.

layla kenan Ita ba’a mata gwaninta, Jiki asanyaye zainab ta kama hanyar fita ɗakin tana tafiya tana waiwayon shureim da ido take Yi mashi alamar Ya sake mata, kada ya manta da shirinsu, Lumshe mata idon da yai ne yasa ta fahimci ya gane me take nufi, Bayan fitar zainab, Layla ta tsare shi da idanuwanta

“me zan yi maka wanda zaisa Ka daina guduna? Haba Shureim saboda na kore ka cikin fushi shine ka kama Hanya ka tafi egypt wurin Ammi, Kasa ta kirani awaya tana ta zazzaga min masifa, ‘ ranta a6ace take yin maganar, har ya harzuƙa zai mayar mata da martani kalaman zainab suka faɗo mashi arai da sauri ya danne fushinsa, abunda ta tsana dashi tana magana Yana shareta, Wuyan farar jallabiyar jikinshi ta damƙa da hannayenta waɗanda ke a sanye da awarwaro da zabba na zallar zinari, Jijjiga shi tai”Shureim so kake baƙin cikin ka ya kashe ni? Na rasa benazir kaima kuma kana neman ɗaura min hawan jini, so ka ke zuciyata ta buga in mutu shureim”? hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, ganin hawaye sun ciko idonta.

Duk da yasan ta yi hakanne don ta samu kanshi, sassauta muryarta tayi tare da sakin Kwalar rigarshi”Kai kaɗai nake gani naji daɗi, Meyasa ba za ka manta da abunda yawuce ba, ina magana kana share ni, kasan bana son hakan, Yana ƙona min rai” baisan sa’adda hawaye suka cigaba da wanke fuskarshi ba, muryarshi na ɗan rawa ya furta”?mommy saboda ni za ki zubar da hawayen ki”? Muryarta a kausashe tace”Shureim, how many times have I cried for you? I understand that you’re trying to drive me crazy,” Shureim ka daina ƙaunata” Tai maganar tana watsa hannayenta’ shiru Ya ɗanyi yana kallon fuskarta, tabbas ya ga 6acin rai acikinta.

“Astagfurillah” jin ya ambaci haka Yasa ta zaro idonta akan fuskarshi
“Mommy, I didn’t know you cared about me that much, I thought you’d stopped loving me, amma yanzu mommy akaina kike zubar da hawayenki”?

Mamakin kalaman shi ne yasa ta kafe shi da ido ba ƙyaftawa, Hadisi Ya soma janyo mata da ayoyin al’kur’ani mai girma waɗanda ke magana akan wanda Ya ƙuntatawa iyayen shi.

“Shureim ka sani kuma kake take sani? Shine Ka rufe ido Kana ƙuntata min? Meyasa”? Marairaice mata fuska yai”ya zanyi! Sharrin zuciyane da kuma sharrin shaiɗan, sune suke azalzalar zuciyata akan abunda Ya faru, sunƙi bari na manta komai,” Dafa kafaɗar shi tai da hannunta ɗaya”Ka yafe min shureim, nayi maka alƙawarin zan tarairaye ka na baka kulawa kamar yadda muke ada, Sannan inaso kamanta da abunda ya wuce, Ba laifin mu bane, mu ne sila, amma kaine ka aikata komai ba tare da ka yi shawara damu ba, kai kasan ba yadda za’ai da hankalin mu da tunanin mu mu goyi bayanka akan aikata hakan, a lokacin da ace ka yi shawara damu wlh shureim ba zamu goyi bayan abunda ka aikata ba” har cikin zuciyarta ta ke magana, Shi kanshi Yaji jikinshi yai sanyi, zuciyar shi ta karaya, tabbas maganar da ta faɗi gaskiya ne.

” Mommy, ni ne ya kamata na nemi yafiyarki, akan gudun ku da nake Yi ke da Daddy, Dan Allah ku yafe min, na gane kuskurena”

yai maganar yana ƙoƙarin zubewa saman gwiwowinsa da sauri ta ɗago da shi ta rungume shi tana ɗan bubbuga bayanshi da yatsun hannayenta, Farin ciki duk Ya cikata, ta manta when last ta ji ɗumin shureim a jikinta, saboda rashin jituwar dake a tsakanin su.

Muryar shi da alamun karaya ya furta mata”Mommy, ana ‘uhibuk kathiran” Hawayen da suka taru acikin idanuwanta ne suka soma gangarowa saman kuncin ta, still ba su raba jikinsu daga na juna ba, martanin maganarshi ta mayar mashi”i love u too My son, ba zan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, Shureim ka faranta min rai,” ta yi maganar tare da raba jikinsu daga na juna, fuskokin su ɗauke da murmushin ƙauna

“Idan har dagaske mun shirya inaso daga yau ka goge duk wasu hotunanta dake a cikin wayarka, kallonsu baida amfani shureim, saboda suke fama maka raunin dake a cikin zuciyar ka”

Shiru yai yana kallon fuskarta, har sai da ta kai ƙarshen maganar, Har ga Allah bai jin zai Iya goge hotonta a wayarshi, don ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya suke yi ba aduk lokacin da ya kalle su, Allah ya jarabce shi da ƙaunarta, Yafi sonta akan kowa na duniyar nan, duk da bata araye.

Gudun kada ta zarge shi, yasa shi yin saurin cewa”saboda farin Cikin ki mommy zan yi deleting ɗinsu, ni kaina bana son abunda zai ƙara shiga tsakanina da ke,”

Gyaɗa kai ta yi “Shureim ka ɗauko wayar ka goge su agabana In gani” tuni yasha jinin jikin shi, ba don yaso ba ya amsa mata da toh, slowly ya juya ya nufi gadon shi ya ɗauko wayar, Kafin Ya kai mata, wayar ta hau ruri, hakan ba ƙaramin daɗi yai mashi ba, Waiwayowa yai still tana a tsaye tana kallon shi”who’s calling u”? Ta jefa mashi tambayar, Nuna mata screen ɗin wayar ya yi sunan Daddy ne Ya bayyana akai” Umarni Ta bashi ya ɗaga kiran Ya kara wayar a kunanshi, Muryar Alhaji Ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi”Shureim Uncle ɗin ka na son ganin ka, gamu nan zamu shigo cikin gidan” muryarshi A sanyaye ya amshi mashi da toh, takaicin shi ɗaya layla taƙi tafiya, ta tsare shi da ido, adan dole sai ya goge hotunanta awayarshi.

A hankali ya zame wayar daga kunnan shi, matsawa yai kusa da ita, Bayan ya cire password Na wayar Ya miƙa mata adai dai kan Gallery ɗinshi, Ta kar6i wayar tana duba hotunan, Ta yi mamakin ganinsu kamar hauka, hada wanda ya ke a rungume da ita saman ƙirjinshi, ta6e baki layla tayi, hankalin shureim ba ƙaramin tashi yai ba ganin zata danna delete all, jikin shi har tsume ya ke yi.

“Assalamu alaikum”! Muryar zainab ce ta katse mata hanzarin ta, a sukwane ta juya tana binta da kallo, a bakin ƙofa ta tsaya”Alhaji ne ya shigo tare da kawun shureim, Shine yace nayi maki magana…” yatsina fuska layla tayi”Naji, ga ni nan zuwa” Miƙa wa shureim wayar tayi”ka tabbatar ga goge su, sannan ka fito ku gaisa da kawunka,” Amsa mata yai da toh, Bayan ya kar6i wayar, fitar ta keda wuya Ya cire memory ɗin wayar, Ya 6oye shi a cikin rigar pillow, Ajiyar zuciya ya sauke Ba ƙaramin daɗi yaji ba, don ji ya ke kamar za’a raba shi da ranshi idan akace ya goge hotunanta.

Toilet ya shiga ya wanko fuskarshi, Ya futo Ya nufi dressing mirror, cikin jerin turarurrukansa ya ɗauki ɗaya ya feshe shi a jikin shi, bayan ya ajiye ya fito daga ɗakin Ya nufi babban palourn.

*GIDAN ƊAN IYA*

Tun da ta fito daga cikin toilet ta ke a tsaye bakin wardrobe, daga ita sai Towel ɗaure a ƙirjinta, Ya sauko har saitin gwiwarta, a ƙalla Tafi ƙarfin mintuna goma, ba tare da ta motsa ba, idanuwanta na akan Jerin suturarta da ke a ninke sun sha guga, ba komai ne ya tsaida ta ba fa ce neman kayan da zasu dace da tarban Manyan baƙin su da zasu Yau, Ruwan ido take yi, duk kayan da ta ɗauko sai taga kamar ba zasu dace da ita ba, Wayarta dake a jiye saman drawer ce ta soma ringing, nan ta ke taji gabanta ya faɗi fatanta Allah yasa basu bane suka ƙaraso, Da ɗan saurinta ta nufi wayar tare da kai hannu ta ɗauketa, ko da ta duba screen ɗin wayar, babu sunan wanda ya kira, Baƙuwar number ce, kokwanto ta shiga yi akan ta ɗaga ko karta ɗaga? Don ita a tsarinta bata ɗaga baƙuwar number in dai ba wadda ta yi saving akan wayarta ba ce, kusan sau uku kiran nashigowa Yana yin rejecting ba tare da ta ɗaga shi ba, tayi kasaƙe kamar an dasa mata Aya,

Shigowa Cikin ɗakin Zahra ta yi, bakinta ɗauke da sallama, turkish gown ce a jikinta launin pink ba ƙaramin kyau tayi mata ba, tayi rolling veil saman kanta. Ganin Aneelerh a tsaye yasa tace”lafiya? Ya akai naga baki shirya ba? Ko kin manta cewa suna a hanya? Sun fa kusa isowa, Na rasa meke damunki, Ko har yanzu kewar baby junaid ɗin ce bata sake ki ba”? Harara Aneelerh ta ɗan jefa mata, Ba tare da tace koma ba, ta ɗaura wayarta saman mattress, kafin ta juya ta nufi wardrobe din Kayan da ta bari a buɗe.

“Zahra zo Ki tayani zabar kayan da zan sanya, Ruwan ido Ya hana ni ɗauka tun ɗazu” murmushi zahra ta saki yayin da take tunkarar wardrobe ɗin”Aunty aneelerh, shiga za ki yi ta mutunci, ta kece raini, Lace ko shadda su zasu fi dacewa, ” Ta yi maganar tare da Kai hannu cikin wardrobe ɗin kayan ta janyo mata wani haɗaɗɗan lace launin golden colour, ta miƙa ma Aneelerh, Fuskarta ɗauke da murmushi ta kar6i Kayan da zahra ta miƙa mata”na yadda ke ƙwararriyace a6angaren iya zabar kayan da zasu dace da mutun, nafi karfin 15 mins ina neman wanda zasu dace dani na kasa, sai da ki ka zo” Zahra tace”kada ki manta aikina ne, burina kiyi kyau auntyna, surukanki su ganki a mutuncenki, bari naje na ɗauko maki sarƙar da zata dace da kayan, ‘ amsa mata Aneelerh tayi da toh, Wuce wa zahra tayi agaban drawer chest Ta zuƙunna ta dauko mata jewelry box dinta, Ta buɗe ta lalubo mata necklace da earrings launin Lace ɗinta, maida box dinta tayi kafin ta miƙe ta daura mata su gaban mirror.

“Aunty aneelerh, Ga su nan saman mirror, Pls Ki shirya da wuri, Ni zan je na taya su mami shirya masu abincin”

Amsa mata ta yi da toh ta ƙara da yi mata godiya, Bayan fitar zahra, Aneelerh ta shirya tsaf cikin Lace ɗinta, riga da skirt, sun yi bala’in yi mata kyau, sun ɗan kama jikinta, shape ɗinta ya fito sosai, Kamar a jikinta aka ɗinka kayan, a gaban mirror ta zauna tana yin make up, lip gloss ta shafa ma la66anta, Ta ɗan shafa hoda, ta ɗauki brush tana gyara jagirarta, ‘ Sumar kanta Ta sauko har saman bayanta, ƙarar Shigowar text a wayarta ne yasa ta ɗan kalli 6angaren da wayar take ajiye saman gado, sai lokacin ta tuna da baƙuwar number da ake ta kiranta ɗazu, sai da ta fara Ɗaura dan kwalin leshin Kafin ta miƙe ta nufi wayar ta ɗauke ta, Da yatsan hannunta ta janyo sakon A hankali ya buɗe, Ta yi mamakin ganin Sunanta da aka rubuta da manyan haruffa, menene ma’anar sakon? Just Aneelerh? Wanene wannan? Kiran number ta soma ƙoƙarin Yi sai dai taƙi shiga, A ƙarshe ta hakura ta daurata saman pillow, Gaban Mirror ta koma ta ɗauki jerin turarurruka tana feshe jikin ta da su, tunawa da baby junaid ɗinta yasa ta ɗan saki murmushi, tayi missing ɗinshi sosai, yau tun da safe Mahboob Yaje kai shi school, Bayan ta haɗa da shi da kuɗin fetur, kusan sati biyu da fara zuwanshi makarantar, kullum da fara’a yake tafiya, yana zumuɗi, da zarar an kaishi Ya ke saka masu rigima sai sun dawo dashi gida, Har atashi daga school ɗin Yana yin kuka, Fuskarshi jawur ake dawo mata da shi. Malaman makarantar har sun canza mashi suna daga Junaid zuwa babyn mommy, saboda sunanta da yake yawan kira masu.

Daga waje tajiyo muryar Zahra tana kwaɗa mata kira”Aunty Aneelerh! ” girgiza kai tayi aranta tace”Ko yaushe ne zahra zata daina Yi min irin wannan kiran talaucin kamar zata ƙararmin da sunana”

Zahra na shigowa ɗakin ta Waro ido waje tana fadin”Wow!!! Tabarakallahu Ahsanul khaliqin Aunty aneelern kinga yadda ki kai kyau? Kamar wadda zata shiga gasar miss world,” harara Aneelerh ta jefa mata fuskarta asake tace”Naji na gode Da yabo, ni dai yanzu faɗa min Kiran menene kike yi min”? Watsa hannu Zahra Tayi”dama ummi ne ta aiko ni zaki ci abinci yanzu ko sai anjima idan sunzo”?
“Yunwa nake Ji zahra, ba zan Iya jira sai sun zo ba, ki samu plate ki zuba min dambun shinkafa, Ki haɗo min da lemu mai sanyi, ”
“Toh, Amma kafin nan mu ɗanyi selfy mana” ta yi maganar tare da Kunna camera din iphone nata, ta ɗaga Wayar Tare da ɗaura kanta saman kafaɗar Aneelerh, gaba ɗaya suka saki murmushi, ‘ kusan hotuna Biyar tayi masu atsaye kafin Ta nufi hanyar fita ɗakin tana faɗin”Idan surukan naki sunzo zamu ƙara yin wasu hotunan tare, Hakan Yana ƙara danƙon zumunci,” fuskar Aneelerh ɗauke da murmushi ta ke bin Bayan Zahra da kallo, gefen gadon ta zauna tana Jiran dawowarta.

*EVIL FOREST*

Tun da garin Allah Ya waye Masu a cikin ƙurmin dajin, Kowan nan su Ya farka, Da wata irin matsiyaciyar yunwa, suna zazzaune abakin bishiya sun jingina bayan su, Sai hamma suke Yi, Jiya basu ci abinci da yawa ba kafin Kwanta, sauran Kayan marmarin da suka rage ne su ka sha, dan ma suna da jumurin yunwa, Hankalin su ba akwance Yake ba, Danish Yaƙi farkawa daga bacci, tsawon awanni tun daren Jiya da Angel ta sanya shi yin bacci yake ta yi, Ko motsi Ba ya yi numfashinsa ne kaɗai ke fita, tun suna sa ran zai farka har sun fara tunanin Anya kuwa Lafiya? Baccin ya wuce na hankali, domin kuwa tuni safiya ta jima da wuce wa sun shiga tsakar rana. Sun tsare shi da ido suna kallon shi, A saman shimfiɗar da Angel ta yi mashi, ya ke a kwance sun ƙudundune shi da bargo, tuntuni su ka so su tada shi daga bacci amma Angel ta hana su, ita aganinta bai kamata su takura mashi ba, tsawon wata ɗaya baya runtsawa kullum shine yin gadinsu, Na yau kawai Ya samu ya runtsa ai bai kamata su katse mashi hutun shi ba.

“Angel Yunwa mu ke Ji” Parveen ce Ta yi maganar, Fuskarta A kumbure ga miyan bacci a gefe da gefen bakinta, sumar kanta A haukace take babu gyara kamar Ƴar mahaukaciya, Angel da ke Fuskantar su tana zaune daga gefen shimfiɗar Danish, fuskarta sam babu walwala, abun ya fara damunta ganin yaƙi farkawa fatanta Allah yasa baccin lafiya ne ya ke yi.
“Genie we are feeling hungry, pls cikina kukan Yunwa yake mini” Jemimah ce tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka, idon Angel akan fuskokinsu, Batul sai hamma take Yi, tana faman yamutsa fuskarta.

“Ki jaraba Tada shi mana, wata’ƙil Ya farka, Tun da kinga mu bamu san kan dajin nan ba, balle mu ce zamu shiga ciki mu nemo abinci” Naufal ne yai maganar muryarshi da kasala.

“Ni zan Iya zuwa na nemo mana abincin sai mu ci” Gabriel Ne yai maganar, hannunshi ɗaya asaman sumar kan Azeeza da ke kwance saman ƙirjin shi.

Girgiza kai Angel ta yi”A’a Gabriel, ba sai ka je ba, Danish ne kaɗai zai Iya shiga dajin nan Ya dawo ba tare da wani abu ya same shi ba,” bubbuga ƙafa jemimah tayi cikin shessheƙar kuka tace”wai genie Ya ki ke so Mu yi ne mu fa yunwa muke ji, Ki tada shi ki tada shi Kin ƙiya so kike mu mutu ko”?

Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan jemimah dake Yiwa angel faɗa, ita kanta Angel kallon nata take yi, ganin yadda ta 6ata fuska, Kumatuntu sun yi jawur da su tsabar fusata.
“Angel ku tada shi mana” Da sauri suka kalli Haris Da yai magana, Tun da su ka baro kurkuku, baya magana daga Eh sai a’a, su kaɗai ne abunda Yake iya furtawa, amma yau sai gashi yayi masu magana, sun ɗanyi mamaki kuma sunji daɗi ga dukkan alamu sauƙi ya samu
Saboda maganar Haris yasa ta kai hannu ta bubbugi kafadar Danish, Muryar ta ƙasa ƙasa take furta sunanshi”Danish wake up! Ka tashi suna jin yunwa,” shiru bai motsa ba, Kusan sau biyar tana yi mashi magana har acikin kunnanshi takai bakinta

Nan fa gabanta ya fara faɗuwa, Parveen tace”ki buge shi mana wata’ƙil ya farka” Ba tare da ta kalli parveen ba tace”bazan Iya ba” ta ambaci hakan tare da cigaba da kwala mashi kira.

“Angel nauyin bacci ne da shi, Ba haka yakamata Ki tayar dashi ba, let me help u, ” Gabriel ne ya ambaci Hakan, Sai da ya fara janye azeeza daga jikinshi, tukunna Ya matsa gaban shimfiɗar Danish, bubbuga kafadarshi ya yi Da ƙarfi haɗi da ambaton Sunanshi”Danish! Danish!” yadda yake kware murya hatta su kansu sautin Ya cikasu, amma wani iko na Allah Danish ko girgiza Bai yi ba, Zuciyar Angel a jagule ta ɗaura Kunnanta saitin ƙirjinshi Bayan ta yaye mashi bargon, jin heart beat ɗinsa yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya sai dai ta yi mamakin dalilin rashin farkawarshi, Hankalin sauran ƴan uwan Yaƙi kwanciya, Gaba ɗaya suka dawo kewaye da shimfidarshi Kowa Ya zuƙunna
Su Azeeza har sun fara shessheƙar kuka suna faɗin Wayyo Allah Danish ɗinmu meke damunka, dan Allah ka farka ka yi mana magana ko hankalin mu ya kwanta, Mu mun haƙura ma da abinci kai kawai muke so ka tashi.

“Ko dai suma ya yi ne? Ku duba cikin gorar ruwan mu idan akwai sauran ruwa ku ɗauko Mu yayyafa mashi” Gabriel ne yai maganar cikin rashin kwanciyar hankali, Angel tace”a’a kada ku watsa mashi ruwa, Zuciyarshi fa tana bugawa, bacci ya ke yi, kunsan Danish da nauyin bacci, Balle kuma da ya ɗauki tsawon kwanaki bai runtsa ba,’ ɗaya bayan ɗaya suke jogana kunnansu saman kirjinshi don su ji idan zuciyarshi na bugawa, Hankalinsu Ya ɗan kwanta da jin sautin heart beat din nashi.
“Nasan nan bada jimawa ba zai farka, Mu ɗan ƙara haƙuri” Miƙewa Jemimah tayi tare da bubbuga ƙafarta, abunka ga yaro ba haƙuri, Yunwa ce ta addabeta, Juyawa tayi gaba ɗaya suka bi bayanta da kallo, agaban korayen ciyayen dake shimfiɗe a wurin ta tsugunna, ta soma tsigowa tana turawa abaki tana ci, hakan da tayi ne ya tuna masu da Ganyen da ake basu a prison, aiko da sauri batul da Parveen da azeeza suka mimmiƙe agaban jamimah su ka zuƙunna kamar akuyoyi haka suke cizgar ciyawa suna ci, tsawa Angel da daka masu”Meye haka dan Allah? Kunsan wani irin ganye ne ku ke ci? Ku daina” a tsawace ta ƙarasa maganar, ta mike ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana kwace ciyawar da suka damƙa a hannun su, Fashe mata da kuka Parveen da jemimah su ka yi Nan take taji zuciyarta ta karya, cikin shessheƙar kuka suke faɗin ba za su iya jurewa ba, yunwa ce ta addabe su, ta taimaka tabar su su ci ganyen, suna jin daɗin shi ahaka.
Idanuwanta acike tab da ƙwalla tace”Is ok, Bari na shiga cikin dajin in nemo mana abincin da zamu ci,” miƙewa Gabriel yai”Zan bi ki Angel” girgiza mashi kai tai”A’a gabriel, Ka zauna ka kula da su Azeeza, Yanzu zan dawo” ba don yaso ba ya amsa mata da toh, Kallon sauran Ƴan uwan nasu tayi”Javed Naufal, Ku kula da su Azeeza, Yanzu zanje na dawo,” Naufal yace”meyasa zaki tafi ke kaɗai, bayan kin faɗa mana mu yi takatsantsan da dajin nan akwai mugayen halittun da zasu Iya cutar damu, why angel? Gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ke kaɗai ba, sai dai mu tafi mu duka,” Yai maganar tare da miƙewa, Javed ma Ya miƙe, haris ne kaɗai Ya rage a zaune yana sauraronsu.
Ita kanta gabanta faɗuwa yake yi gani ta ke yi kamar wani mugun abun zai iya faruwa da ita
Murmushi ta ƙaƙalo akan fuskarta duk don ta kwantar masu da hankulan su yasa tace”Bawani abu fa, da zarar nayi addu’a Allah zai tsare ni har inje in dawo lafiya, ku kwantar da hankalinku” girgiza kai Gabriel yai”bazai yiwu ba Angel, bana so wani abu ya same ki ta silar mu, idan har ba zaki bari mu bi ki ba, To ki bari Danish Ya farka Ya je da kanshi ya samo mana abincin….” tunkan ya ƙarasa maganar Angel tai saurin katse shi da cewa”su Azeeza yunwa su ke Ji, Na yadda Gabriel Ka raka ni mu tafi, ku kuma ku zauna yanzu zamu dawo” Hankalinsu ya ɗan kwanta, Atare da Gabriel Suka nufi Cikin dajin, Hannunta ruƙe da ƙaramin kwandon su, komawa su azeeza su ka yi abakin bishiya suna zaman jiran dawowarsu.

Cikin dajin suka kutsa suna tafiya suna dan tattauna fira a tsakaninsu, ta ko’ina bishiyoyine masu tsayi Da faɗi, Rassansu sun lullu6e wurin da inuwar su.

“Hankalinka ya kwanta ka biyo ni, ni ban san ma ina zamu dosa ba, Ka ta6a shiga daji”? Ta jefa mashi tambaya, girgiza mata kai yai alamar a’a”bazan Iya tunawa ba Angel, na manta da komai na rayuwata, amma inaji araina koda ace ban ta6a shigowa daji ba, zai iya yiwuwa na ta6a kallon shi a waya, Ni yanzu burina mu fita daga Cikin Dajin nan, Ko mun samu mu tona asirin zaluncin da ake yi a cikin kurkukun ƙaddara, Angel na damu da rashin ƴar uwata, ina tsoron kafin mu yi nasara su kashe min ita” yayin da yake yin maganar yanayin fuskarshi ne Ya canza, abun ba ƙaramin ta6a zuciyarshi yake yi ba duk in ya tuna da ƴar uwarshi Gabriellah.
Cikin nuna jin tausayin shi angel tace”ka kwantar da hankalin ka, Idan Allah yasa mai tsawaicin kwanace zamu ganta, in kuma ta riga mu gidan gaskiya, Allah Ya jiƙanta, yana daga cikin ƙaddarar bawa, ba dole ya rayu da abunda ya ke so ba, wata rana ma kowa zai mutu ba wanda za’a bari gadin duniyar…….” fira ta yi daɗi sai nutsawa suke Yi, cikin Dajin ba tare da sunsan inda zasu dosa ba, Ga wata iska mai daɗi da ta ke kaɗawa, wasa wasa Ƙarfin iskar sai ƙaruwa ya ke Yi, ta cika masu idanuwansu daƙyar suke buɗe su.

Yayin da su Angel suka tafi nemo masu abinci, Sun yi zazzaune zaman jiran tsammani, Har sun fara lumshe idanuwan su saboda iskar dake kaɗa masu ba ƙaramin kasala take haifar masu ba, kwatsam! Ba zato ba tsammani kunnuwansu suka soma Jiyo masu wani irin sautin gurnani mai matuƙar rikitarwa da razanarwa, A firgice suka ware idanuwansu, Yayin da zuciyarsu ke buguwa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zata 6allo ƙirjin su, tsananin tsorone Ya kamasu sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansu suke Yi, a ƙoƙarinsu na su gano ta inda sautin gurnani ke fitowa, sai dai sun kasa sani kuma sun kasa ta6uka komai, Azeeza tuni ta shige ma Batul kamar zata koma Cikinta, Jikin su sai faman yin kakarwa yake yi saboda gurnanin ya cika kunnuwansu, Haris dake azaune gaban shimfiɗar Danish muryar shi adabarbarce ya ke ambaton sunanshi”da..da..nish ka tashi, pls ka tashi danish, Wani abu yana tunkaro mu’ Da rarrafe su batul suka ƙarasa gaban shimfiɗar Danish, Cikin fitar hayyaci suke bugun Jikinshi don ya farka ya ceci rayuwarsu, duk sun bi sun ruɗe tsigar Jikinsu ta tashi haiƙam, Har suna haɗa baki wurin ambaton sunanshi”Danish mun shiga uku, dan Allah ka farka, Wannan wani irin sauti ne haka babu daɗin ji, ga Angel bata nan sun tafi tare da Gabriel, Ni dama nasan zai yi wuya mu bar dajin nan da ran mu’ cikin shessheƙar ku ka suke magana hawaye na bin fuskokinsu, Jemimah da azeeza tuni sun rushe da kuka mai sautin gaske, tunkafin ma suga menene ke tunkarosu, sautin kukansu Jemimah shiya ƙara Janyo hankalin Abunda ke nufo su, basu san sune suke Janyo shi ba, babu wanda yai hankalin Ya tsawatar da su akan su daina Yin kukan suyi shiru, ba su yi tunanin yin hakan ba, lokacin da sautin gurnani ya ƙarfafa hatta ganyayyakin dake a wurin Girgixa suke yi, nan take idanuwansu suka tsaya cak akan wurin da suke zargin zai 6ullo, Kamar An Jeho suka faɗo ƙasan wurin, wasu irin Mugayen Halittun namun dawa, masu gashi gashi a jikinsu babu kyan gani gwanin ban ƙyama, Suffarsu tamkar ta majici sai dai sun gurmi maciji a halitta tsaf zasu Iya haɗiye mutun su nannade shi a cikin bakunansu, Tashin hankalin da ba’a sama shi Date, Wata irin gigitacciyar ƙara suka fasa, Ganin Yadda halittun suke Kurɗaɗowa saƙo da lungu masu Yawan gaske gasu manya manya, Gadan gadan suke tunkarosu Harwani nannaɗe Jikinsu suke yi suna harɗewa, tsabar firgi da tsoro ne yasa suka Watsa da gudun gaske kamar zasu Tashi sama, Gudu su ke yi na fitar hayyaci, gudun ceton rai, su kan su basu son Inda zasu dosa ba, wani ƙarin tashin hankalin Halittun da gudu suke binsu, Ga sauri da Allah yai masu, sun fuskanci matsanancin tashin hankali mara misaltuwa, musamman ƙananun cikinsu Azeeza da jemimah duk sun tarwatse kowa Da inda nufa, dan bala’i, Halittun suna lura da kowace kusurwa suka faɗa, Yadda suka raba kawunansu haka suma halittun su ka karkasa kawunansu wurin binsu, Haris da ba ƙoshin lafiya gare shi ba, tuni Numfashin shi ya soma sarƙewa, bakinshi ya soma fitar da jini, Gashi kowa Ya watse sun barshi, Yana ji yana gani halittar nan Ta ta taɗiye ƙafarshi gaba ɗaya ya kife ƙasa, tana gurnani ta wage bakinta masu haƙora a jere babu kyan gani, ta Zurma ƙafafuwanshi…..Innalillah

A 6angaren Azeeza da ke ruƙe da jemimah suna tiƙar gudu, hada tuntu6e sun rasa ina zasu dosa, Jemimah sai kuka take yi tana ambaton sunan Genie, Cikin rashin sanya Wasu muggan ƙayoyi suka Sargaho ƙafafuwansu kusan atare suka rubza ƙasa kansu ya daku.

A 6angaren Batul da parveen da Hannah da suka nufi Hanya ɗaya, Halittun nan sai binsu suke yi, sun rasa ina zasu dosa, suna gudu Sumar kansu Na rufe Masu idanuwansu, ba zato ba tsammani ƙafafuwansu suka zurma a cikin wani rami da ca6ali ya cika shi, gaba ɗaya su ka nutse cikin shi, Ko numfashi basu Iya fitarwa.

Idan muka Koma 6angaren Angel da Gabriel, lokacin da suka ƙaraso bakin wata bishiyar Mangaro sun tsaya suna tunanin hawa saman bishiyar don su tsigo su, atare suka haye suna aikin tsinkar magaro, sai da suka gama ɗibarshi a cikin kwando, Gabriel na yunƙurin zura ƙafarshi Ya sauko ƙasa kwatsam idanuwanshi suka sauka akan kurar dake ƙasan bishiyar tana cin wani namun dawa data kamo, wahalallan yawu ya haɗiya tare da kallon Angel, ita sam bata lura da abunda ya hango ba,
“Gabriel mu sauko mana, Suna jiran mu” Muryarshi Na kakarwa yace”Angel mun shiga uku, wlh kura ce a ƙasa take cin nama,” Sai lokacin ta wurga Idanuwanta ƙasan bishiyar, Gabanta yai mugun bugu, muryarta da tashin hankali ta furta Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Kafin Gabriel ya furta wani abu daga can cikin Dajin ihun muryar Naufal Ta karaɗe kunnuwan su, Kallon Juna su ka yi nan ta ke su ka fahimci babu lafiya a wurin Ƴan uwan su, zufa tuni ta wanke fuskarsu, ganin tana yunƙurin sauka yasa gabriel damƙo hannunta, muryarshi a hargitse yace”Kada ki sauka angel kashe ki za ta yi” Girgiza mashi kai tayi idanuwanta sun rikiɗa jawur dasu tace”ƙwara ta cinye ni, wlh sai naje wurin ƴan uwana, Baka ji ihun naufal ba, Allah kaɗai yasan meke faruwa dasu” kokawa suka soma yi da Gabriel a saman bishiyar, ya hana ta saukowa sai kiciniyar kwace kanta ta ke yi, aiko Suna cikin Yin kokawar nan Gaba ɗayansu suka ƙundumo ƙasa agaban kurar nan, Bakin ta ca6a ca6a da jini, Kafin ta ɗago da ido ta kallesu, Da iya ƙarfinsu na ƙarshe suka yunƙura suka miƙe a guje suka watsa, da gudu itama kurar tabisu tana gurnani, babu wanda bai fita hayyacin shi ba, lokacin da suka faɗo wurin da suka bar su azeeza hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, gabin babu kowa ga kuma Danish a kwance yana ta sharar baccin shi. Kafin Angel tayi yunƙurin zuwa wuri shi kurar nan ta dako uban tsalle ta faɗo masu, Da ƙarfi gabriel Ya fusgi hannunta tana kuka tana ambaton sunan danish Tana miƙa hannu yaja ta da gudu, wani iko na Allah kurar ta tsalle Danish tabisu da gudu, su kawai ta ke hari, kurɗaɗawa suka yi cikin dajin suna gudun famfalaki Kura ta zamar masu masifa ta hanasu sakat………”

*Boss Bature✍️*

Tun bayan da dr shureim ya fito daga bedroom ɗinshi ya nufi Palour, A zazzaune ya samu Alhaji ubaid tare da Uncle musa zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Layla tana a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, Idon shi na akan Uncle ɗin nashi, Ya ɗauki wankan tsadaddiyar shadda mai ɗaukar ido, ƙamshin turaren shi Ya cika palourn, idanuwanshi suna a lumshe, hannun shi na dama haɗaɗɗiyar agogon diamond ce wadda a ƙalla price ɗinta ya kai 300m, mutunne mai ji da naira, hutu ya zauna mashi ko Alhaji ubaid ba zai nuna mashi tarin dukiya ba, ko a muƙami bai kai shi matsayi ba, Alhaji musa ƙanine ga Alhaji ubaid uwa ɗaya uba ɗaya, kuma shine former president, akwai tazarar shekaru a tsakaninsu, A kyawun halitta Musa ya zarce Alhaji ubaid, Yana da hasken fata yayin da Alhaji ubaid yake da duhun fata, Sannan yana da Yalwatacciyar sumar kai tasha gyara ga sajen gefe da gefen fuskarshi baƙi wulik, Kamar matashin saurayi. Ya iya ɗaukar wanka ga aji ga kuma ji da kai.
Daga ƙasan carpet dr Shureim ya zauna cikin girmamawa ya gaishe dasu, Alhaji ubaid ne kaɗai ya amsa mashi, kawun nashi kuwa ko arziƙin kallo bai samu ba, har sai da hajiya layla tace mashi”baka ji shureim yana gashe ka ba”? Ba tare daya buɗe idon shi ba yace”Naji,” sanin halin shi yasa Shureim bai damu ba, Layla dai ce ranta ya 6aci dama ita bata iya 6oye fushin ta, Alhaji ubaid ko murmushi ne akan fuskarshi, Har yau mamakin Halin Ƙanin nashi Yake yi.

“Shureim, kasan shi fa mutumin turaine ba haka yake son ka gaishe shi ba, Ka matsa kusa dashi yaji ɗumin ɗanshi a jikin shi” acewar Alhaji ubaid,

Yatsina fuska layla tayi, aranta kuma ji take kamar ta shaƙe wuyan Alhaji musa, jin kanshi na matuƙar ƙona mata rai, miƙewa shureim yai tare da nufar sofa ɗin da musa ya ke a hakimce, ya zauna daga ƙasa,
“Uncle sannu da zuwa, Ya gajiyar tafiya” sai lokacin ya ɗan ware idanuwanshi tare da kallon shureim na tsawon mintuna, sai da ya mula ya sha iska tukunna ya soma magana
“Babu gajiya atare da ni, kai zanyiwa sannu, ni banzo da niyar in ganka ba, banma yi tunanin kana a ƙasar ba, sai da Ya ya ya ke faɗamin, shureim kafi ƙarfin ka tako kazo gidana ne? Laifin hada ni ya shafa kenan”? Tun da ya soma magana, hajiya layla take jifar shi da harara a fakaice batare da ta bari Alhaji ubaid ya gani ba, ita sam baya burgeta, haushin nuna isar da yake yi take ji,
“Ay min afwa Uncle, bani da kwanciyar hankali ne shiyasa bana samun damar zuwa, amma kuna araina,”
Ta6e baki Alhaji musa yai ba tare da ya furta kalma ba

Hajiya layla tace”To ai kaima ɗin baka damu dashi ba, Ba ka neman shi taya zai yi tunanin kana buƙatar ganin shi a gidan ka……” bata ƙarasa maganar ba, da sauri ta dakata ganin irin kallon da Alhaji ubaid ya ke jefa mata, sam baya son tana shiga tsakanin shureim da ƙanin shi, saboda mugun son shi ya ke yi baya son 6acin ranshi.

“Kare shi za ki yi”? Alhaji musa ne yai maganar sautin muryar shi a kausashe, Shiru tayi bata tanka mashi ba,
“Kada ki shiga tsakanin Uba da ɗansa, Kija baki kiyi shiru” Alhaji ubaid ne yai maganar, Ta6e baki tayi tana faman hura hanci.
“Ae da kabarta yaya ta ƙarasa maganarta,” yai maganar fuskarshi ɗauke da murmushi. Kafin ya kawar da idonshi daga kallonta.

“Shureim, Idan na tashi tafiya abuja atare da kai zamu tafi, bazan barka a gidan nan ba, don Na fahimci akwai masu takura maka, Shiyasa duk ka rame kayi duhu,” Cikin kulawa yake yi mashi maganar, hannun shi ɗaya asaman kafaɗar dr shureim ɗin, Layla ta yi mamakin jin abunda yace, mutumin da ko ƴa’ƴan shi bai sakar masu fuska shine ya ke zancen zai tafi da shureim, kwa6e fuska ta yi don ta fahimci so ya ke ya ƙuntata mata.

Alhaji ubaid yana murmushi yace”naji dadin jin hakan, wata’ƙil idan kuka je can yafi sakewa, don na fahimci shureim baya son zama gida…” kafin ya ƙarasa maganar, layla ta katse shi da cewa ”ae sai ku tsaya kuji ra’ayin shi ko? Idan ya ce yana son zuwa can ɗin,” Tana rufe baki Alhaji musa yace”ai ba shawara nake nema dashi ba, Umarni ne” Cikin isa Ya furta hakan, Kafin ya kalli dr shureim, ka shirya komai naka idan muka tashi tafiya atare zamu tafi”

Lamarin ya ɗaure mata kai, shi dai Dr shureim yai shiru bai tanka masu ba, Girgiza kai Hajiya layla tayi’bazai yiwuwa ba, haba dan Allah duka yaushe muka samu shureim ɗin ya dawo wurin mu, Sannan kuma yanzu kace zaka tafi dashi? Aɗan bari ya huta mana, Shi kaɗai fa nake gani inji daɗi,” rai a6ace take magana, Sun natsu suna sauraronta, sai da takai ƙarshen Aya tukunna Alhaji ubaid yace da ita”meye na tada jijiyoyin wuya? Guduwa zai yi dashi ne? Bafa raba ki zaiyi dashi ba, Yana so ya zauna gidan shi na ɗan wani lokaci,” fuskar Alhaji musa aɗaure yace”idan na ga dama zaici gaba da zama awurina ne kuma ke baki isa ki hana shi ba” murmushin fuskar Alhaji ubaid bai washe ba yace”ba girmanku bane ku tsaya kuna sa’insa akan Shureim sai kace wani ƙaramin yaro, ko da ya ke laifin ka ne shureim tuntuni nake baka shawarar kayi aure ka ƙi yi, da ace kana da Iyali babu wanda ya isa yai iko da kai” da zolaya yayi maganar, Shureim dai ya natsu yana jinsu, Ya jima yana jin takaici yadda rayuwa ta canza mashi, Ya koma tamkar ƙaramin yaro a idon kowa, saboda raunin zuciyarshi.

daƙyar Alhaji ubaid ya samu Ya maida sa’in sar tasu Wasa, dama can basu jituwa tsakanin Layla da ƙanin shi tunfil azal.
“Yakamata mu tashi muje muci abinci, zainab ta shirya mana a dining” layla ce tayi maganar, Ɗaya bayan ɗaya suka miƙe tare da nufar Dining room.

*Kaɗan daga Cikin Na sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya*

*Evil forest*

Sautin Ƙarar Danƙararen Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin Ƙasar america ne Ya karaɗe ko’ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza suke yi saboda ƙarfin iskar fankar Jirgin, Shawagi jirgin yake yi a saman Iska Yana kewaye ko’ina na tsawon mintuna talatin, Yayin da Hot soldiers din dake a tsaye saman jirgin cikin shigarsu Ta ka ki sun ɗaura ɗamarar Yaki, Sai dai ga dukkan alamu Sun kammala gudanar da abunda Ya kawo su Cikin Dajin, Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar helicopter ɗin Hannun shi ruƙe da tactic phone Wayar da sojoji suke yin amfani da ita wurin yin sadarwa ga Manyansu dake acan Headquater, Cikin Harshen turancin Yake Yin magana muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin

“We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest.”

Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya fito……, Nima kuma na ajiye alƙalamina.

 

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button