Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 48

Sponsored Links

Ikraam~ ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 48…… A tare Khaleel da Aliyu suka shiga dakin Mami, Ikram na xaune gefenta tana cin Apple tana bata lbrin practical din da suka yi a Basic science, Mami ta galla ma Khaleel harara tace “me Ikram tayi mka ka jefeta?” Khaleel ya xaro ido yana kallon Aliyu yace “kaji wae na jefeta Aliyu, wllh Mami ban jefeta ba karya take min” Ikram ta murguda masa baki tace “to ba da jifana kke so kayi ba na gudu” Aliyu yyi murmushi ya karaso cikin dakin ya xauna ya gaida Mami, Mami ta amsa tace “ya gida” yace “lfya lau Mami” Khaleel dake kallon Ikram har lkcn yyi kwafa ya karaso cikin dakin, Ikram tace “Mami kina jin abinda yyi min ko” Mami ta harareta tace “rufe min baki” sunkuyar da kanta tayi, Khaleel ya gaida Maminsa, tace “sae ynxu kasan na dawo” yyi murmushi yace “yi hkuri Mami, ina shirin fitowa wancan ta shigo tana min rashin kunya” Ikram ta dago kanta da sauri ta fashe da kuka ta mike tana nuna sa cikin tsawa tace “kai ne kke min rashin kunya, kai ne kke min rashin kunya, kuma daga yau ba ruwana da kai, ba ruwana da kai, kar ka sake kiran sunana Ikram, kar ka sake…..” tsawa Mami ta daka mata, Khaleel ya dinga dariya har da sakkowa daga kujera, Aliyu dae shiru yyi yana kallonta, hanyar fita tayi daga dakin da sauri tana kuka, Mami tace “dawo nn” dawowa tayi ta rungume hannayenta tana kuka kanta a kasa, Mami ta ci gaba da abinda take, a xuciyarta tunanin irin masifar Ikram kawae take, Masifaffiyace ta karshe, abun har tsoro yake ba Mami, Aliyu ya mike ya fita daga dakin, Mami ta juya tana kallon Khaleel dake ta dariya har lkcn, tayi masa mugun kallo tace “fice min a daki” ba musu ya mike ya fita, ta kamo hannun Ikram tana kallonta tace “ba nace ki daina ihu ba Ikram, kuma ba na hanaki wasa da shi ba” ta fashe da kuka tace “shine sae yyi ta neman tsokanana” Mami ta rungumeta tace “to ya isa, kyaleni da shi kawae, xanyi maganinsa, amma ki daina masa rashin kunya kinji” kai kawae ta gyada mata har lkcn tana hawaye, Mami ta share mata fuskarta ta xaunar da ita gefenta, hannunta Mami ta daga tana kallo tace “ina abinda Abbanki ya sa maki a hannnun ki?” Ikram na kallon wrist dinta tace “na cire da safe, Mami ni bana son abun, kuma na gaya ma Ammi jiya tace in cire idan muka xo gida” Mami tace “maxa je ki ki sa, kar ki sake cewa baki so kuma” mikewa tayi ta nufi drawern Mami. Karfe goma Aliyu ya shigo dakin Mami xae wuce, Ikram tayi bacci lkcn, Mami dake gaban computer har lkcn tace “baxa ka kwana ba” girgixa mata kai yyi yace “A’a gida xan wuce Mami” Mami ta juya tana kallonsa tace “to shknn Allah ya kai mu Aliyu” yace “Ameen” har ya bude kofa xae fita ta kirasa, ya juyo yana kallonta, ganin bata ce komai ba yasa ya dawo kusa da ita yace “Na’am Mami” kujera ta nuna masa ya xauna yana kallonta, tace “ka gaya min meye Matsalarka Aliyu, yhu re nt yhur self now adayz, nasan ko wanene kai, tel me yhur prblm dear.” shiru yyi yana kallonta snn ya sunkuyar da kansa, bayan kmr minti uku tace “to tashi kaje, Allah ya rufa asiri son”
[2/25, 08:35] Zjy: Khaleesat Haiydar

Back to top button