Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 37-38

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*37&38*

 

 

……..Tunda shariff yaji Amaan tayi zancen Nasir Acikin labarinta yaji wani irin mik’i yataso masa a k’ahon zuci”dakewa kawai yayi yana sauraronta”gefen zuciyarsa kuma tausayinta ne da tsanar Anty zabba’u….masha Allah! hak’ik’a kinga rayuwa kuma kinga jarabawa”sai muyi fatan Allah yasa k’arshen Abin kenan”Atak’aice yanada kyau ki yawaita yin Azkhar da Addua idan zaki fita daga gida”sannan ki dinga Addu’ar kwanciya bacci”insha Allah kika kiyaye haka babu mugun daya Isa yacutar dake wala mutum ko Aljan”cewar mlm yana mik’ewa tsaye ya musu sallama suka fita shida mus’ab”shariff ya mik’e tsaye yabisu”sai sannan Ammi ta sauke Ajiyar zuciya ta kamo hannun Amaan ,ta aza kanta saman cinyar ta Ahankali tace”komai ya wuce ki dena kuka kinji ko?”zuwa goben insha Allah idan kin rik’e number d’in wasu daga cikin su saiki bayar Akira muyi mgn”nifa Ammi babu ruwana dasu tunda basu nemeni ba…kin manta mlm yace”suma ta rufe bakinsu karsu nemeki?”saidai nasan zuwa yanzun suma nasu sihirin data musu ya k’arye”zasu fara nemanki daga yanzun har zuwa gobe”to Ammi zan bada number d’in mommy sai Akira ta”kuma ni banice zanyi mgn dasuba da hamma zasuyi….shiru tayi sbd jin k’asaitacciyar muryar shariff yayi sallama”Aransa yace “sbd gulma shine tana mgn daga jin na shigo tayi shiru”ita komai sai tayiwa mutane shagwab’a”kan kujerah ya zauna yayi shiru yana danna waya”Aka maka coffee ne?”cewar Ammi sbd tasan dai ba mgn zaiyi ba saidai a tambayesa”Eh Ammi harda fruits idan Akwa”janye kanta Amaan tayi daga saman cinyar Ammi tace”Ammi kiyi zamanki bara naje na had’a masa”to shikenan Amaan dama bacci nakeji bara naje na kwanta”idan kin kamasa ya gama saiki kashe kayan kallon kije ki kwanta”dato ta Amsa ta wuce kitchen”shariff dake zaune yana jinsu sai yaji sun burgesa sbd sunyi kamar uwa da y’arta”Amma d’an zafin kan sai kicin kicin da fuska yayi ya kalli Ammi yace “kin yadda da tsabtarta ne Ammi?”bansan meye zance maka ba shariff”Amaan daice ko ? to kunfi kusa”idanma tsakaninku aka shiga Anjima zaku shirya”tana fad’in hakan ta mik’e tsaye ta wuce d’aki “shi kuma ya d’auki remote ya canza channel zuwa sunnah TV”Ahaka Amaan ta fito daga cikin kitchen d’in tana rik’e da tray”cup d’in coffee d’in na gefe sai plate d’in data zubo fruits d’in, sai goran ruwa da cup gefe”saman center table ta Ajiye masa tana fad’in hamma gashi”beyi mgn ba yadai kalleta sau d’aya ya maida hankalinsa wajen TV”zama kan kujera tayi ta sauke b’oyayyar Ajiyar zuciya tana yin tagumi….ki cire wannan tagumin”taji sautin sanyayyar muryarsa “ta janye da sauri tana satar kallon sa”Aranta tace” yanada kyau sosai”hamma ba yanzun zaka sha bane?”kin bani ne dama?”yamaido mata tambayar hankalinsa na wajen TV “sosai yabata mamaki”saita basar dashi kawai tana tunanin wane irin zafin kaine dashi wai?”idan bazaki baniba kwashe Abinki kije ki kwanta”batace komaiba ta taso ta d’auki cup d’in ta matsa ta zauna gefensa tana fad’in gashi”beyi mgn ba ya Amsa”d’an kurb’a yayi ya lumshe idanuwansa….yayi dad’i?”tab’e baki yayi yana girgiza kansa”Allah yayi dad’i baka san fad’a ne kawai”ta fad’a cikin shagwab’a”cigaba da kurb’a yayi batare daya tankataba….ita kuma tanata kallonsa Ab’oye”pls malama ki dena kallonah karki saka na k’ware mana”uhmm kai tayaya kasan Ina kallonka?”fatana ka gama na kashe kayan kallon naje na kwanta”dama na rik’ekine balle ki jiran?”uhmm sbd Ammi tace”na kashe kayan kallon shiyasa na tsaya”kuma Allah saika tashi tunda parlourn ka Akwai kayan kallo ba sai kayi Acan ba….shiru tayi sbd ganin ya matso dab da ita”ta d’an matsa da sauri”yatab’e baki yana nufar bakinta zai bata sauran coffee d’in daya rage”wayyo hamma ni bana sha”sai kin shashi Allah “toni kawai saika bani sauranka?”kallonta yayi yasaki murmushin gefen baki”wanda yayi masa masifar kyau yace”kinsan Allah koki Amsa ta Arzik’i kona rik’eki na miki d’ura bbu ruwana”itadai kallonsa kawai takeyi”gaba d’aya yamata wani irin kyau”itama da murmushin saman fuskarta tace”to hamma wai miye ribarka idan nasha?”tab’e baki yayi yace”babu, Amma kafin in k’irga ukku wlh ki Amsa”1,2’3.…..da sauri ta Amsa ta shanye”yayi y’ar dariya me sauti yana fad’in kinsan wani abu ?”ta girgiza kanta”dama na cikin baki nane na maido a cup d’in kika shanye….uhmm ! hamma kenan” bbu komai ni bana gudun komai naka”yanzun ka shanye fruits d’in”ko kuwa naje na kwanta?”d’an girgiza mata kansa yayi cikin wani bak’on yanayi yace “ban sallameki ba”batace komai ba ta matso da center table d’in gabansu tace”to bissimillah! beyi mgn ba sai wayarsa daya Azo mata saman cinyarta”tabi wayar da kallo tana d’auka”pic natane tana d’auke da teddy nata tana dariya”d’an murmushi tasaki tace”wayyo hamma nasan nayi Abinda be kama taba ko?”kina dai shirme da saurin b’arema mutane baki kiyi kuka”turo baki tayi tak’i mgn “kinji?hmm! bece komai yaci gaba da shan fruits d’in ita kuma tanata masa latse latse Awaya”Ahaka sadeeq ya shigo cikin parlourn da sallama”shariff ya Amsa masa ya masu barka da hutawa kafin yace”Amaan ya jikin naki?”Ana miki mgn fa”cewar shariff “da sauri tace”da sauk’i yaya sadeeq “bece komai ba ya wuce sama”Ahanakali tace”wlh mantawa nakeyi da wannan sunan da kuke kirana dashi”to yanzun kin tuna ko?”nidai Allah ka kirani da salma ta mana”da Amaan nayi niyar kiranki”kasan ko hamma?”duk me suna yaya sadeeq bbu ruwana dashi”dan hamma sadeeq mugu ne yayita sani kuka”shima na nan gidan bakida ruwa da shi?”Eh mana…. ringing d’in wayarsa yasaka ta mik’a masa wayar tana fad’in yaya mus’ab ne”tab’e baki yayi ya d’auki wayar yak’i yin mgn “mus’ab na dariya yace”dan Allah ka k’yale y’ar mutane taje tayi bacci”raina yabani kana lik’e kusa da ita….doguwar tsuka yaja yana fad’in banza d’an sa Ido”daga haka ya yanke wayar….bacci kikeji?”uhmm! toni kuma ba yanzun zaki kwantaba”Ayya hamma bbu kyau mugunta”gaba d’aya tunda nadawo hayyacina baka wani tattalinah sai mugunta kakemun ko?”ta fad’a cikin shagwab’a”kasa mgn yayi ya mik’e tsaye”itama tsayen ta mik’e ta d’auki tray d’in “muje ka rakani na maida tray d’in”ji yayi bazai iya mata musu ba”saiya bita suka nufi cikin kitchen d’in”bayan ta Ajiye komai tace”harda d’akin Ammi zaka rakani”beyi mgn ba yana dai tsaye yana danna waya”hamma! kallonta yayi”ta sunkuyyar dakai “me kikeso?”bakai bane sai Ayita mgn kayi shiru”nima Allah na iya k’yaliya”ko yaya Nasir idan yazo wajena sai yayi zaman Awa guda batare danace komai ba” saidai yayita zaman…..doguwar tsuka yaja yafice daga cikin kitchen d’in”mamaki da Al’ajabin yabama Amaan “saidai ranta yab’aci”tasha Alwashin gobe insha Allah zatayi waya da safe zuwa yamma iyayenta sun iso washe gari su bar musu gidansu”kodan yaga sunada kud’i shine zai mata haka?”zuciyarta ajagule ta fito daga cikin kitchen d’in ta kashe kayan kallon da hasken d’akin ta wuce d’aki tayi shirin kwanciya bacci”lokacin Ammi ta jima dayin bacci”tunda ta kwanta juye juye kawai da tunane tunane takeyi”tsakin da shariff yamata yak’i barin zuciyarta”da k’yar ta samu tayi bacci….. shariff kuwa ba Amaan ta bashi haushi ba kalamanta datayi game da nasir sune suka bashi haushi har suka fusatashi yayi tsakin”bayan yakoma side d’insa ya shiga wanka”yana wankan yana tunani”damuwarsa Amaan tayi fushi dashi”sbd ya fahimci bataji dad’in tsakin daya mata ba”koda yafito ya shirya ya kwanta yajima yana tunani sannan yayi bacci…..washe gari sai wajen bakwai da y’an mintinah ya tashi”Agaggauce ya sauka daga saman bed d’in yanufi bath room yayo Alwallah….sadda yagama sallah da Adduo’in sa har 7: 45 tayi”gaba d’aya tunanin Amaan ne mak’ale Acikin zuciyarsa”yana sanye da milk d’in gogaggiyar jallabiya ya sakko down stairs d’in”k’amshin girki me dad’i yacika parlourn”ya lumshe Ido,yabi Abdallah da sadeeq da kallo sunata break fast basuma lura dashi ba”da Alama kome suke ci ya musu dad’i”ya Ayyanah haka Aransa”bebi takan suba yanufi d’akin Ammi “Anutse yashigo da sallama”Amaan na tsaye da doguwar riga gownt Ajikinta, kanta bbu d’an kwali ta juya baya tana shirya kayan Ammi dana ta cikin ward rope” da jummai me Aiki ta kawo daga wajen wanki da guga”yayinda Ammin ke zaune gefen bed tana shafa Mai da Alama daga wanka ta fito”Amaan najin sallamarsa k’irjinta yabuga “tana jin yana gaida Ammi”daurewa tayi sbd ganin idon mahaifiyarsa ta juyo ta duk’a tace”Ina kwana?”kallo d’aya yamata ya fahimci fushi takeyi dashi”lafiya qlau”zo muje ki gyaramun d’akina kafin na gama break fast…..ah ah gaskiya shariff ka barta ta huta “tunda muka sallame sallar Asuba yarinyar nan ta keta Aiki”ko break fast ita kad’ai ta had’a tace na kwanta na huta”ga kayanmu tana shiryawa idan ta idar wanka da break zatayi…..lah Ammi nifa ban gajiba zan gyara masa”shidai tsaye yayi yana so su had’a Ido da ita Amma tak’i yarda”ita kanta Ammi har kunya taji sun bata”sbd ganin Shariff yayi tsaye yanata kallon Amaan yak’i tafiya”sai cewa tayi kaje mana zatazo idan ta idar”wai Ammi duk dan sbd y’ar taki kike korata?”Eh yason ranka ne?babu komai Ai zata tafi ko?”koda na tafi zan dinga zuwa Ina miki kwana 2 Ai”rabu dashi Amaan zancen yakeso”shariff bece komai ba yafita”Ammi tace”idan kin gama kimtsawar Anjiman saiki kira sud’in ko?”dato ta Amsa tana rufe ward d’in “ta d’auki mini hijab tasaka ta fito daga cikin d’akin”su ukku duk suna dining area d’in suna break fast “Abdallah na ganinta yace”Anty Amaan dama haka kika iya girki?”d’an murmushi tayi batace komai ba”sadeeq yace”pls kimana lunch Anjima ma”dadai Abdallah keso dana masa Amma banda kai tunda sunanka yaya sadeeq “ta fad’a tana wucewa sama”sai sannan shariff dake saurerensu yatanka”sbd jin sadeeq na fad’in banganeba?”sunan yayanta datake bimawa kenan”shima basa shiri kamar kaida wannan me k’aton kan”yafad’a yana nuna Abdallah murmushi na sub’uce masa “dan yau cikin nishad’i yakejinsa”harta y’an uwan nasa sun lura”sadeeq kuwa dariya yadin gayi yace”wlh yaya kamar kasani duk gidan nan shikad’ai keda k’aton kai….kamar Abdallah yayi kuka yatashi da nufin yaje ya kaima Ammi k’ara, shariff ya rik’e hannunsa yana hararar sa yace”dallah transfer zan maka”Ai yaya dama yaron nan mayen kud’i ne yanzun zakaga ya huce”babu ruwanka dai dashi”cewar shariff yana danna waya Atake yamasa transfer d’in 200f”kafin yaci gaba da break fast d’insa sbd shima girkin yamasa dad’i”yana kuma so yayi maza ya Ida yasameta Acan k’ilan ta sakko daga fushin da takeyi dashi”gaba d’aya sai yaji yarinyar ta burgesa”musammun yadda take bama Ammi girma da hidimta mata”sannan yanzun yadda ta gaidashi cikin girmamawa yaji dad’i Aransa”hakan kuma yatabbatar masa da cewa tasami ingan tacciyar tarbiya Awajen iyayenta…. Ahankali Amaan ta shigo cikin parlourn tana k’are masa kallo”Aranta tana yaba tsarinsa da had’uwarsa”ga daddad’an k’amshin turaren mamallakin parlourn na tashi kamar yana cikin parlourn”babu wani darty data gani Amma wai Ahaka za’a gyara”tunawa tayi da tabarsa yana break fast “idan ya idar k’ilan yashigo”bata son kuma yasameta a d’akin baccinsa”hakan yasa taga gara tafara gyara bed room d’in”da wannan tunanin ta murd’a handle d’in k’ofar ta shiga da sallama”ta lumshe idanuwanta sbd Anan Asalin k’amshin shariff yake”sosai d’akin ya burgeta cikin hanzari ta gyara saman bed d’in ta share d’akin ta goge sannan ta nufi toilet…..turo baki tayi datayi cin karo da boxer d’insa rataye saman hanger”ga wata roba me fad’i daya jik’a jallabiyoyinsa farare kala ukku da vest suma farare kala ukku”kasancewar becika bayar dasu ba wajen wanki”shine ke wanke irin kayan cikin da kansa”cikin mintina 10 ta wanke su tas ta shanya sannan ta wanke bath room d’in”batare data tab’a boxer d’in data gani ba”bayan ta gama ta fito tasami wayoyinsa zube saman bed side drower”saida gabanta yafad’i”wato yashigo cikin d’akin Ina toilet?”ta fad’a Azuciyarta tana fitowa….turus tayi ta kauda kanta sbd ganinsa zaune kan 2 seeter ya mik’e dogayen santala santalan k’afafuwansa saman center table”har jallabiyar jikinsa ta zame ana iya ganin gwiwarsa….oh yah rabbih jikinsa duk gashi”ta fad’a cikin zuciyarta tana jin wani iri da k’yar tace”hamma! zan gyara parlourn ko ciki zaka koma?”me makon yabata Amsar tambayarta sai canza topic d’in yayi da cewa kin gama fushin?”fushi kuma?toni fushin meye zanyi?”ta k’are maganar tana juya idanuwanta Alamar tunani”kinfi kowa sani”k’ilan sbd nayi tsaki kina damuna da zancen saurayinki ko?”yak’are maganar yana tab’e baki had’e da kallonta”kasa mgn tayi saidai ko yaya ta fahimci beson fushinta”idan har kinaso mu shirya dake karki koma yimun zancensa”shikenan hamma dama labari ne nabaka tunda bakaso bazan komayi ba”daga haka ta nufi k’ofa….dama kin gama Abinda nasaki ne?”yafad’a yana cigaba da danne danne a laptop “naga baka tashi bane”kin gama da canne?”uhmm kaje kayi wanka ruwan nacan na had’a maka”kayan dazan saka kin fiddo?ah ah”meyasa ?”kacika tambaya hamma”ni kaje zanzo na fiddo maka”ta fad’a cikin shagwab’a “ya kalleta”Allah yasa zaki iya”kuma kika gudu nida ke ne”daga haka ya mik’e tsaye yana satar kallonta ta wutsiyar Ido ya wuce bed room d’in cikin takunsa na nutsuwa had’e da kamala “Amaan ta sauke b’oyayyar Ajiyar zuciya jikinta Amace tacigaba da gyara parlourn “tana idarwa ta sulale tayi tafiyarta batabi ta kansa ba…. shariff kuwa…✍️

Adinga sharhi

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button