Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 52

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 52….. Karfe goma saura Mami ta aike Ikram taje ta kira mata Aliyu dakin Khaleel, ta gama sa kayan barcinta yar gown iya gwiwa pink colour, snn ta fita xuwa dakin Khaleel, xaune ta tarda su kan gado suna mgna, ta murguda ma Khaleel baki tana gyara dogon gashinta da ya rufe mata ido tace “yayana wae Mami tace in kiraka, kuma fa baka yi min assignment dina ba ka tsaya kana surutu da wancan” ta fadi tana nuna Khaleel, Khaleel yyi murmushi ya kauda kansa hade da kwafa, a tare suka koma dakin Mami da Aliyu yana cewa “ynxu xan maki kanwata ae ban manta ba, kuma ki daina ma yaya Khaleel rashin kunya baki san shima yayanki bne” ta xaro masa ido tace “sae nayi din idan bae daina neman tsokanana ba wllh sae nayi” bae ce mata komai ba suka shiga dakin, Mami tace “wllh ynxu aka kirani emergency hsptl Aliyu, ka daure ka tafi don Allah, ni ban jin fita da daddaren nn” ya dan yi jim snn yace “to shknn Mami bari in tafi” ya dauki car key dinsa ya fita daga dakin Ikram na biye da shi a baya kmr xata yi kuka ta kamo hannunsa tace “to yayana Assignment din fa” yace “owwh hka ne fa” ya durkusa gabanta ya dafata yace “kinga Mami ce ta aikeni Ikram…” tace “to xaka dawo ne” yyi shiru snn yace “kinsan mene ki kai ma Khaleel…..” juya masa baya tayi da sauri kmr xata yi kuka tace “ni baxan kai masa ba kana so ya kore ni ko” ya juyo da ita yace “nasan baxae kore ki ba kanwata, kinsan mene kina xuwa gunsa sae ki durkusa kice don Allah yyi hkuri baxa ki sake ba nasan xae maki, ko kuma ki kai ma Mami kawae ta maki” kmr xata yi kuka tace “Mami xata ce inje inyi da kaina ae an koya min, shi kuma ni baxan iya Kneel down masa ba” ya xaro ido yace “ba assignment kike son a koya maki ba knn, ni kinga ynxu asibiti xan tafi duba wasu basu da lfya” ta turo baki tace “to baxae koreni ba idan naje” ya gyada mata kai yace “ehh amma idan kika durkusa kika basa hakuri” ta karyar da kai tace “to xan basa amma kadan” murmushi yyi ita ma hka, ta rakasa har bakin kofa snn ya durkusa gabanta yana kallonta yace “i luv yhu dear” dariya tayi ta rufe ido ta juya masa baya tace “i luv yhu 2” ya mike yana murmushi yace “tnxx dear” ya daga mata hannu ita ma hka snn ta koma sama, sch bag dinta ta shiga dakin Mami ta dauka snn ta nufi dakin Khaleel, xaune ta tarda shi yana shan tea yana kallo, kallo daya yyi mata ya dauke kansa ta karaso dakin ta durkusa dan nesa da shi ba tare da ta kallesa ba tana murguda baki tace “kayi Hkuri” satan kallonta ya dinga yi bae ce komai ba, ganin yaki cewa komai yasa tana hararansa cikin daga murya tace “nace kayi hkuriii” ya juyo yana kallonta yace “da aka yi me” ta murguda masa baki tace “rashin kunyan da nayi maka” ya dauke kansa yana murmushi bae dae ce komai ba, ta mike fuskarta daure tace “ni Assignment xaka yi min” ya watso mata wani mugun kallo yace “ni xan maki assignment?” ta rike kugu tace “ehh” ya kuma cewa “nii?” tace “ehh” ya gyada kai yana murmushi yace “to sae na rama abinda kika min” ta bata fuska tace “ni me nayi maka to?” yana kallonta ya mike tayi baya da gudu ya girgixa kai yace “ae ni ba dukanki xan yi ba” shirt din da ta xuba masa ruwa daxu ya dauko yana nuna mata yace “nima sae na xuba maki ruwa kmr ynda kika xuba min kafin inyi maki assignment din” kmr xata yi kuka tace “to wae ba nace kayi hkuri ba ko na sani ne?” ya girgixa mata kai yace “ae sae na rama” ta dan marairaice tace “amma ae kadan na xuba maka” yace “nima kadan xan xuba maki” ta dan yi shiru snn tace “to oya xuba min kadan din” fridge taga ya nufa ta xaro ido tace “lahhh ni ba ruwan sanyi na xuba maka ba wllh” yace “ae ba ruwan sanyi bne, ynxun nn na xuba su a fridge kuma ma a kashe fridge din yake, kuma ae nima ruwan gora kika xuba min” bata ce komai ba ya bude fridge din ya dauko table water daya ya goge jikin ruwan da sauri kar ta gane na sanyi ne, ya matso kusa da ita ya bude ruwan ta bata fuska kmr xata yi kuka tace “Allah ni kadan xaka xuba min faa” yace “nasani” tsiyaya mata ruwan yyi a jiki kmr ynda tayi masa daxu ta fasa wani gigitattcen Ihu a tsorace jin ruwan sanyi ne, ajiye goran yyi da sauri ya kamota yace “ke ba ramawa nayi ba” wani ihun ta kuma fasawa ya rungumota da sauri ya rufe bakin yace “ke baki iya wasa bane” dukansa ta shiga yi tana tutturasa tana neman ci gaba da ihunta da kuka amma yaki cire hannunsa daga bakinta, dagata sama yyi ya dauki goran ruwan ya xauna kan gado yana rike da ita cikin lallami yake cewa “to yi shiru gashi kema ki rama” jikinta na rawa ta fixge ruwan daga hannunsa, ya rungumeta yana dariya yace “don Allah kiyi hkuri wllh sanyi nake ji, in kika xuba min baxan maki assignment ba” ta fashe da kuka ya dago kanta yace “to yi hkuri xan baki chocolate dayawa” ta galla masa harara tace “mugu kawae”
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar

Back to top button