Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 7

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E7_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

“ka na nufin ba su mutu ba suna a raye”? A ƙagare ta jefa mashi tambayar, jinjina mata kai yai ba tare da ya furta mata kalma ba, bugun zuciyarta ne ya qaru a sukwane ta juya baya don ta samu damar ƙare masu kallo, bargunan da ya lullu6e su da shi ya hana ta gan su da kyau, jikinta na 6ari ta ƙara sa gaban su ta zuƙunna tare da kai hannu ta ɗage saman bargon, duk wani motsin ta akan idon Danish.

Wani irin farin ciki ne Ya lullu6eta haƙiƙa ta yi al’ajabin wannan iko na Allah, kamar zautacciya haka ta dinga ɗaura kanta saman ƙirjinsu haɗi da jogana kunnanta saitin zuciyar su don ta ji idan tana bugawa, daga kan Jamimah ta fara tana ɗosa kunnanta bugun zuciyar jemimah ya daki dodon kunnan, nan ta ke ta fahimci cewa bacci su ke yi, Tambayoyi ta shiga jefawa kanta, Ta ya ya akai haka ta faru? Dama wanda ya mutu yana tashi? don ita dai a iya saninta idan an mutun ba adawowa, ɗaura kunnanta ta yi saman ƙirjin Azeeza lumshe idanuwanta ta yi wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, jin bugun zuciyar azeeza na har6awa, matsawa ta yi gaban Parveen tunkan ta ɗaura kanta saman ƙirjinta idanuwanta su ka sauka akan ƙaramin bakinta ganin yana motsi yasa ta fahimci tana araye, Lamarin yai matuƙar ɗaure mata kai, ta ya akai su ka rayu! Kuma Danish da kanshi ya tabbatar masu cewa Heart attack ne yai silar mutuwarsu, duk da bata da ƙoshin lafiya hakan bai hana smart brain ɗinta aiki ba, Zurfin tunani ta shiga idan har su Jemaimah su ka iya jure abunda ya faru dasu ya kenan ta 6angaren Sauran ƴan uwansu da su ka baro? Waro idanuwanta waje ta yi yayin da zuciyarta ka harbawa da sauri da sauri, a fujajen ta zabura ta miƙe kamar an zungure ta, ta juya ta nufi Danish dake a zaune Ya ɗan lumshe idanuwanshi, ƙoƙari ya ke ya hana kanshi yin bacci gudun kada yaja masu matsala, zuƙunnawa tai agabanshi

“Danish taya akai su Jamima su ka rayu? Bayan kai da kanka ne ka faɗa mana cewa zuciyarsu ce ta buga” ware idanuwanshi yai akan fuskarta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, damuwarta akan ƴan uwanta, bata damu da kanta ba, ƙarantar shekarunta yafi komai ɗaure mashi kai, yadda harta iya jure waɗannan wahalhalun rayuwar wanda yayi imanin ko wani babban ba zai Iya jurarsu ba.

“Danish bana so ina magana kana share ni, ka faɗa min ta ya ya akai su ka rayu? A iya sanina idan mutun ya mutu baya tashi, Sai gashi su Azeeza sun tashi, ko dai ka yi amfani da sihirinka ne wurin dawo masu da rayuwarsu…”? A ruɗe tai maganar babu kwanciyar hankali atattare da ita, a hankali ya ɗan motsa la66ansa.

“My Angel, u should stop talking about them, ba ki da lafiya u need a rest,” damƙar wuyar best ɗin jikin tai sosai ta fashe mashi da kuka tana faɗin”Danish ka faɗa min dama kasan suna araye shi ne ba ka bari mun goyo su Deeja mun taho da su ba? Me yasa ka yi mana ƙaryar cewa zuciyarsu ce ta buga”? Tana magana tana ku ka, raunin gefen bakin ta tuni ya fara tsastsafo da jini.

Ranta yai mugun 6aci zuciyarta ta harzuƙa, A haukace ta miƙe tana faɗin”Zan koma na taho da su Deeeja, ban damu da in rasa raina ba,” a hanzarce ya miƙe jin abunda tace, ido cikin ido su ke kallon juna”Am sorry Angel i don’t mean to hurt u, kinsan bana ƙarya, sannan bani da amsar da zan baki that’s why nayi shiru, hatta su Azeeza ban san suna araye ba, a daren jiya na yi ƙoƙarin binne su cos bana son ku farka ku taras da gawawwakinsu, hakan zai fama ma ku ciwon da ke a cikin zuciyarku, nayi amfani da sihirina wurin tsaga ƙasa har na fara sanyasu a ciki idona ya sauka akan yatsun ƙafafuwansu dake motsi, i was shocked cos ban yi expecting din zasu rayu ba, kin ji yadda akai nasan suna a raye”

kamar ta so ta fahimce shi sai dai wani sashe na zuciyarta yaƙi aminta dashi, girgiza mashi kai tai”Ni dai zan koma kurkuku in ɗauko su Deeja, Saboda ina ji araina cewa Suna araye”

Ya fahimci damuwace ke ƙoƙarin zautar da ita, Zaiyi wuya ta fahince shi, yasan halin kayansa da rigima ga kafiya da taurin kai, juyawa ta yi tare da nufar ƙofar fita daga kogon dutsen, da sauri Ya bi bayanta tare da ruƙo arm ɗinta ya janyota zuwa jikinshi, sosai ya matseta.

“Angel daji ne fa, ba mu a kusa da kurkukun ƙaddara, ta zarar awanni ce, A daren Jiya bayan mun fita ni ne na ɗauko ku na dawo da ku nan duk don na sauƙaƙa maku wahala” daƙyar ya ke magana, damuwace ƙarara akan fuskarsa, ƙoƙarin raba Jikinta tayi daga nashi.

Zuciyarta ce ke azalzalarta sam bata fahimtar kalamansa, idanuwanta sun makance

“Ka sake ni Danish, nasan ko nace kaje ka ɗauko min su Deeja ba za ka je ba, don haka ni zanje, saboda ina ji araina ƴan uwana suna araye basu mutu ba gashi mun baro su a hannun Azzaluman mutanancan…..” cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar, duk yadda yaso ya hanata tafiya taƙiya, har kwatanta mata haɗarin da dajin gare shi amma ta kafe akan sai taje, sakinta yai idon shi akan bayanta, sam babu kuzari a jikinta ahaka ta fuce daga cikin kogon dutsen, Hasken ranane ya galle mata idonta da sauri ta lumshe su na ɗan sakanni kafin ta ware su tana ƙarewa ƙurmin Dajin kallo, Daddaɗar iskar dajin ce ta ratsa sassan jikinta ni’imtacciyar gaske, hatta sumar kanta sai kaɗawa take yi saboda ƙarfin iskar, saboda taurin kai irin na Angel da kasada, Ahaka ta soma tafiya tana nufar cikin dajin ita ala dole saita gano inda kurkukun ƙaddara ya ke, tun kan aje ko’ina ta fara tsorata da ganin ƙananun halittun da ke yawo Saman bishiyoyi, duk da haka bata sare ba taci gaba da tafiya hada ɗan saurinta da gudunta, ko takalma babu a ƙafarta.

Tun bayan fitarta Danish Ya fito daga cikin kogon dutsen, ya goya hannayenshi saman faffaɗan ƙirjinshi Yana kallon bayanta, Ta yi matuƙar bashi mamaki, duk da ya fahimci babu hankali atattare da ita, in ba haka ba ta ya ya wanda ya tsira yake ƙoƙarin komawa ga halaka. Yarinta ce ke damunta da kuma son ƴan uwanta.

Tana cikin yin tafiyar nan, kukan namun dawa Ya dakatar da ita cak ta tsaya tana ƙarewa wurin da take atsaye kallo, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Snake ɗin dake bin jikin bishiya yana ƙoƙarin saukowa ƙasa, zaro ido waje tai a gigice ta fasa ƙara tare da juyawa da gudun gaske tamkar zata tashi sama, majicin na ƙarasa saukowa yabi bayanta, tashin hankali duk ta bi ta rikice don ta fahimci ita yake bi, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a yin tozali da maciji ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗosu, Tarasa gane ta wace hanya zata bi ta koma cikin kogon dutsen.

Danish ta dinga ƙwalawa kira kamar maƙoshinta zai 6allo, sai da ta gama galabaita cikin rashin sa’a tai tuntu6e da dutse gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa, ƙiris ya rage ta kife ƙasa a lokacin da ba ta yi tsammani ba taji Ya damƙo ta tare da kwantar da ita saman chest ɗinsa.

ƙanƙameshi tayi sosai ta fashe mashi da kuka tana zazzaga mashi masifa akan me zai barta ita kaɗai acikin daji? Idan ma don saboda ta yi mashi kafiya ne, bai ga ita yarinya bace, tun da fara mashi faɗa bai tanka mata ba, hannayen shi biyu suna tallabe da ita, sai da ta yi mai isarta, tukunna ta buɗe kumburarrun idanuwanta akan fuskarshi, tun daga kan tausasan red lips ɗinsa ta soma bi da kallo har izuwa ga dogon hancin sa kafin ta ɗauke idon nata ta ɗaura su kan sexy eyes ɗinshi masu matuƙar jan hankali.

ƙoƙarin shagala su ke yi da kallon Juna, tunawa da ƴan uwansu da su ka baro a kogon dutse ne yasa tayi saurin katse masu kallon ƙurullan da suke bin juna dashi”Danish mu koma kada wani abu ya same su” girgiza mata kai yai in a smoky voice ya furta mata”ba abunda zai same su, ina sane dasu, na rufe kogon dutsen babu wani abun cutarwa da zai Iya tunkarar su”Sam hankalin bai kwanta da kalaman shi ba

“Danish ni dai mu koma,” ashagwa6e tayi mashi maganar, ita kanta batasan ta sanya shagwa6a ba’

“Zamu koma, but before that, Inaso ki raka ni cikin Dajin in nemo mana abunda zamu ci, ko kina so su farka suna Jin yunwa ne”?

Girgiza mashi kai tayi”a’a amma ni ba zan bi ka ba, Ka maida ni cikin kogon dutsen in ya so kai sai ka je nema mana abunda zamuci” kafe ta da ido yai, hakan yasa ta jefa mashi harara haɗi da murguɗa mashi baki, munin fuskarta bai hana shi ganin kyanta ba, musamman da ta yi mashi abunda ke jan hankalin shi gareta, Harara da murguɗe abun A jinin ta ya ke.

“Idan ba za ki bi ni ba, Ga hanya nan ki koma kogon dutsen ni kin ga tafiyana” yai maganar tare da nufar Cikin dajin, da ido tabi bayanshi da kallo, ranta a 6ace yasan ba zata iya kai kanta ba shiyasa yace ta koma, Tunawa da macijin da ya biyota ne yasa ta zabura da gudu tabi bayanshi, Yana cikin tafiya yaji ta zura hannunta cikin nashi, ƙayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi.

Ta yi tsammanin Iya abincin da zasu ci ne zasu nemo, ba ta san plan Ya shirya mata ba, Yanayin Iskar dajin ba ƙaramin ni’ima ta saukar masu ba, Suna tafiya suna kallon Juna, wani irin Sanyi ne ke ratsa zukatan su, dakatawa tai dayin tafiyar ta ɗan kalli fuskarshi”Na gaji Danish ƙafata ciwo ta ke yi min” ba tare da ya amsa mata ba, ya juya mata bayan shi, ta gane me yake nufi, da sauri ta haye Saman bayan Ya miƙe ɗauke da ita, ba ƙaramin daɗi taji ba, shin me yafi ranta gata ga garkuwar kurkuku, ta ƙanƙameshi sosai, lumshe idanuwanta tayi sai faman shaƙar mashi fatar wuyan shi take yi, bai sauke ta a ko’ina ba sai abakin wani tabkeken ruwa mai gudana, Ta jikin dutse ruwan ya ke gangarowa tsaftatacce fari ƙal dashi.

“Mun ƙaraso,” Jin abunda yace ne yasa ta ɗago da kanta, tana ƙarewa wurin kallo, nan ta ke ta ji tana sha’awar shan ruwan, Zuƙunnawa yai ta sauko daga saman bayan nashi, a jere suka tsaya suna bin ruwan da kallo, ga dukkan alamu ya burgesu .

“Danish ƙishi na ke ji, nasan kaima kana ji, mu sha sai mu ɗebi wani mu kai ma su Parveen ko”? Ba tare da ya juyo ya kalli fuskarta ba ya soma magana”Wanka nake so nayi maki, saboda kinyi muni, jikin ki yayi datti”

Har saida gabanta ya faɗi jin abunda yace, juyowa yai da fuskarshi ya kalleta tare da kashe mata ido ɗaya

“za ki iya cire kayan ko in taimaka maki ne”? gabanta ne ya dinga faɗuwa sai ta ga kamar ya canza mata, babu alamun wasa akan fuskar shi yai maganar.

Ganin yana matsowa kusa da ita, yasa ta juya da niyar ta gudu, ko ta ku ɗaya bata kai ga yi ba taji Ya damƙi ƙugunta, ƙarfi ba ɗaya ba, Duk yadda taso ta kubce mashi ta kasa, matseta yai a ƙirjin shi, A hankali Yai amfani da hannun shi ɗaya wurin zame rigar Jikin shi, tare da wandon kakinsa na Giant, ya rage daga shi sai short fari, saman gungurumeman dutsen dake agefen ruwan, ya jefar da uniform ɗinshi.

kamar jinjira haka ya ɗauke ta, kaitsaye Ya nufi Cikin ruwan da ke gangarowa, ba yadda ta iya dashi, Tana kuka tana fadin bataso ya ƙyale ya rabu da ita, ahaka yayi mata wanka tass ya wanketa Kamar yayi amfani da sabulu ita kanta tayi mamikin yadda Jinin jikinta ke fita, Farar fatarta sol ta dawo har wani salƙi takeyi da ɗaukar ido, hatta uniform ɗin da ke ajikinta sun wanku sosai sun manne ma fatarta,

kwantar da kanta yai saman broad chest ɗinshi, Ya cusa yatsun hannunshi cikin sumar kanta yana cuccuɗata da ruwa, Jinin da ya danƙare mata a cikin kan ya dinga fita, gashin kanta ya dawo ainihin launin shi dark brown mai kyan gaske, ba ƙaramin taimakonta yai ba da yayi mata wanka, Ita kanta tasan bazata iya wanke najasar dake a jikinta ba, ƙanƙame jikinshi tayi sosai la66anta na kerma take faɗin”sanyi Danish san yi ni ke ji, tamkar ana ƙara gudun ruwan sun jiƙe sharkaf acikinsa, sai da ya kammala tsaftace mata jikinta tukunna ya ɗaukota saman kafaɗarshi ya dawo da ita Gefen dutsen da ya ɗaura uniform ɗinshi.

Tun da ya sauke ta ta faɗa ma faffaɗan ƙirjinshi, ta zagayo da hannayenta saman bayanshi, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, idanuwanta a lumshe, ita kaɗai tasan daɗin da ta ke ji, da farko taji haushi da ya yi mata wanka, amma yanzu ta fahimci Dalilin dayasa ya tursasa mata yin wanka, jikinta yayi mata daɗi wata irin ni’ima ke sauka, tamkar an yaye mata damuwar dake acikin zuciyarta, sun natsu suna sauraron bugun zuciyar junansu, irin yanayin da yafi son kasancewa tare da ita, yana son Angel dinsa fiye da yadda yake son kanshi, a shirye yake daya sadaukar da ranshi indai akanta ne”

Fatar wuyanta ya ƙurawa ido fara sol sai ƴan tabannin da ba arasa ba, na gurjewar da tayi, ɗaura tafin hannayensa yai asaman bayan nata,

“My Angel!” a kasalance ya furta sunanta shiru bata amsa mashi ba

“Are you feeling sleepy?” kamar yayi magana da bango shiru taƙi buɗe ba ki ta yi magana, ƙoƙarin rabata yayi daga ƙirjinsa, sai dai taƙi bari ya ɗago da ita, ta yi tighting ɗin shi tamkar zata koma cikin shi, baiwar Allah, Dama abuƙace take da ta samu inda zata sassauta raɗaɗin da ke acikin zuciyarta, abubuwan da suka faruwa a rayuwarta ta soma tariyowa tun daga lokacin da ta mallaki hankalin ta, har zuwa rayuwarta a hannun fulanin Daji da kuma faɗowarta gidan kurkukun ƙaddara, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta, jin shessheƙar kukanta ne yasa shi rikicewa ya shiga ambaton sunanta adabarbarce, daƙyar ya iya 6an6arota daga ƙirjinshi, eyes dinshi akan fuskarta ta runtse idonta

“My Angel I don’t want you to dwell on what happened before, I know it hurts you, but please forget about the past. I don’t like to see you cry.

tun da ya soma lallashinta bata buɗe idanuwanta ba, tsawon mintuna kafin a hankali ta ɗago da kanta tare da jingina bayanta jikin dutse.

Matsawa yayi jikin ƙaton dutsen ya miƙa hannu ya ruƙo uniform ɗin shi, A tsanake Ya sanyasu a jikin shi

“Zaki Iya jirana anan”? girgiza mashi kai tayi”tsoro nake ji, ka maida ni cikin ƴan uwana” yaso ta amince ko dan ya samu ya shiga cikin Dajin Ya nemo masu abunda zasu ci, kwantar mata da hankalinta yai”Yanzu zan dawo, bana so ƴan uwanmu su tashi da yunwa pls ki jirani anan, ba abunda zai same ki, kada kije ko’ina” bai jira amsarta ba, ya 6ace ma ganinta.

Tunawa da cewa ita fa yanzu mai ƴanci ce yasa ta ɗan saki murmushi, har ta fara tunanin irin mugun kisan da za ta yi ma waɗanda su ka sadaukar da su, badajimawa ba ta soma Jin motsin tafiyar mutun a firgice ta buɗe idanuwanta lokaci ɗaya ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ganin Danish ne ya dawo hannun shi a ruƙe da Zomayen Daji da ya yo masu farautarsu, ya ruƙe ƙafafuwansu da hannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun ke aruƙe da gorar ruwan, mamaki ne ya kamata ganin zomaye, miƙa mata gorar ruwan yai da sauri tasa hannu ta kar6a, Acike take da ruwa, jera kafaɗa su ka yi suna tafiya suna satar kallon juna, abunda ya ɗaure mata kai yadda Danish yasan komai dangane da Daji mutumin da bai ta6a fita daga cikin kurkuku ba, Yanzu tadaina yi mashi kallon solo6iyo, A Namijinsa ta ke kallon shi.

Lokacin da su ka ƙaraso Gaban Kogon dutsen, Atare su ka shiga Ciki, Ya ajiye zomayen saman korayen ciyayin da ke shimfiɗe ƙasa, ya ɗago da ido ya kalle ta, zanje na haɗo itace yanzu zan dawo, Ta amsa mashi da toh,’

Bayan tafiyarshi ta ajiye gorar ruwan ƙasa, kafin ta nufi shimfiɗar su, ba ta yi mamakin ganin ba su farka ba saboda ta riga ta gane aikin Danishi, gaban akwatin kayansu ta zuƙunna ta buɗe ta curo tsoffin uniform ɗinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ta canza na jikinta da suka jiƙe ta shanya su daga wajen dutsen, dawowa tayi cikin kogon Agaban shimfiɗar ta zuƙunna tana ƙare masu kallo, idanuwanta akan Jemimah da Azeeza, daɗi kamar zai kasheta, a ƙagare ta ke da su farka su ga wurin da Allah ya kawosu tasan zasu sha mamaki da al’ajabi kuma zasu ji daɗin cika masu alƙawarin da ta yi.

Sam ba ta ji motsin shigowarshi ba, har sai da yai mata gyaran murya tukunna ta waiwayo su ka haɗa ido da shi

In zo in tayaka”? girgiza mata kai yai” a’a bana so ki wahala” miƙewa tayi tare da zuwa gabanshi ta zuƙunna tana ƙare mashi kallo, hankalin shi ya koma akan itacen da ya ke jerawa bayan ya kammala ya ɗauki duwatsun jiya da yai amfani wurin rura wuta, duk wani motsin shi akan idonta har ce mata yai “kije ki huta mana, ba kince kina jin sanyi ba? Ki ɗauko bargo” maƙe mashi kafaɗa tai alamar ba za ta je ba.

Bawan Allah shiya zauna zaman gasa masu naman, sai maiƙo yake yi kamar an soya shi da mai, Kitsan jikin zomayen ne ke narkewa, bayan ya kammala ya ɗaura gasasshen naman da ya tsira Jikin icce saman faffaɗan ganyan da ya shimfiɗa a ƙasa.

“Danish” ɗagowa yai tare da kallonta, bakomai ya gani acikin idanuwanta ba face Tsantsar tausayin shi

“Kada ki damu kanki am ok, idan zan shekara inayi maku bauta ba zan gaji ba” kalamanshi sun ƙara sanya mata ƙaunarshi acikin zuciyarta.
“A ina ka samu wannan gorar ruwa”? Tai maganar tana nuna ta da yatsa

“A cikin Daji ba abunda ba zaki Iya samu ba, Hada kan mutun” murmushin gefen fuska ta saki, ga dukkan alamu zasu fara kafa nasu tarihin soyayyar tun acikin Daji.

Ɗagowa yai da lumsassun idanuwanshi ya ɗaura su kan fuskarta

“Can you eat by yourself? Or do I need to feed you?”

Girgiza mashi kai tai” ka wahala sosai, ni ya kamata in baka da hannuna” ya ji daɗin maganarta har ya buɗe baki da niyar mayar mata da martanin maganarta, kwatsam! muryar Jemimah ta katsesu da wani irin sautin mai amo take kwaɗawa Angel kira amatuƙar gigice take fadin”Genie wayyo Allah Genie Zafi Jikina ƙaiƙayi nake ji” Ahanzarce Danish da Angel suka miƙe da sauri suka nufi shimfiɗarsu atare suka zuƙunna agabansu, Hannu biyu Angel ta sanya ta ɗauko ta zuwa saman jikinta, ta ƙanƙameta, Duk tabi ta furgice sai kuka takeyi masu tana harba ƙafafuwanta, Sautin kukanta ne ya farfaɗo da sauran ƴan uwan nasu, Batul ce ta fara miƙewa kamar fatalwa idanuwanta luhu luhu sun kaɗa jawur, baiwar Allah har faɗawa tayi sai uban haske, gashin kanta kuwa a hargitse yake, Buɗe idonta keda wuya ta sauke su akan na Danish dake kallonta, Muryarshi na ɗan rawa ya furta sunanta”Ba..tul” ɗauke idonta tayi daga kan fuskarshi ta mayar dasu Kan kogon dutsen da suke aciki saƙo da lungu tabi da kallo, kukan farin cikine ya kubce mata, Da sauri Danish ya ruƙo hannunta acikin nashi ya kwanto da kanta saman ƙirjinshi, sosai ta ƙanƙameshi tana cigaba da yin kukan.

Farkawa Gabriel yai zumbur ya miƙe yana ambaton sunan Azeeza, da ita ya kwanta acikin ranshi, sai tsuma yake yi yana fitar da huci, Cikin shessheƙar Kuka Angel tace dashi”She’s still alive! Azeezar mu bata mutu ba, suna araye,”

Karaf maganarta ta sauka akan kunnan sauran ƴan uwan su da suka farka, a zazzaune suka miƙe Tun daga kan Javed, Naufal da Hannah mutun uku ne basu motsa ba, parveen Azeeza da Haris, ga dukkan alamu sun farka daga bacci sai dai sun kasa motsawa, Jikinsu ba ƙoshin lafiya, ko yatsan su sun gaza ɗagawa.

Hankulansu gaba ɗaya ya koma kan su, kowan nan su fuskarshi akumbure take suntum, babu walwala ko annuri, dagaske Azeezana bata mutu ba? Gabriel ne yai tambayar yayin da idonshi ke fitar da hawaye, Danish ne ya bashi amsar tambayarshi, Tsabar farin Cikine ya bayyana akan fuskarshi, Rumfa yai ma azeeza da ƙirjinshi motsa la66anta da take yi ne ya tabbatar mashi da cewa tana araye sungumarta yai tare da ɗaurata saman laps ɗinshi, Danish Ya miƙa mashi gorar ruwa don ya bata tasha, Yatsun hannun shi na kerma ya kar6a ya kafa mata abaki, ruwan yana wucewa ta maƙoshinta sai dai ta gaza buɗe idonta, Farin Ciki duk ya cikasu, Naufal ne ya ɗauki Parveen Baiwar Allah anji jiki, miƙa mashi gorar ruwan Gabriel yai ya kar6a yabawa parveen kamar zata haɗa da gorar duka ta shanye, Sai lokacin Danish Ya raba jikin shi daga na Batul Ya rarrafa zuwa gaban Haris dake kwance kamar matacce ya ɗaura hannayenshi biyu wurin ɗago dashi ya kwantar da kansa saman kafaɗarshi, Cikin sanyin murya ya ke ambaton sunanshi”Haris! Haris!” shiru bai amsa mashi ba, jikin shi yai zafi sosai babu alamun lafiya atattare dashi, ɗaura tafin hannun shi yai saman ƙirjinshi bugun zuciyar haris a hargitse yake fita, hakan ba ƙaramin tada mashi hankali yai ba, Yana fargabar wani abu ya same shi.
“Ɗan uwana Rabin raina nasan kana jin muryata pls kada ka bari damuwa tayi maka illa, ina atare da kai” jin muryar Danish acikin kunnanshi yasa shi ƙoƙarin motsa la66ansa sam sautin yaƙi fita, Fahimtar hakan yasa danish matsar da kunnanshi saitin bakin Haris

“Deeja ta mutu! Na rasa Deeja Danish! Bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, zuciyata nauyi take yi min, ka taimaka ma rayuwata” a hargitse yake magana, tsananin tausayin shi ne ya kama Danish, dama sai da ranshi ya bashi cewar akan Deeja ne ya shiga mawuyacin halin nan.

“Haris ka kwantar da hankalin ka, ba mu da tabbacin suna araye ko sun mutu, tun da har su Azeeza suka farka bayan munyi tunanin sun mutu ina saran suma za’a iya samun masu rai acikin su” cikin jin ƙunar rai Haris ya furta”Danish idan har hakane deejana tana araye azzuluman mutanancan zasu Iya kashe min ita, mun barsu fa a kurkuku, Danish ka koma ka ɗauko min ita, idan baso kake na mutu ba’ sosai ya sanya mashi kuka, Rarrashin shi ya dinga yi yana lalla6a shi duk don ya samu ciwon nashi ya lafa.

Waɗanda suka fi jin jiki a cikinsu Jemimah ce da Azeeza sai Haris, Ita parveen tunda taji ta ajikin Naufal ta wartsake, har tana iya ambaton yunwa take ji, Jemimah kuwa taƙi daina yi masu kuka, Sautin kukanta ya karaɗe kogon dutsen kamar ana zare ranta, Hankalin Angel duk yabi ya tashi, Ta rasa ya zatayi da ita, Cikin muryar kuka take yiwa Danish magana akan yazo yataimaka mata, Har ƙwara Azeeza tun da ta ƙanƙame Gabriel bata ƙara motsawa ba, ta lafe mashi idanuwanta arufe suke gam.

Sun rasa ya za su yi dasu, kukan jamima ba ƙaramin tsuma zuciyarsu yake yi ba, taji jiki baiwar Allah, Sunga ƙoƙarinta da har ta iya yin kukan, azabar raɗaɗin gabanta ne ya addabeta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, fuskarta jaga jaga da hawaye, yarinyar da bata wuci shekara goma da watanni ba, ta rasa budurcinta, su kansu sunyi mamakin da ta iya rayuwa, lokacin mutuwarta ne baiyi ba, Tana kuka suna kuka, Babu wanda bai zubar mata da ƙwalla ba in ka cire Danish, kwantar da Haris yai saman shimfiɗar, jikinshi na tsuma ya nufi Angel Ya sanya hannu biyu ya kar6i jemimah daga hannunta, fucewa yai da ita daga Cikin kogon dutsen basu san Inda ya nufa da ita ba.

Tsawon mintuna sai gashi ya dawo rungume da ita a ƙirjinshi, ajiyar zuciya suka sauke Jin tayi shiru tadaina kukan, Akwatin kayansu ya buɗe ya ɗauko mata rigar sanyi, cikin waɗanɗa tsohuwa ta yi masu kyautarsu, Ya sanya mata a jikinta, ga dukkan alamu wanka ya yi mata, bayan ya kammala sanya mata rigar, ya curo mata hula ya zura mata akanta, ya kuma ɗauko Mayafin kayansu, Sai kallon shi suke yi, Danish ya basu mamaki, Asaman bayanta ya yafa mata mayafin ya miƙe tsaye yana lallashinta kamar yadda akeyi wa jarirai, jemimah ta natsu sai faman lumshe idanuwanta takeyi, Jikinta ya lafa sosai ta daina jin raɗaɗi ciwo nata, juyowa yai tare da nufar Angel ya miƙa mata jemimah,

“Zan tafi da Azeeza ki basu naman su fara ci” amsa mashi tayi da toh, ta kar6i jemimah tare da rungume ta a ƙirjinta, bayan Ya ɗauki Azeeza Ya fuce da ita, janyo masu naman tayi zuwa gabansu, duk da halin da suke aciki hakan bai hanasu Cin naman ba, Saboda matsiyaciyar yunwar da suke ji, Mutun ɗayane ya kasa cin naman, ko da Javed Ya tallabo shi ya zaunar dashi Yana tura mashi abaki, Amayar dashi ya dinga Yi, ruwa kaɗai ya iya sha, sun damu da rashin lafiyar Haris Ya galabaita sosai, Jemimah dai ta ɗanci naman Angel ce take bata abaki, har yanzu bata buɗe idanuwanta ba, balle ta san a ina suke.

Shigowa cikin Kogon Danish yai Hannunshi ɗauke da Azeeza, Ya wanke ta tass jikinta sai kakarwa yakeyi, tunkafin ya ƙaraso Gabriel Ya buɗe akwatin kayansu ya ɗauko mata rigar sanyi tare da mayafi, Bayan Danish Ya miƙa mashi ita, Ya sanya mata rigar asaman uniform ɗinta, Ya ɗaura mata mayafi saman kanta, kafin ya kwantar da ita saman ƙirjin shi, Abaki ya dinga gutsuro namanta yana tura mata abaki daƙyar take iya taune shi, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, duk fa wannan budurin da sukeyi Azeeza da Jamimah da Parveen basu san cewa sun bar kurkukun ƙaddara ba, Saboda basa acikin hayyacin su.

Danish bai samu damar cin nashi naman ba, Jira yai sai da suka kammala ɗaya bayan ɗaya ya raka su zuwa bakin ruwan nan suna yin wanka, da taimakon shi Haris ya samu yayi wanka jikin shi ya ɗanyi mashi daɗi, bayan sun kammala Ya ƙara haɗo wasu itacen Ya kunna masu wuta Kogon dutsen ya ɗumama sosai Sanyin da su ke ji ya washe, sun cinye namansu duka, Kaɗan Danish ya samu yaci, kamar masu zaman makoki haka su ka zauna kewaye da wutar da ke ci, Suna kallon junan su kowa da abunda ya ke saƙawa aran shi, jemimah tuni bacci ya ɗauketa kamar jinjira haka Angel ta matseta a ƙirjinta, haka azeezama bacci ne ya ɗauke ta, tana kwance saman jikin gabriel, Haris ya langwa6a kanshi saman kafaɗar Danish, Batul ta ɗaura kanta saman kafadar Angel, Parveen tana a kwance saman ƙirjin naufal, da hannu biyu ya tallabeta, haka zalika Hannah tana arungume jikin Javed, sun natsu suna sauraron kukan namun dawan dake hargowa acikin Dajin, ba zaka ta6a fahimtar yanayin da su ke a ciki ba, kowa da abunda yake saƙawa aranshi.

*OBIE STATE*

In Abuja

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button