Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 40

Sponsored Links

PAGE* 4⃣0⃣

Zarah sawa tayi Aysha taje gidansu khairy takira mata ita nan suka zauna suna ta hirarsu cike da jin dad’i da nishad’i.

Bayan sallar isha’i yarima ne ya iso k’ofar gidansu Zarah wayarsa yad’auka yakirata, zarah ganin maikiranta yasa tayi murmushi sannan tayi picking tare da yin sallama,

Daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi sannan yace gani a waje,.zarah ahankali tace toh zaka shigo kugaisa da su abbah ko?

Jim yarima yayi sai chan yace kizo kishigo da ni, yana fad’in haka yakashe wayarsa.
Zarah mik’ewa tayi tayafa gyalenta sannan tace ma su abbah ga yarima nan zai shigo sugaisa, abbah yace toh badamuwa.

Fitowa tayi waje tagansa zaune cikin motarsa ya jingine kansa a sit d’in da yake zaune sai yafiddo k’afa d’aya a waje inda d’ayar take cikin motar.
Takawa tayi ta isa inda yake tarik’e k’ofar motar tare da yin sallama.
Yarima bud’e idanuwansa yayi da suke lumshe yakalleta, ahankali ya amsa mata.
Murmushi zarah tayi tace sannu da hanya ya aiki?
Yarima saida yajanye idonsa daga kallonta sannan yace Alhmdllh.
Bismillah kashigo kugaisa, cewar zarah.
Ahankali yarima yafito daga motar yamaida yarufe chan kuma sai yabud’e yad’auko hularsa yasaka, kallon zarah yayi da tatsaresa da ido yace kallon fa?
Fuskar zarah d’auke da murmushi tace kayi kyau
‘Dan guntun murmushi yarima yayi sannan yace kema haka.
Dariya zarah tayi tace ni kyaun mi zanyi ai kafini.
Yarima ma kallonta yake yace shikenan mushiga dare yakeyi,
Zarah tsayawa tayi tace wuce gaba sai inbiyoka.
Harararta yarima yayi yace gidankune ko namu?
Murmushi zarah tayi sannan tawuce nan yabi bayanta har cikin gida, da sallamarsa yashiga, nan suka amsa masa.

Saman tabarmar da aka shimfid’a masa yazauna, cike da girmamawa yagaishe da abbah da mama suka amsa tare da tambayarsa mutanen gida.
Kansa sunne k’asa yace duk suna lafiya suna gaisheku.
Abbah yace masha Allah muna amsawa.
Sannan rauda da Aysha suka gaishesa, cikin sakin fuska ya amsa masu tare da tambayar rauda ya k’arfin jiki tace Alhmdllh yanzu ta warke.

Mama kallon zarah tayi tace kikawo masa abinci man,.zarah mik’ewa tayi tace toh mama.
Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh abarsa kawai a k’oshe nake.

Kusan a tare su abbah suka mik’e sannan yace a’a yarima nan ma ai gidane bari mubaka waje kaci, nan suka wuce suka shiga d’aki, daidai lokacin zarah tadawo d’auke da kulolin abinci ta aje gabansa sannan tazauna gefensa, tana bud’ewa wani irin k’amshi yadaki hancin yarima nan tafara serving d’insa, bayan tagama kallonsa tayi fuskarta d’auke da murmushi tace bismillah,
Yarima d’aukar spoon d’in yayi yafara cin burabuscon sannan yakalli zarah da take wasa da gefen gyalenta yace ke bazaki ciba?
Kallonsa tayi tana murmushi tace ni naci d’azun,
Daganan Yarima yacigaba da ci, bai wani ci dayawaba yature plate d’in saidai kunun zak’in da yasha sosai,
Zarah kallon plate d’in tayi tace ba dai ka k’oshiba? Bakafa ci dayawaba.
Yarima kur6ar kunun zak’in yayi sannan yace kinsan banason cin abu mai nauyi da dare.
Zarah shuru tayi sannan takwashe kwanukan, bayan ta dawo Yarima kallonta yayi yace kije kiyi ma su abbah magana muyi sallama dare yakeyi.

Zarah 6ata fuska tayi tace tun yanzu?
Banza Yarima yayi mata,
Ganin haka yasa tamik’e taje tasanar da su abbah, kusan a tare suka fito, sama-sama suka d’anyi hira sannan sukayi musu sallama, har wajen mota yaya rauda da Aysha suka rakasu, Yarima bandir d’in ‘yan 1000 yad’auko yamik’a ma Aysha yace tasiya kayan kwalliya, godia Aysha tayi masa sannan suka tafi.

Tunda suka kama hanya ba wanda yayi magana har suka isa gida, yana yin parking d’in motar daidai lokacin sumayya tafito daga 6angaren iyayenta, tsaye tayi fuskarta d’auke da murmushi tana jiran Yarima yafito, zarah ce tafara fitowa sannan Yarima, ganin zarah yasa fara’ar da yake fuskar sumayya tagushe ahankali tace ina Yarima yaje da wannan matsiyaciyar? Watau dakansa ma yake kaita anguwa? tsanar zarah ce taji tak’aru a cikin zuciyarta, batasan lokacin da suka iso inda takeba saidai ji tayi yarima ya ce kekuma daga ina kike?

Sumayya ta6e baki tayi tace daga wajen ummah na amso wani sak’one, zarah d’an rissinawa tayi tace Aunty sumayya ina wuni?
Wata uwar harara sumayya tawurga mata tare da jan tsaki sannan tawuce tabi bayan yarima da yayi gaba,
Zarah ko kad’an batayi mamakin hakan ba nan tabi bayansu tawuce part d’inta.

Cire kayan jikinta tayi tashiga wanka, bayan tafito tayi shirin bacci nan tabi lafiyar gado takwanta.

Sumayya har part d’in yarima tabisa lokacin yana shirin cire kaya yashiga wanka tsaye tayi tana kallonsa, kallonta yayi yace ya dai?
Sumayya ta6e baki tayi tace gaskiya yarima baka kyauta min.
Da mamaki yarima yakalleta kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace da akayi miki mi?
Matsowa tayi kusa da shi tace akan me zaka d’auketa kakaita anguwa alhali tana da motarta kuma zaka iya sawa akaita.

Murmushi yarima yayi yace ko da ace iyayenki ba a tare muke da suba zan iya d’aukarki in kaiki sumayya ammah banda gidan abokai dan baya cikin tsarina, yana fad’in haka yawuce yaje yashigewarsa bathroom,

Sumayya fitowa tayi cikin fushi tawuce part d’inta.

Yarima bayan ya fito shima shirin bacci yayi yakwanta.

Sumayya ma koda takwanta sak’e-sak’e kawai take a ranta ta yadda zata kawar da zarah, dan gani take itace kawai matsalarta a rayuwa.

*BAYAN KWANA BIYU*

Sumayya ce zaune a bedroom d’inta nan ta aika aka kira mata zabba’u bayan tazo tsugunnawa tayi tagaisheta cike da girmamawa, fuskar sumayya ba yabo ta amsa sannan tace kinsan dai ba akan komai zan kirakiba sai akan waccen matsiyaciyar yarinyar, kud’i sumayya tamik’a mata jikin zabba’u yana rawa takar6a tace ranki yadad’e me kikeso wlh zan iya komai kifad’i yadda kikeso ayi yanzu.

Murmushin mugunta sumayya tayi sannan tace matso kiji abinda nakeso kiyi min dan yau banso taje wajen yarima,
Dasauri zabba’u tamatso sumayya bata damu da tsamin da jikin zabba’u yakeba nan tayi mata rad’a a kunne, washe baki zabba’u tayi tace angama indai dan wannan d’an aikin ne ranki yadad’e kikwantar da hankalinki

Murmushin Jin dad’i sumayya tayi sannan tace haka nakeso zaki iya tafiya, bayan zabba’u ta fita sumayya zagaye d’akin tashiga yi cike da jin dad’i cikin d’aga murya tace yes yau burina zai cika.

 

Wajen k’arfe tara yarima kiran zarah yayi yace tahad’a mai coffee.
Bayan tagama saida tak’ara gyara jikinta sannan tazumbula hijab tafito, kuyanginta tasallama sannan tad’auki cup d’in coffeen tanufi part d’in yarima, tafiya take wani tsantsi taji ya ja ta wata irin k’ara tasaki kafin takai k’asa nan duka coffeen yazube a jikinta, duk yadda taso tamik’e kasawa tayi nan tafara hawaye saboda wani irin zafi da zugi dak’afar takeyi mata, waige tashiga yi ko Allah ya sa taga wani saida tayi kusan min biyar ahaka sai ga wata baiwarta tazo wuce, ganin zarah yasa tarud’e cikin sauri ta iso inda take tace ranki yadad’e meyake faruwa da ke?
Zarah tana cije baki cike da dauriya tace taimakamin intashi nan baiwar tataimaka mata tatayar da ita duk yadda zarah taso tataka k’afar kasawa tayi daga k’arshe saidai baiwar tarik’eta tana k’engasawa suka koma part d’in zarah, nan saman gado tazaunar da ita tare da taimaka mata tacire hijab d’inta,

Zarah jingine kanta tayi da jikin gadon tare da runtse ido, baiwar cike da rikicewa tace ranki yadad’e bari inje infad’a ma yarima, har ta mik’e cikin sauri zarah tarik’ota dak’yar tabud’e baki tace kar kifad’a masa please je kikira min sahura (kuyanga) dasauri baiwar tafita daga d’akin,

bayan minti biyu sai gasu sundawo, a firgice Sahura tanufi wajen gadon tace ranki yadad’e me yake faruwa da ke?

Murmushin k’arfin hali tayi tace kar kidamu bawani abu ‘yar fad’uwace nayi, yanzu so nake kitaimaka kihad’omin coffee kikai ma yarima.

Sahuru matsar k’wallah tafarayi tace ranki yadad’e ya akayi hakan takasance?
Murmushi zarah tayi tace kidaina kuka inaji miyar ku6ewa ce aka d’an zubar da ita ammah nidai yanzu kitaimaka kije kihad’a min coffeen, mik’ewa sahura tayi tace toh ranki yadad’e Allah yabaki lafiya,
Gyad’a kai kawai zarah tayi, bayan sun fita ta6a k’afar tad’anyi kad’an dasauri taruntse ido tare da furta wash saboda wani irin zafi da taji, ahankali takwanta tare da runtse idonta tanajin wani irin zogi.

 

A chan 6angaren yarima zaune yake a parlour yana kallo ammah gabad’aya hankalinsa baya ga kallon kad’an-kad’an ya duba time ammah shuru zarah batashigo ba, nan yak’ule tsaki kawai yake ja.

‘Daya daga cikin guards d’insane yashigo yace ranka yadad’e wata kuyangace tazo ta ce gimbiya ta aikota
Yarima izini yabada yace abarta tashigo.

Sahura ce tashigo d’auke da cup tsugunnawa tayi cike da girmamawa tace ranka yadad’e gimbiya ce ta umurceni inkawo maka coffee,
Yarima da tunda tafara maganar bai kalletaba sai alokacin yajuyo yawatsa mata wani mugun kallo yace ke nasa kihad’o min ko ita? Kikoma kimaida mata abunta kice ita tafi k’arfin tazo takawo min?

Duk’ar da kanta kuyangar tayi tace ranka yadad’e kagafarceni wlh gimbiya bata jin dad’ine,
Yarima a firgice yace bata jin dad’i? Me yasameta?
Kuyangar k’ara duk’ar da kanta tayi tace ranka yadad’e lokacin da tafito zata kawo maka sai tazame yanzu tana chan k’afarta ke ciwo.

Yarima a firgice yace what! Garin ya hakan yafaru.
K’ara duk’ar dakanta tayi tace kagafarceni miyar ku6ewace aka zubar a waje itace ta zameta.

Yarima lumshe idonsa yayi tare da jin gine kansa jikin kujerar da yake zaune, d’aga ma kuyangar hannu yayi alamun tatafi, saida tak’ara duk’ar da kanta tagaishesa sannan tatashi tafita tabar d’akin.

Yarima wani iri yakeji a ransa ya dad’e zaune sannan yamik’e yafito yanufi part d’in zarah, bai samu kowaba a parlournta yana shiga bedroom yatarar da ita zaune saman gado kuyanginta biyu tsugunne k’asa suna yi mata sannu,
Yarima bai kula da gaisuwar da kuyangin sukeyi masaba yanufi wajen zarah, cikin sauri kuyangin sukabar d’akin.

Yana zuwa rikicewa yayi ganin yadda take cize le6e, k’afar yarik’o a rud’e yace sannu ko muje asibiti? Nan kawai yake miki ciwo?
Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cike da mamakin ganin yadda yarikice mata,
Ganin haka yasa yarima yasaki k’afar tare da zama yadafe kansa dogon numfashi yaja sannan yad’ago kansa yakalleta yace garin ya hakan tafaru?
Zarah murmushi tayi tace inaji wani yazubar da miyar ku6ewace bai luraba nima bansan da itaba nataka shine nafad’i ammah dasauk’i.

Yarima rik’o k’afartata yayi yana dubawa ahankali yafara murza mata, wata irin k’ara zarah tasaki tare da ruk’unk’umesa nan k’wallah tafara fita daga idonta cikin muryar kuka tace please kadaina akwai zafi,

Yarima shi kansa saida yalumshe idonsa ahankali yajanyeta daga rik’on da tayi masa tare da tallabo mata kai yana kallon cikin idonta yace kidaure ind’an murza miki kar tayi tsami inyaso gobe sai muje hospital bazanyi miki da zafiba,

Zarah share k’wallar idonta tayi tace please kayi min ahankali wlh da zafi.
Yarima murmushi yayi yace kar kidamu ahankali zanyi miki.
Sakinsa Zarah tayi sannan takoma takwanta nan Yarima yajanyo k’afartata yad’aura saman jikinsa, ahankali yashiga murzawa yana kallon Zarah da take cize le6e, haka yayi ta murza mata ahankali chan daga baya sai yakoma murzawa da k’arfi nan Zarah tasaki k’ara tare da rik’o hannunsa, Yarima cigaba yayi da murzawa inda yakejin kukan nata har cikin ransa haka yadaure yacigaba da murza har saida yaga kumburin ya d’an sa6e sannan yabarta, Zarah jikinsa tafad’a tacigaba da rusa kuka, rungumeta yayi tare da lumshe idonsa ahankali kamar mai rad’a yace kukan ya isa haka please,
Zarah cigaba tayi da kukan nan yarima yashiga d’an bubbuga mata bayanta ahaka tad’an rage sautin kukan nata, sun dad’e a haka daga k’arshe bacci yad’auketa
ahankali yarima yakwantar da ita tare da gyara mata kwanciyar sai alokacin yakula da hannunta da tak’one ya yi ja abunka da farar mace dan ma Allah ya taimaketa k’unar bata tashiba, shafa hannun yayi cike da tausayi nan zarah tamotsa, tausayintane yak’ara kamasa, har ya mik’e zai tafi sai kuma yaji baya iya tafiya yabarta dan haka yadawo yakwanta gefenta tare da zuba mata ido cike da tausayinta ahaka shima bacci yad’aukesa.

kiran sallar asubane yatashesa kallon zarah yayi da take baccinta sannan yaduba k’afar yaga kumburin ya safka ahankali yasafko daga saman gadon yashiga toilet d’inta yad’auro alwallah bayan ya fito a d’akin yashimfid’a darduma yayi sallah,

yana zaune saman dardumar yana addu’a zarah tafarka, ido tazuba masa cike da mamaki, cikin ranta tace kar dai ace nan d’akin yakwana?
Kallon agogo tayi ganin 6am yasa tatashi zaune dak’yar tare da safko k’afarta k’asa tamik’e tana fara taku d’aya tasaki wata irin k’ara tare da komawa tazauna.

Yarima cikin sauri yashafa addu’an yataso yazo inda take yace kin farka? Ya k’afar taki?
Zarah cize le6e tayi sannan tace dasauk’i, rik’ota yarima yayi yace muje kiyi alwallah,
Zarah k’engesawa take ahankali yarima yana rik’e da ita har suka shiga toilet, tsaye yayi yana kallonta ganin haka yasa Zarah tamarairaice fuska kamar zatayi kuka tace please kafita.
ta6e baki yarima yayi sannan yafita tare da janyo mata k’ofar.

Bayan ta gama knocking d’in k’ofar tayi nan yarima yabud’e yana rik’e da ita yazo da ita wajen darduma, saida yazaunar da ita saman darduma sannan yaje yad’auko mata hijab tasaka sannan yakoma saman gadon yazauna yana kallonta, daga zaune tayi sallar,

Bayan ta gama ganin tanaso tatashi yasa yarima yaje yad’auketa cak yamaidata saman gado yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta, Zarah shigewa tayi jikinsa nan yarima yarungumeta ahaka suka koma baccinsu.

Wajen k’arfe goma yafarka ahankali yazareta daga jikinsa sannan yamik’e yafita yabar d’akin yakoma part d’insa.
Nan yarubuta drugs yaba guard d’insa yace yasiyo masa sannan yashiga bathroom yayi wanka.

Bayan ya fito shiryawa yayi bai ko tsaya breakfast ba yafito saida yakar6i drugs d’in sannan yawuce part d’in zarah.

ko da yashiga bedroom d’in zaune take saman gadonta tana ta fama zata zage zip d’in rigarta amman ta kasa, shigowar yarima yasa tabisa da kallo, suna had’a ido nan tajanye idonta garesa tare da gaishesa,
Yarima saida yazauna gefenta sannan ya amsa mata tare da tambayarta ya jiki, zarah tace Alhmdllh sannan tacigaba da kai hannu zata zage zip d’in rigar,
Ganin takasa yasa yarima yakai hannunsa zai zage mata, zarah kallonsa take shima yazuba mata ido suna kallon juna bata san lokacin da yazage zip d’inba saidai ji tayi ya salu6e mata hannuwan rigar ta safka k’asa, zaro ido tayi cikin sauri tafad’a jikinsa tarungumesa tareda kare k’irjinta,
sun dad’e a haka sannan yarima yajanyeta daga jikinsa tare da d’auko towel d’in da yaga an aje gefe yamik’a mata, cikin sauri zarah takar6a tad’aura tare da duk’ar da kanta k’asa cike da jin kunya,

Cike da rashin damuwa yarima yamik’e sannan yace muje inrakaki toilet d’in, zarah bata musaba tamik’a mai hannunta yatasheta tsaye yana rik’e da ita har suka shiga toilet sannan yafito tare da jawo mata k’ofar yakoma saman gado yazauna yana jira tafito.

Bayan kamar minti goma sai gata tabud’e k’ofar, cikin sauri yarima yaje yarik’ota yazo yazaunar da ita bakin gado sannan yad’auko mata lotion tashafa, Bayan ta shafa magani yad’auka yashafa mata a k’afar yana d’an murzawa zarah saboda zafi har da ‘yar k’wallarta, dakansa yaje yabud’e wardrobe yad’auko mata kaya yamik’a mata sannan yaduba agogon hannunsa yace bari insa akawo miki breakfast kiyi sannan ga tabs nan kisha guda biyu ni nawuce hospital,

Zarah binsa tayi da kallo har ya juya ya fara tafiya tace am bakajiba,
tsayawa yayi cak batare da ya juyoba, ahankali tace nagode sosai da taimakon da kayi min.
Yarima murmushi yayi sannan yabud’e k’ofar yafita.
Zarah ma murmushin tayi nan tafara saka kayanta.

Bayan tagama nan aka kawo mata breakfast tayi sannan tasha magani takoma takwanta, tunda takwanta tunanin yarima kawai take musamman ma idan tatuna hidimar da yayi mata daga jiya zuwa yau dan batayi tunanin samun hakan daga garesaba ta dalilin haka har yakwana part d’inta, murmushine yasu6uce mata, wani irin sonsane taji yana fizgarta.

 

A chan 6angaren gimbiya sumayya koda kuyangarta tazo mata da labarin abinda yafaru da zarah tayi murna sosai har d’aga hannuwanta tayi tai ddu’a Allah yasa ta sanadiyar haka zarah tagurgunce a ranar baccinta tayi cikin jin dad’i da kwanciyar hankali.

 

Wajen k’arfe 12pm zarah ce a parlour zaune saman cushion ta mik’e k’afafuwanta, gefenta plate ne mai d’auke da tufa tana ci, sumayya ce tashigo da sallamarta fuskarta d’auke da murmushi.

Ba zarah ba hatta kuyanginta sunyi mamakin ganinta cikin wannan yanayin, gaba d’ayan kuyangin zarah suka duk’a suka gaisheta
Sumayya nuni tayi musu alamun subar d’akin.
Cikin sauri suka tashi suka fita,
saman d’aya daga cikin cushin d’in tazauna har a lokacin fuskarta d’auke da murmushi takalli zarah da tazuba mata ido tace gimbiya zarah ashe tsautsayi yafad’a miki, gaskiya banji miki dad’iba toh waima garin ya hakan takasance da ke? Ke bama hakaba Ina fatan dai baki gurgunceba.

Zarah tunda sumayya tafara maganar tazuba mata ido cike da mamaki, chan sai tayi murmushi tace kar kidamu tsautsayi ne da k’addara, kuma da kike maganar gurgwancewa ko da ace na gurgunce ai ba abun damuwa bane tunda Allah ne daman yabani k’afar dan ya kar6a alokacin da yakeso shine zan damu bayan naci moriyarta? Inaso kisani ni nayarda da k’addara nasan duk abinda zai sameni daga ubangijine.

Ta6e baki sumayya tayi tace hakan ya yi kyau saidai fa natayaki murna da baki nakasaba dan kinsan babu yadda za’ayi yarima yazauna da gurguwa.

‘Daga mata hannu zarah tayi tace please ya isa haka idan kin gama abinda yakawoki zaki iya fita dan a yanzu banda lokacinki.

Dariyar mugunta sumayya tayi sannan tamik’e tsaye tace dakyau zarah am naga kamar kina jin jikin buguwar da kikayi bari dai inbarki kid’an samu kihuta saidai ince sai mun had’e a karo nagaba.

Murmushi zarah tayi tace kar kidamu nagode sosai, saduwar alkhairi.

nan sumayya tawuce tafita daga d’akin zarah binta tayi da kallo sannan daga baya tajinge kanta a jikin cushin d’in da take tare da maida numfashi

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_*Sak’on gaisuwa mai tarin yawa agareka Dr S Fulani*_

_Yau page d’in nakine *Sadiya Sidi Sa’id*, ko da ace sau goma zan mallaka miki page toh bazan ta6a gajiya ba saboda cancatarkice tasa haka, nagode sosai da soyayyar da kike nunamin_

Back to top button