Kurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 21

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E21_

 

*Daga alƙalamin Boss Bature*

 

A ƙalla sun shafe mintuna suna kallon Allon tsafin, ga dukkan alamu sun girgiza da ganin abun da idanuwan su ke gane masu, Hankulan su sun yi matuƙar tashi, abun ya yi mugun ɗaure masu kai, bakomai bane suke kallo acikin Allon tsafin face Garkuwar kurkuku tare da Angel, duk wani motsinsu akan idonsu tamkar video haka suke ganinsu, lokaci ɗaya Allon tsafin yayi duhu hoton fuskokin su ya 6ace.

Kowan nan su ya sauke Ajiyar zuciya, sun natsu suna jiran jin bayani daga bakunan shuwagaban nin su.

Ɗaya daga cikinsu ne yai gyaran murya, da wata irin kakkausar murya mai sautin gaske tamkar bata mutun ba, ya soma Yin magana Cikin harshen su na shahararrun matsafa ni kuma ina fassara maku.

“Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu miƙe tsaye mun nema ma kanmu mafita ba, to tabbas za’ayi nasara akan mu, Ko a tarihi ba’a ta6a samun prisoners ɗin da suka tsira daga kurkukun ƙaddara ba, su ne na farko kuma sune na ƙarshe, da farko sunyi nasarar ƙetare kurkuku da taimakon Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani mahaluƙin da ya isa ya iya ƙetare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya ɗauke shi munyi nasarar yi mashi abunda ya dawo gare mu sai dai wani abun al’ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi, kamar yadda kuka gani a allon tsafin mu, shin me ya jawo hakan”? Yai tambayar yayin da yake gyaran zaman shi.

Mutumin dake a gefenshi, Ya ɗaura da cewa”Yarinyar da ke atare da shi itace silar komai, kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, Cewa itace za ta yi silar tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara, gangancin da mu ka yi shine Haɗa su wuri ɗaya da garkuwar mu, sakamakon shaƙuwar da sukayi a tsakanin su, taja shi ga faɗawa tarkon sonta, mu kan mu bamu ta6a tsammanin Garkuwar prison zai Iya kamuwa da matsanancin so irin haka ba” dakatawa yai da yin maganar yana motsa yatsun hannunsa, kafin ya cigaba da cewa

“Sai dai har yanzu bamu rasa power ɗinmu ba, Garkuwa namu ne har abada, mu ke ruƙe da masarrafin da zamu Iya sarrafa linzamin shi, mu kaɗai ne mu ke da iko da shi, ba zamu ta6a yin danasanin Ɗaura shi amatsayin magajin kurkukun ƙaddara ba, kuskure ɗaya da muka tabka shine sakacin da mu ka yi da har ya samu nasarar guduwa daga kurkuku, Ni ban damu da sauran Yaran da suka ku6uta ba, saboda basu da amfani a wurinmu, mun ci moriyar su, mutun ukun ne sune rauninmu, Na farko Garkuwarmu dole sai da shi za’a Iya Cin galaba akanmu, Na biyu ƙaddarar kurkuku, yarinyar ta fi sauran hatsari tun da har ta Iya Jan hankalin garkuwarmu, wanda nayi imanin da ace babu ƙauna a tsakanin shi da yarinyar ba zai ta6a taimakon sauran ƴan uwan shi don su gudu daga tarkon mu,” Ya faɗa yana mai jan dogon numfashi Ya fetsar da shi, ya cigaba da faɗin “Itace silar komai, kuma itace kaɗai zata Iya sarrafa shi bayan mu, idan kuwa hakan Ya faru zai Iya fallasa mana sirrin mu ya kuma taimaka wurin ruguza kurkukun ƙaddara”! Da ƙarfi Ya ambaci hakan Yana mai nuna fusatar shi.

“Yarinya ta ƙarshe itace bugun zuciyar kurkukun ƙaddara, kamar yadda ya zo mana a allon tsafin mu, idan har muka samu nasarar Cire Zuciyarta daga ƙirjinta zamu samu ƙarfin Iko fiye da wanda muke da shi a yanzu, Ita kuma ƙaddarar kurkuku dole mu dawo da ita cikin mu idan har muna son ta zamar mana ƙaddara mai kyau, barin ta awaje shi zaisa ta zamto mummunar ƙaddara agare mu” Tamkar mayunwacin zaki haka yake kora masu jawabi yana fitar da huci.

Bayan ya rufe baki Na gefen shi ya soma magana da wata irin murya ta dattawa waɗanda suka Shahara a fagen zalunci.

“Tun fil azal, Banso Muka damƙa amanar mu ga tsohuwa tamira ba, dama tun lokacin Sai da na musa akan hakan, Ni dama nasani Jinin Habibullah ba zasu ta6a zama amintattun mu ba, sai gashi sun yaudaremu sunci amanar kurkuku, sun kashe mana Zafreen ɗaya daga cikin shuwagabannin mu, babu wanda ya ta6a tsammanin zasu Ci amanar mu ita da ɗanta Salsabeel, sai da suka bari mun basu yarda mu su kuma suka butulce mana, haƙiƙa Nayi takaicin rasa gangar jikin tamira, da ba abun da zai hana mu azabtar da ita, mu sa6ule naman jikinta sannan muyi farfesun shi muba ma Karnuka su shanye roman, amma duk da haka bamu makaro ba, Zamu huce haushin mu akan ɗanta Salsabeel” mutumin da yayi maganar babu ɗigon imani akansa.

Bayan ya dasa aya a maganar shi, wani daga cikin shuwagabannin Ya numfasa tare da cewa”Garkuwa ya yi mana mummunar 6arnar da ba zamu Iya gyarata ba, bamu ta6a tsammanin zai Iya yi mana haka ba, sai dai ba zamu Iya hukunta shi ba, saboda shi jinin mu ne, abu ɗaya da zamu Iya yi mashi shine mu hana shi jin daɗin rayuwarshi da Yarinyar, mu shiga tsakaninsu, horon da zamu bashi kenan, sannan zamu ci gaba da sarrafa shi wurin azabtar da mutane, kafin muyi nasarar dawo da su Cikin mu, hikmar yin hakan mutane zasu fara tsoranshi suna nuna mashi ƙyamata, zai ji duk duniya kamar ba’a sonshi ne, kunga anan zai yi tunanin mu kaɗaine gatanshi, kurkukune kaɗai inda zai zauna yayi rayuwarshi ba tare da ƙuntata ba, daga lokacin daya fara wannan tunanin mu kuma zamu samu damar kwashesu su ukun mu dawo da su cikin mu”! Ya kai ƙarshen maganar tare da buga hannun arm chair ɗin da yake a zaune, gaba ɗaya matsafan suka fashe da dariya mai sautin gaske tamkar ana bubbuga ganga, jikinsu har jijjiga ya ke yi saboda tsabar yadda suke yin dariyar kamar dokuna.

“Mun Fi ƙarfin mutun, Ko mutuwa tsoron tunkararmu take Yi, shiyasa muka daɗe muna sheƙe ayarmu, shan jinin mutune da cin tsokar naman su yanzu muka fara, Rainon Yara ba zamu fasa ba, zamu cigaba da tarasu a cikin kurkukun ƙaddara muna biyan buƙatarmu dasu domin samun ƙarfin ikonmu” Ihu suka dinga Yi sunayin shewa sautin muryoyinsu tamkar zasu fasa bangon Fadar, kusan atare matsafan suke miƙe tsaye suna taka rawarsu ta matsafa, kowan nan su, ya ɗauki abunda yake ra’ayin ci asaman table wasu giya, wasu farfesun naman mutun wasu jini wasu kuma naman dabbobi suke ci, Yayin da wasun su a tsaye suke saduwa da junansu kamar dabbobi wa’iya zubillah.

*DAULAR OBIE ESTATE*

*Dr. jazz❤*

Ƙudundune yake acikin bargo, saman katafaren gadonshi na gidan Sir mubarak, cikin muryar raɗa yake yin magana a wayar shi.

“I’m not working today, I’m at home. yanzu haka da ni ke yi maka magana Ina akwance saman gadona” shiru ya ɗanyi yana sauraron mutumin da suke yin wayarshi, can yaci gaba da cewa”Boss Man kasan bana wasa da aikin ka, idan ka bani umarni jiki na rawa nike yin shi, ko jiya na shiga gidan gonar na duba lafiyar kajin, sai dai muce Alhamdulillah, Jikin su yayi kyau baka ga yadda suke tafiya ba tsokar jikinsu har girgiza take yi saboda ƙoshin lafiyar dake gare su” ya ƙare maganar muryarshi da sautin dariya

“My Boss Man, Amma dani da kai zamu ɗubi na azumi ko? Ko zamu bari sai sallah Ayi layya da su”? Tuntsirewa yayi da dariya jin amsar da mutumin ya bashi muryarshi cikin harshen turanci yake yi mashi magana.

“Amma ai kasan nayi ƙoƙari, tun da na fara kiwon kajin nan wlh ko ɗaya ban ta6a gigin kamawa don in yanka ba, kuma miyau na ya biya fa” da shagwa6a ya ƙare maganar.

Abun da bai sani ba, tun da ya fara yin wayar, Sir mubarak Ya shigo ɗakin jikinshi sanye da kakin sojoji, Hannunsa biyu ruƙe da faffaɗan plate, daga saman shi an jera Chocolate raspberry cupcakes.

Ya shigo ɗakin ne da niyar ya faranta mashi, tun lokacin da turai ta faɗa mashi game da gorin da Hajiya saratu ke yi mashi akan cewa shi ba mahaifin shi bane sai yaji ya ƙara ƙaunar yaron yana matuƙar sonshi.

Lamarin Ya ɗaure mashi kai, ba tun yau ba, Ya jima yana mamakin wayar da dr jazz ke yi akan Kajin gidan gona, cikin tafiyar sanɗa Sir mubarak Ya ƙarasa shiga ɗakin ya zauna gefen gadon shi hannun shi ruƙe da plate din, Ya kasa kunne Yana sauraron tattaunawar jazz da Boss man din shi.

Jin shiru Jazz bai ƙara yin magana ba yai tunanin ko ya kammala yin wayar ne, Gyaran murya ya yi mashi.

Jazz da ke ƙudundune cikin bargo yai lamo jikinshi ya kama yin kerma jin muryar Sir mubarak Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba.

“Jazz nasan idonka Biyu Ka tashi inason magana dakai” A hankali Ya zame bargon, Ƴar singlet ce ajikinshi tare da Gajeran wando, sumar kanshi duk ta hargitse.

Yana faman mutsustsuke ido da hannu ya saci kallon Sir mubarak
Muryarshi da kasala Ya furta
“Daddy ina kwana, ka tashi lafiya, ya mommy’ adabarbarce ya ambaci hakan sam bai lura da plate din hannunsa ba.

Babu alamun zai amsa mashi gaisuwar tashi, wani irin kallon tuhuma Yake jefa mashi, Ƴan kame kame jazz ya kama Yi, don Ya fahimci dadyn nasa yaji komai da ya ke faɗi a wayarshi.

“Jazz, da wa ka ke yin magana a waya? muryar shi a kausashe Ya jefa mashi tambayar.

Cikin rawar murya Jazz yace”daddy abokina ne dr fawan ai na faɗa maka tare da shi muka buɗe gidan kaji muna yin kiwon su’ yaƙi yarda su haɗa ido da uncle mubarak.

Gyaɗa kai yai”Jazz zan ƙara jan kunnanka akan Ka kiyaye mutanan da za ka yi mu’amala dasu! Bana son kayi abunda zaka Yi danasani, Ni bana zargin ka da wani abu, Ina yi maka kyakkyawan zato My son, Nasihar da zanyi maka shine Kaji tsoron Allah komi za ka yi a duniyar nan kada ka manta Allah Yana ganin ka, kuma zaka koma gare shi ne, jin daɗin duniyar nan ƙalilan nan komai da muka samu anan zamu barshi, a kowani yanayi na rayuwa mutawa zata Iya riskar mutun, me yakamata muyi? Mu kasance muna aikata aikin Alkhairi akoda yaushe, sannan duk runtsi duk wuya kada ka ta6a karya zuciyar wanda ya aminta dakai…..” cikin kwantar da murya Sir mubarak Yake yi mashi nasiha, jikinshi duk yai sanyi, idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla Ya ɗago Yana kallon fuskar Sir mubarak, Har Ila yau yana mamakin Halin Sir mubarak da Obinna suna da mutunci da daraja ɗan adam, duk da kasancewar shi ɗan mai aikin gidansu sun maida shi tamkar jinin su, tun kafin Ya mallaki hankalinshi suke yin ɗawainiya dashi, cin shi shan shi suturarshi da karatun shi sune suka ɗauki nauyin komai na rayuwarshi.

Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar sir mubarak ta katse shi”Ina magana ka tsareni da ido” da sauri Ya sunnar da kanshi ƙasa, Ƙwallar da suka taru cikin idonshi tuni sun soma gangarowa saman kuncinsa.

“Jazz Why are you crying”? Ya faɗa yana duban face dinsa.

cikin shessheƙar kuka ya soma magana”nagode sosai daddyna, ina matuƙar alfahari dakai, saboda ƙaunar da kuke nuna mun kai da baba, ban ta6a danasanin kasancewata acikin family dinku ba, Ina jin daɗin nasihar da ka ke yi min daddy, ka maidani tamkar ɗanka komai na rayuwa kana Yi min…” murmushin gefe fuska sir mubarak yaɗan saki.

“My son ya isa Haka, share hawayenka, Ni dai fatana Ka ruƙe mutuncinka Jazz, Kada ka bani Kunya, inaso ka zama abunda duniya zata yi alfahari dakai”

Jinjina kai yai tare da ɗago da kai Ya ɗaura rinannun idanuwanshi akan fuskar Sir Mubarak “In sha Allah, Nayi maka alƙawarin hakan, Zan kama mutuncina kuma bazan ta6a baka kunya ba”

Miƙa mashi plate din hannun shi yayi

“Your mother made this for you. I know how much you love cupcakes.” fuskarshi ɗauke da ƙayataccen murmushi Yake dubanshi, Hannun Dr Jazz Har kerma Yake yi wurin kar6ar Plate din
“Kayi brush kuwa? Naga kamar yanzu ka farka daga bacci,”

Girgiza kai yai”ban kaiga Yi ba, Yanzu zan shiga toilet din’
“Okey, Ka ajiye plate din idan ka fito sai kaci” ƙaƙaro murmushi yai akan face dinsa”Okay, Dad, I appreciate your care.”
Miƙewa sir mubarak Yai”Ni zan wuce Office, ka kula mun da kanka”

“Daddy Allah Ya dawo min dakai Lafiya, Allah ya tsare mun ya kare mun kai daddyna”

Yaji daɗin maganar Jazz, har saida ya dan juyo ya kalle shi kafin Ya fuce daga ɗakin”
Nauyayyar Ajiyar zuciya Jazz ya sauke, kalaman Sir mubarak sun tsaya mashi aranshi, Cikin sanyin murya ya furta”Am sorry My daddy, Na riga dana jefa kaina Cikin Tarkon da bazan Iya fidda kaina ba, addu’arka kawai nake buƙata Allah Ya bani ikon cinye jarabawar nan”!! Ya ƙare maganar tare da saukowa daga saman gadon ya ɗaura plate din hannun shi saman Table Ya nufi toilet Ya shige.

*Hajjaty the head maids*

A tsanake Take Yin tafiya tana nufar haɗaɗɗen garden din gidan, ta ɗauki wankan Sari Launin Ja, Hannunta biyu ruƙe da Tray na Kayan Marmari tare da mugs biyu na black tea, ta ko’ina ƙamshin turare ne ke fita a jikinta, tasha uban ado na sarƙar wuya da awarwaro, make up din fuskarta Ya ƙara mata Kyau.

Tun kafin ta ƙarasa shiga garden din idanuwanta suka hango mata, Obinna tare da babban amininsa daya kawo mashi ziyara, kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane Inyamuri ne, fari ne fat sumar kanshi da jagirarshi dukkansu hurhurace, hatta dogon Gemunshi fari ne fat kalar na Obinna, sunyi shigar Manyan Kaya na hausawa, zaman hular kanshi zai ƙara tabbatar maka da ƙabilar shi, suna a zaune saman shimdiɗar da Hajjaty tayi masu ta alfarma, kowan nan su ya tada kanshi saman tuntun kalar na sarakuna.

Tun kafin ta ƙaraso gabansu, ƙamshin turarenta Ya daki hancinan su, abokin obinna Ya furta”masha Allah” Ya kafe ta da ido yana faman Jan gemunshi.

Zuƙunnawa tayi agabansu Ta sauke tray din, cikin girmamawa ta gaishe da abokin”sannu da zuwa, ina wuni Ya iyali” lumshe idonshi yai tare da ware su kan fuskarta, Obinna dake kallonshi ya fahimci kamar baya a hayyacinsa, hajjaty ta tafi da imaninsa, har Ya gaza buɗe baki Ya amsa mata gaisuwarta, Sai faman bin jikinta yake yi da kallon ƙurulla duk tabi ta tsargu.

“Ba ka ji tana gaishe ka ba ne”? Sai da obinna Ya ambaci hakan tukunna Ya iya motsa la66ansa wurin furta”Lafiyalou madam, fatan na same ku lafiya”? Muryarta na rawa ta furta lafiya lou

“Obie, dama matarnan tana agidan nan har yanzu? Yayi tambayar ne saboda lokacin da tazo yi masu shimfiɗa bai kaiga zuwa gidan ba.

Harara obinna ya ɗan watsa mashi a fakaice, kafin ya bashi amsar tambayar shi sai da ya fara kallon hajjaty yace”tashi ki tafi, mun gode” miƙewa ta yi tare da juya ta nufi hanyar fita garden din tsabar sauri kamar zatayi tuntube.

Bayan tafiyarta obinna ya dubi aminin nasa”shegen bisa, faɗamin waya koya maka kallon mata? Ni dai ya iya sanina dakai mace bata agabanka, sai gashi yau kana neman zauce wa saboda kaga Mace” da zolaya ya yi mashi maganar.

Tuntsirewa Inyamurin yai da dariya yana faɗin”Don kawai na gani na yaba, matar ce ba ƙaramin burgeni take yi ba, inason mace mai tsafta da iya ado, sannan kasan Ni ma’aboci son ƙamshine, gaskiya ta tafi da imanina, ka taimaka min inaso na mallake ta, dagaske nake ba wasa ba”

Da mamaki akan fuskar obinna ya ɗan zaro idona yana kallon shi, yayi mamakin jin abun da ya furta, kuma ga dukkan alamu dagaske yake har cikin ranshi.

“Amma dai zolaya ce wannan ko”?
Jan gemun shi yai tare da cewa”na ta6a yi maka zolaya akan irin wannan maganar”? Girgiza kai Obie yai” Bamu ta6a ba, sai dai nayi mamakin kalamanka, tun da muka taso baka ta6a nuna kana buƙatar mace ba, ka haramtawa kanka tara Iyali, gaba daya rayuwarka akan kasuwancinka ta ƙare”

Fuskar Inyamurin da fara’a ya yace”wannan karan dagaske nake, Inasonta da aure mutumina, ka yi min hanyar da zan samu shiga wurinta, don bana son abun ya ɗau lokaci” farin cikine tsantsa akan fuskar obinna abunda yajima yana yi mashi fata

“In sha Allah, zanyi maka ƙoƙarin yin hakan, nima nayi maka sha’awar auranta, Matar tana da hankali da natsuwa”

Cigaba da tattaunawa sukayi a tsakaninsu.

A 6angaren Hajjaty kuwa, Jikinta duk yai sanyi tun da ta baro garden din gabanta ke faɗuwa, tsigar jikinta na tashi, duk akan kallon da abokin obinna yayi mata.

Gaba ɗaya hankalin ta baya atare da ita, tafiya ta ke yi Zuciyarta nayi mata saƙe saƙe, har ta ƙaraso entry hall tana ƙoƙarin bi ta ƙofar palourn Cikin rashin sani suka bangaji juna ita da Hajiya saratu da ke ƙoƙarin fitowa daga falon, Ta kimtsa cikin shiga ta alfarma, da alama wurin aiki zataje.

Da sauri Hajjaty ta ɗago su ka yi tozali da Hajiya saratu, Rass taji gabanta Ya faɗi, Muryarta na kerma ta furta”kiyi haƙuri ban lura dake ba…” daƙyar ta ƙare maganar ganin irin ƙasƙantaccen kallon da Hajiya saratu ke watsa mata.

Tana huci ta furta”baki da hankaline? Ko makauniya ce ke? Wato tsabar nuna isa har kin kai matsayin da zaki iya haɗa kafaɗa ni ko”! Fuskarta a ɗaure tamau tayi maganar.

Hankalin Hajjaty ba ƙaramin tashi yai ba, sam bata lura da pravin dake abayan Hajiya saratu ba, Ya shirya cikin black suit, hannunshi ruƙe da wayarshi daya kara a kunnanshi, Waya yake yi amma hankinsa na akan Hajjaty da hajiya saratu

“Bada sanina na bangaje ki ba, hankalina baya atare dani”

Harara Hajiya Saratu ta watsa mata tamkar ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa”Ƴar rainin wayau, wai bana hanaki shafa mahaukacin turaren nan a jikinki ba? Ke baki da hankaline? an gaya maki Zawarci haukane” Rai a6ace ta faɗi hakan tare da ruƙo Mayafin Sarin Hajjaty da hannunta.

Idanuwanta tuni sun ciko tab da ƙwalla.

“Wlh daga rana irin ta yau idan na kuskura na ƙara jin ƙamshin turaren ƴan borin nan naki saina sauke maki kwandon rashin mutunci akanki,”

Azafafe ta ƙare maganar, tare da ingiza hajjaty tayi taga taga zata faɗi, Pravin harya Yunƙura zai tarbeta, da sauri Ya fasa ganin matsiyacin kallon da Hajiya saratu ta watsa mashi

“Wuce muje” cike da isa ta ba shi umarni, da sauri Yabi bayanta suka nufi parking space.

Da ido hajjaty tabi su da kallo, hawaye tuni sun wanke fuskarta, jikinta na rawa ta nufi cikin gidan, masu aikine ke ta kai komo acikin babban palourn.

Ba tare data bari sunyi tozali da wani ba, tayi saurin nufar bedroom dinta, harta kusa shiga taci karo da twins sunyi shirin zuwa office.

Atare suka ɗago suna kallonta, muryarta na rawa ta furta”ina kwananku kun tashi lafiya”
Harara Zayn ya watsa mata”ji wata tambayar rainin wayau nan, taya zaki tambayi mun tashi lafiya? Bayan gamu kin gan mu a tsaye kan ƙafafunmu”

Zaid yace”Zayn, please watch your tongue Hajjaty tamkar uwa take agare mu,” a harzuƙe yace”what! ƴar aikin ce zata zama uwar mu? oh Ko dan saboda tana ƴar india? To ai mu ba indiyawa bane ubanmu ne ɗan can, Nifa baki burgeni saboda ban yadda dake ba, ina zargin hada ke ake cin amanar mahaifiyar mu”

Afirgice Hajjaty ta zazzare ido tana duban fuskar zayn da yayi mata, tuni zufa ta soma tsastsafo mata.

“Pls zayn ya isa haka, idan ba zaka girmamata ba, bai kamata kana gaya mata magana akan idonta ba” yai maganar tare da jan hannun Zayn suka nufi hanyar fita palourn.

Ba zata Iya jure wulaƙancinsu ba, da sauri ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta faɗa saman gado ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita.

Hajiya saratu tuni ta shige cikin mota, pravin na atsaye ya ruƙe murfin motar”Lafiya? Ba zaka shigo bane”? Tayi maganar tana dubanshi ganin yaƙi motsawa Ya kafe ta da ido.

“Bana so na 6ata maki lokaci, Ki tafi kawai Ni zanje a motata” da mamaki akan fuskarta tace”saboda me”?

“Cikina ne Ya 6aci ina buƙatar shiga toilet, ” yai maganar yana shafa flat stomach dinsa
Ta6e baki tai sam bata kawo komai aranta ba tace”Okey, saina dawo” duƙowa ya yi saitin fuskarta ya manna mata peck a fore head dinta”Ki kulamin da kanki My wife, zanyi missing dinki, Ni kona minti ɗaya banaso kiyi nesa dani” kwa6e fuska tayi

“kalaman ka ba zasu hanani tafiya office ba, sai dai su 6ata min lokacina, pls ka kula min da kanka,” murmushin yaƙe ya sakar mata, Aranshi bai ji daɗin maganarta ba, halinta ne bata Iya kalaman soyayyaba kuma ba ta cika son yana yi mata ba.

“please take care of ur self, ayi aiki lafiya”ya ƙare maganar tare da tura murfin motar ya rufe mata ita.

Security din dake zaune a driver seat na motar yaja ta suka nufi shantalelen titin da zai fiddasu daga estate din.

Shu’umin murmushine Ya bayyana akan fuskar Pravin, Jiki na rawa Ya juya ya nufi entry hall, adai dai lokacin twins sun fito hannunsu ruƙe cikin na juna suka ci karo da shi.

Gaba daya suka tsareshi da ido suna kallon shi
Fuskarshi da fara’a ya furta”Kyawawan samarina har Kun kammala Shiryawa za’a tafi office,” zaid ne yai ƙoƙarin faɗin”daddy, ina kwana ka tashi Lafiya” Ya amsa mashi da lafiyalou My son, kafin ya maida dubanshi ga Zayn da ya haɗe rai.

“Lafiya zayn ka tsare ni da ido? Ko ba ka da lafiya ne”? Basarwa yai”lafiyata qalou daddy, just nayi missing dinka ne, amma ya akai daddy naga ka dawo gida? Ba aiki zakaje ba”?

“Key ɗin mota ɗina na bari a ɗaki, shi zanje na ɗauko” zayn yace”bari na ɗauko maka key din” yai maganar yana ƙoƙarin juyawa a hanzarce pravin ya damƙi hannunsa”bana so ku makara yakamata ku wuce ku tafi office, zanje na ɗauko da kaina, Ku kulamin da kanku,’ bai jira amsar su ba, yabi ta gefensu ya nufi cikin falon.

“Zaid sai da na faɗa maka matarcan baƙar munafuka ce, saboda ita daddy yayi mana ƙaryar zai je ya ɗauko car key a ɗaki” Yana huci yayi maganar
Zaid yace”please bro, ka yi mashi kyakkyawan zato, bai kamata kana zarginsu ba”

Tsoki Zayn yaja”wlh duk ranar dana gano ainihin abunda suke aiwatarwa saina tona masu asiri awurin mommy, ita kuma matar can saina koreta daga gidanmu ta koma can ƙauyansu na Indiya,” ya ƙare maganar tare da jan hannun zaid suka nufi motarsu.

Hajjaty na akwance cikin mawuyacin hali, idanuwanta sunyi luhu luhu sun rune zuwa Ja, sai faman shessheƙar kuka take yi, Har ya shigo ɗakin bata sani ba, Haye wa yai saman gadon ya zauna daga gefenta, Cikin sanyin murya Ya furta”My heart beat” har cikin kunnanta ta ji muryarshi, sai dai takasa ɗagowa ta kalle shi, hakan Ya tabbatar mashi da ranta Ya 6aci.

“kiyi hakuri, banji daɗin kalaman da saratu ta furta maki ba, ba yadda zanyi ne shiyasa ban dakatar da ita ba, nasan ranki ya 6aci but pls ki daure,”

Cikin shessheƙar Kuka tace”bazan iya jurewa ba, nagaji nagaji nagaji da irin wulaƙacin da suke Yi mini, sun tsaneni basu ƙaunar ganina, ita da zayn shima yaci mutuncina, zaid ne kaɗai ke ƙaunata”

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya, Kafin Yace”pls Ki ɗago muyi magana”
“Ai bana son kallonka, raina ƙara 6aci yake yi” lumshe idonshi yai haɗi da ware su saman Bayanta.

“Ban ji zafin kalamanki ba, saboda laifina ne, Ni ne silar komai, ” sai da yai wannan furucin ta ɗago da kanta, tana fuskantar ceilling, taƙi Yarda su haɗa ido.
Ba zato ba tsammani taji Ya kwanto da kanshi saitin fuskarta, ƙamshin turarensu ya addabi hancinansu.

“Ki faɗamin me kikeso nayi maki wanda zai kwantar maki da hankalinki”
Harara ta watsa mashi muryarta da shagwa6e ta furta”pls ka tashi ka tafi office, ka zauna kana 6ata lokaci akaina”
“Saboda kin cancanta ne, lokacina nakine, har aikin sai in fasa zuwa idan kinaso” Yai maganar Yana kashe mata ido.

Batasan ya akai ta tsinci kanta da sakar mashi murmushi.
“Inaso na faranta maki, don haka ki shirya dama kin faɗamin kinason haihuwa” zare mashi ido tayi’acikin gidan nan? Salon aganni da ciki a tuhumeni” da zolaya yace”sai kice na Obinna ne, kinga shikenan kin kashe bakin magana’ fashewa sukayi da dariya cike da nishadi.

“Idan hakan ta faru ko kowa zai ƙyaleni, Hajiya saratu saita kasheni” jan kumtunta yai da hannunshi”Ai ko dana kasheta nima,” lumshe ido tayi”pravin ka tashi ka tafi office aiki na jiranka.

‘Waya faɗa maki Ina yin aiki ni? Nifa salary kaɗai nake kwasa, bana yin Aikin komai ko naje office din, P.a dina ke taimaka min,” ya ƙare maganar tare da ɗaura tafin hannunsa ɗaya saman chest dinta, a hankali yaci gaba da yin squeezing dinsu, numfashintane ya soma canzawa ta soma cizon la66anta.

“Faɗamin Ina kika je”? Cikin yanayi najin shauƙi ta amsa mashi da cewa”Garden naje kaima Obinna da amininsa Kayan marmari” ganin ya ɗaure fuskarshi yasa tace”lafiya’
“Mutumin bai kwantamin araina ba! Bana son kina zuwa wurin obinna idan abokanansa suka zo, dattawan nan shegen son mata garesu, musamman irinki babu namijin da zai ganki ya kawar da idon shi”

Ta6e la66anta tayi yayin da suke kallon juna “Are you jealous of me?Meyasa shi obinna baka kishi da shi sai abokanan…” kasa ƙarasa maganar ta yi jin ya mannata da ƙirjinshi”saboda shi na yarda dashi, bazai ta6a nuna kwaɗayi akanki ba, dattijon yana da kamun kai, kuma baida burin ƙara aure tun da matanshi suka rasu, shi ko amininsa Jan kunne tsaf zai Iya cewa yana sonki”

“Idan hakan Ya faru mai za ka yi mashi” tayi maganar tana shafa Wuyanshi da yatsun hannunta.
Kashe mata ido ɗaya yai kafin Ya bata amsa da cewa
“Gemun shi zan tsige” dariya suka saki, da sauri Ya haɗe bakinshi da nata, Hannayenshi Biyu tallabe da kanta tamkar zasu cinye harsunan junasu.

*San Antonio Texas*

*Army headquarter*

Babbar headquater ce mallakin sojojin san antonio, Haɗaɗɗen gini mai girma da faɗi, launin fentin head quater din army green ne, Tun daga bakin entry way na shiga headquater din zaka fara cin karo da Giant soldiars Cikin ta da wajenta maƙil Yake da Gwarazan sojoji sadaukan Gaske masu ƙirar zakuna, kowan nan su Ya kimtsa cikin shiga ta Kakinsu, ƙafafuwansu sanye da army boots, sun ruƙe Jibga jibgan bindigu a hannuwansu, haka zaika ƙugunansu a soke suke da pistols, babu wasa akan fuskarsu cikin taku na majiya ƙarfi suke kewage ko’ina na Gate din shiga headquater din.

Danƙareriyar motace Haɗaɗɗiyar gaske mai numfashi ƴar ubansu ƙirar Mercedes-benz S-class launin black ta sharoro da matsakaicin gudu kaitsaye ta nufi Bakin Hq din, tunkafin ta ƙaraso sojojin suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen ne wannan ɗan kasada mai shirin zuwa lahira yake yi masu tuƙin ganganci a saman titin su.

Sai da mai motar yakusa zuwa gabansu, Ya rage gudun motar, tamkar na cikin motar baisan da sojojin dake tsaron headquater dinba, Ya soma ƙoƙarin kutsawa zai ƙetare gate din, aiko kamar mayunwatan zakuna suka tunkari motar, Wasu fusatattu daga cikinsu tuni sun saita motar da bindigar hannusu, da kakkausar murya suke faɗin

“Hey! Stop the car! Otherwise we’ll attack you”!

Gaba ɗaya sun kewaye motar, Da ƙarfi wani baturen Soja Ya daki gaban motar da tafin hannunsa tamkar zai 6alle ta, A harzuƙe ya furta

“Ka sauke glass ɗin motar, Idan ba haka ba zaka fuskanci horo mai tsanani daga gare mu”

duk wannan suratan da sukeyi na cikin motar yaƙi fitowa babu alamun zai buɗe murfinta, Hakan ba ƙaramin hayaƙa su yayi ba”

“You’re running out of time. I want you to come out of the car now! If you don’t, I won’t hesitate to shoot! This isn’t a game, I’m serious. you have five seconds!” baturen sojan da ya dafe motar da tafin hannunsa ne Ya furta hakan, Sai da suka gama harzuƙa Zuciyarsu a maƙogaro, a lokacin da basuyi tsammani ba, mamallakin motar Ya tura murfin Ya buɗe, Rai 6ace suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen ne wannan uban Ji da kan.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button