Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 28

Sponsored Links

Alhamdulillah angama sauka lafiya kowa sesa musu albarka yakeyi anata hotuna Abba da baba kuwa se hira sukeyi kamar wayanda suka dade da sanin junan su duk dade abba nason yatambaye baba dangane da lamarin fanan amma se kawai yabari suka cigaba da hirarsu su ummi ma suna zaune da mama da hajiyarsu amira se anty firdausi da sauran yan uwa ana hira kowa se yaba halin ummi yakeyi dukda takasance balarabiya kuma manyan masu kudi amma ko ajikinta tasaki jiki dasu anata shan hira karban junior tayi ahannun anty firdausi tana mishi wasa. Hango fanan da zeenat,Amira, suhaima,auta su fawwaz sedaukan su pics sukeyi gajiya da hoton fanan tayi takoma gefe kan wani plastic chair tazauna tana rike kanta dake sarawa sallama taji wani mutum yamata juyawa tayi takalleshi ganin babban mutum ne yasa cikin mutuntawa tagaidashi duk acikin tawagar su alaramma sukazo Shima kamar wani babbane murmushi dauke afuskanshi yace ” baiwar Allah dafarko de sunana Sulaiman Ahmad gombe mazaunin gombe ne ni tun lokacin danaganki naji kin matukar burgeni inbadamu zan iya samun dama ” tunda yafara magana take kallonshi gaba daya kalaman bakinshi da yanda yazo yasameta setaji abin yamata bankwarakwai haka dan tunda tazo duniya babu namijin daya taba fuskantar ta yace yana sonta itama dama ba bukatar hakan takeyi ba nan take tadaure fuska da kamar bazatace mishi komai ba se can Kuma tace ” Allah sarki yayana kayi hakuri nidin matar aure ce! Barima intashi intafi kar mijina yaganmu tare yayi zargin wani abu” tafada tana barin wajan shikam yamakasa tafiya taya zaayi takasance matar aure haka yabawa zuciyarsa hakuri dan wallahi tunda yadora ido akanta yaji tamishi azuciyarshi kuwa se astangafurullah yakeyi yakula matar aure duk da bashida masaniya. Tattarawa sukayi suka fito domin anfara watsewa suhaima juyawa tayi zatama fanan magana karaff idonta yasauka acikin na fawwaz dake binta da kallon love yana sakin mata murmushi gabanta ne yafadi dasauri tabar wajan dariya tabashi ganin yanda take tafiya ko juyowa takiyi, jikin motar duk suka tsaya sunawa su fanan Allah yasanya alkhari lura da azaad baya wajan ne yasa ummi kiran daya daga cikin securities din tana tambayarsa Ina son bata amsa yayi da yana cikin motar knocking tamishi, zaune yake yana waya da yaseer yaji knock ganin ummi ne yasa yabude kofar, ” son kafito kugaisa da iyayen fanan zasu huce ” ummi tagama magana tana riko hannunshi fitowa yayi suka nufi indasuke tsaye, cikin mutuntawa yagaishesu amma fuskan nan ba yabo ba fallasa amsawa sukayi fuska asake. Fanan se satan kallonshi takeyi sallama sukayi suna musu godiya dukkansu suka shiga motocinsu suka tafi taro yayi kyau sede muce Allah yasanya alkhari.
____gaba dayansu agajiye suka koma gida zama sukayi afalo sunata kallon pics din da akayi agun ganin suhaima tayi shurune yasa ya usman yace ” suhai meyake damunki” itakuwa gaba daya wani iri takejinta barinma inta rufe idonta fuskan fawwaz take gani a lokacin da yake mata murmushi girgiza kai tayi tace ” klau na ya usman kawai gajiya ne ” bawai dan ya yarda ba kawai yagyada mata kai atare suka shiga daki ita da fanan suka kwanta aikuwa suna kwanciya kuwa bacci yayi awon gaba dasu. Da sallama abakin mama tashiga dakin baba azaune tasameshi hannunshi rike da babban list na shago yana dubawa dan dazun wani yaron shagon yakawo mishi zama tayi akusa dashi tayi tagumi , lokaci daya jikinshi yayi sanyi dan yasan abinda takewa tagumi. Sa hannu yayi yajanye tagumin datayi sannan yace” mamansu dan Allah kidena kina tayarmin da hankali aduk sanda naganki cikin yanayi nadamuwa! Yanda kika damu da fatima haka nima nadamu da ita dukda yanzu tafara taka matakin rabuwa damu amma kisani akwai dan sauran lokaci dazamu kasance da ita” yagama mgn damuwa karara akan fuskanshi, hawaye kawai mama takeyi ” ya bazan damu ba yata wacce nahaifa dakaina zata tafi tabarni nahar abada ace hankalina yakwanta aduk sanda nadaga ido naga fanan senayi kukan rabuwa da ita! Kaddararta tariga datazo ahaka itadin shugaba ce agun wasu jinsin amma zanso yata tadawo gareni duk daren dadewa ko inada rai ko banida rai ” dauriya kawai baba yakeyi amma ji hake kamar yayi kuka kozeji dadin abinda yake mishi ciwo arai jawota yayi jikinshi yana lallashinta.
____ ” wayyo baby please kiss me! Kaji ” cewar aneesa dake zaune abakin lallausan gadon azaad se turo mishi baki takeyi sede yayi kissing dinta, ko kallon inda take beyiba yajuya yabata baya hayewa saman gadon tayi kwanta asaman jikinshi tana shafa mishi fuska jinta ajikinsane yasa yatashi zaune yatsareta da ido cikin sexy voice yace” kici gaba danunamin salon naki iskancin kinji se inga ubanda zesa in aureki” yafada yana watsa mata mugun kallo Jin abinda yafada ne yasa dasauri tasauka akan gadon tana bashi hakuri ganin yaki kulatane yasa tafara kukan munafurci cikin tsawa yace” get out aneesa” fita tayi adakin da gudu dan karta hassalashi yace yafasa auren . Kwantawa yayi dan yasamu yayi bacci aneesa tahanashi toilet yafada yayi wanka yafito yashafa lotion yafeshe jikinshi da different perfumes masu dadi yawuce dressing room yashirya cikin kana nan kaya wando jeans se riga Tshirt baka medogin hannu yayi stuking rigar bakaramin bayyana kirar jikinsa yayi ba daura agogo yayi ahannunshi yasa sun glass yayi kyau sosai danshi kowani irin kaya yasa yana fitting dinshi barinma kaya me duhun Color kasancewarshji fari shisa komai yake mai kyau, yadawo bedroom yadau wayarsa yafito falonshi , samun Faisal yayi azaune akan daya daga cikin lutsa_lutsan kujerun falon ” good afternoon sir ” cewar faisal gyada mishi kai kawai azaad yayi. Wucesa yayi, yayi gaba bin bayansa Faisal yayi a main falo yasamesu suna zaune zasuyi lunch zama yayi shima, Abba ne yace ” faisal kazauna mana ” cike da kunyan Abba faisal yazauna shima serving dinsu rice and stew wanda yaji nama kamar zasuyi magana se coslow,shuru sukayi sunacin abinci ba abinda akeji se qaran spoons, tura abincin gaba yayi alamun yakoshi ya yagi tissue yagoge bakinshi. Gaba daya sun kammala cin abincin mikewa Faisal yayi yana hamdala, ciki_ciki azaad yayi magana wanda inbawai kasa kunne kayiba bazakaji meyace ba ” nizan wuce inada meeting” girgiza kai Abba yayi yana tunanin ko yaushe azaad ze fara magana sosai kamar kowa oho adduah sukamai yayi gaba Faisal nabinsa, binshi da kallo sukayi harsuka bar falon ummi ce tayi ajiyar zuciya tace ” ohhhh son! I wonder when will he change his ways gaba daya mutum ace kullum fuska adaure kamar wanda akawa wani abu ” dariya zeenat tayi tace ” to ai ummi yafi burgewa ahaka bakisan yanda yan mata suke crushing akanshi bane ” dakuwa ummi tamata tace ” ungo naki zee nace ungo nan” dariya su Abba sukasa kafin yace ” nikam sunsamu kyakyawar fahimta kuwa shida aneesa ?” Jin ya ambaci sunan aneesa ne suka bata fuska ummi tace ” hmmmm maybe yanzu suna samu tunda tana gidan nan dazunma tazo dukda bana sonta amma inason inga auren son itakuma Allah yashiryeta ” tagama magana tana barin falon gaba daya tahaura upstairs zeenat ma bin bayanta tayi, areef abin dariya yabashi hararansa fawwaz yayi yace” what’s funny!?” Yatsa yadaura akan libs dinshi ,Abba yar dariya yayi yace” tom nima nagudu kumana gadin falon ” Shima yawuce part dinshi.
Karfe 3 dede Mr azaad suka fito daga meeting bude mishi motar faisal yayi shima yashiga driver yajasu suka nufi AZAAD THE BILLIONAIRE COMPANY tun kafin su iso marry dagudu tashiga office din sakatariya jamila dake aiki a laptop tace mata ” madam ogah is here ooo ” cike da zumudi sakatariya jamila ta mike tabude hand bag dinta tadauki powder tashafa tasa Janbaki wani turare acikin yar karamar kwalba wanda bokanta yabata ta dangwala tashafa ajikinta tafito se girgiza manya_manyan nonuwanta dasuka kwanta takeyi shigowa cikin company yayi ma’aikata nata gaisheshi hannu kawai yadaga musu karasowa tayi gabanshi cikin kissa tace ” barka da zuwa ogah” mugun kallo yawatsa mata kafin yace ” daga yau inkika karasa wannan stupid perfume din am going to fire you idiot kawai” yawuce cikin office dinshi . Wani irin kololon bakin ciki ne yatokare wuyan sakatariya bayanda ta iya haka ta koma office dinta takwashi files takaimai .
____ ” ah ah malam muhammad karmuyi haka dakai mu ai iya hakama Fatima tafitar damu domin kowa yanzu maganar makarantanmu yake ga kyaututukanta nan wannan halak malak dinta ne” cewar ya mu’alim dinsu fanan kusan su uku sukazo har gidansu domin mikawa fanan kyautanta . Kyaututukan dukansu suna baje akan center table din falon, keys din gida da keys din mota , da takardunsu ga kudaden dasuke daure band_band kusan 4million , dasauransu baba ne yace ” malam lawan dan Allah kudauka kuma kuje ayi gyare_gyaren a makaranta dakuma sadaqa nagama magana ” baba yafada yana ware musu 2ml ” “gashi nan karku musa min kuce bazaku karba ba itama Fatima ai yace agunku kuna da iko da komai nata” cewar baba ya mu’alim ne yaraba 2ml din into two yadau 1ml yace ” tunda kamatsa wannan ma ya Isa Allah yasa albarka muna godiya” bahaka baba yaso ba amma bayason musu shisa yamishi shuru dan shi anashi raayin sudauki 3ml din ko 2ml amma sunki mikewa sukayi zasu tafi baba yamike yarakasu tare damusu godiya yadawo falon, har time din su fanan basu tashi abacci ba fitowar mama yayi dede dashigowan su ya Usman falon ganin kyaututukan fanan ne yasa suka samu waje suka zauna suna dubawa, baba ne yace akira mishi fanan din yaji ta bakinta tunda hakkinta ne mama ce tamike taje tasamesu se shan bacci sukeyi hankalinsu akwance bubbuga pillow tayi dama dukkansu ba gwanayen dogon bacci bane mikewa sukayi da sallati abakinsu ” to kutashi baccin ya isa haka aikun huta babanku nason ganinku afalo” tayi maganar tana fita adakin toilet suhaima tashiga ta wanko fuskanta hakama fanan suka fito. Samunsu sukayi dukansu azaune zama Suma sukayi suna musu barka da rana, fara magana baba yayi yace ” fanan ga kyaututukanki nan dazun malamanku suka tafi yanzu yakike gani zaayi dasu?” Karewa kayayyakin kallo tayi kafin tace ” baba nikam duk yanda kayi dasu dedene nabakasu kyauta ” takarasa magana tana hamma dan haryanzu baccin takeji be isheta ba, dariya taso bawa baba wai nabakasu kyauta ” to Allah yamiki albarka yanzu de gidajen zaasa yan haya aciki motar kuma dama Usman ne bashida motar seya dauka kekuma ga gold dinda matar mainasara tabaki dakuma shagon saloon din da patient dinki yabada mamanku kuma tadauki 1ml itada suhaima da auta, shikuma al ameenu yadauki dubu dari biyar yakara akan business dinshi se sauran yan uwa dazaa rabawa ” godiya sukayi sosai suka shiga kitchen daura abincin dare.

 

Back to top button