Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 57

Sponsored Links

{57}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Yanayin yanda ya ganni kaɗai ya isa ya gamsar dashi ina cikin damuwa baya ga dishewa da muryata tayi banda kankancewar da idanuwana suka yi alamun nasha kuka da yawa,

“baby…. What’s happening?” yace dani cikin kulawa yana kokarin zama kusa dani,

“babu komai”

“ban yarda ba, idan babu komai why do you looks like this?”

Wasu sabbin hawayen na fara yi duk da bana son yi a gabansa,

“am sorry baby, sorry…… Stop crying…..” shi da kansa ya fahimci damuwata da kuma dalilin kasancewata a haka tunda dama abune da yasani yana damuna tun tuni,

“Baby kar muyi fushi da kaddarar da Allah ya saukar mana, muyi hakuri muci wannan jarrabawar Kinji, ki kara hakuri Allah will not leave us empty handed….”

“Haba ƴar kyakkyawa, uhmmm…. Kyakkyawa son kowa ƴar baiwa……. Ko a kwalliya ba irin taki, fagen ado babu tamkarki……” murmushi nayi na kalleshi jin yadda ya takarkare yana rero min waka baiti bayan baiti wanda ban taba sanin ya iya ba ashe duk wakokin da suke trending a tiktok before muyi bacci da nake gani yana ji, haka yaci gaba da yimin kalamai masu dadi har naji sanyi a raina zuciyata ta daidaita kuma ta dan huce, cewa yayi in shirya mu fita sai muje muci abinci tunda banci komai ba shima kuma haka,

Wanka muka yi atare muka shirya na saka doguwar gown nayi rolling shikuma ya sha kananan kaya muka fita,

Wani sananne kuma hadadden wurin cin abinci ya kai mu wanda ni banma taba sanin wurin ba sai yau, nan aka kawo mana menu kowa yayi order din abinda yake so shi amala yayi order da miyar ganye nikuma mandi rice with grilled chicken and violent salad Sai snacks,irin yanda yaga inata santin wurin ina yabashi yasa shi cemin,

“Baby to ko zaki fara business din abinci ne? Naga kina son harkar cooking dinnan dagaske….”

“yes oo, amma anya kana ganin zan iya kuwa?”

“why not baby, idan kina so i will give you 100% support but kafin wannan lokacin I have a plan for you gaskiya”

“wanne plan ne?”

“ina son kiyi joining online university kiyi masters dinki after that sai ki fara business cause you can’t do both of them lokaci daya, you have to do it separately, good idea yes…? ”

“uhmmm hakanma yayi and am deeply grateful”

“Don’t mention it my sugar baby, am ready to do everything just to make you happy…. I mean everything my love” ya fada yana rike da hannuna,

“Thanks for loving me with all your heart…. I love you”

Cike da farin ciki muka gama cin abincin sannan muka fita bayan ya biya, wani wurin muka sake biyawa shi kuma ice cream ake siyarwa zalla nan muka sha muka nufi gida kuma a takaice dai bamu muka koma gida ba sai wurin 10.

Tun daga ranar ya soma processing admission dina online har aka dace ya samu wata online university wadda you can study in Nigeria but graduated in Canada dole idan ka gama to can zaka je ka karbo certificate, Allah kadai ya san yawan kudin da ya kashe wurin yimin registration inda zan karanci computer science dama kuma akai nayi degree, tsohuwar laptop dina yakai ya sake zuba kudi ya karbo min sabuwa mai tsada wadda da ita ne zanyi karatun, tunda na fara kuma sai damuwata ta tafi domin yanzu lokacina kadanne lokacin karatu yafi yawa ko chat na daina yi sosai sai infi 1 week ma ban leka ba ganin haka yasa Bishra ta kirani tana tambayata wai “yaya widat yanzu kin daina chat ne?”

“wallahi ban daina ba Bishra kawai dai karatu ne ya dau zafi wannan masters da wahala yake ni da na san haka yake ma ai da bazan yi ba” dariya tayi tace gara dai in daure inyi din kamar yau zan gama Allah ya taimaka nan muka yi sallama naci gaba da yiwa chat a sha ruwan tsintsaye sai dai shi uban gayyar ina bashi time dinsa yadda ya kamata duk da wani lokacin har over time yake yi. Sai yanzu na yarda zaman banza ke sa mutum har yake samun lokutan yin wasu abubuwan marassa amfani amma daga lokacin da kake da abin yi tofa shikenan sai kayi dagaske sannan zaka yi abu mai ma’ana ma, ni yanzu wani shiga neighbors da wani fita duk bana yi kuma dama can dinma ni bamai yawan shige shige bace amma yanzu abin har yafi na baya dan rai da rai ina gida dan business dina da nake yi jifa jifa kuwa ina nan ina dan yi babu laifi amma shi dinma samz ke kara min kwarin gwiwar yi, ai ban farga ba sai ji nayi bikin gidanmu ya zo gashi zan fara exams ai nan duk nabi na burkice babu wani abu da akayi dani sai kudi da na tura asissiya min anko na sannan amarya ma asiya mata wasu abubuwan akan wanda aka siya mata, shi kansa yanzu da zan fara exams dinnan hakuri yake yi dani dan bani da cikakkiyar nutsuwa so nake yadda ya kashe kudi sosai inyi masa abinda zai ji dadi shiyasa dan dole shima ya daga min ƙafa duk da wani lokacin karatun ma tare muke yi saboda wani turancin yafi karfina sai dai shi ɗin,

Ranar da na gama kuwa kamar zai yi me dan murna saboda yanzu ne yasan zai samu kulawa 100%, girki nayi masa ranar na nutsuwa nasha kwalliya tun kafin ya dawo nayi masa hotuna na tura masa ta WhatsApp ai take ya rude ya rikice wai so nake in hanashi zaman office? Gwalo nayi masa kafin nace nidai ina jiransa,

“ok baby am coming….. I love you”

“I love you too” nace dashi ina kissing dinsa, tun daga nan fa ya kasa nutsuwa 6 dinma bata yi ba sai gashi ya dawo saboda abunne dama ya hadar masa biyu ga ina exams gashi kuma ina period to yanzu kuma duk na gama daga period din har exams din shiyasa yaketa wannan zumudin,

Tun da na bude masa kofa na taroshi ya kankame ni yasa ajikinsa yake kissing wuyana dama dinkin jikina na fitina ne an wulakanta atamfar babu laifi wurin dinki, riga da skirt ne style din zuge mu shana saboda gaban rigar a bude yake rabin kirjina duk awaje sai zip da aka saka, haka kuma nayima jikina barin turare banda almiski da na game dukkan cinyoyina har zuwa matse matsi, ni kaina na san yau ba sauki ne dama kuma haka nake so saboda naji wani Dr yace idan akayi mu’amala ana gama period ana samun rabo idan Allah ya nufa to nikuma yanzu bukata ta kenan shiyasa ma bana yi masa taurin kai bare in tsaya jan aji, kafin na fara exams ma har tambaya nake da kaina saboda tsabar yadda na kwallafa cikin nan araina.

Kwana biyu ya diba yana cin amarcinsa kuma yana shan sha’aninsa duk da yana fita office.

***

“Ni ina ganin wannan karon ki gwada bazai hanaki ba tunda ai an kwana biyu rabonki da kiga yaronki, sannan ina ganin ku tafi tare da Felicia ta yuyu a wannan tafiyar kiga an dace asirin ya sake shi hankalinsa ya dawo gareshi har sun daidaita” madam comfort ta fada tana kallon mommy fuskarta ƙunshe da alamun damuwa,

“Babu matsala ni na san yadda zanyi masa har ya amince koda baiyi niyyar amincewa dinba…. Karki damu kawai kice Felicia ta shirya nan da 2 days zamu tafi”

Ai cike da murna madam comfort ta koma gida tana zuwa ta kira Felicia ta soma fesa mata abinda ake ciki,

“Felicia karki yarda kiyi wasa da damar ki, duk tsanani duk rintsi duk tashin hankali ki tabbatar burin mu ya cika this time around….. I repeat ki tabbatar kinyi abinda ya dace”

“mommy karki damu zanyi duk yadda zanyi har sai nazo miki da magana mai dadi i promise you….”

“Thank you my daughter, Allah ya baki nasara, amma wannan karon ina son kiyi amfani da kirsa da kisisina sannan kiyi amfani da kyawun da kike dashi wurin jawo hankalinsa”

“mommy karki damu, wallahi tallahi na rantse miki da girman Allah a wannan karon sai dai a mutu amma sai na cika miki burin ki sai komai yazo karshe, ba samz ba ko uwarsa ce wannan karon na shirya ta mutu matsawar burin mu zai cika…”

“haka nake son ji kuma yanzu ne nasan dagaske kin gadoni ta kowanne fanni”

Cikin kwanaki biyu suka gama kulle kullensu, itama mommy kuma ta samu amincewar daddy bayan ta shirya masa kaidi irin na mata, dan tun bayan da suka rabu da madam comfort ta koma gida ta kwanta hajaran majaran kamar gaske a haka daddy ya dawo ya sameta ganin kamar zata mutu saboda yanda take jin jiki nan ta yunkura ta tashi dakyar tana yamutsa fuska Hadiza na riketa,

“dan Allah kayi hakuri kuma ka taimaka min inje gidan samz ya kaini asibiti inda za a kula dani…..”

“Haba maman Mary ya zaki je ki dora musu nauyi shida iyalinsa….”

Sai da mommy ta hadiye wani yawu mai daci da gafi saboda jin abinda daddyn yace kafin ta sake marairaicewa tace,

“babu wata dawainiya da zasu yi dani saboda da Hadiza zamu tafi dan ta kula dani kawai nidai amincewarka nake bukata…”

“to indai hakane shikenan na amince Allah ya baki lafiya amma dai ki fara sanar dashi kafin kije musu ko”

“ehh zan fada masa”

Lokacin da mommy ta fada masa zasu zo Abuja nikuma lokacin saura kwana biyu in tafi Kano bikin Bishra wanda saura sati daya kuma ina son inje a danyi shirye shirye dani kafin bikin, sam koda wasa bai fada min su mommy zasu zo ba sai ya ja bakinsa yayi shuru ya barni naci gaba kawai da shirye shiryen tafiyata shikuma sai shagwaba yake wai zan tafi in barshi, washe gari ya rakani muka tafi tamkar ba zamu rabuba saboda yadda muka yi ta mannewa juna, ina tafiya yana dawowa daga rakani su mommy suna ƙarasowa da ita da Hadiza da kuma Felicia wadda suka shiryo makarkashiya ita da mahaifiyarta,

Fuskar shi babu yabo babu fallasa ya karbesu dan harga Allah baya farin ciki da wannan zuwan da suka yi danma bana nan amma duk da haka ya san tunda suka zo tofa matsala itama ta sauka a gidan, Hadiza ke zungurar mommy tana cewa “mommy kiga gidan da suka dawo? Kiga kyawun gidan, kiga yadda ya saka furnitures masu tsada”

“rabu dashi zanyi maganin su daga shi har matar tashi”

Daidai lokacin ya karaso ya taresu tare da haurawa dasu sama inda apartment dinmu yake,

“mommy you are highly welcome”, Felicia kuwa tunda ya kalleta sau ɗaya bai sake kallon ko wurin da take ba saboda wani irin haushin ta yake ji kuma yana ganin ta ya tuna da abinda taso yimin,

“Ina ita wannan mayyar munafuka?” mommy ta fada cikin fada da nuna kin jini lokacin da suka shiga cikin falo,duk da yasan ni take nufi amma sai bai amsa ba,

“Yanzu Samuel haka ka zabarwa kanka? Ka dauko yarinya dangin Mayu duk sun bi sun lashe maka kurwa sun tsafeka baka ji baka gani a kanta sai yadda yayi dakai? Yarinya juya ko haihuwa bata yi amma a haka kake zaune da ita…”

Sai lokacin ya iya tankawa jin mommy ta ambaci juya” mommy waye yace miki juya ce mata ta? ”

” to idan ba juya ba mecece? Ta haihu ne? Yau shekararku nawa da aure?”

” mommy ita ba juya bace, last time ta samu ciki kuma har cikin ya girma ma sai ya lalace… Ko daddy ya san maganar sannan kuma duk kun sani”

Taɓe baki mommyn tayi kafin ta rufe shi da fada, “saboda sun mayar da kai wawa marar tunani ba, babu wani ciki da take dashi lokacin ma kawai sun raina maka hankali ne”

Ya san duk yadda zai yi mata bayani ba zata yarda ba kuma ba zata fahimta ba shiyasa ya rabu da ita yabar maganar bayan tayi fadanta ta gama ya tashi duk snacks din da nayi masa kafin in tafi saboda ya dan rinka ragewa before ya fita yaci abinci ko ya dafa duka ya fito musu dashi sannan ya fita yana jin damuwa na saukar masa, ya rasa sai yaushe mommy zata gane gaskiya, ya rasa sai yaushe zata kaunaci duk wani abu wanda yake so kuma yake kauna, tunda yabar gidan bai koma ba sai lokacin da zai kwanta bacci domin baya son wannan tashin hankalin na mommy gashi yana ta kiran wayata amma baya samu saboda rashin network nikam dama tunda na isa gida banma sake bi ta kan wayata ba kai banma san inda na jefa ta ba amma dai na san komai dare sai munyi waya dashi kafin nayi bacci,

Lokacin da ya koma gidan duk sun kwanta sai iya Felicia kadai wacce ke zaune falo sanye da night gown marar kauri dan ta dan bayyanar da surarta kaɗan,bai kulata ba ya wuceta zai shiga bedroom cikin sauri ta dakatar dashi,

“samz….”

Tsayawa yayi ya juya batare da ya kalleta ba nan ta taso tazo inda yake tsaye ya juya mata baya…….

 

*_Ummi Shatu_*

Check Also
Close
Back to top button