Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 106

Sponsored Links

Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 106…. A ranar da yamma
Maryam ta bar gidan ya kai ta daya daga cikin gidajensa da ke
dan nesa da wanda Ikram take, da farko Ikram bata wani damu
ba da Khaleel ya gaya mata Maryam xata bar gidan, sae da
Maryam ta tashi tafiya bayan an gama kwashe mata kayanta ta
rungume Ikram tace ta yafe mata in ta taba mata laifi bata sani
ba, nn jikin Ikram yyi sanyi taji kuma bata son rabuwa da
Maryam don a iya saninta basu taba samun misunderstandin
ba tun bayan rashin kunyar da tayi mata farkon xuwanta gidan,
tayi kuka ssae Maryam tayi assure dinta xata dinga xuwa ko
don sbda Sudais, karfe biyar na yamma Khaleel da kansa ya
wuce da ita duk da Ikram ta so binsu yace ta bari xai kai su
gobe. Bayan isha Khaleel ya dawo gidan don girkin Ikram ne
dama, tana kwance kan gadonta ta hade kafarta ta daura
Sudais tana masa wasa yana ta dariya yana xuba mata yawu
a fuskarta, Khaleel na shigowa dakin ta mike xaune da sauri,
ya xauna kusa da su ya karbi sudais yana kallonsa, mikewa
tayi ya kamo hannunta da sauri yace “ina xaki kuma” bata ce
komai ba ya mayar da ita ya xaunar gefensa yana kallon
fuskarta, kwan kwasa kofar aka yi hade da sallama Ikram ta
mike da sauri ta amsa sallamar Mama jummai tace “yyi bacci
ne ki bani shi in shimfide sa Ikram” Ikram ta karasa ta bude
kofar tace “A’a bae yi ba wasa yake yi Mama Jummai” jummai
tace “to idan yyi baccin ki kawo min shi kwanciya xanyi” Ikram
tace “to” snn Jummai ta juya ta wuce Ikram ta rufe kofar, har
karfe goma saura Sudais na hannun Khaleel idonsa biyu yana
wasan sa, Ikram ta mike daga kwancen da take ta shiga
wanka don tun daxu taki ajiye sudais bare tayi wankan, ko da
ta fito Sudais yyi bacci Khaleel na rungume da shi, samun
kanta tayi ranar da kasa yin komai gaban Khaleel don da da
ne tayi shafe shafenta gabansa ba komai bne har ma tasa
kaya gabansa, amma yau sae ta sami kanta da kasa yin hkn,
ta nemi kujera kawae ta xauna don dama hijab na jikinta ta
mayar da hankalinta gun News din da yake kallo a TV, mikewa
yyi ya bude dakin ya fita yana rike da sudais, ta bisa da kallo
har ya rufo kofar, sae a snn ta mike ta nufi gaban Madubinta ta
xauna kan stool din gaban Madubin ta cire hijab din jikinta ta
shiga gyara jikinta da turarruka da mayyuka masu kamshi kmr
ynda ta saba, har ta gama shirin baccinta bayan kmr minti
ashirin Khaleel bae shigo dakin ba, ta tsaya gaban Madubi rike
da net din da xata sa ma gashinta tana kare ma kanta kallo,
silk material fari tas iya gwiwa ne jikinta gaba daya surar
jikinta a bayyane suke, sae ta samu kanta da jin kunyar kayan
duk da ba ranar ce rana ta farko da ta fara sa shi ba, ta nufi
drawern kayanta da sauri ta bude ta ciro xani tana kkrin
daurawa kan rigar aka bude kofar dakin, hkn bae hanata daura
xaninta ba, ya karaso cikin dakin yana kallonta ta dauke kanta
ta dauki Hijab dinta ta shiga linkewa, kan gado ya nufa yyi
kwanciyarsa, ba tare da ta kallesa ba bayan ta ajiye Hijab din
hannunta tace “Sudais fa” jin bae ce komai ba yasa ta juya
tana kallonsa, yace “na kai sa gun Mama Jummai, ko tare
xaku kwana” tace “ehh mana, ko in je in samesu a can kar ya
tashi cikin dare ya dinga kuka” ya dan yi murmushi yace “ehh
je ki samesu” kmr jira take har da murmushinta tace “to” ta
dauki Hijab dinta da ta linke ta ajiye xata sa ta fita ya fixgota
ta fado kansa ya kashe wutan dakin yana mata rada a kunne
yace “in kika tafi gun Sudais shi kuma babansa yyi ya, wa xae
kwana da baban Sudais baki san yana bukatar ki kusa da shi
ba” kwace kanta ta shiga yi a tsorace kmr xata yi kuka tace
“ya Khaleel don Allah ka bari in tafi, kar Sudais ya dinga
nemana” Khaleel ya girgixa mata kai ya shige jikinta a hankali
yace “Sudais baxae yi kuka ba yasan kina gun babansa” bae
jira me xata ce ba ya tura bakinsa cikin nata ya shiga mata
wani mahaukacin kiss.

Back to top button