Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 105

Sponsored Links

Khaleesat Haiydar 105….. Khaleel na gama parkin Ikram ta bude motar ta fito Jummai ma ta fito rike da Sudais da jakar kayan abincinsa suka nufi balcony, cikin motar Khaleel ya dauki wayarsa ya kira Maryam, bugu biyu ta daga yace “Kin dawo Dear” yyi shiru yana sauraran bayanin ta snn yace “ohk sae kin dawo” jakar kayan sudais dake seat din gaba ya dauka ya fito ya kulle motar ya nufi balcony don bude masu gidan Kafin ya fito da kayan cikin booth, yana bude gidan suka shiga Ikram ta nufi sama jummai na biye da ita suka shiga dakinta, kwantar da sudais Jummai tayi tace “Maryam bata nn ne” Ikram tace “nima ban sani ba” kayan jikinta ta shiga cirewa ta daura xani tace “bari in yi wanka Mama Jummai” Jummai dake kkrin hada ma Sudais feeder kan ya fara nema tace “to je kiyi” ikram ta dan duka kusa da Sudais dake kwance kan gado yana cixan yatsunsa da gum dinsa ta daura goshinta kan nasa tana masa wasa, dariya ya shiga yi yana kallonta snn ta daura masa kiss a bakinsa ta shiga bathroom. ko da ta fito bbu su cikin dakin, tana tsaye gaban Madubi tana goge dogon gashinta da ta wanke da tawul karami Khaleel ya shigo dakin, kallo daya tayi masa ta madubi ta dauke kanta, ya karaso dab da bayanta a hankali yana kallon fuskarta ta Madubin, kasa ci gaba da abinda take tayi ta kuma kasa kallon Madubin, ya juyo da ita a hankali tana facin dinsa taga hawaye cike idonsa, sunkuyar da kanta tayi da sauri ita ma hawayen na neman taruwa idonta, ya rungumeta a hankali ya lumshe idonsa ta daura kanta kan kirjinsa tana kuka a hankali, ya dago kanta shi ma yana hawayen yace “baki sona har ynxu ko Ikram” girgixa masa kai tayi a hankali ta mayar da kanta kan kirjinsa, ya rungumeta tsam ya daura fuskarsa kan gashinta ya shiga magana a raunane “am srry Ikram ki yafe min abinda nayi maki jiya plss, kar ki kuma cewa baki sona Ikram ban san ya xanyi da raina ba, ban san wani irin so nake maki ba Ikram” muryarsa na rawa ya karashe mgnr, bata ce komai ba sae kukan da take ssae, ya dago kanta yana kallon cikin idonta ya saka bakinsa cikin nata, ta lumshe idonta da sauri, dae dae nn aka bude kofar suka rabu da sauri, Maryam ce ta shigo, ba shiri ta juya ta fita ta rufo masu kofar, Khaleel ya juya yana ta kallon Ikram da ta kasa hada ido da shi, yyi dan yi murmushi ya juya ya fita daga dakin, xubewa kan gado tayi tana kuka ssae, sae ynxu taji son Khaleel a ranta, ta kuma ji kishin Maryam 4 d 1st tym har cikin ranta, kasa xaman gadon tayi ta sulalo kasa a hankali tana ci gaba da kukanta, dakin Maryam Khaleel ya shiga, tana xaune ta kunna TV tana kallo amma da ganinta kasan kallon dae kawae take, ya karaso ya xauna gefenta yace “ya hanya” ba tare da ta kallesa ba tace “da gdya” ya dan yi shiru snn yace “hope komai ya wuce ynxu dear” ta dan yi murmushi tace “tuni ma, amma ina son ka min favour daya Khaleel” Khaleel na kallonta yace “ina jin ki” shiru tayi kmr me tunanin abinda xata ce, yace “kinyi shiru kuma Dear” ta sunkuyar da kanta tace “ina son ka raba mana gida da Ikram don Allah” da mmki yace “sbda me” a hankali tace “ban son watarana in fara kishi da ikram Khaleel, na dauki Ikram matsayin kanwata ta jini, tana bani girma ynda ya kamata nima ina bata, Ikram hnkli take karawa ynxu, ko ba yanxu ba ni nasan xaman lfyan mu baxae dore ba,” tayi shiru snn ta ci gaba a sanyaye “kuma ni ba auren soyayya muka yi da kai ba Khaleel ni kadae ke sonka hasalima sae da na aminta da deals dinka ka aureni Khaleel ban son watarana ka min gori sbda Ikram Khaleel, kuma…” kasa karawa tayi hawaye na bin kuncinta, Khaleel ya rungumota a hankali yace “naji xan raba maku gida Maryam, ki kwantar da hankalin ki duk irin son da nake ma Ikram baxae sa in walakanta ki ba kuma kema ina sonki equally, kin min abinda idan na ki ki ban maki halacci ba Maryam” kuka ssae take a jikinsa, har ta kusa sa shi hawayen shi ma, ya kasa cewa komai.
[2/25, 08:43] Zjy:

Back to top button